Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Za Ka Iya Zama Aminin Allah

Za Ka Iya Zama Aminin Allah

WASU SUNA GANIN CEWA . . .

Allah bai damu da mu ba ko kuma Allah ya yi nesa da mu, mai tsarki ne sosai kuma ba za a iya kusantar sa ba.

GA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.”​—Yaƙub 4:8.

“Ku danƙa masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.”​—1 Bitrus 5:7.

ME ZA MU YI DON MU KUSACI ALLAH?

  • Ka riƙa addu’a.​—Zabura 145:​18, 19.

  • Ka saurare shi.​—Zabura 32:8.

  • Ka riƙa bin shawararsa.​—Karin Magana 3:​5, 6.

  • Kada ka fid da rai a ƙoƙarin da kake yi don ka kusaci Allah.​—Matiyu 7:​7, 8.