Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 2

Mu Yabi Jehobah a Cikin Ikilisiya

Mu Yabi Jehobah a Cikin Ikilisiya

“Zan yabe ka a cikin taron jama’a.” ​—ZAB. 22:22.

WAƘA TA 59 Mu Yabi Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne ra’ayin Dauda game da Jehobah, kuma me hakan ya sa ya yi?

SARKI DAUDA ya ce: “Yahweh da girma yake, ya cancanci yabo mai yawa.” (Zab. 145:3) Dauda ya ƙaunaci Jehobah sosai, kuma hakan ya sa ya ‘yabe shi a cikin taron jama’a.’ (Zab. 22:22; 40:5) Babu shakka, kana ƙaunar Jehobah sosai kuma ka amince da abin da Dauda ya ce: “Ya Yahweh, Allah na kakanmu Isra’ila, albarka ta tabbata gare ka, har abada abadin!”​—1 Tar. 29:​10-13.

2. (a) Ta yaya za mu yabi Jehobah? (b) Wace matsala ce waɗansu ke fuskanta, kuma mene ne za mu tattauna?

2 A yau, hanya ɗaya da muke yabon Jehobah ita ce ta wajen yin kalami a taronmu. Amma ’yan’uwa da yawa suna fuskantar wata babbar matsala. Suna so su riƙa yin kalami a taro, amma tsoro yana hana su yin hakan. Ta yaya za su magance wannan matsalar? Waɗanne shawarwari ne za su taimaka mana mu riƙa yin kalami masu ban-ƙarfafa a taro? Kafin mu amsa tambayoyin nan, bari mu tattauna dalilai huɗu da suka sa muke yin kalami a taro.

ABIN DA YA SA MUKE YIN KALAMI A TARO

3-5. (a) Kamar yadda Ibraniyawa 13:15 ya nuna, me ya sa muke yin kalami a taro? (b) Muna bukata ne mu yi kalami daidai da wasu? Ka bayyana.

3 Jehobah ya ba dukanmu gatar yabon sa. (Zab. 119:108) Yin kalami a taro yana cikin “hadayar yabo” da muke miƙa wa Allah, mu ne za mu yi hakan da kanmu, babu wanda zai taya mu. (Karanta Ibraniyawa 13:15.) Jehobah ba ya bukatar hadayarmu ko kuma kalaminmu ya zama daidai da na wasu!

4 Jehobah ya san cewa dukanmu mun bambanta kuma yanayinmu ba ɗaya ba ne. Don haka, yana farin ciki idan muka ba shi hadaya daidai ƙarfinmu. Ka yi tunanin irin hadayu da Jehobah ya amince Isra’ilawa su riƙa bayarwa. Wasu Isra’ilawa suna da ƙarfin ba da ɗan rago ko kuma akuya. Talakawa kuma suna iya ba da “kurciyoyi biyu ko ’yan tattabaru biyu.” Ban da haka, idan Ba’isra’ile ba zai iya ba da tsuntsaye biyu ba, Jehobah ya amince mutumin ya “kawo kilo ɗaya na garin hatsi mai laushi.” (L. Fir. 5:​7, 11) A zamanin, garin hatsi bai da tsada, duk da haka, Jehobah yana farin ciki idan mutum ya ba da hadayar gari “mai laushi.”

5 Har yau, ra’ayin Allah bai canja ba. Idan muka yi kalami, Jehobah ba ya bukatar dukanmu mu “iya magana” kamar Afolos ko kuma mu motsa mutane kamar Bulus. (A. M. 18:24; 26:28) Abin da Jehobah yake bukata shi ne mu ba da kalami daidai gwargwadon ƙarfinmu. Shin ka tuna da gwauruwar da ta ba da hadaya ’yan tagulla biyu da ba su kai kobo ba. Jehobah ya daraja ta domin ta ba da hadaya gwargwadon ƙarfinta.​—Luk. 21:​1-4.

Yin kalami a taro yana amfanar mu da masu sauraro (Ka duba sakin layi na 6-7) *

6. (a) Kamar yadda Ibraniyawa 10:​24, 25 ya nuna, ta yaya muke amfana daga kalamin wasu? (b) Ta yaya za ka nuna godiya don kalamin da suka ƙarfafa ka?

