Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 6

Jehobah Ubanmu Yana Kaunar Mu Sosai

Jehobah Ubanmu Yana Kaunar Mu Sosai

“Sai ku yi addu’a kamar haka. ‘Ubanmu wanda yake cikin sama.’”​—MAT. 6:9.

WAƘA TA 135 Jehobah Ya Ce: “Ɗana Ka Yi Hikima”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ake bukata a yi kafin a tattauna da sarkin Fasiya?

A CE kana zama a birnin Fasiya wajen shekaru 2,500 da suka shige. Kana so ka tattauna wani batu mai muhimmanci sosai da sarkin, sai ka je daular sarkin a Shushan. Amma kafin ka tattauna da sarkin, dole ne sai ya gayyace ka tukun. Idan ka shiga fādarsa ba tare da gayyata ba, za a kashe ka!​—Esta 4:11.

2. Yaya Jehobah yake so mu ji game da tattaunawa da shi?

2 Muna matuƙar farin ciki cewa Jehobah ba ya kamar wannan sarkin Fasiya! Jehobah ya fi kowane sarki ɗan Adam iko, duk da haka, za mu iya tattaunawa da shi a kowane lokaci. Ba ya so mu ji tsoron tattaunawa da shi. Alal misali, duk da cewa Jehobah yana da manyan laƙabi kamar su, Mahalicci da Mafi Iko da kuma Allah Maɗaukaki, ya ce mu kira shi “Uba” wanda suna ne mai sauƙi. (Mat. 6:9) Muna farin ciki sosai cewa Jehobah yana so mu kusace shi!

3. Me ya sa za mu iya kiran Jehobah Ubanmu, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Ya dace mu kira Jehobah “Uba” domin shi ne ya ba mu rai. (Zab. 36:9) Ya kamata mu yi masa biyayya domin shi Ubanmu ne. Idan muka bi dokokinsa, za mu sami albarka sosai. (Ibran. 12:9) Ɗaya cikin albarkun shi ne yin rayuwa har abada a sama ko kuma a duniya. A yanzu ma muna amfana. A wannan talifin, za a tattauna yadda muka tabbata cewa Jehobah Uba ne mai ƙauna a yanzu da kuma yadda muka san cewa ba zai taɓa yasar da mu a nan gaba ba. Amma da farko, bari mu tattauna dalilin da ya sa muke da tabbaci cewa Ubanmu na sama yana ƙaunar mu sosai kuma yana kula da mu.

JEHOBAH YANA ƘAUNAR MU KUMA YANA KULA DA MU

Jehobah yana so ya kusace mu, yadda uba mai ƙauna yake so ya kusaci yaransa (Ka duba sakin layi na 4)

4. Me ya sa yake yi wa wasu wuya su ɗauki Jehobah a matsayin Ubansu?

4 Yana maka wuya ka ɗauki Jehobah a matsayin Uba? Wasu suna iya ji cewa Jehobah ba ya daraja mu domin ya fi mu girma sosai. Suna shakka cewa Allah Maɗaukaki ya san da su kuma yana kula da su. Amma duk da haka, Ubanmu mai ƙauna ba ya so mu ji hakan. Shi ya ba mu rai kuma yana so mu ƙulla dangantaka da shi. Bayan da manzo Bulus ya ambata wannan gaskiyar, sai ya gaya wa masu sauraronsa a Atina cewa Jehobah “bai yi nesa da kowannenmu ba.” (A. M. 17:​24-29) Jehobah yana so kowannenmu ya tattauna da shi yadda yara suke tattaunawa a sake da iyayensu masu ƙauna.

5. Mene ne muka koya daga labarin wata ’yar’uwa?

5 Yana kuma iya yi wa wasu wuya su ɗauki Jehobah a matsayin Uba domin mahaifinsu bai ƙaunace su ba. Ku yi la’akari da furucin wata ’yar’uwa. Ta ce: “Mahaifina yana min ashar sosai. A lokacin da na soma nazarin Littafi Mai Tsarki, ya yi mini wuya in kusaci Jehobah. Amma ra’ayina ya canja sa’ad da na san Jehobah sosai.” Kai ma kana jin haka kuwa? Idan haka ne, kada ka yi sanyin gwiwa. Sannu a hankali, za ka ɗauki Jehobah a matsayin Uba mafi ƙauna.

