Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Taimaka wa Waɗanda Ba Su da Addini ko Ba Su Yarda da Allah Ba Su Koya Game da Mahaliccinsu

Ku Taimaka wa Waɗanda Ba Su da Addini ko Ba Su Yarda da Allah Ba Su Koya Game da Mahaliccinsu

Ka taɓa yin jinkirin yin waꞌazi ga waɗanda ba su da addini ko ba su yi imani da Allah ba, don kana ganin ba za su saurare ka ba? Idan haka ne, ka tuna cewa akwai waɗanda ba su da addini har da waɗanda ba su yi imani da Allah ba da suka zama Shaidun Jehobah. A yawancin lokuta, abin da suke bukata shi ne, mu ɗan taimaka musu su ga tabbaci cewa akwai Allah.—Ro 1:20; 10:14.

KU KALLI BIDIYON NAN KU TUNA CEWA MARASA BANGASKIYA ZA SU IYA ZAMA MASU BANGASKIYA!WAƊANDA BA SU DAMU DA ADDINI BA, SAI KU AMSA TAMBAYA TA GABA:

Ta yaya labarin Tommaso ya taimaka maka ka kasance da raꞌayin da ya dace game da yin waꞌazi ga waɗanda ba su da addini ko ba su yi imani da Allah ba?