Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za Mu Kāre Kanmu Daga Daya Cikin Dabarun Shaidan

Yadda Za Mu Kāre Kanmu Daga Daya Cikin Dabarun Shaidan

DA AKWAI wasu mutane da suka ziyarci Isra’ilawa sa’ad da suke shirin haye Kogin Urdun zuwa Ƙasar Alkawari. Su waye ne waɗannan mutanen? Mata ne da ba Isra’ilawa ba, kuma sun gayyaci mazan Isra’ilawa zuwa wani biki. Mazan suna iya ganin cewa wannan gayyatar babban gata ne. Samun sabbin abokai da yin rawa da kuma cin abinci mai ɗanɗano suna sa mutum farin ciki sosai. Waɗannan mata ba sa bin al’adu da kuma ƙa’idodin da ke cikin Dokar da Allah ya ba Isra’ilawa. Amma, wataƙila wasu maza Isra’ilawa suna ganin waɗannan matan ba za su iya rinjayar su ba.

Mene ne ya faru? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mazansu suka fara yin lalata da matan mutanen Mowab.” Waɗannan matan suna so maza Isra’ilawa su bauta wa allolin ƙarya kuma sun yi nasara! Hakan ya sa “fushin Yahweh ya kunna a kansu.”​—L. Ƙid. 25:​1-3.

Waɗannan Isra’ilawa sun taka Dokar Allah a hanyoyi biyu: Sun bauta wa gumaka kuma sun yi lalata. Dubbai sun mutu don wannan rashin biyayyar. (Fit. 20:​4, 5, 14; M. Sha. 13:​6-9) Me ya sa abin da suka yi ya zama da ban haushi sosai? Domin sun kusan shiga Ƙasar Alkawari. Da a ce mazan ba su taka Dokar Allah ba, da waɗannan dubban Isra’ilawa sun haye Urdun sun shiga Ƙasar Alkawari.​—L. Ƙid. 25:​5, 9.

Domin wannan abin da ya faru, manzo Bulus ya ce: “Waɗannan abubuwan da suka faru da su misali ne, an kuma rubuta ne don a yi mana gargaɗi, mu da ƙarshen zamani ya same mu.” (1 Kor. 10:​7-11) Babu shakka, Shaiɗan ya yi farin ciki sosai cewa waɗannan Isra’ilawa sun yi zunubi mai tsanani kuma hakan ya hana su shiga Ƙasar Alkawari. Muna bukatar mu koyi darasi daga kuskurensu domin mun san Shaiɗan zai yi farin ciki sosai idan ya hana mu shiga sabuwar duniya!

MUGUWAR DABARA

Shaiɗan yana rinjayar Kiristoci a yau ta wajen yin amfani da dabarun da ya saba yin amfani da su kuma ya yaudari mutane da yawa. Kamar yadda aka ambata ɗazu, ya yi amfani da lalata don ya ruɗi Isra’ilawa. A zamaninmu, lalata ta ci gaba da zama mugun tarko. Kuma tarko da Shaiɗan ya fi yin nasara da shi don ya rinjaye mu shi ne batsa.

A yau, mutum yana iya kallon hotunan batsa ba tare da kowa ya sani ba. Shekaru da suka shige, mutum da yake son ya kalli batsa zai je gidan fim ko kuma wuraren da ake sayar da littattafan da ke ɗauke da batsa. Wataƙila mutane da yawa ba sa zuwa waɗannan wuraren domin kada mutane su gan su. Amma yanzu, mutum zai iya shiga Intane ya kalli hotunan batsa a wurin aiki ko kuma a motar da aka faka. A ƙasashe da yawa, namiji ko ta mace tana iya kallon batsa ba tare da barin gida ba.

Ban da haka, na’urori sun sa kallon batsa ya kasance da sauƙi. Yayin da mutane suke tafiya a kan titi ko suna cikin bas ko jirgin ƙasa, suna iya kallon hotunan lalata a wayoyinsu.

Kallon batsa yana kawo lahani ga mutane da yawa fiye da yadda ya yi a dā. Me ya sa? Domin yana da sauƙi yanzu a kalli batsa ba tare da kowa ya sani ba. Mutane da yawa masu kallon batsa suna ɓata aurensu kuma ba su da daraja. Ƙari ga haka, suna ɓata lamirinsu. Mafi muni ma, suna ɓata abokantakarsu da Allah. Hakika, batsa tana shafan masu kallon ta sosai kuma mugun sakamakon yana daɗewa. A wasu lokatai, mutum ba ya iya magance mugun sakamakon kallon batsa.

Amma ya kamata mu sani cewa Jehobah yana iya kāre mu daga wannan tarko na Shaiɗan. Idan muna so Jehobah ya kāre mu, wajibi ne mu yi abin da maza Isra’ilawa suka kasa yi. Ya kamata mu yi wa Jehobah “biyayya.” (Fit. 19:5) Muna bukatar mu san cewa Allah ya tsani batsa sosai. Me ya sa muka ce hakan?