6. Kamar yadda Matiyu 11:27 ta nuna, wace hanya ɗaya ce Jehobah ya yi amfani da ita don ya taimake mu mu ɗauke shi a matsayin Uba?

6 Hanya ɗaya da Jehobah ya taimaka mana mu ɗauke shi a matsayin Uba mai ƙauna shi ne ta wajen sa a rubuta furucin Yesu da kuma ayyukansa a cikin Littafi Mai Tsarki. (Karanta Matiyu 11:27.) Yesu ya yi koyi da halayen Ubansa sosai har ya ce: “Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban.” (Yoh. 14:9) Sa’ad da Yesu yake duniya, yana yawan kwatanta Jehobah a matsayin Uba. A littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna kaɗai, Yesu ya kira Jehobah “Uba” wajen sau 200. Me ya sa Yesu ya yi magana sosai game da Jehobah? Dalili ɗaya shi ne domin mutane su kasance da tabbaci cewa Jehobah Uba ne mai ƙauna.​—Yoh. 17:​25, 26.

7. Wane darasi ne muka koya daga Jehobah don yadda ya bi da Ɗansa?

7 Ka yi la’akari da darasin da muka koya daga yadda Jehobah ya bi da Ɗansa. Jehobah yana jin addu’o’in Yesu a kowane lokaci kuma yana amsa su. (Yoh. 11:​41, 42) Ko da wace irin jarrabawa ce Yesu ya fuskanta, ya ji cewa Jehobah ya ƙaunace shi kuma ya taimaka masa.​—Luk. 22:​42, 43.

8. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya biya bukatun Yesu?

8 Yesu ya yarda cewa Ubansa ne ya ba shi rai kuma shi ne yake kula da shi, shi ya sa ya ce: “Saboda [Uba] ne kuma nake rayuwa.” (Yoh. 6:57) Yesu ya dogara sosai ga Ubansa kuma Jehobah ya biya bukatunsa na zahiri. Abu mafi muhimmanci kuma, ya taimaka masa ya kasance da aminci.​—Mat. 4:4.

9. Ta yaya Jehobah ya nuna wa Yesu cewa shi Uba ne mai ƙauna?

9 Domin Jehobah Uba ne mai ƙauna, ya sa Yesu ya san cewa yana goyon bayan sa. (Mat. 26:53; Yoh. 8:16) Ko da yake Jehobah bai kāre Yesu daga dukan abubuwan da suka cutar da shi ba, amma ya taimaka masa ya jimre. Jehobah ya tabbatar wa Yesu da cewa wahalar da zai sha ba za ta jima ba. (Ibran. 12:2) Jehobah ya nuna cewa yana kula da Yesu ta wajen saurarar sa da yi masa tanadi da koyar da shi da kuma goyon bayan sa. (Yoh. 5:20; 8:28) Yanzu, bari mu ga yadda Ubanmu na sama yake kula da mu yadda ya kula da Yesu.

YADDA UBANMU YAKE KULA DA MU

Uba ɗan Adam yana (1) saurarar yaransa da (2) yi musu tanadi da (3) koyar da su da kuma (4) kāre su. Hakazalika, Ubanmu na sama yana kula da mu (Ka duba sakin layi na 10-15) *

10. Kamar yadda Zabura 116:1 ta nuna, ta yaya Jehobah yake nuna cewa yana ƙaunar mu?

10 Jehobah yana jin addu’o’inmu. (Karanta Zabura 66:​19, 20.) Jehobah ba ya so mu riƙa yin addu’a a wasu lokuta kawai, amma ya ce mu riƙa addu’a a kowane lokaci. (1 Tas. 5:17) Za mu iya yin addu’a ga Allah a kowane lokaci, ko da a wane wuri muke. Yana saurarar mu a kowane lokaci. Idan muka san cewa Jehobah yana jin addu’o’inmu, hakan yana sa mu kusace shi. Wani marubucin zabura ya ce: “Ina ƙaunar Yahweh gama yana jin muryata.”​—Zab. 116:1.

