Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 44

Ku Yi Abokan Kirki Kafin Karshe Ya Zo

Ku Yi Abokan Kirki Kafin Karshe Ya Zo

“A koyaushe aboki yana nuna ƙauna.”​—K. MAG. 17:17.

WAƘA TA 101 Mu Riƙa Hidima da Haɗin Kai

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

Za mu bukaci abokan kirki a lokacin ƙunci mai girma (Ka duba sakin layi na 2) *

1-2. Kamar yadda 1 Bitrus 4:​7, 8 suka nuna, mene ne zai taimaka mana mu jimre a mawuyacin lokaci?

‘ƘARSHEN’ wannan zamanin ya yi kusa sosai, saboda haka, za mu fuskanci matsaloli masu tsanani. (2 Tim. 3:1) Alal misali, bayan da aka yi zaɓe a wata ƙasa a Afirka, sai aka soma tashin hankali. ’Yan’uwanmu sun sha wahala sosai fiye da wata shida saboda tashin hankalin. Mene ne ya taimaka musu a wannan lokacin? Wasu sun nemi mafaka a gidajen ’yan’uwan da ke yankunan da ba a faɗa. Wani ɗan’uwa ya ce: “A irin wannan yanayin, na yi farin ciki sosai domin ina tare da abokaina, kuma mun ƙarfafa juna.”

2 Sa’ad da aka soma ƙunci mai girma, za mu yi farin ciki idan muna da abokai da suke ƙaunar mu. (R. Yar. 7:14) Saboda haka, yana da muhimmanci mu ƙulla abokantaka na kud da kud a yanzu. (Karanta 1 Bitrus 4:​7, 8.) Za mu iya koyan darasi daga Irmiya, wanda abokansa ne suka cece shi a lokacin da ake gab da halaka Urushalima. * Ta yaya za mu iya yin koyi da Irmiya?

KU BI MISALIN IRMIYA

3. (a) Da me zai iya sa Irmiya ya ware kansa daga mutane? (b) Mene ne Irmiya ya gaya wa Baruch, wane sakamako ne hakan ya kawo?

3 Irmiya ya kasance tare da mutanen da ba su da aminci har wajen shekara 40. Waɗannan sun ƙunshi maƙwabta da kuma wataƙila wasu danginsa da ke garinsu a Anatot. (Irm. 11:21; 12:6) Amma bai ware kansa ba. Maimakon haka, ya gaya wa Baruch sakatarensa yadda yake ji, kuma mun san hakan domin an rubuta a Littafi Mai Tsarki. (Irm. 8:21; 9:1; 20:​14-18; 45:1) Babu shakka, yayin da Baruch yake rubuta abubuwan da Irmiya ya fuskanta, hakan ya sa sun ƙaunaci da kuma mutunta juna.​—Irm. 20:​1, 2; 26:​7-11.

4. Mene ne Jehobah ya gaya wa Irmiya ya yi, ta yaya wannan aikin ya sa dangantakar Irmiya da Baruch ta yi danƙo sosai?

4 Irmiya ya kwashi shekaru da yawa yana wa Isra’ilawa kashedi game da abin da zai faru da Urushalima. (Irm. 25:3) A lokacin da Jehobah ya ƙara ce wa mutanen su tuba, ya gaya wa Irmiya ya rubuta saƙon a cikin littafi. (Irm. 36:​1-4) Babu shakka, yayin da Irmiya da Baruch suke yin hidimar Allah tare, wanda wataƙila ya ɗau watanni da yawa, sun tattauna batutuwa da suka ƙarfafa juna.

5. Ta yaya Baruch ya zama abokin kirki ga Irmiya?

5 Bayan da suka gama rubutun, Irmiya yana da tabbaci cewa abokinsa Baruch zai sanar da saƙon. (Irm. 36:​5, 6) Baruch ya yi wannan aiki mai wuya da gaba gaɗi. Babu shakka, Irmiya ya yi alfahari da Baruch sa’ad da ya je haikali kuma ya idar da saƙon! (Irm. 36:​8-10) Sa’ad da dattawan Yahuda suka ji abin da Baruch ya yi, sun gaya masa ya karanta musu littafin! (Irm. 36:​14, 15) Sai dattawan suka gaya wa Sarki Yehoyakim abin da Irmiya ya faɗa. Dattawan sun yi la’akari da Baruch kuma suka ce masa: Ka “gudu ka ɓoye, kai da Irmiya! Kada kuma ku yarda wani ya san inda kuka ɓuya.” (Irm. 36:​16-19) Hakan shawara ce mai kyau!

