Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Goyi Bayan Mulkin Allah Yanzu!

Ka Goyi Bayan Mulkin Allah Yanzu!

A ce za a yi ambaliyar ruwa da za ta shafi yankinku. Kuma gwamnati ta yi sanarwa cewa: “KOWA YA BAR NAN! KU GUDU KU NEMI MAFAKA!” Idan kana so ka tsira, me za ka yi? Babu shakka, za ka gudu ka nemi mafaka.

Hakazalika, akwai wani bala’i da ke zuwa kuma zai shafi kowannen mu. Yesu ya kira wannan bala’in “azaba mai zafi.” (Matiyu 24:21) Ba zai yiwu mu kauce wa bala’in nan ba. Amma akwai abin da za mu iya yi don mu kāre kanmu. Me ke nan?

A Huɗubar da Yesu Ya Yi a kan Dutse, ya gaya mana abin da za mu yi. Ya ce: “Ku ci gaba da biɗan Mulkin [Allah] farko, da adalcinsa.” (Matiyu 6:​33, New World Translation) Ta yaya za mu bi wannan umurnin?

Ku biɗi Mulkin Allah farko. Hakan yana nufin cewa za mu ɗauki Mulkin Allah da muhimmanci fiye da kome. (Matiyu 6:​25, 32, 33) Me ya sa? Domin ’yan Adam ba za su iya magance matsalolin duniyar nan ba. Mulkin Allah ne kaɗai zai iya magance su.

Ku biɗi adalcinsa. Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu mu bi dokokin Allah da kuma ƙa’idodinsa. Me ya sa? Domin idan muka ce duk abin da muka ga dama ne za mu yi, hakan zai jefa mu cikin bala’i. (Karin Magana 16:25) Amma idan muka bi ƙa’idodin Allah, za mu amfana kuma za mu faranta wa Allah rai.​—Ishaya 48:​17, 18.

Ku ci gaba da biɗan Mulkin Allah farko, da adalcinsa. Yesu ya ce neman kuɗi zai janye hankalin wasu mutane, domin za su ga kamar dukiyarsu za ta cece su. Wasu kuma za su bar damuwa a kan yadda za su kula da kansu da kuma iyalansu ta hana su biɗan Mulkin Allah.​—Matiyu 6:​19-21, 25-32.

Amma Yesu ya yi alkawari cewa waɗanda suka biɗi Mulkin Allah farko za su sami abin biyan bukata yanzu, kuma za su ji daɗin albarku da yawa a nan gaba.​—Matiyu 6:33.

Ko da yake almajiran Yesu a ƙarni na farko sun biɗi Mulkin Allah farko da adalcinsa, Allah bai kawar da shan wahala a zamaninsu ba. Amma Allah ya kāre su. Ta yaya ya yi hakan?

Bin ƙa’idodin Allah ya kāre su daga matsalolin da suka sami waɗanda suka ƙi bin abin da Allah ya faɗa. Sun yi imani cewa Mulkin Allah zai zo, kuma hakan ya taimaka musu su jimre sa’ad da rayuwa ta yi musu wuya sosai. Ƙari ga haka, Allah ya ba su “ikon da ya fi” na ’yan Adam don su iya jimre matsalolinsu.​—2 Korintiyawa 4:​7-9.

ZA KA BIƊI MULKIN ALLAH FARKO?

Kiristoci a ƙarni na farko sun biɗi Mulkin Allah farko kamar yadda Yesu ya umurce su. Sun yi wa’azin Mulkin Allah a ko’ina a lokacin. (Kolosiyawa 1:23) Akwai waɗanda suke hakan a yau kuwa?

Ƙwarai kuwa! Shaidun Jehobah sun san cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai hallaka wannan mugun zamanin. Shi ya sa suke iya ƙoƙarinsu su bi umurnin da Yesu ya bayar cewa: “A ba da wannan labari mai daɗi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma, sa’an nan ƙarshen ya zo.”​—Matiyu 24:14.

Me za ka yi yanzu da ka ji wannan labari mai daɗi game da Mulkin Allah? Muna ƙarfafa ka ka yi abin da wasu mazaunan birnin Biriya a ƙasar Makidoniya suka yi a ƙarni na farko. Sa’ad da manzo Bulus ya yi musu wa’azin Mulkin Allah, sun “karɓi maganar hannu biyu-biyu.” Sai suka yi ta “binciken rubutacciyar maganar Allah” don su gan ko abin da suka ji gaskiya ne, kuma sun bi abin da suka koya.​—Ayyukan Manzanni 17:​11, 12.

Kai ma za ka iya yin hakan. Idan ka biɗi Mulkin Allah da adalcinsa, za ka sami kāriya yanzu, kuma a nan gaba za ka zauna lafiya, hankalinka a kwance har abada.