Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 8

Ku Guji Kishi Don Ku Yi Zaman Lafiya

Ku Guji Kishi Don Ku Yi Zaman Lafiya

“Bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu don mu aikata abin da zai kawo salama da ƙarfafawar juna.”​—ROM. 14:19.

WAƘA TA 113 Salamar da Muke Morewa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne ya faru a iyalin Yusufu domin ’yan’uwansa suna kishin sa?

YAKUBU yana ƙaunar dukan yaransa, amma ya fi son ɗansa Yusufu mai shekara 17. Mene ne ’yan’uwan Yusufu suka yi? Sun soma kishin sa sosai, kuma hakan ya sa suka tsane shi. Yusufu bai yi abin da zai sa ’yan’uwansa su tsane shi ba. Duk da haka, sun sayar da shi ya zama bawa kuma suka yi wa mahaifinsu ƙarya cewa dabba ce ta kashe ɗansa da yake ƙauna. Kishinsu ya jawo matsala a iyalin kuma sun sa mahaifinsu baƙin ciki sosai. ​—Far. 37:​3, 4, 27-34.

2. Kamar yadda Galatiyawa 5:​19-21 suka nuna, me ya sa kishi yake da lahani?

2 A Littafi Mai Tsarki, kishi * yana cikin mugayen halayen da aka lissafa a matsayin ‘ayyukan halin mutuntaka’ da za su iya hana mutum shiga Mulkin Allah. (Karanta Galatiyawa 5:​19-21.) A yawanci lokaci, kishi ne ke jawo ɓacin rai da faɗa da kuma yawan fushi.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Misalin ’yan’uwan Yusufu ya nuna mana yadda kishi zai iya ɓata dangantaka kuma ya jawo matsala a iyali. Ko da yake ba za mu yi irin abin da suka yi ba, dukanmu ajizai ne kuma zuciyarmu tana iya yaudarar mu. (Irm. 17:9) Saboda haka, a wasu lokuta muna iya soma kishin wasu. Bari mu tattauna wasu misalai a Littafi Mai Tsarki da za su iya taimaka mana mu ga dalilan da suka sa za mu iya soma kishin wasu. Ƙari ga haka, za mu tattauna wasu hanyoyin da za mu iya guje wa kishi kuma mu yi zaman lafiya.

MENE NE ZAI IYA JAWO KISHI?

4. Me ya sa Filistiyawa suka yi kishin Ishaƙu?

4 Arziki. Ishaƙu mutum ne mai arziki, shi ya sa Filistiyawa suka soma kishin sa. (Far. 26:​12-14) Har ma suka toshe rijiyar da dabobbinsa suke shan ruwa. (Far. 26:​15, 16, 27) Kamar Filistiyawa, wasu mutane a yau suna kishin waɗanda suka fi su arziki. Ba son abin mutanen kaɗai suke yi ba, amma suna so su raba su da kayansu.

5. Me ya sa limaman Yahudawa suke kishin Yesu?

5 Mai farin jini. Limaman Yahudawa sun yi kishin Yesu domin mutane da yawa suna son shi. (Mat. 7:​28, 29) Yesu wakilin Allah ne kuma yana koyar da gaskiya. Duk da haka, limaman sun yaɗa mugayen ƙarairayi game da shi don su ɓata sunansa. (Mar. 15:10; Yoh. 11:​47, 48; 12:​12, 13, 19) Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin? Wajibi ne mu guji yin kishin mutanen da ’yan’uwa a ikilisiya suke ƙauna domin halayensu masu kyau. A maimakon haka, muna so mu yi koyi da su.​—1 Kor. 11:1; 3 Yoh. 11.

6. Ta yaya Diyoturifis ya yi kishi?

6 Gata a ƙungiyar Jehobah. A ƙarni na farko, Diyoturifis ya yi kishin waɗanda suke ja-goranci a ikilisiya. Ya so ya “zama na farko” a tsakanin ’yan’uwa. Don haka, ya soma yaɗa ƙarairayi game da manzo Yohanna da kuma ’yan’uwan da ke ja-goranci. (3 Yoh. 9, 10) Ko da yake ba za mu taɓa yin abin da Diyoturifis ya yi ba, amma muna iya soma kishin wani ɗan’uwa da ya sami gatan da muke sa rai za mu samu, musamman ma idan muna tunani cewa mu ne ya kamata a ba wannan gata.