6. Mene ne Irmiya da Baruch suka yi sa’ad da suka fuskanci tsanantawa?

6 Sarki Yehoyakim ya yi fushi sosai sa’ad da ya ji abin da Irmiya ya rubuta. Sai ya sa aka ƙone littafin kuma ya ce a kamo Irmiya da Baruch. Amma Irmiya bai tsorata ba, sai ya ba Baruch wani littafi don ya sake rubuta saƙon Jehobah. Baruch ya rubuta ‘dukan kalmomin da suke a littafin da Sarki Yehoyakim na Yahuda ya ƙona a wuta.’​—Irm. 36:​26-28, 32.

7. Mene ne ya faru yayin da Irmiya da Baruch suke aiki tare?

7 Mutanen da suka jimre jarrabawa tare sukan ƙulla dangantaka ta kud da kud. Saboda haka, Irmiya da Baruch sun san juna sosai kuma sun zama aminai yayin da suke aiki tare don su sake rubuta littafin da Sarki Yehoyakim ya ƙona. Ta yaya misalin waɗannan maza biyu masu aminci ya taimaka mana?

KU RIƘA GAYA MUSU ABIN DA KE ZUCIYARKU

8. Mene ne zai iya hana mu samun abokai na kud da kud, kuma me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa ba?

8 Zai iya yi mana wuya mu gaya wa mutane yadda muke ji idan wani ya taɓa ɓata mana rai. (K. Mag. 18:​19, 24) Ko kuma muna ganin cewa ba mu da lokaci da ƙarfin yin abokai. Amma, bai kamata mu riƙa tunanin cewa hakan ba zai yiwu ba. Idan muna so ’yan’uwanmu su taimaka mana sa’ad da muke fuskantar jarrabawa, wajibi ne mu koyi amincewa da su a yanzu kuma mu riƙa gaya musu abin da ke zuciyarmu. Hakan yana da muhimmanci idan muna so mu zama aminansu.​—1 Bit. 1:22.

9. (a) Ta yaya Yesu ya nuna ya amince da abokansa? (b) Ta yaya faɗin abin da ke zuciyarka zai taimaka maka ka ƙulla dangantaka ta kud da kud? Ka ba da misali.

9 Yesu ya nuna ya amince da abokansa ta wajen gaya musu abin da ke zuciyarsa. (Yoh. 15:15) Muna iya yin koyi da shi ta wajen gaya wa abokanmu abubuwan da ke sa mu farin ciki, suke damun mu kuma suke ɓata mana rai. Ku saurara da kyau sa’ad da abokinku yake muku magana. Kuna iya fahimta cewa suna fuskantar abin da kuke fuskanta. Ban da haka, wataƙila kuna da maƙasudai iri ɗaya. Ka yi la’akari da misalin wata ʼyar shekara 29 mai suna Cindy. Ta ƙulla abokantaka da wata majagaba ’yar shekara 67 mai suna Marie-Louise. Cindy da Marie-Louise sukan fita wa’azi tare a kowace ranar Alhamis da safe. Ƙari ga haka, sukan yi taɗi a kan batutuwa dabam-dabam. Cindy ta ce: “Ina jin daɗi tattauna batutuwa masu muhimmanci da abokaina domin hakan yana taimaka mini in san su da kyau kuma in fahimce su.” Dangantakarku za ta yi danƙo sosai, sa’ad da kuka gaya wa abokanku abin da ke zuciyarku kuma kuka saurare su sa’ad da suke magana. Kamar Cindy, za ku ƙarfafa dangantakarku da abokanku idan kuna gaya musu abin da ke zuciyarku.​—K. Mag. 27:9.

KU YI AIKI TARE

Aminai suna wa’azi tare (Ka duba sakin layi na 10, 16, da 18)

10. Kamar yadda Karin Magana 27:17 ta nuna, ta yaya za mu amfana sa’ad da muka yi aiki tare da ’yan’uwanmu?

10 Kamar Irmiya da Baruch, sa’ad da muka yi aiki tare da ’yan’uwanmu kuma muka lura da halayensu masu kyau, hakan zai sa mu kusace su. (Karanta Karin Magana 27:17.) Alal misali, yaya kake ji sa’ad da kake wa’azi tare da abokinka kuma ka ga yadda ya kāre imaninsa da gaba gadi? Babu shakka, kana farin ciki sa’ad da yake magana game da Jehobah da nufe-nufensa da dukan zuciyarsa, kuma hakan na sa ka daɗa ƙaunar sa.

