Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 13

Ku Nuna Kun Damu da Mutane a Wa’azi

Ku Nuna Kun Damu da Mutane a Wa’azi

“Ya kuma ji tausayinsu, . . . Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.”​—MAR. 6:34.

WAƘA TA 70 Ku Nemi Masu Zuciyar Kirki

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane halin Yesu ne yake ratsa maka zuciya? Ka bayyana.

ƊAYA daga cikin halayen Yesu masu kyau shi ne ya fahimci matsalolin da muke da su domin mu ajizai ne. Sa’ad da yake duniya, ya yi “farin ciki tare da masu farin ciki” kuma ya “yi kuka tare da masu kuka.” (Rom. 12:15) Alal misali, lokacin da mabiyansa guda 70 suka dawo daga wa’azi suna farin ciki domin sun yi nasara, Yesu ya yi “farin ciki.” (Luk. 10:​17-21) Amma, sa’ad da ya ga mutane na baƙin ciki a lokacin da Li’azaru ya mutu, “abin ya dami Yesu a zuciya sosai.”​—Yoh. 11:33.

2. Mene ne ya taimaka wa Yesu ya nuna ya damu da mutane?

2 Duk da cewa Yesu kamili ne, ya ji tausayin mutane kuma ya nuna ya damu da su. Abin da ya taimaka wa Yesu ya yi hakan shi ne ƙaunarsa ga mutane. Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, Yesu ya fi son “ ’yan Adam.” (K. Mag. 8:31) Domin yana ƙaunar mutane, ya yi ƙoƙari don ya fahimci yadda suke ji. Manzo Yohanna ya bayyana cewa: Yesu “ya san abin da yake a zuciyar ɗan Adam.” (Yoh. 2:25) Yesu ya nuna ya damu da mutane sosai. Saboda haka, mutane sun saurari wa’azinsa game da Mulkin Allah. Idan muka nuna cewa mun damu da mutane, hakan zai taimaka mana mu yi nasara a wa’azinmu.​—2 Tim. 4:5.

3-4. (a) Idan mun damu da mutane, yaya za mu ɗauki yin wa’azi? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Manzo Bulus ya san cewa yana da hakkin yi wa mutane wa’azi, kuma mu ma mun san cewa muna bukatar mu riƙa wa’azi. (1 Kor. 9:16) Amma idan mun damu da mutane, hakan zai taimaka mana mu fahimci cewa muna yin wa’azin ne domin muna so mu taimaka wa mutane, ba kawai don ya zama dole mu yi hakan ba. Mun san cewa “ya fi albarka a bayar da a karɓa.” (A. M. 20:35) Idan muna yin wa’azi domin muna so mu taimaka wa mutane, za mu yi hakan da farin ciki.

4 A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya nuna cewa mun damu da mutane a wa’azi. Za mu fara tattauna darasin da za mu iya koya daga yadda Yesu ya nuna ya damu da mutane. Bayan haka, za mu tattauna hanyoyi huɗu da za mu bi misalinsa.​—1 Bit. 2:21.

YESU YA JI TAUSAYIN MUTANE A WA’AZI

Tausayi ne ya motsa Yesu ya yaɗa saƙo mai ban ƙarfafa (Ka duba sakin layi na 5-6)

5-6. (a) Su waye ne Yesu ya ji tausayin su? (b) Me ya sa Yesu ya nuna tausayi ga mutanen da ya yi wa wa’azi, kamar yadda aka annabta a Ishaya 61:​1, 2?

5 Ku yi la’akari da yadda Yesu ya nuna ya damu da mutane. Akwai lokacin da Yesu da mabiyansa suka gaji domin sun yi wa’azi na tsawon lokaci ba tare da sun huta ba. Ban da haka, ba “su sami damar cin abinci ba.” Sai Yesu ya tafi da mabiyansa “wurin da ba kowa” domin su “ɗan huta.” Amma jama’a suka riga Yesu da mabiyansa zuwa wurin. Mene ne Yesu ya yi sa’ad da ya iso wurin kuma ya ga mutanen? “Ya ji tausayinsu * domin suna kamar tumakin da ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.”​—Mar. 6:​30-34.

6 Me ya sa Yesu ya ji tausayin waɗannan mutanen? Ya lura cewa suna “kamar tumakin da ba su da makiyayi.” Wataƙila Yesu ya lura cewa wasu cikinsu talakawa ne kuma suna aiki tuƙuru domin su biya bukatun iyalinsu. Wasu kuma suna makoki don an yi musu rasuwa. Idan haka ne, Yesu ya fahimci yanayinsu. Kamar yadda aka tattauna a talifin da ya gabata, wataƙila Yesu ma ya fuskanci irin waɗannan matsalolin. Yesu ya damu da mutane, kuma hakan ya motsa shi ya ta’azantar da su.​—Karanta Ishaya 61:​1, 2.

