Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 49

‘Akwai Lokacin’ Yin Aiki da Kuma Hutu

‘Akwai Lokacin’ Yin Aiki da Kuma Hutu

“Ku zo mu tafi wurin da ba kowa, don ku ɗan huta.”​—MAR. 6:31.

WAƘA TA 143 Mu Ci Gaba da Ƙwazo da Tsaro da Jira

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Waɗanne ra’ayoyi ne mutane da yawa suke da shi game da aiki?

TA YAYA yawancin mutane suke ɗaukan aiki a wurin da kake zama? A ƙasashe da yawa, mutane suna aiki na dogon lokaci sosai fiye da dā. Sau da yawa, mutane da suke aiki sosai ba sa hutawa, ba sa zama da iyalansu kuma ba sa ƙarfafa dangantakarsu da Allah. (M. Wa. 2:23) Wata matsala kuma ita ce, wasu mutane sun fi son zaman-kashe-wando kuma sukan ba da hujjar yin hakan.​—K. Mag. 26:​13, 14.

2-3. Waɗanne misalai ne Jehobah da Yesu suka kafa mana game da aiki?

2 Ka yi tunanin yadda ra’ayin Jehobah da Yesu ya bambanta da ra’ayoyi dabam-dabam da mutane suke da shi game da aiki. Babu shakka cewa Jehobah mai son aiki ne sosai. Yesu ya nuna hakan sa’ad da ya ce: “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina yi.” (Yoh. 5:17) Allah ya yi aiki sosai sa’ad da ya halicci mala’iku da yawa da taurari da sammai da duniya. Ƙari ga haka, muna ganin abubuwa masu kyau da Allah ya halitta a duniya. Shi ya sa wani marubucin zabura ya ce: “Ya Yahweh, ina misalin yawan ayyukanka, cikin hikima ka yi su duka! Duniya cike take da halittunka.”​—Zab. 104:24.

3 Yesu ya yi koyi da Jehobah. Shi mai hikima ne sosai kuma ya taimaka sa’ad da Allah “ya yi sammai.” Yesu ‘gwani’ mai aiki ne tare da Jehobah. (K. Mag. 8:​27-31) Bayan haka, Yesu ya yi aiki na musamman sa’ad da yake duniya. Wannan aiki yana kamar abinci a gare shi, kuma ayyukansa sun nuna cewa Allah ne ya aiko shi.​—Yoh. 4:34; 5:36; 14:10.

4. Mene ne Jehobah da Yesu suka koya mana game da hutu?

4 Shin waɗannan misalan suna nufin cewa ba ma bukatar mu huta sa’ad da muke yin aiki? A’a. Jehobah ba ya bukatar hutu domin ba ya gajiya. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “ya huta” bayan ya halicci sammai da duniya. (Fit. 31:17) Hakan yana nufin cewa Jehobah ya daina halittar abubuwa kuma ya keɓe lokaci don ya ji daɗin abin da ya yi. Ƙari ga haka, duk da cewa Yesu ya yi aiki tuƙuru sa’ad da yake duniya, ya nemi lokaci ya huta kuma ya ci abinci da abokansa.​—Mat. 14:13; Luk. 7:34.

5. Wace fama ce mutane da yawa suke yi?

5 Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mutanen Allah su riƙa yin aiki sosai. Ya kamata bayinsa su zama masu aiki tuƙuru maimakon masu ƙyuya. (K. Mag. 15:19) Wataƙila kana yin aiki don ka biya bukatun iyalinka. Kuma dukan almajiran Kristi suna da hakkin yin wa’azi. Duk da haka, kana bukatar samun isasshen hutu. Shin a wasu lokuta kana fama ne ka samu isasshen lokacin hutu don aikinka da kuma hidimarka? Yaya za mu san yawan lokaci da muke bukata don aiki da kuma hutu?