11-12. Ka ba da misalin yadda yin wa’azi da ’yan’uwa zai taimaka mana mu ƙarfafa abokantakarmu.

11 Ka yi la’akari da labarai biyu da suka nuna cewa yin wa’azi tare da ’yan’uwa yana sa su zama abokai. Wata ’yar’uwa mai suna Adeline, ’yar shekara 23 ta gaya wa kawarta mai suna Candice su je su yi wa’azi a yankunan da ba a yawan wa’azi. Adeline ta ce: “Muna so mu ƙara ƙwazo a wa’azi kuma mu ji daɗinsa sosai. Ban da haka, muna so abin da zai ƙarfafa mu mu yi iya ƙoƙarinmu a hidimarmu ga Jehobah.” Ta yaya yin wa’azi tare ya amfane su? Adeline ta ce: “Kowace rana bayan mun gama wa’azi, mukan tattauna yadda muke ji da yadda tattaunawa da mutane ya ƙarfafa mu. Ƙari ga haka, mun ga yadda Jehobah ya taimaka mana a hidimarmu. Mun ji daɗin tattaunawa sosai kuma mun ƙara sanin juna da kyau.”

12 Laïla da Marianne ’yan’uwa mata biyu ne daga Faransa kuma ba su da aure. Sun je yin wa’azi na makonni biyar a babban birnin Bangui da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Laïla ta ce: “Ni da Marianne mun fuskanci ƙalubale, amma mun ƙulla dangantaka ta kud da kud don muna tattaunawa sosai kuma muna ƙaunar juna. Na ƙara mutunta Marianne yayin da na ga yadda ya yi mata sauƙi ta saba da sabon yanayi. Ban da haka, tana ƙaunar mutanen sosai kuma tana da ƙwazo.” Ba sai ka je wata ƙasa ba kafin ka more irin wannan dangantakar ba. A kowane lokaci da ka fita wa’azi tare da wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa, kana da zarafin sanin su da kyau. Kuma hakan zai taimaka muku ku ƙarfafa abokantakarku.

KU MAI DA HANKALI A KAN HALAYENSU MASU KYAU, KU RIƘA GAFARTAWA

13. Mene ne za mu lura sa’ad da muka yi aiki tare da abokanmu?

13 A wasu lokuta, sa’ad da muka yi aiki tare da abokanmu, mukan ga halayensu masu kyau da kuma kasawarsu. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da abokantaka da su? Ka sake yin la’akari da misalin Irmiya. Mene ne ya taimaka masa ya mai da hankali ga halaye masu kyau na abokansa kuma ya gafarta musu?

14. Mene ne Irmiya ya koya game da Jehobah, kuma yaya hakan ya taimaka masa?

14 Irmiya ne ya rubuta littafin da ke ɗauke da sunansa, kuma wataƙila shi ne ya rubuta littafin Sarakuna na 1 da na 2. Wannan aikin ya taimaka masa ya ga cewa Jehobah yana nuna jinƙai ga ’yan Adam ajizai. Alal misali, Irmiya ya san cewa sa’ad da Sarki Ahab ya tuba, Jehobah bai ƙyale masifar da ya nufa ta faru a zamaninsa ba. (1 Sar. 21:​27-29) Hakazalika, Irmiya ya san cewa Manasseh ya fi Ahab yin zunubi ga Jehobah. Duk da haka, Jehobah ya gafarta wa Manasseh domin ya tuba. (2 Sar. 21:​16, 17; 2 Tar. 33:​10-13) Waɗannan misalan sun taimaka wa Irmiya ya zama mai haƙuri kuma ya nuna jinƙai ga abokansa.​—Zab. 103:​8, 9.

15. Ta yaya Irmiya ya yi koyi da Jehobah sa’ad da abin duniya ya janye hankalin Baruch?

15 Ka yi la’akari da yadda Irmiya ya taimaka wa Baruch sa’ad da abin duniya ya janye hankalinsa. Maimakon Irmiya ya yasar da abokinsa Baruch, ya taimaka masa ta wajen gaya masa saƙon Allah kai tsaye. (Irm. 45:​1-5) Waɗanne darussa ne muka koya daga wannan labarin?