KA TSANE TA KAMAR JEHOBAH

Ka yi tunani a kan wannan: Dokokin da Allah ya ba al’ummar Isra’ila sun bambanta da dokokin da sauran al’ummai ke bi. Muna iya kwatanta dokokin da ganuwar da ke kāre su don kada mutanen da ke kewaye da su su rinjaye su da halayen banza. (M. Sha. 4:​6-8) Waɗannan dokokin sun nuna sarai cewa Jehobah ya tsani lalata.

Jehobah ya bayyana abubuwan da ba su dace ba da al’umman ke yi, kuma ya gaya wa Isra’ilawa cewa: ‘Ba za ku yi rayuwa irin ta mutanen Kan’ana inda zan kai ku ba. . . . Ƙasar ta ƙazantu, ina kuwa hukunta ta saboda laifofinta.’ Ga Jehobah, Kan’anawa sun ƙazantar da ƙasar domin abubuwan da suke yi.​—L. Fir. 18:​3, 25.

Ko da yake Jehobah ya hukunta Kan’anawa, wasu mutanen sun ci gaba da yin lalata. Fiye da shekaru 1,500 bayan haka, Bulus ya bayyana halayen mutanen da Kiristoci ke zaune a tsakaninsu, ya ce: “Ga kuwa rashin kunya gare su. Sun ba da kansu ga yin lalata, suna sha’awar yin kowace irin ƙazanta.” (Afis. 4:​17-19) A yau, mutane da yawa suna lalata kuma suna alfahari da abin da suke yi. Bayin Jehobah suna bukatar su yi iya ƙoƙarinsu don su guji kallon abubuwan da ba su dace ba da mutanen duniyar nan ke kallo.

Kallon batsa yana nuna cewa mutum ba ya daraja Allah. Jehobah ya halicce mu a kamaninsa da irin halayensa. Ya halicce mu a hanyar da za mu san abin da ya dace da wanda bai dace ba, idan ya zo ga batun jima’i. Ya yi tanadin jima’i domin ma’aurata su ji daɗinsa. (Far. 1:​26-28; K. Mag. 5:​18, 19) Amma wace manufa ce waɗanda suke ƙarfafa kallon batsa da kuma masu wallafa ta suke da ita? Suna ƙin ƙa’idodin da Allah ya kafa. Hakika mutanen da ke saka hannu a batsa suna raina Jehobah ko kuma sa a raina shi. Allah zai hukunta waɗanda suka ƙi bin ƙa’idodinsa ta wajen ƙarfafa kallon batsa da kuma wallafa ta.​—Rom. 1:​24-27.

Mutanen da suke kallo ko kuma karanta batsa da gangan fa? Wasu na iya ganin cewa wannan nishaɗin bai da haɗari. Amma suna goyon bayan waɗanda ke ƙin ƙa’idodin Jehobah. Wataƙila ba su da wannan manufa sa’ad da suka soma kallon batsa. Amma bayin Jehobah suna bukatar su tsani batsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku da kuke ƙaunar Yahweh, ku ƙi mugunta!”​—Zab. 97:10.

Yana iya yi ma waɗanda suke son su guji kallon batsa wuya su yi hakan. Mu ajizai ne, kuma muna bukatar mu saka ƙwazo don mu guji sha’awoyin da ba su dace ba. Ƙari ga haka, da yake mu ajizai ne, muna iya ruɗan kanmu cewa kallon batsa ba laifi ba ne. (Irm. 17:9) Amma mutane da yawa da suka zama Kiristoci sun yi nasarar guje wa kallon batsa. Sanin hakan zai ƙarfafa ka idan kana fama da wannan matsala. Ka yi la’akari da yadda Kalmar Allah za ta taimaka maka ka guji kallon batsa.

KADA KA CI GABA DA SHA’AWAR LALATA

Kamar yadda muka ambata ɗazu, Isra’ilawa da yawa sun bar sha’awoyin banza su jawo musu sakamako marar kyau. Hakan yana iya faruwa a yau ma. Yaƙub ɗan’uwan Yesu ya bayyana haɗarin, ya ce: “Kowane mutum dai . . . sa’ad da mugun kwaɗayinsa ya ruɗe shi, ya kuma sha kansa. Mugun kwaɗayi kuwa in ya yi ciki yakan haifi zunubi.” (Yaƙ. 1:​14, 15) Idan mutum ya bar sha’awoyin banza a zuciyarsa, zai iya yin zunubi. Don haka, muna bukatar mu kawar da tunanin banza kuma kada mu riƙa tunani a kansu.

Idan ka lura cewa kana son tunanin abubuwan da ba su dace ba, ka ɗauki mataki nan take. Yesu ya ce: “Idan kuwa hannunka ko ƙafarka yana sa ka ka yi zunubi, ka yanke shi ka yar. . . . Idan kuma idonka yana sa ka ka yi zunubi, sai ka cire shi ka yar.” (Mat. 18:​8, 9) Yesu ba ya nufin cewa mu yi waɗannan abubuwan a zahiri. Yana nufin mu kawar da duk wani abin da zai iya sa mu yin tuntuɓe. Ta yaya za mu bi wannan shawarar a batun batsa?

