Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 34

Yadda Za Mu Yi Farin Ciki Sa’ad da Muka Soma Sabuwar Hidima

Yadda Za Mu Yi Farin Ciki Sa’ad da Muka Soma Sabuwar Hidima

“Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba, da ƙaunar da kuka nuna masa.”​—IBRAN. 6:10.

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-3. Waɗanne dalilai ne suke sa ’yan’uwan da ke hidima ta cikakken lokaci su daina hidimarsu?

WANI ɗan’uwan mai suna Robert da matarsa Mary Jo, sun ce: “Bayan mun yi shekaru 21 muna yin hidima a ƙasar waje, iyayena da na matata sun soma rashin lafiya. Mun yi farin cikin kula da su, amma mun yi baƙin ciki domin mun bar ƙasar da muke so.”

2 Wani ɗan’uwa mai suna William da matarsa Terrie, sun ce: “Mun yi kuka sa’ad da aka sanar da mu cewa ba za mu iya ci gada da yin hidimarmu ba sanadiyyar rashin lafiya. Muna son yi wa Jehobah hidima a wata ƙasa, amma yanzu ba za mu iya yin hakan ba.”

3 Wani ɗan’uwa mai suna Aleksey, ya ce: “Mun san cewa gwamnati tana so ta rufe ofishinmu. Duk da haka, mun yi baƙin ciki sosai sa’ad da aka rufe Bethel kuma dukanmu muka bar wurin.”

4. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Ƙari ga haka, an ba ’yan’uwa da yawa har da waɗanda suke hidima a gidajen Bethel a faɗin duniya sabuwar hidima. * Yana iya yi ma waɗannan ’yan’uwa masu aminci wuya su bar hidimar da suke jin daɗin yi. Mene ne zai iya taimaka musu su su yi farin ciki a sabuwar hidimarsu? Ta yaya za ka taimaka musu? Amsoshin waɗannan tambayoyin za su taimaka wa dukanmu mu riƙa farin ciki sa’ad da yanayinmu ya canja.

YADDA ZA MU YI FARIN CIKI IDAN MUKA SOMA SABUWAR HIDIMA

Me ya sa yake yi wa waɗanda ke hidima ta cikakken lokaci wuya su bar hidimarsu? (Ka duba sakin layi na 5) *

5. Idan aka canja hidimarmu, a waɗanne hanyoyi ne hakan zai iya shafanmu?

5 Ko da muna hidima a Bethel ko kuma wata hidima ta cikakken lokaci, muna iya ƙaunar mutanen da kuma wurin sosai. Saboda haka, muna baƙin ciki idan za mu bar yin hidimar, musamman idan za mu bar wurin ne don ana tsananta mana. (Mat. 10:23; 2 Kor. 11:​28, 29) Ƙari ga haka, zai iya kasancewa da wuya idan muka ƙaura zuwa wani wuri dabam domin za mu soma koyan wata al’ada. Muna iya fuskantar wannan matsalar ko da ƙasarmu muka koma. Robert da Mary Jo sun ce: “Mun manta al’adunmu da kuma yadda ake wa’azi a yarenmu. Mun ji kamar mu baƙi ne a ƙasarmu.” Wasu da suka fara sabuwar hidima suna iya fuskantar matsalar tattalin arziki. Hakan yana iya sa su karaya. Mene ne zai taimaka musu?

Yana da muhimmanci mu kusaci Jehobah kuma mu dogara gare shi (Ka duba sakin layi na 6-7) *

6. Ta yaya za mu kusaci Jehobah?

6 Ka kusaci Jehobah. (Yaƙ. 4:8) Ta yaya za mu yi hakan? Ta wajen dogara gare shi domin shi “mai jin addu’o’i” ne. (Zab. 65:2) Littafin Zabura 62:8 ta ce: “Ku faɗa masa dukan zuciyarku.” Jehobah “yana aikata abubuwa fiye da dukan abin da za mu roƙa, ko abin da za mu yi tunaninsa.” (Afis. 3:20) Yana ba mu fiye da abubuwan da muka roƙa a addu’o’inmu. Jehobah yana iya yi mana abin da ba mu yi zato ba don ya magance matsalolinmu.

7. (a) Me zai taimaka mana mu ci gaba da kusantar Jehobah? (b) Kamar yadda Ibraniyawa 6:​10-12 suka nuna, wane sakamako ne za mu samu idan muka ci gaba da bauta wa Jehobah?

