Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 28

Ku Ci Gaba da Bauta wa Jehobah Idan An Saka wa Aikinmu Takunkumi

Ku Ci Gaba da Bauta wa Jehobah Idan An Saka wa Aikinmu Takunkumi

“Ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.”​—A. M. 4:​19, 20.

WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Me ya sa bai kamata mu yi mamaki ba idan aka saka wa aikinmu taƙunƙumi? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

A SHEKARA ta 2018, masu shela fiye da 223,000 ne suke zama a ƙasashen da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi ko kuma aka hana mu yin wasu abubuwan ibada. Wannan ba abin mamaki ba ne. Kamar yadda muka koya a talifin da ya gabata, za a tsanantawa Kiristoci na gaskiya. (2 Tim. 3:12) Ko da a ina ne muke zama, hukumomi suna iya hana mu bauta wa Allahnmu Jehobah ba zato-ba-tsammani.

2 Idan gwamnati a ƙasarku ta saka wa aikinmu taƙunƙumi, kana iya tambayar kanka: ‘Idan ana tsananta mana hakan yana nufin Jehobah bai amince da mu ba ne? Taƙunƙumi zai hana mu bauta wa Jehobah ne? Zai dace in ƙaura zuwa wata ƙasa ne?’ A wannan talifin, za mu tattauna waɗannan tambayoyin. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda za mu ci gaba da bauta wa Jehobah sa’ad da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi da kuma abubuwan da muke bukatar mu guje wa.

IDAN ANA TSANANTA MANA, HAKAN YANA NUFIN JEHOBAH BAI AMINCE DA MU BA NE?

3. Kamar yadda 2 Korintiyawa 11:​23-27 suka nuna, wane tsanantawa ne Bulus ya fuskanta, kuma me muka koya daga misalinsa?

3 Idan gwamnati ta saka wa aikinmu taƙunƙumi, muna iya soma tunanin cewa Allah yana fushi da mu. Amma ku tuna cewa tsanantawa ba ya nufin cewa Jehobah yana fushi da mu. Alal misali, Jehobah ya amince da manzo Bulus sosai. Har ma ya sami gatar rubuta wasiƙu 14 a littafin Helenanci na Kirista, ban da haka ma, shi manzon Yesu ne ga waɗanda ba Yahudawa ba. Duk da haka, ya fuskanci tsanantawa sosai. (Karanta 2 Korintiyawa 11:​23-27.) Abin da manzo Bulus ya fuskanta ya koya mana cewa Jehobah yana barin bayinsa masu aminci su fuskanci tsanantawa.

4. Me ya sa mutanen duniya suka tsane mu?

4 Yesu ya bayyana mana dalilin da ya sa za a tsananta mana. Ya ce za a tsananta mana domin mu ba na duniya ba ne. (Yoh. 15:​18, 19) Idan ana tsananta mana, hakan ba ya nufin cewa Jehobah ba ya goyon bayan mu. Amma yana nuna cewa muna yin abin da ya dace!

TAƘUNƘUMI ZAI HANA MU BAUTA WA JEHOBAH NE?

5. Maƙiyanmu za su iya hana mu bauta wa Jehobah ne? Ka bayyana.

5 Maƙiyanmu ba za su iya hana mu bauta wa Jehobah ba. Da yawa daga cikinsu da suka yi ƙoƙarin yin hakan, ba su yi nasara ba. Ka yi la’akari da abin da ya faru a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu. A lokacin, gwamnatoci a ƙasashe da yawa sun tsananta wa Shaidun Jehobah. Ba a ƙasar Jamus kaɗai aka saka wa aikinmu taƙunƙumi ba, amma har da ƙasar Ostareliya da Kanada da kuma wasu ƙasashe. Mene ne ya faru? Sa’ad da aka soma yaƙin a shekara ta 1939, akwai masu shela 72,475 kawai a faɗin duniya. Amma rahotannin sun nuna cewa sa’ad da aka daina yaƙin a 1945, adadinsu ya ƙaru zuwa 156,299. Babu shakka, sun ƙaru fiye da ninki biyu!