A duk lokacin da ka ga hotunan batsa, kada ka soma tunanin cewa, ‘Wannan ba matsala ba ce, zan iya magance ta.’ Kana bukatar ka kawar da idanunka nan take. Ka kashe talabijin nan da nan. Ka kashe kwamfutarka ko wayarka ba tare da ɓata lokaci ba. Ka yi tunanin wani abu mai kyau. Yin hakan zai hana ka yin tunanin banza.

ME ZA MU YI IDAN MUNA TUNA DA HOTUNAN BATSA DA MUKA TAƁA KALLO?

Me za ka yi idan ka daina kallon hotunan batsa, amma har yanzu kana tuna batsar da ka taɓa kallo? Mutum yana iya ɗaukan shekaru yana tuna hotunan batsa da ya kalla. Irin wannan tunanin yana iya zuwa ba zato ba tsammani. Idan hakan ya faru, kana iya soma tunanin yin abin da bai dace ba, kamar yin wasa da al’aurarka. Saboda haka, ka kasance a shirye domin ka watsar da waɗannan tunani idan ka soma yin su.

Ka ƙuduri niyyar sa tunaninka da kuma ayyukanka su faranta ran Allah. Ka zama kamar manzo Bulus da ya ‘horar da jikinsa, ya mai da shi bawansa.’ (1 Kor. 9:27) Kada ka bar tunanin banza ya mai da kai bawa. Amma ‘ka sabunta tunaninka da hankalinka. Ta haka, za ka iya tabbatar [wa kanka] abin da yake nufin Allah, wato abin da yake mai kyau, abin karɓa ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.’ (Rom. 12:2) Ka tuna cewa yin abubuwan da suka dace ne kaɗai za su sa ka farin ciki.

Yin abubuwan da suka dace ne kaɗai za su sa ka farin ciki, ba bin sha’awoyin jikinka ba

Ka yi ƙoƙari ka haddace wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki. Idan tunanin banza ya zo maka, kana iya bimbini a kan ayoyin nan da ka haddace. Nassosi kamar Zabura 119:37 da Ishaya 52:11 da Matiyu 5:28 da Afisawa 5:3 da Kolosiyawa 3:5 da kuma 1 Tasalonikawa 4:​4-8 za su taimaka maka ka kasance da ra’ayin Jehobah game da kallon hotunan batsa da kuma abin da yake so ka riƙa yi.

Me za ka yi idan kana ganin ba za ka iya daina kallon batsa ko kuma tunanin batsa ba? Ka bi misalin Yesu. (1 Bit. 2:21) Bayan Yesu ya yi baftisma, Shaiɗan ya jarabce shi. Mene ne Yesu ya yi? Ya yi tsayayya da Shaiɗan. Yesu ya ambata ayoyi da yawa sa’ad da yake yin tsayayya da Shaiɗan. Ya ce: “Tafi daga nan kai Shaiɗan!” Sai Shaiɗan ya tafi. Kamar yadda Yesu ya guji faɗawa tarkon Shaiɗan, kai ma ka guji hakan. (Mat. 4:​1-11) Shaiɗan da mutanensa za su ci gaba da ƙoƙarin sa ka riƙa yin tunanin abubuwan da ba su dace ba, amma kada ka bari su rinjaye ka. Da taimakon Jehobah, kana iya daina kallon hotunan batsa, kuma ka yi nasara a kan maƙiyinka.

KA YI ADDU’A GA JEHOBAH KUMA KA YI MASA BIYAYYA

Ka ci gaba da roƙon Jehobah ya taimaka maka. Bulus ya ce: “Ku faɗa wa Allah bukatunku ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. Ta haka kuwa Allah zai ba ku salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanku da tunaninku cikin Almasihu Yesu.” (Filib. 4:​6, 7) Allah zai ba ka salamar da za ta taimaka maka ka guji yin abin da bai dace ba. Idan ka kusaci Jehobah, ‘shi kuwa zai yi kusa da kai.’​—Yaƙ. 4:8.

Za mu sami kāriya daga tarkon Shaiɗan idan dangantakarmu da Mahaliccinmu tana da ƙarfi sosai. Yesu ya ce: “Mai mulkin duniyar nan yana zuwa, amma ba shi da iko a kaina.” (Yoh. 14:30) Me ya sa Yesu yake da irin wannan gaba gaɗin? Ya ce: “Wanda ya aiko ni kuwa yana tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, gama kullum ina yin abin da yake so.” (Yoh. 8:29) Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ba zai taɓa yasar da kai ba, idan ka yi ƙoƙarin faranta masa rai a dukan ayyukanka. Ka guji kallon hotunan batsa, kuma yin hakan zai sa ka guji tarkon Shaiɗan.