7 Don mu kusaci Jehobah muna bukatar mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kullum da kuma yin tunani a kan abin da muke karantawa. Wani ɗan’uwan da ke wa’azi a ƙasar waje a dā, ya ce: “Kamar yadda kake yi a hidimarka a dā, ka ci gaba da yin ibada ta iyali da kuma shirya taro a kowace mako.” Ban da haka, ka ci gaba da yin iya ƙoƙarinka don ka riƙa yin wa’azi a sabuwar ikilisiyar da kake. Jehobah yana tuna waɗanda suka ci gaba da bauta masa da aminci duk da cewa ba za su iya yin dukan abubuwan da suke yi a dā ba.​—Karanta Ibraniyawa 6:​10-12.

8. Ta yaya abin da ke 1 Yohanna 2:​15-17 zai taimaka maka ka sauƙaƙa salon rayuwarka?

8 Ka sauƙaƙa salon rayuwarka. Kada ka bar matsalolin duniyar nan su sa ka daina bauta wa Jehobah. (Mat. 13:22) Kada ka saurari mutanen da ba sa bauta wa Jehobah ko kuma danginka da suke ƙoƙarin taimaka maka ta wajen ba ka shawara cewa kana bukatar ka nemi kuɗi sosai don ka more rayuwa. (Karanta 1 Yohanna 2:​15-17.) Ka dogara ga Jehobah domin ya yi alkawarin zai biya dukan bukatunmu “a kan kari.”​—Ibran. 4:​16, Littafi Mai Tsarki; 13:​5, 6.

9. Kamar yadda Karin Magana 22:​3, 7 suka nuna, me ya sa muke bukatar mu guji karɓan bashi idan ba ma bukata, kuma mene ne zai taimaka mana mu yanke shawarar da ta dace?

9 Kada ka ci bashi idan ba ka bukata. (Karanta Karin Magana 22:​3, 7.) Mutum yana iya kashe kuɗi sosai idan zai ƙaura, kuma hakan yana iya sa ya ci bashi. Don haka, ka guji karɓan bashi don sayan abubuwan da ba ka bukata. Idan muna cikin damuwa, yana iya yi mana wuya mu san yawan bashin da muke bukatar mu karɓa. Alal misali, sa’ad da muke kula da wani danginmu marar lafiya. A irin wannan yanayin, ka tuna cewa “addu’a da roƙo” ga Jehobah, zai taimaka maka ka yanke shawarwarin da suka dace. Jehobah zai amsa addu’arka ta wajen ba ka salamar da za ta ‘tsare zuciyarka da tunaninka’ don ka kasance a natse kuma ka yanke shawarar da ta dace.​—Filib. 4:​6, 7; 1 Bit. 5:7.

10. Ta yaya za mu sami sabbin abokai?

10 Ka kasance da dangantaka mai kyau da mutane. Ka gaya wa abokanka na kud da kud abin da ke damunka da kuma matsalolin da kake fuskanta, musamman ma waɗanda suka taɓa samun kansu a irin yanayinka. Yin hakan zai taimaka maka ka daina damuwa. (M. Wa. 4:​9, 10) Mutanen da ka ƙulla abokantaka da su a hidimarka a dā za su ci gaba da zama abokanka. Duk da haka, kana bukatar ka ƙulla abokantaka da mutane a sabon wurin da kake hidima. Ka tuna cewa idan kana so ka sami abokai kana bukatar ka riƙa nuna alheri. Ta yaya za ka sami sabbin abokai? Ka riƙa gaya wa mutane abubuwan da ka more a hidimarka ga Jehobah don su ga cewa kana farin ciki. Wasu a ikilisiya ba za su fahimci dalilin da ya sa kake son hidima ta cikakken lokaci ba, amma wasu za su so su sani kuma za su zama abokanka. Amma kada ka cika yin magana game da kanka ko abubuwan da ka yi a hidimar Jehobah ko kuma abubuwan da ke sa ka baƙin ciki.