7. Ta yaya za mu yi koyi da Yesu?

7 Mene ne muka koya daga Yesu? Kamar Yesu, muna zama tare da mutanen da ke “kamar tumakin da ba su da makiyayi.” Suna fuskantar matsaloli sosai. Amma muna da abin da suke bukata, wato saƙon Mulkin Allah. (R. Yar. 14:6) Saboda haka, muna yin koyi da Yesu ta wajen yin wa’azi game da Mulkin Allah domin muna jin “tausayin marasa ƙarfi da masu bukata.” (Zab. 72:13) Muna jin tausayin mutane kuma muna so mu taimaka musu.

YADDA ZA MU RIƘA NUNA TAUSAYI

Ka yi la’akari da abin da kowane mutum ke bukata (Ka duba sakin layi na 8-9)

8. A wace hanya ce za mu nuna mun damu da mutane a wa’azi? Ka ba da misali.

8 Mene ne zai taimaka mana mu nuna mun damu da mutanen da muke yi ma wa’azi? Muna bukatar mu yi tunani a kan yadda mutanen da muke haɗuwa da su a wa’azi suke ji. Bayan haka, muna bukatar mu bi da su yadda za mu so a bi da mu idan muna yanayinsu. * (Mat. 7:12) Bari mu tattauna hanyoyi huɗu da za mu iya yin hakan. Da farko, ka yi tunani a kan abin da kowane mutum yake bukata. Sa’ad da muke wa’azi, muna nan ne kamar likitoci. Likitan da ya ƙware zai yi tunani a kan abin da marar lafiya ke bukata. Zai yi masa tambayoyi, sa’an nan ya saurari marar lafiyar da kyau yayin da yake gaya masa abin da ke damunsa. Bayan haka, maimakon ya gaya masa magungunan da zai riƙa sha, likitan zai yi wa marar lafiyar gwaje-gwaje don ya san ainihin abin da ke damunsa, sai ya faɗi irin jinyar da zai yi masa. Mu ma muna bukatar mu bi wannan misalin sa’ad da muke wa’azi. Muna bukatar mu fahimci yanayin mutanen da muka haɗu da su a wa’azi da kuma ra’ayinsu.

9. Mene ne za mu guji yi a wa’azi? Ka bayyana.

9 Sa’ad da ka haɗu da mutum a wa’azi, kada ka zata ka san yanayinsa ko kuma abubuwan da ya yi imani da su da kuma dalilin da ya sa ya yi imani da hakan. (K. Mag. 18:13) A maimakon haka, ka yi masa tambayoyi don ka san ra’ayinsa. (K. Mag. 20:5) Idan ba laifi ba ne a al’adarku, ka tambaye shi game da aikinsa da iyalinsa da tarihinsa da kuma ra’ayinsa. Idan ka san waɗannan abubuwan, ka yi ƙoƙarin taimaka masa kamar yadda Yesu ya yi.​—Ka Gwada da 1 Korintiyawa 9:​19-23.

Ka yi tunanin irin matsalar da mutumin da kake yi wa wa’azi yake fuskanta (Ka duba sakin layi na 10-11)

10-11. Kamar yadda 2 Korintiyawa 4:​7, 8 ya nuna, a wace hanya ce kuma za mu iya nuna cewa muna tausaya wa mutane? Ka ba da misali.

10 Na biyu, ka yi tunanin irin matsalolin da mutane ke fuskanta. Da yake dukanmu ajizai ne, muna iya fahimtar yanayinsu domin mu ma muna fuskantar matsaloli. (1 Kor. 10:13) Mun san cewa rayuwa a wannan zamanin tana da wuya sosai. Jehobah ne yake taimaka mana mu jimre. (Karanta 2 Korintiyawa 4:​7, 8.) Ka yi tunanin mutanen da ba su da dangantaka da Jehobah. Babu shakka, zai yi musu wuya su yi rayuwa a duniyar nan ba tare da taimakonsa ba. Kamar Yesu, muna tausaya musu, saboda haka muna yi musu wa’azin “labari mai daɗi.”​—Isha. 52:7.