6. Wane sakamako mai kyau ne tsanantawa zai iya kawowa? Ka ba da misali.

6 Maimakon tsanantawa ya ba mu tsoro, yana iya sa mu kasance da ƙarfin gwiwar ci gaba da bauta wa Jehobah. Alal misali, da akwai wasu ma’aurata da suke da yaro kuma suna zama a ƙasar da gwamnati ta saka wa aikinmu taƙunƙumi. Maimakon hakan ya ba ma’auratan nan tsoro, sun soma yin hidimar majagaba. Matar har ta yi murabus daga aikinta don ta yi wannan hidimar. Mijin kuma ya ce taƙunƙumin ya sa mutane son sanin abubuwa game da Shaidun Jehobah. A sakamakon haka, ya kasance wa ɗan’uwan da sauƙi ya soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Ban da haka ma, taƙunƙumin ya sake kawo wani sakamako mai kyau. Wani dattijo a ƙasar ya ce, mutane da yawa da suka daina bauta wa Jehobah sun soma halartan taro kuma suka soma yin wa’azi.

7. (a) Mene ne muka koya daga Littafin Firistoci 26:​36, 37? (b) Mene ne za ka yi idan aka saka wa aikinmu taƙunƙumi?

7 Idan maƙiyanmu suka saka wa aikinmu taƙunƙumi, suna so ne su tsorata mu don mu daina bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, suna iya yaɗa ƙaryace-ƙaryace, su tura hukumomi su bincika gidanmu, su kai mu kotu ko kuma su saka mu a kurkuku. Suna ganin za mu tsorata domin sun saka wasu daga cikinmu a kurkuku. Idan muka bari suka tsorata mu, hakan yana iya sa mu rage ƙwazo ko kuma mu daina bauta wa Jehobah. Ba ma so mu zama kamar waɗanda aka ambata a Littafin Firistoci 26:​36, 37. (Karanta.) Ba za mu bar tsoro ya sa mu rage abubuwan da muke yi don ibada ko kuma mu daina bauta wa Jehobah ba. Mun dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu kuma ba za mu tsorata ba. (Isha. 28:16) Muna roƙon Jehobah ya yi mana ja-goranci domin mun san cewa da taimakonsa, babu wata gwamnati da za ta iya hana mu bauta wa Allah.​—Ibran. 13:6.

ZAI DACE IN ƘAURA ZUWA WATA ƘASA NE?

8-9. (a) Wace shawara ce kowane Kirista yake bukatar ya yanke wa kansa da kuma iyalinsa? (b) Mene ne zai taimaka mana mu tsai da shawarar da ta dace?

8 Idan gwamnati a ƙasarku ta saka wa aikinmu taƙunƙumi, wataƙila kana iya tunanin ƙaura zuwa wata ƙasa don ka bauta wa Jehobah a cikin kwanciyar hankali. Kai ne za ka tsai da wannan shawarar. Amma kafin ka tsai da shawarar, zai dace ka yi nazarin abin da Kiristoci a ƙarnin na farko suka yi sa’ad da ake tsananta musu. Bayan an kashe Istafanus, mabiyan Yesu a Urushalima sun ƙaura zuwa Yahudiya da Samariya da Finikiya da Kubrus da kuma Antakiya. (Mat. 10:23; A. M. 8:1; 11:19) Kana iya yin nazarin abin da Bulus ya yi sa’ad da aka sake soma tsananta wa Kiristoci. Bulus ya ci gaba da zama a wurin ko da yake mutanen suna tsananta wa mabiyan Yesu kuma zama a wurin yana da haɗari sosai. Bulus ya yi hakan ne domin yana so ya ci gaba da yin wa’azi da kuma ƙarfafa sauran ’yan’uwa da suke wuraren da ake tsananta musu sosai.​—A. M. 14:​19-23.

