Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 5

Za Mu Tafi Tare da Ku

Za Mu Tafi Tare da Ku

“Ka bar mu mu bi ka gama mun ji cewa Allah yana tare da ku.”​—ZAK. 8:23.

WAƘA TA 26 Kun Yi Domin Ni

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

Waɗansu tumaki (“mutum goma”) suna ganin gata ne su bi shafaffu (“mutumin Yahuda”) wajen bauta wa Jehobah (Ka duba sakin layi na 1-2)

1. Mene ne Jehobah ya ce zai faru a zamaninmu?

JEHOBAH ya annabta abin da zai faru a zamaninmu cewa: “Mutum goma za su kama hannun rigar mutumin Yahuda. Mutanen nan za su zo daga kowane yare na kowace al’umma suna cewa, ‘Ka bar mu mu bi ka gama mun ji cewa Allah yana tare da ku.’” (Zak. 8:23) “Mutumin Yahuda” a ayar nan yana wakiltar mutanen da Allah ya shafe da ruhu mai tsarki. Ana kuma kiran su “Isra’ila ta Allah.” (Gal. 6:16) “Mutum goma” suna wakiltar waɗanda suke da begen yin rayuwa har abada a duniya. Sun san cewa Jehobah ya albarkaci wannan rukunin shafaffu kuma suna ganin cewa ya dace su bi su wajen bauta wa Jehobah.

2. Ta yaya “mutum goma” suke ‘bin’ shafaffu?

2 Ko da ba zai yiwu a san sunan kowanne cikin shafaffu a duniya a yau ba, * waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya za su iya bin shafaffu. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya ce “mutum goma” za su ‘kama hannun rigar mutumin Yahuda,’ suna cewa: ‘Ka bar mu mu bi ka gama mun ji cewa Allah yana tare da ku.’ Wannan ayar ta ambata mutumin Yahuda guda ɗaya. Amma kalmar nan “ku” tana nufin mutane da yawa. Hakan yana nufin cewa mutumin Yahuda ba mutum ɗaya ba ne kawai amma yana wakiltar rukunin shafaffu. Waɗanda ba shafaffu ba suna bin shafaffu wajen bauta wa Jehobah. Amma, ba sa ɗaukan shafaffu a matsayin shugabansu domin sun san cewa Yesu ne Shugabansu.​—Mat. 23:10.

3. Waɗanne tambayoyi ne za a amsa a wannan talifin?

3 Tun da akwai shafaffu a duniya har yau, wasu suna iya yin tunani: (1) Yaya ya kamata shafaffu su ɗauki kansu? (2) Yaya ya kamata mu bi da waɗanda suke cin gurasa da kuma shan ruwan inabi a taron Tuna da Mutuwar Yesu? (3) Ya kamata mu riƙa damuwa cewa adadin su yana ƙaruwa ne? Za a amsa tambayoyin nan a wannan talifin.

YAYA YA KAMATA SHAFAFFU SU ƊAUKI KANSU?

4. Wane kashedi da ke 1 Korintiyawa 11:​27-29 ne ya kamata shafaffu su yi tunani sosai a kai, kuma me ya sa?

4 Ya kamata shafaffu su yi tunani sosai a kan gargaɗin da ke 1 Korintiyawa 11:​27-29. (Karanta.) Ta yaya wani shafaffe zai ci gurasa kuma ya sha ruwan inabi cikin “rashin cancanta” a taron Tuna Mutuwar Yesu? Zai yi hakan idan yana cin gurasar da shan inabin amma ba ya bin dokokin Jehobah. (Ibran. 6:​4-6; 10:​26-29) Shafaffu sun fahimci cewa wajibi ne su kasance da aminci idan suna so su sami “ladan nasara, wanda shi ne dalilin kiran nan zuwa sama wanda Allah ya yi . . . ta wurin Almasihu Yesu.”​—Filib. 3:​13-16.