Zuciyarmu tana kama da ƙasa, halayenmu masu kyau kuma suna kama da fure mai kyau. Amma kishi yana kamar ciyawa. Kishi yana iya hana mu kasancewa da halaye masu kyau kamar ƙauna da tausayi da kuma alheri (Ka duba sakin layi na 7)

7. Ta yaya kishi zai iya shafan mu?

7 Kishi yana kama da ciyawa. Idan kishi ya shiga zuciyarmu, yana iya kasancewa da wuya mu kawar da shi. Halaye kamar su fahariya da kuma son kai suna iya jawo kishi. Ƙari ga haka, kishi yana iya hana mu kasancewa da halaye masu kyau kamar su ƙauna da tausayi da kuma alheri. Da zarar mun ga cewa mun soma kishi, muna bukatar mu kawar da wannan mugun hali daga zuciyarmu. Ta yaya za mu guji yin kishi?

KA ZAMA MAI TAWALI’U DA WADAR ZUCI

Ta yaya za mu guji yin kishi? Da taimakon ruhu mai tsarki, muna iya guje wa kishi kuma mu kasance da wadar zuci da kuma tawali’u (Ka duba sakin layi na 8-9)

8. Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu guji kishi?

8 Muna iya guje wa kishi ta wajen zama masu tawali’u da kuma wadar zuci. Idan muna da waɗannan halaye masu kyau, ba za mu riƙa kishi ba. Tawali’u zai taimaka mana mu guji ɗaukan kanmu da muhimmanci ainun. Mutum mai sauƙin kai ba ya tunanin cewa shi ne ya cancanci samun abu fiye da kowa. (Gal. 6:​3, 4) Mutum mai wadar zuci yana gamsuwa da abin da yake da shi kuma ba ya gwada kansa da wasu. (1 Tim. 6:​7, 8) Idan mutum mai tawali’u ne da kuma wadar zuci, zai yi farin ciki idan ya ga wani ya sami ci gaba.

9. Kamar yadda Galatiyawa 5:16 da Filibiyawa 2:​3, 4 suka nuna, mene ne ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu yi?

9 Muna bukatar taimakon ruhun Allah don mu guji kishi kuma mu zama masu tawali’u da kuma wadar zuci. (Karanta Galatiyawa 5:16; Filibiyawa 2:​3, 4.) Ruhun Jehobah zai taimaka mana mu bincika tunaninmu da kuma muradinmu. Da taimakon ruhu mai tsarki, za mu iya guje wa tunanin da bai dace ba kuma mu soma tunani mai kyau. (Zab. 26:2; 51:10) Bari mu tattauna misalin Musa da kuma Bulus, mutanen da suka yi nasara wajen guje wa kishi.

Wani Ba’isra’ile matashi ya ruga wurin Musa da Joshuwa don ya gaya musu cewa maza biyu a sansanin suna yi kamar su annabawa ne. Joshuwa ya ce Musa ya hana mazan yin hakan, amma Musa ya ƙi. Maimakon haka, ya gaya masa cewa yana farin ciki da Jehobah ya naɗa mazan da ruhunsa. (Ka duba sakin layi na 10)

10. Wane yanayi ne ya jarraba Musa? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

10 Musa yana da iko sosai, kuma bai yi ƙoƙarin hana wasu samun wannan iko ba. Alal misali, wata rana, Jehobah ya ɗauki wasu ruhunsa daga Musa kuma ya ba rukunin dattawan Isra’ilawa da suke tsaye kusa da tantin taro. Jim kaɗan, Musa ya ji labari cewa an ba dattawa biyu da suke tantin taro ruhu mai tsarki kuma sun soma yi kamar annabawa. Mene ne Musa ya yi sa’ad da Yoshuwa ya gaya masa cewa ya hana dattawa biyun? Musa bai yi kishi domin Jehobah ya ba maza biyun nan ruhu mai tsarki ba. A maimakon haka, ya yi farin ciki domin gatan da mazan suka samu. (L. Ƙid. 11:​24-29) Wane darasi ne za mu iya koya daga Musa?