9 Mene ne wannan labarin ya koya mana? Magidanta ne za su yanke shawarar ko zai dace su ƙaura. Amma kafin magidanci ya yanke shawarar, yana bukatar ya yi addu’a kuma ya yi la’akari da yadda ƙaura zai shafi iyalin. A wannan batu, kowanne Kirista ne zai “ɗauki kayan kansa.” (Gal. 6:5) Bai kamata mu shari’anta mutane domin shawarar da suka yanke ba.

BAUTA WA ALLAH SA’AD DA AKA SAKA WA AIKINMU TAƘUNƘUMI

10. Wane umurni ne ’yan’uwan da ke ofishinmu da kuma dattawa za su ba mu?

10 Ta yaya za mu ci gaba da bauta wa Jehobah sa’ad da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi? ’Yan’uwa a ofishinmu za su ba dattawa umurnin da kuma shawarwari game da yadda za su sami abubuwan da za su taimaka musu su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah da yadda za su riƙa taro da kuma yin wa’azi. Idan ’yan’uwan da ke ofishinmu ba su sami damar ba dattawa waɗannan umurnin ba, dattawa za su taimaka muku ku ci gaba da bauta wa Jehobah. Za su yi muku ja-goranci da ya jitu da Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu.​—Mat. 28:​19, 20; A. M. 5:29; Ibran. 10:​24, 25.

11. Me ya tabbatar maka da cewa za ka riƙa samun abubuwan da za su sa ka ci gaba da bauta wa Jehobah, kuma me kake bukatar yi don ka kāre su?

11 Jehobah ya yi alkawari cewa zai yi wa bayinsa tanadin abubuwan da za su taimaka musu su ƙarfafa dangantakarsu da shi. (Isha. 65:​13, 14; Luk. 12:​42-44) Saboda haka, ka kasance da tabbaci cewa ƙungiyar Jehobah za ta yi tanadin abubuwan da kake bukata don ka sami ƙarfafa. Mene ne kai ma kake bukatar ka yi? A lokacin da aka saka wa aikinmu takunkumi, ka nemi wuri mai kyau don ka ɓoye Littafi Mai Tsarki da kuma wasu littattafanmu. Kada ka ajiye waɗannan littattafai, har da waɗanda suke na’ura a wurin da zai yi sauƙin ganowa. Kowannenmu yana bukatar ya yi iya ƙoƙarinsa don ya ƙarfafa bangaskiyarsa.

Da taimakon Jehobah za mu ci gaba da yin taro babu tsoro (Ka duba sakin layi na 12) *

12. Ta yaya dattawa za su tsara taro a hanyar da ba zai jawo hankalin mutane ba?

12 Me zai faru da taro da muke yi? Dattawa za su tsara yadda za ku riƙa yin taron a hanyar da ba zai ja hankalin mutane ba. Suna iya ba da umurni cewa mu riƙa yin taro a rukuni-rukuni kuma za su tsara lokaci da wurin da za mu riƙa yin wannan taron a kai a kai. Kana iya kāre ’yan’uwanka ta wajen yin magana a hankali sa’ad da kuke shigowa da kuma ficewa daga wurin taron. Ban da haka, za ka bukaci saka tufafin da ba zai jawo hankalin mutane ba.

Ko da gwamnati ta saka wa aikinmu taƙunƙumi ba zai hana mu bauta wa Jehobah ba (Ka duba sakin layi na 13) *