11. Ta yaya Jehobah yake amsa addu’o’inmu?

11 Ba jin addu’o’inmu kaɗai Jehobah yake yi ba, amma yana amsa addu’o’in. Manzo Yohanna ya tabbatar mana da cewa: “Idan mun roƙi kome bisa ga nufinsa [Allah], zai saurare mu.” (1 Yoh. 5:​14, 15) Jehobah zai iya amsa addu’o’inmu a hanyar da ba mu yi zato ba. Ya san abin da ya fi dacewa da mu. Saboda haka a wasu lokuta, yana amsa addu’armu nan take ko kuma ya so mu ɗan jira.​—2 Kor. 12:​7-9.

12-13. A waɗanne hanyoyi ne Ubanmu na sama yake yi mana tanadi?

12 Jehobah yana yi mana tanadi. Yana yin abin da yake so dukan ubanni su yi. (1 Tim. 5:8) Yana biyan bukatun zahiri na yaransa. Ba ya so mu riƙa damuwa saboda abinci da tufafi da kuma wurin kwana. (Mat. 6:​32, 33; 7:11) Domin Jehobah Uba ne mai ƙauna, ya yi shiri don mu sami biyan bukatunmu a nan gaba.

13 Abu mafi muhimmanci da Jehobah yake tanada mana shi ne sa mu ƙulla dangantaka mai kyau da shi. Jehobah ya yi amfani da Kalmarsa wajen nuna mana gaskiya game da kansa da nufinsa da manufar rayuwa da kuma abubuwan da za su faru a nan gaba. A lokacin da muka koyi gaskiya, ya taimaka mana ta wajen yin amfani da iyayenmu ko kuma wani mai shela don ya koyar da mu. Kuma ya ci gaba da yin amfani da dattawa a ikilisiya da kuma ʼyan’uwa maza da mata don ya taimaka mana. Bugu da ƙari, Jehobah yana yin amfani da ikilisiyar Kirista don koyar da mu. Jehobah yana yin amfani da waɗannan hanyoyin don ya nuna cewa shi Uba ne mai kula sosai.​—Zab. 32:8.

14. Me ya sa Jehobah yake koyar da mu, kuma yaya yake yin haka?

14 Jehobah yana koyar da mu. Ba ma kamar Yesu domin mu ajizai ne. Saboda haka, Jehobah yana yin amfani da horo don ya koyar da mu a lokacin da hakan ya dace. Kalmarsa ta ce: “Ubangiji yakan horar da duk wanda yake ƙauna.” (Ibran. 12:​6, 7) Jehobah yana horar da mu a hanyoyi da yawa. Alal misali, zai iya yin amfani da abin da muka karanta a Kalmarsa ko muka ji a taro don ya yi mana gyara. Ko kuma zai iya yin amfani da dattawa don ya taimaka mana. Ko da wace hanya ce Jehobah ya yi amfani da ita, ƙauna ce take motsa shi ya yi mana horo.​—Irm. 30:11.

15. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake kāre mu?

15 Jehobah yana taimaka mana mu jimre jarrabobi. Kamar yadda uba yake kula da yaransa a mawuyacin lokaci, Ubanmu na sama yana kula da mu sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Yana yin amfani da ruhunsa don ya kāre dangantakarmu da shi. (Luk. 11:13) Jehobah yana kuma taimaka mana sa’ad da muke baƙin ciki. Alal misali, ya sa mu kasance da bege cewa rayuwa za ta gyaru a nan gaba. Wannan begen yana taimaka mana mu jimre. Ka yi la’akari da wannan: Ko da wane irin mummunar abu ne ya same mu, Ubanmu mai ƙauna zai magance mana shi gabaki ɗaya. Dukan jarrabobin da muke fuskanta za su ƙare wata rana, amma albarkun da Jehobah zai yi mana za su dawwama har abadan abadin.​—2 Kor. 4:​16-18.

UBANMU BA ZAI TAƁA YASAR DA MU BA

16. Mene ne ya faru bayan Adamu ya ƙarya dokar Ubansa mai ƙauna?

16 Yadda Jehobah ya bi da Adamu da Hauwa’u bayan sun ƙarya dokarsa ta nuna irin ƙaunar da yake mana. A lokacin da Adamu ya yi rashin biyayya, ya fitar da kansa da kuma yaran da zai haifa daga iyalin Jehobah. (Rom. 5:12; 7:14) Amma Jehobah ya ɗauki mataki don ya taimaka wa ’yan Adam.

