Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Iyaye, Ku Taimaka Wa Yaranku Su Sami Hikimar Allah

Iyaye, Ku Taimaka Wa Yaranku Su Sami Hikimar Allah

Wata hanya mafi kyau da iyaye za su iya sa yaransu su sami hikima daga Allah ita ce, su taimaka musu su amfana a taron ikilisiya. Abin da yara suka gani, suka ji kuma suka faɗa a kalaminsu a taro, za su iya taimaka musu su koya game da Jehobah kuma su zama abokansa na kud da kud. (M.Sh 31:12, 13) Idan ku iyaye ne, ta yaya za ku taimaka wa yaranku su amfana daga taro?

  • Ku yi ƙoƙari ku riƙa halartar taro a Majamiꞌar Mulki.—Za 22:22

  • Ku yi ƙoƙari ku riƙa cuɗanya da ꞌyanꞌuwa a Majamiꞌar Mulki kafin a soma taro da kuma bayan an tashi.—Ibr 10:25

  • Ku tabbata cewa kowa a iyalin yana da littattafan da za a yi amfani da su a taro

  • Ku taimaka wa yaranku su shirya kuma su yi kalami da kansu.—Mt 21:15, 16

  • Ku riƙa maganar da ta dace game da taronmu da kuma umarnan da ake ba mu

  • Ku taimaka wa yaranku su riƙa yin ayyuka kamar share Majamiꞌar Mulki da kuma yi magana da tsofaffi a ikilisiya

Taimaka wa yaranku su kusaci Jehobah ba ƙaramin aiki ba ne kuma a wasu lokuta, zai iya sa mutum ya ji kamar ba zai iya ba. Amma Jehobah zai taimaka muku.—Ish 40:29.

KU KALLI BIDIYON NAN IYAYE, KU DOGARA GA TAIMAKON JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Yaya gajiya ta shafi Zack da Leah?

  • Me ya sa iyaye suke bukata su dogara ga Jehobah?

  • Ta yaya Zack da Leah suka dogara ga Jehobah don su yi nasara?