13. Mene ne za mu iya koya daga labarin ’yan’uwanmu a Ƙasashen Tarayyar Soviet?

13 Ƙalubalen da za mu fuskanta a wa’azi zai bambanta sosai dangane da wurin da muke zama. Amma da yake muna ƙaunar Jehobah kuma muna jin daɗin gaya wa mutane game da Mulkinsa, za mu ci gaba da yin wa’azi. (Luk. 8:1; A. M. 4:29) Wata ’yar tarihi mai suna Emily B. Baran ta yi magana game da wa’azin da Shaidun Jehobah suka yi a Ƙasashen Tarayyar Soviet. Ta ce: “Sa’ad da gwamnati ta hana Shaidun Jehobah yin wa’azi, sun soma yi wa maƙwabtansu da abokan aikinsu da kuma abokansu wa’azi. A lokacin da aka saka su a kurkuku don suna wa’azi, Shaidun sun ci gaba da yin wa’azi a kurkukun.” Duk da cewa an saka wa aikinmu taƙunƙumi, ’yan’uwanmu a Ƙasashen Tarayyar Soviet ba su daina yin wa’azi ba. Idan aka saka wa aikinmu taƙunƙumi a ƙasar da kuke, ku ƙuduri niyyar ci gaba da yin wa’azi.

ABUBUWAN DA MUKE BUKATAR MU GUJE WA

Muna bukatar mu san lokacin da ya kamata mu yi shiru (Ka duba sakin layi na 14) *

14. Wane tarko ne Zabura 39:1 za ta taimaka mana mu guje wa?

14 Ka mai da hankali da abubuwan da kake gaya wa mutane. Sa’ad da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi, muna bukatar mu san “lokacin yin shiru.” (M. Wa. 3:7) Muna bukatar mu guji gaya wa mutane abubuwan da bai kamata su sani ba, kamar sunayen ’yan’uwanmu da wurin da muke yin taro da yadda muke yin wa’azi da kuma yadda muke samun littattafai. A ƙasar da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi, ba za mu gaya wa hukumomi ko abokanmu ko kuma danginmu abubuwan nan ba. Idan muka gaya musu, za mu iya saka ’yan’uwanmu a cikin haɗari.​—Karanta Zabura 39:1.

15. Mene ne Shaiɗan zai so ya yi mana, kuma ta yaya za mu guji faɗawa cikin tarkonsa?

15 Kada mu bar saɓani ya raba kanmu. Shaiɗan ya san cewa idan ba mu da haɗin kai ba za mu yi nasara ba. (Mar. 3:​24, 25) Don haka, zai yi ƙoƙarin sa mu kasa kasancewa da haɗin kai. Ta yin hakan, yana so mu riƙa faɗa da juna maimakon mu yi tsayayya da shi.

16. Wane misali mai kyau ne ’Yar’uwa Gertrud Poetzinger ta kafa mana?

16 Har Kiristoci da suka manyanta ma suna bukatar su guji wannan tarko. Ka yi la’akari da misalin wasu ’yan’uwa mata biyu masu suna Gertrud Poetzinger da Elfriede Löhr. An saka su da waɗansu ’yan’uwa mata a kurkuku. ’Yar’uwa Gertrud ta soma kishin Elfriede domin tana yin jawabi mai daɗi sosai. Daga baya, Gertrud ta ji kunya kuma ta roƙi Jehobah ya taimaka mata. Ta rubuta cewa: “Muna bukatar mu aminci cewa waɗansu suna da baiwa fiye da mu.” Ta yaya ta daina yin kishi? ’Yar’uwa Gertrud ta mai da hankali ga halaye masu kyau na Elfriede da kuma yadda take da fara’a. Ta yin hakan, ta ƙarfafa dangantakarta da Elfriede. An saki dukansu daga kurkuku kuma bayan haka, sun bauta wa Jehobah da aminci har suka gama rayuwarsu a duniya. Idan muka yi ƙoƙari don mu sasanta saɓanin da muka samu da ’yan’uwanmu, ba za mu bar kome ya sa mu kasa kasancewa da haɗin kai ba.​—Kol. 3:​13, 14.

