Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jehobah Yana Daraja “Amin” da Muka Furta

Jehobah Yana Daraja “Amin” da Muka Furta

JEHOBAH yana daraja ibadarmu sosai. Yana “kasa kunne ya lura” da dukan bayinsa kuma yana daraja dukan ƙoƙarin da muke yi don mu yabe shi. (Mal. 3:16) Alal misali, ka yi la’akari da wata kalma da wataƙila ka taɓa furtawa sau da yawa. Kalmar ita ce “Amin.” Jehobah yana ɗaukan wannan kalmar da muhimmanci kuwa? Ƙwarai kuwa! Don mu san dalilin, bari mu bincika ma’anar kalmar da kuma yadda aka yi amfani da ita a Littafi Mai Tsarki.

“SAI DUKAN JAMA’A SU AMSA, SU CE, ‘AMIN!’”

Kalmar nan “amin” tana nufin “ya kasance haka” ko kuma “hakika.” An ɗauko ta ne daga kalmar Ibrananci da take nufi “ka yi imani” da kuma “ya tabbata.” A wasu lokuta, ana amfani da kalmar sa’ad da ake shari’a. Bayan mutum ya yi rantsuwa sai ya ce “amin” don ya tabbatar cewa abin da ya faɗa gaskiya ne, kuma ya amince da dukan sakamakon da abin da ya faɗa zai jawo. (L. Ƙid. 5:22) Idan ya ce “amin” a gaban jama’a, hakan zai sa ya zama masa dole ya cika alkawarin da ya ɗauka.​—Neh. 5:13.

Littafin Maimaitawar Shari’a sura 27 ta bayyana yadda aka yi amfani da kalmar nan “amin” a zamanin dā. Bayan Isra’ilawa sun shiga Ƙasar Alkawari, an umurce su su taru a tsakanin Tudun Ebal da Tudun Gerizim domin su saurari Dokar da Jehobah ya ba su. Sun taru ne ba don su saurari Dokar kaɗai ba, amma don su nuna sun amince da Dokar da Allah ya ba su. Sa’ad da aka karanta musu sakamakon taka Dokar, sun nuna amincewarsu ta wajen cewa “Amin!” (M. Sha. 27:​15-26) Ka yi tunanin yadda dubban maza da mata da kuma yara suka ɗaga murya suka ce amin! (Yosh. 8:​30-35) Babu shakka, ba za su taɓa mantawa da wannan ranar ba. Isra’ilawa sun ci gaba da cika alkawarinsu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Isra’ilawa kuwa suka bauta wa Yahweh cikin dukan kwanakin da Yoshuwa yake da rai, haka kuwa suka ci gaba da bauta wa Yahweh bayan mutuwarsa dukan kwanakin dattawan da suka ragu, waɗanda suka san dukan ayyukan da Yahweh ya yi domin Isra’ilawa.”​—Yosh. 24:31.

Yesu ma ya yi amfani da kalmar nan “amin” don ya nuna cewa abin da yake faɗa gaskiya ne, amma ya yi hakan a hanya ta musamman. Maimakon ya yi amfani da “amin” don ya amsa abin da aka faɗa, ya yi amfani da ita (da aka fassara “hakika” a Hausa) don ya gabatar da gaskiyar furucinsa. A wasu lokuta, yana maimaita kalmar nan ya ce “hakika, hakika.” (Mat. 5:18; Yoh. 1:​51, Littafi Mai Tsarki.) Ta hakan, ya tabbatar wa masu sauraronsa cewa abin da yake faɗa gaskiya ne. Yesu ya yi magana a wannan hanyar ne domin shi Allah ya ba ikon cika dukan alkawuran da Allah ya yi.​—2 Kor. 1:20; R. Yar. 3:14.