5. Yaya ya kamata shafaffu su ɗauki kansu?

5 Ruhun Jehobah yana taimaka wa bayinsa su zama masu tawali’u ba masu fahariya ba. (Afis. 4:​1-3; Kol. 3:​10, 12) Saboda haka, shafaffu ba sa ganin sun fi sauran mutane. Sun san cewa Jehobah ba ya ba shafaffu ruhu mai tsarki fiye da sauran bayinsa. Kuma ba sa ganin sun fi kowa sanin koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ba za su taɓa gaya wa mutane cewa su soma cin gurasar da shan ruwan inabin ba. Maimakon haka, su masu tawali’u ne kuma sun san cewa Jehobah ne kawai zai iya zaɓan mutum ya je sama.

6. Kamar yadda yake a 1 Korintiyawa 4:​7, 8, me ya kamata shafaffu su riƙa yi?

6 Ko da yake shafaffu suna ganin gata ne da aka zaɓe su su je sama, ba sa ɗauka cewa mutane za su riƙa girmama su saboda wannan gatan. (Filib. 2:​2, 3) Kuma sun san cewa Jehobah bai gaya wa kowa ba sa’ad da ya shafe su da ruhu mai tsarki ba. Saboda haka, shafaffe ba zai yi mamaki ba idan wasu ba su gaskata nan da nan cewa an shafe shi ba. Ya tuna cewa Littafi Mai Tsarki ya gaya mana kada mu yi saurin amince da mutum da ya ce Allah ya ba shi wani gata na musamman. (R. Yar. 2:2) Da yake shafaffe ba ya so mutane su riƙa daraja shi fiye da sauran mutane, ba zai gaya wa mutane a karo na farko da ya haɗu da su cewa an shafe shi da ruhu mai tsarki ba. Kuma ba zai yi fahariya game da hakan ba.​—Karanta 1 Korintiyawa 4:​7, 8.

7. Me ya kamata shafaffu su guji yi, kuma me ya sa?

7 Shafaffun Kiristoci ba sa ganin cewa ya kamata su riƙa kasancewa tare da sauran shafaffu kawai ba, kamar dai suna cikin wani rukuni ne. Ba za su nemi wasu shafaffu ba don su tattauna game da gatarsu na zuwa sama ba, ko kuma su haɗu don su yi nazarin Littafi Mai Tsarki su kaɗai ba. (Gal. 1:​15-17) ’Yan’uwa a ikilisiya ba za su kasance da haɗin kai ba idan shafaffu suka yi hakan. Ƙari ga haka, yin hakan zai saɓa wa ruhu mai tsarki da ke taimaka wa mutanen Allah su kasance da salama da kuma haɗin kai.​—Rom. 16:​17, 18.

YAYA YA KAMATA MU BI DA SHAFAFFU?

Bai kamata mu bi da shafaffu ko kuma ’yan’uwa da suke ja-goranci a matsayin taurari ba (Ka duba sakin layi na 8) *

8. Me ya sa ya kamata mu yi hankali da yadda muke bi da waɗanda suke cin gurasa? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

8 Yaya ya kamata mu bi da ’yan’uwa shafaffu? Ba zai dace ba mu riƙa girmama mutum ainun, ko da shi shafaffe ne. (Mat. 23:​8-12) Sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da dattawa, ya ƙarfafa mu mu ‘bi gurbin bangaskiyarsu,’ amma bai ce mu mai da wani ɗan Adam shugabanmu ba. (Ibran. 13:7) Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ce wasu sun isa a girmama su sosai. Amma ya faɗi hakan domin suna aiki tuƙuru wajen yin magana “da koyarwa,” ba domin su shafaffu ba ne. (1 Tim. 5:17) Idan muna yaba wa shafaffu ainun da kuma ɗaukaka su, ba za su ji daɗi ba. * Ban da haka, muna iya sa su zama masu girman kai. (Rom. 12:3) Babu wani a cikinmu da zai so ya sa wani shafaffe ya yi irin wannan babban kuskure!​—Luk. 17:2.

9. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja shafaffu?