RA’AYI MAI KYAU GAME DA AIKI DA HUTU

6. Ta yaya littafin Markus 6:​30-34 ya nuna cewa Yesu yana da ra’ayin da ya dace game da yin aiki da kuma hutu?

6 Yana da muhimmanci mu kasance da ra’ayin da ya dace game da aiki. An hure Sarki Sulemanu ya rubuta cewa: “Ga kowane abu akwai lokacinsa.” Ya ambata lokacin shuka da ginawa da kuka da dariya da rawa da kuma wasu ayyuka. (M. Wa. 3:​1-8) Hakika, yin aiki da kuma hutu abubuwa biyu ne masu muhimmanci a rayuwa. Yesu yana da ra’ayin da ya dace game da yin aiki da kuma hutu. Akwai lokacin da manzanninsa suka dawo daga wa’azi kuma “ba su sami damar cin abinci ba.” Yesu ya ce musu: “Ku zo mu tafi wurin da ba kowa, don ku ɗan huta.” (Karanta Markus 6:​30-34.) Ko da yake Yesu da almajiransa ba su sami isasshen hutu da suke so ba, Yesu ya san cewa dukansu suna bukatar hutu.

7. Ta yaya bincika dokar ranar Assabaci zai taimaka mana?

7 A wasu lokuta, muna bukatar mu huta ko kuma mu canja yadda muke ayyukanmu na yau da kullum. Wani abu da Allah ya shirya wa mutanensa a zamanin dā, wato Assabaci zai taimaka mana mu ga hakan. A yau, ba ma bin dokar da Allah ya ba Isra’ilawa, duk da haka za mu amfana daga abin da ta ce game da Assabaci. Abin da za mu koya zai iya taimaka mana mu bincika ra’ayinmu game da aiki da kuma hutu.

ASSABACI RANAR HUTU CE DA KUMA IBADA

8. Kamar yadda aka nuna a Fitowa 31:​12-15, mene ne ake yi a ranar Assabaci?

8 Kalmar Allah ta ce Allah ya daina halittar abubuwa bayan rana ta shida. (Far. 2:2) Amma, Jehobah yana son yin aiki kuma a wasu hanyoyi, “yana aiki har yanzu.” (Yoh. 5:17) A dokar ranar Assabaci, an bi tsarin hutun da Jehobah ya yi da aka ambata a littafin Farawa. Allah ya ce ranar Assabaci alama ce tsakaninsa da Isra’ilawa. Ranar Assabaci “ranar hutu ce ta musamman, wadda aka keɓe da tsarki ga Yahweh.” (Karanta Fitowa 31:​12-15.) An hana kowa yin aiki, wato yara da manya da bayi, har da dabbobi. (Fit. 20:10) Hakan ya taimaka ma mutanen su mai da hankali ga abubuwan da suka shafi ibadarsu.

9. A zamanin Yesu, wane ra’ayi marar kyau game da ranar Assabaci ne wasu suke da shi?

9 Ranar Assabaci ta dace da mutanen Allah, amma shugabannin addinai da yawa a zamanin Yesu sun kafa dokoki masu wuya game da wannan ranar. Sun ce bai dace a karya kan hatsi a ci a ranar Assabaci ba ko kuma a warkar da marar lafiya. (Mar. 2:​23-27; 3:​2-5) Ba ra’ayin da Allah yake so mutane su kasance da shi ke nan ba, kuma Yesu ya bayyana hakan ga masu sauraron sa.

Iyalin Yesu sun mai da hankali ga ibada a ranar Assabaci (Ka duba sakin layi na 10) *

10. Me muka koya a littafin Matiyu 12:​9-12 game da yadda Yesu ya ɗauki ranar Assabaci?

10 Yesu da mabiyansa waɗanda Yahudawa ne sun kiyaye ranar Assabaci domin suna bin Dokar da aka ba da ta hannun Musa. * Amma Yesu ya faɗi da kuma yi abubuwa da yawa da suka nuna cewa ba laifi ba ne a yi alheri da kuma taimaka wa mutane a ranar Assabaci. Ya ce: “Ba a hana yin aikin alheri a Ranar Hutu ta Mako ba.” (Karanta Matiyu 12:​9-12.) Yesu ba ya ganin cewa taka doka ne idan mutum ya yi alheri da kuma taimaka wa mutane a ranar Assabaci. Ayyukan Yesu sun nuna dalilin da ya sa aka kafa ranar Assabaci. An kafa ta domin mutanen Allah su mai da hankali ga ibadarsu sa’ad da suke hutawa daga ayyukansu na yau da kullum. Yesu ya yi girma a iyalin da suka yi amfani da ranar Assabaci don su bauta wa Allah. Mun san hakan domin abin da muka karanta game da Yesu sa’ad da yake garinsu Nazarat. Ayar ta ce: “Ya shiga Majami’a a Ranar Hutu ta Mako kamar yadda ya saba. Ya tashi zai yi karatu.”​—Luk. 4:​15-19.