11 Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai suna Sergey. Kafin ya soma bauta wa Jehobah, Sergey shiru-shiru ne kuma yana jin kunya. Ban da haka, yana yi masa wuya ya yi magana da mutane. Sai ya amince a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ya ce: “Da na soma nazari, na koyi cewa Kiristoci suna da hakkin yi wa mutane wa’azi. A dā ina ganin cewa ba zan iya yin hakan ba.” Amma ya yi tunanin mutanen da ba su taɓa jin wa’azi ba, kuma ya fahimci cewa rayuwa ba za ta yi musu sauƙi ba domin ba su san Jehobah ba. Ya ƙara cewa: “Abubuwan da nake koya sun sa ni farin ciki da kwanciyar hankali sosai. Hakan ya sa na ga cewa wasu ma na bukatar su san gaskiya.” Sa’ad da Sergey ya soma jin tausayin mutane, hakan ya taimaka masa ya soma kasancewa da gaba gaɗi a wa’azi. Ya ce: “Na yi mamaki sosai cewa yin wa’azi ya taimaka mini in kasance da gaba gaɗi. Ƙari ga haka, gaya wa mutane game da abin da na yi imani da shi ya ƙarfafa bangaskiyata sosai.” *

Yana iya ɗaukan lokaci kafin mutumin da kake nazari da shi ya sami ci gaba (Ka duba sakin layi na 12-13)

12-13. Me ya sa muke bukatar mu yi haƙuri da waɗanda muke nazari da su? Ka ba da misali.

12 Na uku, ka riƙa haƙuri da waɗanda kake nazari da su. Ka tuna cewa ba su taɓa yin tunani a kan gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki da ka sani ba. Mutane da yawa suna daraja imaninsu sosai. Suna iya ganin cewa addininsu yana da muhimmanci domin yana taimaka musu su kusaci iyalinsu ko kuma mutanen yankinsu. Ƙari ga haka yana taimaka musu su ci gaba da bin al’adarsu. Ta yaya za mu taimaka musu?

13 Ka yi la’akari da wannan misalin: Idan gada ya tsufa kuma ana bukatar a gina wani, mene ne ake yi? A yawanci lokaci za a ci gaba da amfani da tsohon yayin da ake gina sabo. Da zarar an kammala sabon sai a rushe tsohon gadan. Hakazalika, idan muna so mutane su daina bin abin da suka yi imani da shi, muna bukatar mu taimaka musu su san koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai. Bayan haka, muna iya sa su canja ra’ayinsu na dā. Yana iya ɗaukan lokaci kafin mu taimaka wa mutane su canja ra’ayinsu.​—Rom. 12:2.

14-15. Ta yaya za mu taimaka wa mutanen da ba su san cewa za a yi rayuwa har abada a aljanna a duniya ba? Ka ba da misali.

14 Idan muna haƙuri da mutane a wa’azi, ba za mu yi zaton cewa za su fahimci ko kuma su amince da gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki nan da nan ba. A maimakon haka, jin tausayin su zai sa mu taimaka musu su yi tunani sosai a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Alal misali, ka yi la’akari da yadda za mu iya taimaka wa mutum ya fahimci begen yin rayuwa a aljanna a duniya. Mutane da yawa ba su san cewa ’yan Adam za su rayu a duniya har abada ba. Wataƙila sun gaskata cewa idan mutum ya mutu ba zai sake rayuwa ba. Ko kuma suna tunani cewa dukan mutanen kirki za su je sama. Ta yaya za mu taimaka musu?

15 Ka yi la’akari da yadda wani ɗan’uwa yake taimaka wa mutane su fahimci begen yin rayuwa har abada a duniya. Da farko, yana karanta musu Farawa 1:28. Bayan haka, sai ya tambaye mutumin, a ina ne Allah yake so mutane su yi rayuwa kuma a wane irin yanayi. Mutane da yawa suna amsawa, “A duniya a cikin yanayi mai kyau.” Sai ɗan’uwan ya karanta Ishaya 55:11 kuma ya tambaye su ko nufin Allah ya canja. A yawanci lokaci wanda ake yi ma wa’azi zai ce a’a. A ƙarshe, ɗan’uwan yana karanta Zabura 37:​10, 11 kuma ya yi tambaya cewa mene ne zai faru da ’yan Adam a nan gaba. Domin ɗan’uwan yana yin amfani da Littafi Mai Tsarki, ya taimaka wa mutane da yawa su fahimci cewa har yanzu Allah yana son mu yi rayuwa har abada a aljanna a duniya.

Nuna alheri, kamar tura wa wani wasiƙa mai ban-ƙarfafa yana iya kawo sakamako mai kyau (Ka duba sakin layi na 16-17)

16-17. Kamar yadda Karin Magana 3:27 ya nuna, a waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna wa mutane cewa mun damu da su? Ka ba da misali.