11. Me zai taimaka muku ku riƙa farin ciki a aurenku?

11 Idan ka bar hidima ne domin matarka ko mijinki yana rashin lafiya, kada ki ɗora masa laifi. Ko kuma idan ka bar hidimar ne domin kana rashin lafiya, kada ka riƙa baƙin ciki ka soma tunanin cewa ka ci ma’anar matarka ko mijinki. Ka tuna cewa ku “ɗaya” ne, kuma kun yi alkawari cewa za ku kula da juna ko da mene ne ya faru. (Mat. 19:​5, 6) Idan kuma ka bar hidimarka ne saboda matarka ta yi juna-biyu, ka tabbata cewa yaron da ta haifa ya san cewa kuna ƙaunar sa fiye da hidimarku. Ku tabbatar masa da cewa yana da daraja sosai a gare ku. (Zab. 127:​3-5) Ban da haka, ku faɗa masa abubuwan da kuka mora a hidimarku. Yin hakan zai motsa yaronku ya so yin amfani da rayuwarsa don ya bauta wa Jehobah kamar yadda kuka yi.

TA YAYA ’YAN’UWA ZA SU TAIMAKA?

12. (a) Ta yaya za mu taimaka wa waɗanda ke hidima ta cikakken lokaci su ci gaba da yin hidimarsu? (b) Ta yaya za mu taimaka musu su saba da sabuwar hidimarsu?

12 Ikilisiyoyi da yawa da kuma ’yan’uwa suna taimaka wa waɗanda ke hidima ta cikakken lokaci don su ci gaba da yin hakan. Suna yin hakan ta wajen ƙarfafa su ko biyan bukatunsu ko kuma kula da iyalinsu. (Gal. 6:2) Idan aka turo wasu da a dā suke hidima ta cikakken lokaci zuwa ikilisiyarku, kada ku soma tunanin cewa sun yi wani laifi ne shi ya sa aka ce su daina hidimar. * A maimakon haka, ku taimaka musu su saba da wurin. Ku marabce su kuma ku yaba musu domin aikin da suka yi, ko da ba za su iya yin abubuwa kamar dā ba domin rashin lafiya. Ku yi ƙoƙari ku san su, ku koya daga labarinsu da kuma iliminsu.

13. Ta yaya za mu taimaka wa waɗanda aka canja musu hidima?

13 ʼYan’uwan da aka canja musu hidima suna iya bukatar taimakonka don su sami gida da aiki, su san inda ake shigan mota da dai sauransu. Amma abin da suka fi bukata shi ne ka fahimci yanayin da suke ciki. Wataƙila su ko kuma wani a iyalinsu yana rashin lafiya. Ko kuma wataƙila suna makoki domin wani nasu ya rasu. * Ko da ba su yin magana game da abin da ke faruwa da su, suna iya yin baƙin ciki domin suna kewar abokansu. Yana iya ɗaukan lokaci kafin su daina jin hakan, kuma suna iya ruɗewa.

14. Ta yaya ’yan’uwa suka taimaka ma wata ’yar’uwa ta soma farin ciki a sabuwar hidimarta?

14 Idan ka yi wa’azi tare da su kuma ka ƙarfafa su da misalinka, hakan zai taimaka musu su saba da hidimarsu. Wata ’yar’uwa da ta ɗau shekaru da yawa tana yin hidima a wata ƙasa ta ce: “A hidimar da nake yi a dā, ina yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a kowace rana. A sabuwar hidimar da nake yi, yana da wuya in ga mutumin da zai yarda in karanta masa Littafi Mai Tsarki ko kuma in nuna masa bidiyo. Amma ’yan’uwa a ikilisiyar suna gaya mini in raka su don su yi nazari da ɗalibansu. Ganin yadda ɗaliban waɗannan ’yan’uwa masu ƙwazo suke samun ci gaba ya sa na kasance da ra’ayin da ya dace. Na koyi yadda zan soma tattaunawa da mutane a yankin, kuma hakan ya taimaka mini in soma farin ciki a sabuwar hidimata.”

KA CI GABA DA YIN IYA ƘOƘARINKA!

Ka yi ƙoƙarin faɗaɗa hidimarka a ƙasarku (Ka duba sakin layi na 15-16) *

15. Me zai taimaka maka ka yi nasara a hidimarka?

15 Kana iya yin nasara a sabuwar hidimar da kake yi. Kada ka yi tunanin cewa ka yi wani laifi a hidimarka ta dā ko kuma ba ka da daraja. Ka yi tunanin hanyoyi da yawa da Jehobah yake taimaka maka kuma ka ci gaba da yin wa’azi. Ka yi koyi da Kiristoci a ƙarni na farko. Ko da a ina ne suka sami kansu sun ci gaba da yin “shelar labarin nan mai daɗi.” (A. M. 8:​1, 4) Idan ka ci gaba da yin wa’azi, za ka yi nasara sosai. Alal misali, majagaba da yawa da aka kora daga wata ƙasa, sun ƙaura zuwa ƙasar da ke kusa da su kuma a wurin ana bukatar masu shela a yaren da majagaban suka iya. A cikin watanni, an kafa sababbin rukunoni.