“SAI DUKAN MUTANE SUKA AMSA, ‘AMIN!’ SUKA YABI YAHWEH”

Isra’ilawa sun yin amfani da wannan kalmar “amin” sa’ad da suke yabon Jehobah da kuma yin addu’a a gare shi. (Neh. 8:6; Zab. 41:13) Ta wajen cewa “amin” bayan addu’a, waɗanda suke saurara suna nuna cewa sun amince da abin da aka ce a addu’ar. Ƙari ga haka, dukan waɗanda ke wurin suna farin cikin bauta wa Jehobah a wannan hanyar. Abin da ya faru ke nan sa’ad da Sarki Dauda ya dawo da Akwatin Alkawari zuwa Urushalima. Bayan bikin da suka yi, ya yi addu’a mai kama da waƙa da ke rubuce a littafin 1 Tarihi 16:​8-36. Addu’ar ta ƙarfafa mutanen, “sai dukan mutane suka amsa, “Amin! Amin!” Suka yabi Yahweh.” Hakika, sun yi farin cikin bauta wa Jehobah tare.

Kiristoci a ƙarni na farko ma sun yi amfani da kalmar nan “amin” sa’ad da suke yabon Jehobah. Marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar a wasiƙunsu. (Rom. 1:25; 16:27; 1 Bit. 4:11) Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya nuna cewa halittun ruhu suna ɗaukaka Jehobah ta wajen cewa: “Amin! Yabi Allah!” (R. Yar 19:​1, 4) Kiristoci a ƙarni na farko suna ce “amin” sa’ad da aka yi addu’a a taronsu. (1 Kor. 14:16) Amma, ba sa yin amfani da kalmar haka kawai.

DALILIN DA YA SA YA KAMATA MU CE “AMIN”

Da yake mun koyi yadda bayin Allah a zamanin dā suka yi amfani da kalmar nan “amin,” mun fahimci dalilin da ya sa ya dace mu yi amfani da ita don kammala addu’a. Idan muka yi amfani da kalmar nan don kammala addu’armu, muna nuna cewa mun amince da abin da muka ce a addu’ar. Ƙari ga haka, idan muka ce “amin” da babban murya ko kuma a zuciyarmu sa’ad da ake addu’a a wurin da jama’a suke, muna nuna cewa mun amince da abin da aka ce a addu’ar. Ka yi la’akari da wani dalilin da ya sa furta “amin” yake da muhimmanci.

Muna mai da hankali sosai a ibadarmu. Muna bauta wa Jehobah ba kawai ta amincewa da abin da aka faɗa a addu’a ba, amma har ta abin da muke yi sa’ad da ake yin addu’ar. Domin muna so mu amince da abin da aka ce a addu’a, hakan yana sa mu mai da hankali don mu ji abin da ake faɗa a addu’ar.

Yana sa mu kasance da haɗin kai a ibadarmu. Sa’ad da ake addu’a a taro, muna jin abin da sauran ’yan’uwa a ikilisiya suke ji. (A. M. 1:14; 12:5) Idan dukan ’yan’uwa suka ce “amin,” hakan zai sa mu kasance da haɗin kai. Ko da mun ce “amin” da babbar murya ko kuma a cikin zuciyarmu, hakan yana iya motsa Jehobah ya amsa addu’armu.

“Amin” da muke furtawa yana sa a daɗa yabon Jehobah

Muna yabon Jehobah. Jehobah yana lura da duk ƙoƙarin da muke yi a hidimarsa. (Luk. 21:​2, 3) Yana ganin abin da muke yi da kuma abin da ke zuciyarmu. Idan muna saurarar taro ta waya, muna bukatar mu tabbata cewa Jehobah yana saurarar “amin” da muke faɗa. Idan muka ce “amin,” hakan yana daɗa sa mu yabi Jehobah tare da ’yan’uwanmu.

Muna iya ganin kamar faɗin “amin” ba wani abu mai muhimmanci ba ne, amma yana da muhimmanci sosai. Wani littafin bincike ya ce: “Ta wajen yin amfani da wannan kalmar,” bayin Allah suna nuna cewa suna da “ƙarfin hali, sun amince da abin da aka ce kuma suna da bege.” Bari dukan “amin” da muke furtawa ya sa a daɗa yabon Jehobah.​—Zab. 19:14.