9 Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja shafaffu? Bai kamata mu tambaye su yadda suka zama shafaffu ba. Hakan bai shafe mu ba, kuma ba mu da iko mu sani. (1 Tas. 4:11; 2 Tas. 3:11) Ƙari ga haka, bai kamata mu yi tunani cewa mazajensu ko matansu ko iyayensu ko kuma danginsu shafaffu ne ba. Wannan gatan ba gādo ba ne da mutum yake samu daga iyalinsa. Amma Allah ne yake ba mutum gatan. (1 Tas. 2:12) Ya kamata mu guji yin tambayoyin da za su ɓata wa mutane rai. Alal misali, bai kamata mu tambayi matar ɗan’uwan yadda take ji game da yin rayuwa a duniya har abada ba tare da mijinta ba. Ballantana ma, muna da tabbaci cewa a sabuwar duniya, Jehobah zai “ƙosar da kowane mai rai bisa ga bukatarsa.”​—Zab. 145:16.

10. Ta yaya za mu kāre kanmu idan muka guji yin sha’awar mutane?

10 Za mu kāre kanmu idan muka guji daraja shafaffu fiye da sauran ’yan’uwa. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya ce wasu shafaffu za su iya yin rashin aminci. (Mat. 25:​10-12; 2 Bit. 2:​20, 21) Amma idan muka guji yin sha’awar mutane, ba za mu bi mutane ba, har da shafaffu ko sanannu ko kuma waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah. (Yahu. 16) Sa’an nan idan suka yi rashin aminci ko kuma suka daina tarayya da ikilisiya, ba za mu yi rashin bangaskiya ba ko kuma daina bauta wa Jehobah.

SHIN YA KAMATA MU DAMU DA ADADIN SHAFAFFU NE?

11. Mene ne yake faruwa da adadin masu cin gurasar?

11 Shekarun baya, adadin mutanen da suke cin gurasar kuma suke shan ruwan inabin ya ragu. Amma a kwana-kwanan nan, adadin yana ƙaruwa. Ya kamata mu bar hakan ya dame mu? A’a. Bari mu ga abin da ya sa bai kamata mu damu ba.

12. Me ya sa bai kamata mu damu da adadin mutanen da suke cin gurasar ba?

12 “Allah ya san waɗanda suke nasa.” (2 Tim. 2:19) ’Yan’uwa da suke ƙirga adadin mutane da ke cin gurasar ba sa kamar Jehobah domin ba su san ko su waye ne ainihin shafaffu ba. Saboda haka, adadin ya ƙunshi mutanen da suke ganin su shafaffu ne amma Jehobah bai shafe su ba. Alal misali, wasu da suke ci a dā sun daina ci daga baya. Wasu kuma wataƙila suna da wata matsala da ta shafi hankalinsu da ya sa suke ganin za su yi sarauta da Kristi a sama. Hakika, ba za mu iya sanin ainihin adadin shafaffu nawa suka rage a duniya ba.

13. Shin Littafi Mai Tsarki ya faɗi adadin shafaffu da za su rage a duniya sa’ad da aka soma ƙunci mai girma?

13 Shafaffu za su kasance a wurare dabam-dabam a faɗin duniya a lokacin da Yesu zai kai su sama. (Mat. 24:31) Littafi Mai Tsarki ya ce a kwanaki na ƙarshe, shafaffu kaɗan ne za su rage a duniya. (R. Yar. 12:17) Amma bai faɗi adadin da zai rage ba sa’ad da aka soma ƙunci mai girma.

Mene ne ya kamata mu yi idan wani yana cin gurasar? (Ka duba sakin layi na 14)