17. Mene ne Jehobah ya yi nan da nan bayan Adamu ya ƙarya dokarsa?

17 Jehobah ya yanke wa Adamu hukunci, amma ya yi alkawari cewa zai taimaka wa yaransa. Nan da nan, ya ce zai sake marabtar ʼyan Adam cikin iyalinsa. (Far. 3:15; Rom. 8:​20, 21) Jehobah ya sa hakan ya yiwu ta wajen aiko da Ɗansa Yesu ya mutu a madadinmu. Da yake ya aiko da Ɗansa ya mutu dominmu, ya nuna cewa yana ƙaunar mu sosai.​—Yoh. 3:16.

Idan mun bijire amma muka tuba, Ubanmu mai ƙauna, Jehobah, yana a shirye ya marabce mu (Ka duba sakin layi na 18)

18. Mene ne ya tabbatar mana da cewa Jehobah yana ƙaunar mu ko da mun bijire?

18 Ko da yake mu ajizai ne, Jehobah yana so mu kasance cikin iyalinsa kuma yana a shirye ya taimaka mana. Za mu iya ɓata masa rai ko kuma mu ɗan bijire daga hanya, amma Jehobah ba ya yasar da mu. Yesu ya yi amfani da kwatancin wani ɗa mubazzari wajen kwatanta yadda Jehobah yake ƙaunar yaransa sosai. (Luk. 15:​11-32) Uban wannan ɗa mubazzari bai fid da rai cewa ɗansa zai dawo ba. Sa’ad da yaron ya dawo gida, ubansa ya marabce shi sosai. Hakazalika, idan mun bijire daga bautar Jehobah kuma mun yi tuban gaske, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Ubanmu mai ƙauna yana a shirye ya marabce mu.

19. Ta yaya Jehobah zai gyara abubuwan da Adamu ya ɓata?

19 Ubanmu zai gyara dukan abubuwan da Adamu ya ɓata. Bayan da Adamu ya yi tawaye, Jehobah ya yanke shawarar zaɓan mutane 144,000 don su zama abokan mulkin Ɗansa a sama. Za su yi aiki a matsayin firistoci da sarakai. A lokacin da Yesu da waɗannan abokansa suka soma mulki, za su sa mutane masu biyayya a duniya su zama kamiltattu. Bayan an yi wa mutane jarrabawa ta ƙarshe, Allah zai ba su rai na har abada. A lokacin, Ubanmu zai yi farin cikin ganin cewa yaransa maza da mata kamiltattu sun cika duniya. Wannan zai zama lokaci mai ban sha’awa sosai!

20. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mu sosai, kuma me za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mu sosai. Shi Uba ne mafi kirki. Yana jin addu’o’inmu kuma yana tanadar da dukan bukatunmu. Yana koyar da mu kuma yana goyon bayan mu. Ƙari ga haka, zai albarkace mu sosai a nan gaba. Muna farin ciki matuƙa cewa Ubanmu Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana kula da mu! A talifi na gaba, za mu tattauna yadda za mu nuna godiya don ƙaunar Jehobah a gare mu.

WAƘA TA 108 Ƙauna ta Gaskiya Daga Allah

^ sakin layi na 5 Muna yawan ɗaukan Jehobah a matsayin Mahaliccinmu da kuma Maɗaukakin Sarki. Amma muna da dalilai masu kyau na ɗaukansa a matsayin Ubanmu mai ƙauna da ke kula da mu. Za a tattauna dalilan a wannan talifin. Za mu kuma ga abin da ya tabbatar mana da cewa Jehobah ba zai taɓa yasar da mu ba.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTUNA: Hotunan nan huɗu sun nuna wani uba da ɗansa: uban yana saurarar ɗansa, yana tanadar da bukatun ’yarsa, yana koyar da ɗansa kuma yana ƙarfafa shi. Hannun Jehobah da aka nuna a hoton ya tuna mana cewa haka ma Jehobah yake kula da mu.