6 Muna ƙarfafa juna da kalaminmu. (Karanta Ibraniyawa 10:​24, 25.) Dukanmu muna murna idan muka ji kalami dabam-dabam a taronmu. Ban da haka, muna farin ciki idan ƙaramin yaro ya yi kalami. A duk lokacin da wani ya yi kalami a kan abin da ya koya, hakan na ƙarfafa dukanmu sosai. Ƙari ga haka, muna sha’awar ganin yadda wasu ke nuna gaba gaɗi don yin kalami duk da cewa suna kunya ko kuma suna koyan yarenmu. (1 Tas. 2:2) Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don ƙoƙarin da suke yi? Muna iya gode musu don kalaminsu bayan an tashi taro. Wata hanya kuma da za mu nuna godiya ita ce ta wajen yin kalami. Idan muka yi hakan, mu ma za mu ƙarfafa wasu.​—Rom. 1:​11, 12.

7. Ta yaya za mu amfana idan muka yi kalami a taro?

7 Za mu amfana idan muka yi kalami a taro. (Isha. 48:17) Ta yaya? Da farko, idan muna so mu yi kalami a taro, hakan zai motsa mu yi shiri sosai. Idan muka yi shiri sosai, za mu fahimci Kalmar Allah. Fahimtar Kalmar Allah zai taimaka mana mu yi amfani da abubuwan da muka koya. Na biyu, za mu fi jin daɗin taron idan mu ma muka yi kalami. Na uku, za mu tuna abin da muka yi kalami a kai domin mun saka ƙwazo don yin hakan.

8-9. (a) Ta yaya Malakai 3:16 ya nuna yaya Jehobah yake ji idan muka yi kalami? (b) Wane ƙalubale ne wasu ke fuskanta?

8 Jehobah yana farin ciki idan muka yi kalami game da imaninmu. Muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana jin kalaminmu kuma yana farin ciki domin ƙoƙarin da muke yi don yin kalami a taro. (Karanta Malakai 3:16.) Yana nuna hakan ta wajen yi mana albarka idan muka yi iya ƙoƙarinmu mu faranta masa rai.​—Mal. 3:10.

9 Hakika, muna da dalilai da yawa na yin kalami a taro. Duk da haka, wasu suna jin tsoron ɗaga hannunsu don yin kalami. Idan kana jin hakan, kada ka yi sanyin gwiwa. Bari mu tattauna wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da wasu misalai da kuma wasu shawarwari da za su taimaka mana mu riƙa yin kalami a kowane lokaci.

YADDA ZA MU DAINA JIN TSORO

10. (a) Tsoron mene ne wasu cikinmu suke ji? (b) Idan kana tsoron yin kalami, wane hali mai kyau ne hakan ya nuna cewa kana da shi?

10 Gabanka na faɗiwa a duk lokacin da ka ɗaga hannu don ka yi kalami? Idan haka ne, ba kai kaɗai ne kake jin hakan ba. Gaskiyar ita ce, yawancinmu na jin tsoro a duk lokacin da muke so mu yi kalami. Kafin ka iya magance wannan matsalar kana bukatar ka san dalilin da ya sa kake jin tsoro. Kana jin tsoro cewa za ka manta da abin da za ka faɗa ne ko kuma za ka faɗi abin da ba daidai ba? Kana tsoro cewa kalaminka ba zai yi daɗi kamar na wasu ba? Irin wannan tsoron yana da kyau. Me ya sa? Domin ya nuna cewa kana da tawali’u kuma kana ganin wasu sun fi ka. Jehobah yana son wannan hali. (Zab. 138:6; Filib. 2:3) Amma Jehobah yana son ka riƙa yabon sa kuma ka riƙa ƙarfafa ’yan’uwa a taro. (1 Tas. 5:11) Yana ƙaunar ka kuma zai sa ka kasance da gaba gaɗin yin kalami.

11. Wace shawara ce a Littafi Mai Tsarki za ta taimaka mana?

11 Ka yi la’akari da wasu abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya ce. Kalmar Allah ta bayyana cewa dukanmu mukan yi kuskure a abin da muka faɗa da kuma yadda muka faɗe shi. (Yaƙ. 3:2) Jehobah ba ya bukatar mu zama kamilai kuma ’yan’uwa ma ba sa bukatar hakan. (Zab. 103:​12-14) Dukanmu bayin Jehobah ne kuma ’yan’uwanmu suna ƙaunar mu. (Mar. 10:​29, 30; Yoh. 13:35) Sun san cewa a wasu lokuta ba ma faɗin abin da muke so mu faɗa.

12-13. Mene ne muka koya daga labarin Nehemiya da Yunana?