MENE NE RA’AYINKA GAME DA AIKI?

11. Wane ne ya kafa wa Yesu misali mai kyau game da aiki?

11 Yusufu ya koya wa Yesu yadda zai zama kafinta da kuma ra’ayin Allah game da aiki. (Mat. 13:​55, 56) Ƙari ga haka, Yesu ya ga yadda Yusufu yake aiki tuƙuru a kowace rana don ya tallafa wa iyalinsa. Kuma daga baya Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Ya kamata a biya wa mai yin aiki hakkinsa.” (Luk. 10:7) Hakika, Yesu ya san yadda ake aiki mai wuya.

12. Waɗanne nassosi ne suka nuna abin da Kalmar Allah ta ce game da yin aiki tuƙuru?

12 Manzo Bulus ma ya san yadda ake yin aiki tuƙuru. Aikinsa na musamman shi ne gaya wa mutane game da Yesu da kuma koyarwarsa. Duk da haka, Bulus ya yi aiki don ya biya bukatunsa. Mutanen Tasalonika sun san cewa ya yi “fama da wahala” yana “aiki dare da rana” don kada ya sa wa kowa ‘nauyin’ biyan bukatunsa. (2 Tas. 3:8; A. M. 20:​34, 35) Wataƙila Bulus yana magana game da aikinsa na ɗinka tanti ne. Sa’ad da yake Koranti, ya zauna tare da Akila da Biriskila kuma “suka yi ta aiki tare” da yake sana’arsu iri ɗaya ne. Sa’ad da Bulus ya ce yana aiki “dare da rana,” hakan ba ya nufin cewa yana aiki ba hutu. Bulus bai yi aikin ɗinka tanti a ranar Assabaci ba. A ranar, yana yin amfani da wannan zarafin don ya yi wa’azi ga Yahudawa da ba sa aiki a ranar Assabaci.​—A. M. 13:​14-16, 42-44; 16:13; 18:​1-4.

13. Mene ne muka koya daga misalin Bulus?

13 Manzo Bulus ya kafa misali mai kyau. Ya yi aiki don ya biya bukatunsa. Duk da haka, yana gaya wa mutane game da Allah a kai a kai. (Rom. 15:16; 2 Kor. 11:23) Bulus ya ƙarfafa mutane su yi koyi da shi. Akila da Biriskila ‘abokan aikinsa ne cikin Almasihu Yesu.’ (Rom. 12:11; 16:3) Bulus ya ƙarfafa Korantiyawa su “yalwata cikin aikin Ubangiji.” (1 Kor. 15:58; 2 Kor. 9:8) Ban da haka, Jehobah ya hure manzo Bulus ya rubuta cewa: “Duk wanda ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”​—2 Tas. 3:10.

14. Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya yi furuci da ke littafin Yohanna 14:12?

14 Aiki mafi muhimmanci a wannan kwanaki na ƙarshe shi ne yin wa’azi da kuma almajirtarwa. Kuma Yesu ya annabta cewa aikin da almajiransa za su yi zai fi nasa! (Karanta Yohanna 14:12.) Hakan ba ya nufin cewa za mu yi mu’ujizai yadda ya yi. Maimakon haka, mabiyansa za su yi wa’azi da koyarwa a wurare da yawa fiye da nasa. Za su yi wa’azi da koyarwa ga mutane da yawa kuma na dogon lokaci fiye da shi.

15. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu, kuma me ya sa?

