Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hakika Rayuwa Tana da Amfani

Hakika Rayuwa Tana da Amfani

Faizal ya kamu da ciwon zuciya shekara ɗaya bayan rasuwar matarsa. Rashin lafiyar ya yi tsanani har ya bukaci a yi masa tiyata. Ya ce: “Sa’ad da na karanta littafin Ayuba, na gane cewa Jehobah yana da dalili mai kyau na rubuta labarin a cikin Littafi Mai Tsarki. Idan muna baƙin ciki kuma muka karanta labarin wani a cikin Littafi Mai Tsarki wanda shi ma ya yi fama da baƙin ciki kamar namu, hakan yana ƙarfafa mu.” Ya kuma ƙara da cewa: “Duk da haka, rayuwa tana da muhimmanci.”

Tarsha tana ƙarama sa’ad da mahaifiyarta ta rasu. Ta ce: “Sanin Mahaliccinmu yakan sa rayuwa ta kasance da amfani, ya sa ni farin ciki kuma ya sa na kasance da bege duk da cewa ina cikin damuwa. Za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ƙarfafa mu da kuma taimaka mana mu ci gaba da jimrewa kullum.”

TALIFOFIN da muka tattauna a baya sun nuna yadda baƙin ciki yake sa mutane su gaji da rayuwa. Yayin da kake fama da matsaloli, za ka iya ji kamar rayuwa ba ta da wani amfani ko kuma ka ga kamar ba wanda ya damu da kai. Amma ka tabbata cewa Allah ya damu da wahalar da kake sha domin kana da daraja a wurinsa.

Marubucin Zabura sura 86 ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah, shi ya sa ya ce: “Zan kira gare ka a lokacin wahalata, gama za ka amsa mini.” (Zabura 86:7) Amma za ka iya cewa, ‘Ta yaya Allah zai amsa mini “a lokacin wahalata”?’

Mai yiwuwa Allah ba zai magance maka matsalolinka nan take ba, amma Kalmarsa ta ce zai ba ka kwanciyar hankali don ka iya jimrewa. Kalmarsa ta ce: “Kada ku damu da kome, sai dai a cikin kome ku faɗa wa Allah bukatunku ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya, Ta haka kuwa Allah zai ba ku salama irin wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanku da tunaninku.” (Filibiyawa 4:​6, 7) Don Allah ka lura da yadda ayoyin nan suka tabbatar mana da cewa Allah yana kula da mu.

Allah Yana Kula da Kai

‘Allah bai manta da [tsunsaye] ba. . . . Kun fi ɗan tsuntsu daraja barkatai.’​Luka 12:​6, 7.

KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Wasu mutane ba sa ɗaukan tsuntsu da daraja, amma suna da daraja a gun Allah. Allah yana kula da kowannensu, dukansu suna da daraja a wurinsa. Allah yana ɗaukan mutane da daraja sosai fiye da tsuntsaye. A cikin abubuwan da Allah ya halitta a duniya, ’yan Adam ne suka fi daraja domin ya halicce su a cikin “siffarsa” kuma za su iya kasancewa da halayensa masu kayu.​—Farawa 1:​26, 27.

“Ya Yahweh, ka riga ka bincike ni ka kuwa san ni. . . . Kakan gane da tunanina . . . Bincike ni, za ka kuwa san zuciyata.”​Zabura 139:​1, 2, 23.

KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Allah ya san kowane ɗayanmu. Ya san tunanin zuciyarka da kuma damuwarka. Ko da wasu sun kāsa fahimtar matsalolinka, Allah ya damu da matsalolinka kuma yana son ya taimaka maka. Saboda haka, rayuwa tana da muhimmanci.

Rayuwarka Tana da Amfani

“Ji addu’ata, ya Yahweh, bari kukana ya zo gare ka. . . . Ka kasa kunne gare ni; sa’ad da na yi kira, amsa mini da sauri. . . . Za ka juya, ka ji addu’ar marasa ƙarfi.”​Zabura 102:​1, 2, 17.

KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Allah ya san duk baƙin cikin da ’yan Adam suke ciki tun daga lokacin da suka soma shan wahala. (Zabura 56:8) Har naka baƙin cikin ma ya sani. Allah yana sane da dukan matsalolinka domin kana da daraja a wurinsa.

“Kada fa ka ji tsoro, gama ina tare da kai, kada ka damu, gama ni ne Allahnka; Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka . . . Ni Yahweh Allahnka . . . nake ce maka, ‘Kada ka ji tsoro, ni ne mai taimakonka.’”​Ishaya 41:​10, 13.

KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Allah yana a shirye ya taimaka maka. Zai ɗaga ka idan ka faɗi.

Rayuwa Za Ta Yi Kyau a Nan Gaba

“Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.”​Yohanna 3:16.

KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Allah yana ƙaunar ka sosai shi ya sa ya aiko da Ɗansa Yesu ya mutu domin ya fanshe ka daga zunubi da mutuwa. Fansar ta ba ka damar yin rayuwa da farin ciki har abada. *

Ko da yake a wasu lokuta za ka yi baƙin ciki kuma ka ji kamar ka gaji da rayuwa, ka yi nazarin Kalmar Allah da kyau kuma ka ba da gaskiya ga alkawuran da Allah ya yi. Hakan zai sa ka yi farin ciki kuma za ka gaskata cewa rayuwarka tana da amfani.

^ sakin layi na 19 Don ƙarin bayani a kan yadda za ka iya amfana daga mutuwar Yesu, ka kalli bidiyon nan Ka Tuna da Mutuwar Yesu a www.pr418.com/ha. Ka duba ƙarƙashin LITTATTAFAI > BIDIYOYI > TARO DA HIDIMARMU.