Ta yaya dattawa za su yi koyi da Musa a nuna tawali’u? (Ka duba sakin layi na 11-12) *

11. Ta yaya dattawa za su yi koyi da Musa?

11 Idan kai dattijo ne, shin an taɓa gaya maka ka koyar da wani don ya yi aikin da kake so sosai? Alal misali, wataƙila kana da gatan gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro kowane mako. Amma idan kai mai tawali’u ne kamar Musa, hankalinka ba zai tashi ba idan aka ce ka koyar da wani ɗan’uwa don a nan gaba ya yi aikin da kake yi. A maimakon haka, za ka yi farin cikin taimaka wa ɗan’uwan.

12. Ta yaya Kirista a yau zai iya nuna wadar zuci da kuma tawali’u?

12 Ka yi la’akari da wani yanayi da ’yan’uwa tsofaffi da yawa suke fuskanta. Sun yi shekaru da yawa suna yin hidima a matsayin masu tsara ayyukan rukunin dattawa. Amma da suka kai shekara 80, sun daina wannan hidimar da yardar rai. Ƙari ga haka, da zarar masu kula da da’ira sun kai shekara 70, suna daina hidimarsu kuma a ba su sabuwar hidima. Ban da haka, a ’yan shekaru da suka wuce, masu hidima a Bethel da yawa a faɗin duniya sun soma wata hidima. Waɗannan ’yan’uwa masu aminci ba su tsane ’yan’uwa da suke yin ayyukan da a dā suke yi ba.

13. Mene ne zai iya sa Bulus yin kishin manzannin Yesu 12?

13 Manzo Bulus ya kafa misali mai kyau na kasancewa da wadar zuci da kuma tawali’u. Bulus bai yi kishin mutane ba. Ya yi wa’azi sosai, amma domin shi mai tawali’u ne, ya ce: “Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzannin Yesu, ban ma isa a ce da ni manzo ba.” (1 Kor. 15:​9, 10) Manzannin Yesu guda 12 sun kasance tare da Yesu sa’ad da yake duniya, amma Bulus bai zama Kirista ba har sai bayan da Yesu ya mutu kuma aka ta da shi. Ko da yake daga baya Bulus ya zama ‘manzon Yesu ga waɗanda ba Yahudawa ba,’ amma bai sami gatan kasancewa cikin manzannin Yesu guda 12 ba. (Rom. 11:13; A. M. 1:​21-26) Maimakon ya yi kishin manzanni 12 nan don dangantakarsu da Yesu, Bulus ya kasance da wadar zuci.

14. Mene ne za mu yi idan muna da wadar zuci da kuma tawali’u?

14 Idan muna da wadar zuci kuma mu masu tawali’u ne, za mu riƙa yin koyi da Bulus kuma mu riƙa daraja ikon da Jehobah ya ba wasu. (A. M. 21:​20-26) Jehobah ya shirya dattawa su riƙa ja-goranci. Duk da cewa su ajizai ne, Jehobah yana ɗaukan su a matsayin “baiwa iri-iri.” (Afis. 4:​8, 11) Idan muna daraja dattawa da kuma bin ja-gorancinsu, za mu kusaci Jehobah kuma za mu zauna lafiya da ’yan’uwanmu.

KU YI ƘOƘARI KU YI ABIN DA ZAI KAWO SALAMA

15. Mene ne muke bukatar yi?

15 Ba za mu yi zaman lafiya da ’yan’uwanmu ba idan muna kishin juna. Muna bukatar mu kawar da kishi daga zuciyarmu kuma mu guji sa wasu yin kishi. Muna bukatar mu ɗauki wannan mataki mai muhimmanci idan muna so mu yi biyayya ga Jehobah kuma “mu yi iyakacin ƙoƙarinmu don mu aikata abin da zai kawo salama da ƙarfafawar juna.” (Rom. 14:19) Mene ne za mu iya yi don mu taimaka wa ’yan’uwa su guji kishi, kuma su yi zaman lafiya?