Aminai suna gafarta wa juna (Ka duba sakin layi na 16)

16. Kamar yadda aka nuna a Karin Magana 17:​9, mene ne muke bukatar mu yi don mu ƙarfafa abokantakarmu?

16 Hakika, ’yan’uwanmu ajizai ne. Saboda haka, muddin mun ƙulla abokantaka da su, ya kamata mu ci gaba da yin hakan. Idan abokanmu suka yi kuskure, muna bukatar mu ba su shawara daga Kalmar Allah. (Zab. 141:5) Idan suka ɓata mana rai, muna bukatar mu gafarta musu. Muddin mun gafarta musu, wajibi ne mu mance da batun. (Karanta Karin Magana 17:9.) A wannan kwanaki na ƙarshe, yana da muhimmanci mu mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwanmu maimakon kasawarsu! Yin hakan yana sa mu ƙarfafa abotarmu, kuma yana da kyau mu yi hakan yanzu domin za mu bukaci abokai na kud da kud a lokacin ƙunci mai girma.

KU RIƘA ƘAUNAR ’YAN’UWA

17. Ta yaya Irmiya ya zama abokin kirki a mawuyacin lokaci?

17 Annabi Irmiya ya zama abokin kirki a mawuyanci lokaci. Alal misali, bayan da Ebedmelek ya ceci Irmiya daga rijiya, Ebedmelek ya ji tsoro cewa dattawan Urushalima za su kashe shi. Sa’ad da Irmiya ya ji hakan, bai yi shiru ba da fatan cewa abokinsa zai iya jimrewa. Duk da cewa Irmiya yana kurkuku, ya yi iya ƙoƙarinsa ya ƙarfafa abokinsa Ebedmelek ta wurin gaya masa alkawarin da Jehobah ya yi.​—Irm. 38:​7-13; 39:​15-18.

Aminai suna taimaka wa ’yan’uwa a mawuyacin lokaci (Ka duba sakin layi na 18)

18. Kamar yadda Karin Magana 17:17 ta nuna, mene ne ya kamata mu yi sa’ad da abokinmu yake shan wahala?

18 A yau, ’yan’uwanmu suna fuskantar matsaloli dabam-dabam. Alal misali, da yawa cikinsu suna shan wahala saboda girgizar ƙasa ko kuma yaƙe-yaƙe. Idan hakan ya faru, muna iya gayyatar waɗannan ’yan’uwa su zauna tare da mu. Wasu suna iya ba su kuɗi. Amma dukanmu muna iya roƙon Jehobah ya taimaka ma ’yan’uwanmu. Idan mun ji cewa wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta yi sanyin gwiwa, wataƙila ba za mu san abin da za mu faɗa ba ko abin da za mu yi ba. Duk da haka, za mu iya taimaka musu. Alal misali, muna iya keɓe lokaci don mu kasance da su. Za mu iya saurarar su sosai sa’ad da suke magana. Ƙari ga haka, muna iya karanta musu wani nassi mai ban ƙarfafa da muka fi so. (Isha. 50:4) Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka kasance da abokanka sa’ad da suke bukatar ka.​—Karanta Karin Magana 17:17.

19. Ta yaya ƙulla abota na kud da kud yanzu zai taimaka mana a nan gaba?

19 Wajibi ne mu ƙuduri niyyar ƙulla da kuma ƙarfafa abotarmu da ’yan’uwa yanzu. Me ya sa? Domin magabtanmu za su yi ƙoƙari su yi amfani da ƙaryace-ƙaryace don su raba kanmu. Za su yi ƙoƙari su sa mu daina amincewa da kuma tallafa wa juna. Amma ba za su yi nasara ba. Ba za su iya sa mu daina ƙaunar juna ba. Babu abin da za su yi da zai sa mu daina abotarmu ba. Ƙari ga haka, za mu ci gaba da wannan abokantaka har zuwa ƙarshen wannan zamani da kuma har abada!

WAƘA TA 24 Ku Zo Tudun Jehobah

^ sakin layi na 5 Yayin da ƙarshen wannan zamanin ke kusatowa, muna bukatar mu sa dangantakarmu da ’yan’uwa ta yi danƙo sosai. A wannan talifin, za mu tattauna abin da za mu iya koya daga labarin Irmiya. Za mu kuma ga yadda ƙulla abokantaka na kud da kud zai taimaka mana a mawuyacin lokaci.

^ sakin layi na 2 Ba a jera abubuwan da suka faru a littafin Irmiya bisa lokacin da suka faru ba.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTUNA: Wannan hoton yana nuna abin da zai iya faruwa a lokacin ƙunci mai girma. ’Yan’uwa da yawa suna taro a saman gidan wani ɗan’uwa. Domin su abokai ne, sun ƙarfafa juna a wannan lokacin jarrabawa. Waɗannan ’yan’uwan sun soma wannan abokantaka kafin a soma ƙunci mai girma.