12 Ka yi tunani a kan wasu labarai a Littafi Mai Tsarki da za su taimaka maka ka daina jin tsoro. Ɗaya cikinsu shi ne Nehemiya wanda ya yi aiki a fadar sarki. Nehemiya yana baƙin ciki domin ya ji cewa ganuwar Urushalima da kuma ƙofarta sun lalace. (Neh. 1:​1-4) Ka yi tunanin yadda gabansa ya faɗi sa’ad da sarki ya tambaye shi abin da ke sa shi baƙin ciki! Nan da nan, Nehemiya ya yi addu’a kafin ya amsa sarkin. Don haka, sarkin ya taimaka wa mutanen Allah sosai. (Neh. 2:​1-8) Ka yi tunanin abin da ya faru da Yunana. Sa’ad da Jehobah ya gaya wa Yunana ya je ya yi wa mutanen Nineba wa’azi, Yunana ya ji tsoro kuma ya gudu ya tafi wani wuri dabam. (Yona 1:​1-3) Amma da taimakon Jehobah, Yunana ya yi aikin da aka ba shi, kuma wa’azin da ya yi ya taimaka wa mutanen Nineba. (Yona 3:​5-10) Labarin Nehemiya ya koya mana muhimmancin yin addu’a kafin mu ba da amsa. Labarin Yunana kuma ya koya mana cewa Jehobah zai taimaka mana mu bauta masa ko da muna jin tsoro. Ban da haka ma, yin kalami a taro ba shi da wuya kamar yi wa mutanen Nineba wa’azi.

13 Waɗanne shawarwari ne za su taimaka maka ka riƙa yin kalami masu ban-ƙarfafa? Bari mu tattauna wasu misalai.

14. Me ya sa muke bukatar mu yi shiri sosai don taro, kuma a wane lokaci ne za mu iya yin hakan?

14 Ka yi shiri don kowane taro. Idan ka yi shiri, hakan zai taimaka maka ka kasance da gaba gaɗin yin kalami a taro. (K. Mag. 21:5) Gaskiya ne cewa dukanmu muna da lokaci dabam-dabam da muka keɓe don shirya taro. Wata ’yar’uwa gwauruwa da ta ba shekara 80 baya tana soma shirya Hasumiyar Tsaro da za a nazarta da zarar makon ya soma. Ta ce: “Na fi jin daɗin taro sosai idan na yi shiri.” Wata ’yar’uwa mai suna Joy da take aiki na cikakken lokaci ta keɓe Asabar da Lahadi don ta riƙa yin nazarin Hasumiyar Tsaro. Ta ce: “Yana da sauƙi in tuna abin da na nazarta idan bai daɗe da na yi hakan ba.” Wani dattijo mai suna Ike da yake da ayyuka da yawa kuma yana yin hidimar majagaba ya ce: “Na fahimci cewa zai fi dacewa in riƙa yin nazari kaɗan-kaɗan a cikin mako maimakon in ɗau sa’o’i da yawa ina yin hakan.”

15. Ta yaya za ka yi shiri sosai don taro?

15 Mene ne yin shiri sosai don taro ya ƙunsa? Kafin ka soma nazari, ka yi addu’a ga Jehobah don ya ba ka ruhu mai tsarki. (Luk. 11:13; 1 Yoh. 5:14) Ƙari ga haka, ka yi amfani da ’yan mintoci don ka duba abin da kake son ka yi nazari a kai. Ka yi tunani a kan jigo da ƙananan jigon da hotunan da tambayoyin bita da kuma akwatuna. Yayin da kake nazarin kowane sakin layi, ka karanta nassosin. Ban da haka, ka yi bimbini a kan bayanin da aka ba da kuma ka mai da hankali musamman a kan darussan da kake son ka yi kalami a kai. Idan ka yi shiri da kyau, za ka amfana sosai daga taron kuma zai fi maka sauƙi ka yi kalami.​—2 Kor. 9:6.

16. Waɗanne kayan bincike ne muke da su, kuma yaya kake amfani da su?

16 Idan zai yiwu ka yi amfani da kayan bincike da ke na’ura a yaren da ka iya. Ta ƙungiyarsa, Jehobah ya yi tanadin kayan bincike a cikin na’ura don a taimaka mana mu riƙa yin shiri don taro. Manhajar JW Library® na sa mu iya saukar da littattafai a cikin na’urarmu ko wayoyinmu. Hakan zai taimaka mana mu yi nazari ko mu karanta ko kuma mu saurari abin da muke so a kowane lokaci da kuma a duk inda muke. Wasu suna amfani da wannan manhajar don yin nazari a lokacin da suke shan iska a wurin aiki ko a makaranta ko kuma sa’ad da suke tafiya. Ƙari ga haka, Watchtower Library da LABURARE NA INTANEsuna sa ya yi mana sauƙi mu yi bincike sosai a kan nazarin da muke yi.

Wane lokaci ne kake shirya taro? (Ka duba sakin layi na 14-16) *

17. (a) Me ya sa yake da kyau ka shirya kalami da yawa? (b) Me ka koya daga bidiyon nan Ka Zama Abokin Jehobah​—Ka Shirya Kalaminka?