16. Ta yaya za mu taimaka wa mutane su guji yin kishi?

16 Halinmu da kuma ayyukanmu suna iya shafan mutane sosai. Mutanen duniya suna so mu riƙa “taƙama da abubuwan” da muke da su. (1 Yoh. 2:16) Amma wannan halin yana jawo kishi. Muna iya guji sa wasu yin kishi idan muka guji yawan magana game da abubuwan da muke da su ko kuma abubuwan da muke so mu saya. Wata hanya kuma da za mu guji sa wasu yin kishi ita ce ta wajen ɗaukan gatar da aka ba mu yadda ya dace. Idan muna yawan magana game da abubuwan da muke yi, muna iya sa mutane yin kishi. A maimakon haka, idan muka nuna cewa mun damu da mutane kuma muka mai da hankali ga abubuwa masu kyau da suke yi, za mu taimaka musu su kasance da wadar zuci kuma su yi zaman lafiya a ikilisiya.

17. Mene ne ’yan’uwan Yusufu suka yi, kuma me ya sa?

17 Zai yiwu mu daina yin kishi ne? Ƙwarai kuwa! Mu sake yin la’akari da misalin Yusufu. Shekaru da yawa bayan ’yan’uwan Yusufu sun wulaƙanta shi, sun sake haɗuwa da shi a Masar. Kafin Yusufu ya bayyana kansa, ya gwada ’yan’uwansa don ya ga ko sun canja halinsu. Yusufu ya shirya don ya ci abinci da ’yan’uwansa, kuma a wajen ya mai da wa ƙanensa Banyamin hankali fiye da sauran. (Far. 43:​33, 34) Duk da haka, ’yan’uwansa ba su yi kishin Banyamin ba. A maimakon haka, sun nuna cewa sun damu da ɗan’uwansu da kuma mahaifinsu. (Far. 44:​30-34) Da yake ’yan’uwan Yusufu sun kawar da kishi daga zuciyarsu, hakan ya sa sun kawo salama a iyalinsu. (Far. 45:​4, 15) Hakazalika, idan muka guji kishi, za mu taimaka wa iyalinmu da kuma ’yan’uwa a ikilisiya su yi zaman lafiya.

18. Kamar yadda Yaƙub 3:​17, 18 suka nuna, mene ne zai faru idan muka taimaka wa ’yan’uwa su yi zaman lafiya?

18 Jehobah yana so mu guji kishi kuma mu zauna lafiya da mutane. Muna bukatar mu yi ƙoƙari don mu yi abubuwa biyun nan. Kamar yadda muka tattauna a wannan talifin, dukanmu muna iya yin kishi. (Yaƙ. 4:5) Kuma muna kewaye da mutanen duniya da ke ɗaukaka yin kishi. Amma idan muka zama masu tawali’u da wadar zuci da kuma masu nuna godiya, hakan zai taimaka mana mu guji yin kishi. Ƙari ga haka, za mu taimaki ’yan’uwa su yi zaman lafiya kuma su kasance da halaye masu kyau.​—Karanta Yaƙub 3:​17, 18.

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

^ sakin layi na 5 Akwai salama a ƙungiyar Jehobah. Amma idan muka soma kishin juna, hakan zai iya jawo matsala. A wannan talifin, za mu tattauna abin da ke jawo kishi. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda za mu guji wannan mugun hali da kuma yadda za mu yi zaman lafiya.

^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: Kamar yadda aka bayyana a Littafi Mai Tsarki, kishi yana iya sa mutum ya soma son abin wani har ma ya soma tunanin ƙwace abin.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTUNA: Sa’ad da ake taron dattawa, an umurci wani ɗan’uwa tsoho da ke gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro ya koya wa wani dattijo matashi aikin. Ko da yake ɗan’uwan yana son yin aikin, ya goyi bayan shawarar da dattawan suka yanke ta wajen ba ɗan’uwa matashin shawarwari da kuma yaba masa.