16 Na huɗu, ka nemi hanyoyin da za ka nuna ka damu da mutane. Alal misali, idan ka ziyarci wanda kake nazari da shi a lokacin da bai dace ba, kana iya ba shi haƙuri kuma ka koma a lokacin da ya dace. Mene ne za ka yi idan wanda kake nazari da shi yana bukatar ka ɗan taimaka masa da wani aiki? Idan wani da ba ya iya fita waje don rashin lafiya yana so ka taimaka masa da wasu aikace-aikace fa? A irin wannan yanayin, muna iya taimaka wa mutumin.​—Karanta Karin Magana 3:27.

17 Sa’ad da wata ’yar’uwa ta nuna alheri, ta sami sakamako mai kyau. Da yake ta damu da mutane, ’yar’uwar ta rubuta wasiƙa kuma ta tura wa wani iyalin da ɗansu ya rasu. A wasiƙar, ta yi amfani da wasu Nassosi masu ban-ƙarfafa. Mene ne mutanen da aka tura wa wasiƙar suka yi? Mahaifiyar ta ce: “Jiya ina baƙin ciki sosai, amma wasiƙarki ta taimaka mini. Na gode miki sosai don wannan wasiƙa mai ban-ƙarfafa da kika turo mana. Jiya na karanta wasiƙar fiye da sau 20. Na yi mamaki sosai cewa kin damu da mu, har kin tura mana wannan wasiƙar da ta ƙarfafa mu. Muna miki matuƙar godiya.” Babu shakka, za mu sami sakamako mai kyau idan muka yi ƙoƙarin fahimtar irin matsalar da mutane ke fuskanta, kuma muka taimaka musu.

KA SAN ABIN DA JEHOBAH YAKE BUKATA A GARE KA

18. Kamar yadda 1 Korintiyawa 3:​6, 7 ya nuna, wane ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi a wa’azi, kuma me ya sa?

18 Zai dace mu kasance da ra’ayin da ya dace sa’ad da muke wa’azi. Jehobah ne yake amfani da mu don ya taimaka wa mutane su san shi. Don haka, ba aikin da muke yi ne ya fi muhimmanci ba. (Karanta 1 Korintiyawa 3:​6, 7.) Jehobah ne yake jawo mutane su bauta masa. (Yoh. 6:44) A ƙarshe, kowane mutum ne zai tsai da shawarar ko zai bauta Jehobah ko a’a. (Mat. 13:​4-8) Ka tuna cewa yawanci mutane ba su amince da wa’azin Yesu ba, duk da cewa shi ne Malami da ya fi kowa a duniya ƙwarewa! Don haka, kada mu yi sanyin gwiwa idan mutane da yawa a cikin waɗanda muke so mu taimaka musu sun ƙi saurarar wa’azinmu.

19. Wane sakamako ne za mu samu idan mun nuna mun damu da mutane a wa’azi?

19 Za mu sami sakamako mai kyau idan mun damu da mutane a wa’azinmu. Ban da haka, za mu ji daɗin wa’azi, kuma za mu yi farin ciki sosai don muna bayarwa. Ƙari ga haka, muna taimaka wa mutane masu zuciyar kirki su sami rai na har abada a nan gaba. (A. M. 13:48) Don haka, “duk sa’ad da muke da zarafi, sai mu kyautata wa dukan mutane.” (Gal. 6:10) Hakan zai sa mu farin ciki domin muna ɗaukaka Ubanmu wanda ke sama.​—Mat. 5:16.

WAƘA TA 64 Mu Riƙa Yin Wa’azi da Farin Ciki

^ sakin layi na 5 Idan muna jin tausayin mutane, hakan zai sa mu riƙa farin ciki, ban da haka, za mu sami sakamako mai kyau a wa’azinmu. Me ya sa? A wannan talifin, za mu tattauna darussa da za mu iya koya daga misalin Yesu da kuma hanyoyi huɗu da za mu nuna muna jin tausayin waɗanda muka haɗu da su sa’ad da muke wa’azi.

^ sakin layi na 5 MA’ANAR WASU KALMOMI: Kalmar nan tausayi da aka yi amfani da ita a Littafi Mai Tsarki tana nufin nuna mun damu da mutumin da ke shan wahala ko kuma da aka nuna wa rashin adalci. Idan mun damu da mutane, hakan zai taimaka mana mu yi ƙoƙarin tallafa musu.

^ sakin layi na 8 Ka duba talifin nan “Ka Bi da Mutane a Hidimarka Yadda Za Ka So Su Bi da Kai” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 2014.

^ sakin layi na 11 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 2011, shafuffuka na 21-22 a Turanci.