17 Idan zai yiwu, ka yi shirin yin kalami a kowane sashen taro. Me ya sa? Domin ba za a kira ka a duk lokacin da ka ɗaga hannu ba. Wataƙila wasu za su ɗaga hannu a lokacin kuma mai gudanar da taron zai kira ɗaya cikinsu. Ban da haka, don a gama taron a kan lokaci, mai gudanar da taron zai rage yawan mutanen da ya kira su yi kalami a kowane sashe. Saboda haka, kada ka yi fushi ko kuma sanyin gwiwa idan bai kira ka ba sa’ad da ka fara ɗaga hannu. Amma, idan ka shirya kalami da yawa, za ka sami zarafin yin hakan. Kana iya yin shirin karanta wani nassi, kuma idan za ka iya, ka yi shirin yin kalami da naka kalmomi. *

18. Me ya sa ya dace mu riƙa yin gajeren kalami?

18 Ka yi gajeren kalami. Sau da yawa, gajeren kalami mai sauƙi ya fi ƙarfafa ’yan’uwa. Saboda haka, ka yi ƙoƙari ka riƙa yin gajeren kalami, kamar na sakan 30 kawai. (K. Mag. 10:19; 15:23) Yana da muhimmanci ka kafa misali mai kyau na yin gajeren kalami idan ka daɗe kana yin kalami a taro. Idan kana yin kalami na mintoci da yawa, wasu suna iya jin tsoron yin kalami don suna ganin cewa ba za su iya yin kalami yadda kake yi ba. Ƙari ga haka, gajeren kalami yana sa ’yan’uwa da yawa su sami damar yin kalami a taro. Saboda haka, idan kai aka fara kira, ka yi kalami mai sauƙi kuma ka ba da amsa kai tsaye ga tambayar. Kada ka yi kalami a kan duka darussan da ke sakin layin. Idan aka tattauna muhimman darussan da ke sakin layi, kana iya yin kalami a kan wasu batutuwa.​—Ka duba akwatin nan “ Me Zan Iya Yin Kalami a Kai?

19. Ta yaya mai gudanar da nazarin zai taimaka maka, amma me ya kamata ka yi?

19 Ka gaya wa mai gudanar da nazarin cewa za ka so ka yi kalami a kan wani sakin layi. Idan kana so ka yi hakan, ya kamata ka gaya masa kafin a soma taron. Idan lokacin yin kalamin ya kai, ka ɗaga hannunka sosai nan da nan don mai gudanar da nazarin ya gan ka.

20. Ta yaya taron ikilisiya yake kamar abinci da kake ci da abokanka?

20 Ka ɗauki taron ikilisiya kamar abincin da kake ci da abokanka. A ce abokanka a ikilisiya sun gayyace ka liyafa kuma suka ce ka dafa abinci. Yaya za ka ji? Wataƙila hankalinka zai ɗan tashi, amma za ka yi iya ƙoƙarinka don ka dafa abin da kowa zai ji daɗin ci. Jehobah wanda ya gayyace mu ya yi tanadin abubuwa masu kyau a taronmu. (Zab. 23:5; Mat. 24:45) Kuma yana farin ciki sa’ad da muka yi iya ƙoƙarinmu don mu kawo kyauta mai sauƙi. Saboda haka, ka yi shiri da kyau kuma ka yi kalami sosai gwargwadon iyawarka. Ta yin hakan, kana cin abin da Jehobah ya tanada kuma kana kawo kyautar da za ka ba ’yan’uwa a taro.

WAƘA TA 2 Jehobah Ne Sunanka

^ sakin layi na 5 Dukanmu muna ƙaunar Jehobah kuma muna jin daɗin yabon sa kamar yadda Dauda ya yi. Muna da damar nuna cewa muna ƙaunar Allah a duk lokacin da muka halarci taro. Amma yin kalami a taro yana yi wa wasu cikinmu wuya sosai. Idan kana fuskantar wannan matsalar, talifin nan zai taimaka maka ka san abin da ya sa kake jin tsoro da kuma yadda za ka daina yin hakan.

^ sakin layi na 17 Ka kalli bidiyon nan Ka Zama Abokin Jehobah​Ka Shirya Kalaminka a dandalin jw.org/ha. Ka duba ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > YARA.

^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTUNA: ’Yan’uwa a ikilisiya suna yin kalami a Nazarin Hasumiyar Tsaro.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTUNA: Wasu ’yan’uwa da aka nuna ɗazu a taro. Ko da yake yanayin kowannensu ya bambanta, sun keɓe lokacin yin nazarin talifin da za a nazarta a taro.