16. Ta yaya za ka yi farin ciki a sabuwar hidima da kake yi?

16 “Farin cikin da kuke da shi cikin Yahweh shi ne tushen ƙarfinku.” (Neh. 8:10) Dangantakarmu da Jehobah ne ya kamata ya riƙa samu farin ciki, ba hidimarmu ba ko da muna son ta sosai. Don haka, idan muna so mu riƙa farin ciki, muna bukatar mu kusaci Jehobah kuma mu dogara gare shi. Ka tuna cewa ka soma son hidimar da kake yi a dā ne domin ka yi iya ƙoƙarinka don taimaka wa mutane a wurin. Idan ka yi iya ƙoƙarinka a sabuwar hidimarka, za ka ga yadda Jehobah zai taimaka maka ka soma son hidimar.​—M. Wa. 7:10.

17. Me muke bukatar mu tuna game da hidimar da muke yi yanzu?

17 Muna bukatar mu riƙa tuna cewa za mu ci gaba da bauta wa Jehobah har abada, amma hidimar da muke yi ba na dindindin ba ne. A sabuwar duniya, dukanmu za mu sami sabuwar hidima. Aleksey wanda aka ambata ɗazu ya bayyana cewa canje-canjen da ya samu a hidimarsa suna shirya shi ne don nan gaba. Ya ce: “Na san cewa Jehobah yana wanzuwa kuma za a yi sabuwar duniya, amma ina ganin sun yi nesa da ni. Yanzu na kusaci Jehobah kuma ina ji kamar sabuwar duniya za ta zo nan da nan.” (A. M. 2:25) Ko da wane hidima muke yi, muna bukatar mu ci gaba da kusantar Jehobah. Ba zai taɓa yasar da mu ba, amma zai taimaka mana mu yi farin ciki idan muka yi masa hidima gwargwadon ƙarfinmu ko da wane hidima muke yi.​—Isha. 41:13.

WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna

^ sakin layi na 5 A wasu lokuta, ’yan’uwan da ke hidima ta cikakken lokaci suna daina yin hidimar ko kuma ana canja musu hidima. A wannan talifin, an tattauna irin ƙalubalen da suke fuskanta da kuma abin da zai taimaka musu su yi farin ciki a sabuwar hidimarsu. Ƙari ga haka, an tattauna yadda wasu za su iya ƙarfafa su da taimaka musu da kuma ƙa’idodin da za su taimaka wa dukanmu mu yi farin ciki sa’ad da yanayinmu ya canja.

^ sakin layi na 4 Ban da haka, sa’ad da wasu ’yan’uwa suka kai wasu shekaru, sun bar wa matasa aikin da suke yi. Ka duba talifofin nan, “Tsofaffi​—Jehobah Yana Daraja Ku Don Amincinku” a Hasumiyar Tsaro ta Satumba 2018 da kuma “Ku Kasance da Kwanciyar Rai Idan Yanayinku Ya Canja” a Hasumiyar Tsaro ta Oktoba 2018.

^ sakin layi na 12 Dattawan ikilisiyar da suka bari suna bukatar su tura wa sabon ikilisiyar wasiƙa ba tare da ɓata lokaci ba, domin ’yan’uwan su ci gaba da yin hidima a matsayin majagaba ko dattawa ko kuma bayi masu hidima.

^ sakin layi na 13 Ka duba talifin nan “Help for Those Who Grieve,” a Awake! na 2018, lamba ta 3.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTO: Wasu ma’aurata da za su bar yin wa’azi a ƙasar waje suna yin ban-kwana da ’yan’uwan da ke ikilisiyarsu.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTO: Ma’auratan sun yi addu’a ga Jehobah ya taimaka musu su jimre matsalolin da suke fuskanta a ƙasarsu.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTO: Da taimakon Jehobah, ma’auratan sun sake soma yin hidima ta cikakken lokaci. Suna yin amfani da yaren da suka koya sa’ad da suke wa’azi a ƙasar waje don su yi wa baƙi wa’azi.