14. Kamar yadda Romawa 9:​11, 16 suka nuna, me muke bukatar mu sani game da zaɓan shafaffu?

14 Jehobah ne yake yanke shawara a kan lokacin da zai zaɓi shafaffu. (Rom. 8:​28-30) Jehobah ya soma zaɓan shafaffu bayan ya ta da Yesu daga mutuwa. Kamar dai dukan Kiristoci a ƙarni na farko shafaffu ne. Amma shekaru da yawa bayan haka, yawancin mutane da suke da’awa su Kiristoci ne ba su bi Kristi ba. Duk da haka, a waɗannan shekarun, Jehobah ya shafe Kiristoci ƙalilan da suka bi koyarwar Kristi. Yesu ya kwatanta su da alkama da za ta yi girma a cikin ciyawa. (Mat. 13:​24-30) A kwanaki na ƙarshe, Jehobah ya ci gaba da zaɓan mutane da za su kasance cikin shafaffu 144,000. * Saboda haka, idan Allah ya yanke shawara cewa zai zaɓi wasu dab da ƙarshen zamanin nan, bai kamata mu yi shakkar abin da yake yi ba. (Karanta Romawa 9:​11, 16.) * Wajibi ne mu yi hankali don kada mu zama kamar ma’aikata da Yesu ya kwatanta a cikin kwatancinsa. Sun yi gunaguni game da yadda ubangijinsu ya bi da waɗanda suka soma aiki a sa’a ta ƙarshe.​—Mat. 20:​8-15.

15. Shin dukan shafaffu ne suke cikin “bawan nan mai-aminci, mai hikima,” da aka ambata a Matiyu 24:​45-47? Ka bayyana.

15 Ba dukan waɗanda suke da begen zuwa sama ba ne ke cikin “bawan nan mai-aminci, mai hikima” ba. (Karanta Matiyu 24:​45-47.) Kamar yadda Jehobah da Yesu suka yi a ƙarni na farko, suna amfani da ’yan’uwa ƙalilan wajen ciyar da mutane da yawa a yau da kuma koyar da su. Shafaffun Kiristoci kaɗan ne a ƙarni na farko suka rubuta littattafan Matiyu zuwa Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna. A yau, shafaffu kaɗan ne kawai ke da hakkin tanadar wa mutanen Allah “abincinsu a kan lokaci.”

16. Mene ne ka koya a wannan talifin?

16 Mene ne muka koya a wannan talifin? Jehobah ya zaɓi ya sa yawancin bayinsa su rayu har abada a duniya. Kuma zai sa mutane ƙalilan su yi sarauta da Yesu a sama. Jehobah yana yi wa dukan bayinsa albarka, wato “mutumin Yahuda” da kuma “mutum goma.” Kuma ya bukaci dukansu su bi umurni guda kuma su riƙe aminci. Wajibi ne su zama masu tawali’u, kuma su bauta masa da haɗin kai. Ƙari ga haka, dukansu na bukatar su yi aiki tuƙuru don a yi zaman lafiya a cikin ikilisiya. Yayin da ƙarshen zamanin nan yake gabatowa, bari mu ci gaba da bauta wa Jehobah kuma mu riƙa bin Kristi a matsayin “garke ɗaya.”​—Yoh. 10:16.

^ sakin layi na 5 A wannan shekarar, za a yi taron Tuna da Mutuwar Kristi a ranar Talata, 7 ga Afrilu. Yaya ya kamata mu ɗauki waɗanda suka ci gurasar kuma suka sha ruwan inabin a ranar? Ya kamata mu damu cewa adadin masu cin gurasar yana ƙaruwa? Za mu sami amsoshin waɗannan tambayoyi a talifin nan da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta Janairu 2016.

^ sakin layi na 2 Kamar yadda Zabura 87:​5, 6 suka nuna, wataƙila a nan gaba Allah zai bayyana sunayen dukan waɗanda suke sarauta da Yesu a sama.​—Rom. 8:19.

^ sakin layi na 8 Ka duba akwatin nan Ƙauna “Ba Ta Yin Rashin Hankali” da ke Hasumiyar Tsaro ta Janairu, 2016, shafi na 27.

^ sakin layi na 14 Ko da Ayyukan Manzanni 2:33 ta nuna cewa ta wurin Yesu ne aka zubo ruhu mai tsarki, amma Jehobah ne yake zaɓan kowanne mutum.

^ sakin layi na 14 Don ƙarin bayani, ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu, 2007 na Turanci.

WAƘA TA 34 Mu Zama Masu Aminci

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTUNA Shafi na 28: Rashin kunya ne idan ’yan’uwa suka kewaye wani wakilin hedkwatarmu da matarsa don su ɗauki hoto a taron yanki!