Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Dogara ga Jehobah Saꞌad da Ake Cin Zalin Ka

Ka Dogara ga Jehobah Saꞌad da Ake Cin Zalin Ka

Masu cin zali suna iya ji mana rauni kuma su sa mu baƙin ciki. Idan muna jin tsoron yadda suke adawa da bautarmu, hakan yana iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Ta yaya za ka kāre kanka daga masu cin zali?

An ci zalin bayin Jehobah da yawa, amma da taimakon Jehobah sun jimre. (Za 18:17) Alal misali, Esta ta yi magana a madadin Yahudawa don ta fallasa muguntar da Haman yake ƙullawa. (Es 7:1-6) Kafin Esta ta yi hakan, ta yi azumi don ta nuna ta dogara ga Jehobah. (Es 4:14-16) Jehobah ya albarkace ta don matakin da ta ɗauka, ya kāre ta da kuma mutanensa.

Matasa, idan wani yana cin zalinku, ku nemi taimakon Jehobah kuma ku gaya wa wani babba game da matsalar kamar iyayenku. Babu shakka, Jehobah zai taimaka muku kamar yadda ya taimaka wa Esta. Mene ne kuma za ku iya yi don ku jimre da masu cin zali?

KU KALLI BIDIYON NAN RAYUWAR MATASAMENE NE ZAN YI IDAN AKA CI ZALI NA? SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne matasa za su iya koya daga labarin Charlie da Ferin?

  • Mene ne iyaye za su iya koya daga abin da Charlie da Ferin suka faɗa game da taimaka wa yaransu idan ana cin zalin su?