15 Idan kana aiki, ka yi wa kanka waɗannan tambayoyin: ‘An san ni da saka ƙwazo a wajen aikinmu? Ina gama aikina da wuri kuma ina yin aikin da kyau?’ Babu shakka, shugaban aikinku zai amince da kai sosai idan kana yin hakan. Ƙari ga haka, mutanen da ke wurin aikinku za su so su saurari wa’azinka. Idan ya zo ga batun yin wa’azi da kuma koyarwa, ka yi ma kanka waɗannan tambayoyin: ‘An san ni a matsayin mai yin wa’azi da ƙwazo? Ina yin shiri sosai sa’ad da nake so in yi wa wani wa’azi a ƙaro na farko? Ina saurin komawa in ziyarci mutanen da suka saurari saƙonmu? Ƙari ga haka, ina saka hannu a fannoni wa’azi dabam-dabam?’ Idan kana yin abubuwan nan, za ka ji daɗin hidimarka.

MENE NE RA’AYINKA GAME DA HUTU?

16. Ta yaya halin Yesu da manzanninsa game da hutu ya bambanta da na mutane da yawa a yau?

16 Yesu ya san cewa a wasu lokuta shi da manzanninsa suna bukatar su huta. Amma, mutane da yawa a lokacin da kuma a yau suna kamar mawadacin da Yesu ya yi kwatanci da shi. Mutumin ya gaya wa kansa cewa: “Bari ka huta, ka yi ta ci, ka yi ta sha, kana jin daɗinka.” (Luk. 12:19; 2 Tim. 3:4) Mutumin ya fi mai da hankali ga hutu da kuma shaƙatawa. Amma Yesu da manzanninsa ba su sa jin daɗi ya zama abin da ya fi muhimmanci a rayuwarsu ba.

Kasancewa da ra’ayin da ya dace game da yin aiki da kuma hutu zai taimaka mana mu mai da hankali ga yin ayyukan da za su sa mu farin ciki (Ka duba sakin layi na 17) *

17. Yaya ya kamata mu yi amfani da lokacin hutu?

17 A yau, muna ƙoƙari mu yi koyi da Yesu ta wajen yin amfani da lokacin hutu ba don hutawa kawai ba. Amma muna amfani da hakan don mu yi wa mutane wa’azi da kuma halartan taro. Halartan taro da yin wa’azi suna da muhimmanci sosai a gare mu. Saboda haka, muna yin iya ƙoƙarinmu don mu riƙa yin waɗannan abubuwa a bautarmu a kai a kai. (Ibran. 10:​24, 25) Ko a lokacin da muka yi tafiya, muna halartan taro a duk inda muke. Ban da haka, mukan nemi zarafi mu yi wa mutane wa’azi.​—2 Tim. 4:2.

18. Mene ne Sarkinmu Yesu Kristi yake so mu yi?

18 Muna godiya sosai cewa Sarkinmu Yesu Kristi ba ya so mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Kuma ya taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da yin aiki da kuma hutu. (Ibran. 4:15) Yana so mu riƙa hutawa. Ban da haka, yana so mu yi aiki tuƙuru don mu biya bukatunmu kuma mu ji daɗin yin wa’azi. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda Yesu ya ’yantar da mu daga wani irin bauta.

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

^ sakin layi na 5 A Nassosi mun koyi yadda za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da aiki da kuma hutu. Wannan talifin zai taimaka mana mu bincika halinmu game da aiki da kuma hutu. Don a yi hakan, za mu bincika Assabaci da Isra’ilawa suke yi kowane mako a dā.

^ sakin layi na 10 Almajiran Yesu sun daraja ranar Assabaci sosai shi ya sa suka daina yin turaren da za su yi amfani da shi a jana’izar Yesu har sai bayan ranar Assabaci.​—Luk. 23:​55, 56.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTO: Yusufu yakan kai iyalinsa majami’a a ranar Assabaci.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTO: Wani mahaifi da yake aiki don ya biya bukatun iyalinsa yana amfani da lokacin hutu don yin ayyuka da suka shafi ibadarsa, har ma a lokacin da shi da iyalinsa suke hutu.