17. Me ya sa muke bukata mu riƙa bin umurni?

17 Ka riƙa bin ja-goranci a kowane lokaci. Za mu guji faɗawa cikin matsala idan muka bi umurnin da ƙungiyar Jehobah da kuma dattawa suka ba mu. (1 Bit. 5:5) Alal misali, a wata ƙasa da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi, dattawa sun umurci ’yan’uwa cewa kada su ba da littattafai sa’ad da suke wa’azi. Amma wani ɗan’uwa da ke hidimar majagaba a wannan yanki bai bi wannan umurnin ba. Wane sakamako hakan ya jawo? Ba da daɗewa ba bayan shi da wasu ’yan’uwa suka kammala wa’azi, ’yan sanda suka tare su. ’Yan sandan sun bi su kuma suka ƙwace dukan littattafan da suka ba mutane. Mene ne wannan labarin ya koya mana? Muna bukatar mu riƙa bin umurni ko da ba mu amince da shi ba. Jehobah yana farin ciki idan ya ga muna bin umurnin mutanen da ya naɗa su yi mana ja-goranci.​—Ibran. 13:​7, 17.

18. Me ya sa muke bukatar mu guji kafa dokokin da ’yan’uwa ba sa bukata?

18 Kada ku kafa dokokin da mutane ba sa bukata. Idan dattawa suka kafa dokoki da mutane ba sa bukata, hakan zai sa abubuwa su yi wa ’yan’uwa wuya. Ɗan’uwa Juraj Kaminský ya faɗi abin da ya faru a lokacin da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi a ƙasar Czechoslovakia na dā. Ya ce: “Da hukuma ta kama dattawa da yawa, waɗanda suka rage da suke yin ja-gorancin a ikilisiya da kuma da’irori sun soma kafa nasu dokoki.” Jehobah bai ba mu ikon kafa wa ’yan’uwanmu dokoki ba. Dattijon da yake kafa wa ’yan’uwa dokokin da ba sa bukata ba ya kāre su, amma yana ƙoƙarin nuna iko a kan bangaskiyarsu ne.​—2 Kor. 1:24.

KADA KU DAINA BAUTA WA JEHOBAH

19. Duk da ƙoƙarin Shaiɗan, wane tabbaci ne 2 Tarihi 32:​7, 8 suka sa mu kasance da shi?

19 Maƙiyinmu Shaiɗan ba zai daina tsananta wa bayin Jehobah masu aminci ba. (1 Bit. 5:8; R. Yar. 2:10) Shaiɗan da mutanensa za su yi ƙoƙarin hana mu bauta wa Jehobah. Amma kada hakan ya sa mu tsorata. (M. Sha. 7:21) Jehobah yana tare da mu kuma zai ci gaba da taimaka mana ko da an saka wa aikinmu taƙunƙumi.​—Karanta 2 Tarihi 32:​7, 8.

20. Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?

20 Bari dukanmu mu kasance da irin ƙuduri da Kiristoci a ƙarni na farko suka yi sa’ad da suka gaya wa hukuma a zamanin cewa: “Ko daidai ne a wurin Allah mu fi jin maganarku fiye da maganar Allah? Sai ku duba ku gani. Don mu kam, ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.”​—A. M. 4:​19, 20.

WAƘA TA 73 Ka Ba Mu Ƙarfin Zuciya

^ sakin layi na 5 Mene ne za mu yi idan gwamnati ta saka wa aikinmu taƙunƙumi? A wannan talifin, za mu ga shawarwari game da abubuwan da za mu yi da kuma waɗanda za mu guje wa don kada mu daina bauta wa Allah!

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTO: Hotunan suna nuna Shaidun Jehobah da ke ƙasashen da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi. ’Yan’uwa a wani rukuni suna yin taro a ɗakin ajiya a gidan wani ɗan’uwa.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTO: Wata ’yar’uwa (a hagu) tana hira da wata mata kuma ta yi amfani da wannan damar don ta yi wa’azi.

^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTO: ’Yan sanda suna tuhumar wani ɗan’uwa, amma ya ƙi ya gaya musu batutuwa game da ikilisiyarsu.