Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Yana Kuɓutar da Waɗanda Suka Fid da Zuciya

Jehobah Yana Kuɓutar da Waɗanda Suka Fid da Zuciya

A wasu lokuta, mukan yi baƙin ciki. Yin baƙin ciki ba ya nufin cewa ba mu da bangaskiya ga Jehobah. Jehobah ma ya faɗa cewa yakan yi baƙin ciki a wasu lokuta. (Fa 6:5, 6) Idan muna baƙin ciki sosai a kowanne lokaci kuma fa?

Ka nemi taimakon Jehobah. Jehobah ya damu da yadda muke ji. Ya san lokacin da muke farin ciki da baƙin ciki. Ya fahimci dalilin da ya sa muke yin wani tunani da kuma abin da ya sa muke jin wani iri. (Za 7:9b) Abin da ya fi muhimmanci shi ne, Jehobah ya damu da mu kuma zai taimaka mana mu jimre idan muna fama da baƙin ciki ko kuma tsananin damuwa.—Za 34:18.

Ka lura da abin da kake tunani a kai. Yin tunanin da bai dace ba zai iya sa mu baƙin ciki har ma ya shafi dangantakarmu da Jehobah. Saboda haka, zai dace mu kāre tunaninmu.—K. Ma 4:23.

KU KALLI BIDIYON NAN YADDA ꞌYANꞌUWANMU SUKE MORE SALAMA DUK DA TSANANIN DAMUWA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne abubuwa ne Nikki ta yi don ta jimre da tsananin damuwa?

  • Me ya sa Nikki ta ga cewa tana bukatar ta nemi taimakon likita?—Mt 9:12

  • A waɗanne hanyoyi ne Nikki ta dogara ga Jehobah ya taimaka mata?