Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Ta yaya ake yin tafiye-tafiye da jirgin ruwa a zamanin dā?

A ZAMANIN Bulus, babu ainihin jirgin ruwa da ke ɗaukan fasinjoji. Idan mutane suna so su yi tafiya, suna bincike ko akwai matuƙin jirgin ruwa da ke ɗaukan kayan ’yan kasuwa da zai je wurin da suke so su je. Ban da haka, suna tambaya ko matuƙin zai so ya ɗauki fasinjoji. (A. M. 21:​2, 3) Ko da mutum ya shiga jirgin ruwa da ba zai je wurin da yake so ba, yakan shiga wani jirgi da zai kai shi kusa da wurin da yake so ya je.​—A. M. 27:​1-6.

Ba a kowane lokaci ba ne ake tafiya da jirgin ruwa, kuma matuƙan jirgin ruwa ba sa bin wani tsari. Sanyi da kuma ruwan sama mai tsanani yana iya hana su yin tafiya. Ban da haka, matuƙan jirgin ruwa sukan ƙi yin tafiya idan suka yi tunani cewa wani mugun abu zai faru. Wataƙila sun ga hankaka tana kuka a kan jirgin, ko kuma sun ga jirgin da ya halaka a baƙin teku. Matuƙan jirgin ruwa sukan soma tafiya sa’ad da suka ga cewa yanayin yana da kyau. Saboda haka, wanda ke so ya yi tafiya yakan je gaɓar teku da jakarsa kuma ya jira sa’ad da za a yi sanarwa cewa jirgin ya kusan tashi.

Wani ɗan tarihi mai suna Lionel Casson ya ce: “A birnin Roma, yakan yi wa mutane sauƙi su sami jirgin yin tafiya ba tare da sun sha wahalar neman jirgi da kansu ba. Akwai ofisoshi da yawa a babban filin da ke garin Ostia kuma akwai tashar jirgin ruwa a baƙin Kogin Tiber. Kamfanoni dabam-dabam da ke wannan tashar ne suke da waɗannan ofisoshin. Ma’aikata da ke garin Narbonne [Faransa a yau] suna da ofishi. Ma’aikata da ke birnin Carthage [Tunisiya a yau] suna da ofishi, . . . da dai sauran su. Duk wanda yake neman jirgin da zai bi, zai je ofishin da ke kula da jigilar jiragen da ke zuwa garin da zai je.”

Mutane sun fi son tafiya da jirgin ruwa, amma yana tattare da matsaloli sosai. Manzo Bulus ya yi hatsari sau da yawa a jirgin ruwa sa’ad da yake tafiye-tafiyen yin wa’azi.​—2 Kor. 11:25.