Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 9

Bari Jehobah Ya Sanyaya Zuciyarka

Bari Jehobah Ya Sanyaya Zuciyarka

“Sa’ad da damuwoyi sukan yi mini yawa, ta’aziyyarka takan ƙarfafa raina.”​—ZAB. 94:19.

WAƘA TA 44 Addu’ar Wanda Ke Cikin Wahala

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne zai iya sa mu alhini, kuma ta yaya hakan zai iya shafan mu?

KA TAƁA damuwa sosai game da wasu matsaloli? * Wataƙila kana baƙin ciki cewa wasu sun faɗi ko kuma yi abin da ya ɓata maka rai. Kana iya yin alhini game da abin da ka faɗa ko kuma ka yi. Alal misali, mai yiwuwa ka yi kuskure kuma kana damuwa cewa Jehobah ba zai taɓa gafarta maka ba. Ƙari ga haka, kana iya yin tunani cewa domin kana damuwa ainun game da wani abu, hakan ya nuna cewa ba ka da bangaskiya kuma kai mugu ne. Amma hakan gaskiya ne kuwa?

2. Waɗanne misalai ne a Littafi Mai Tsarki suka nuna cewa yin alhini ba ya nufin rashin bangaskiya?

2 Ka yi la’akari da wasu misalai a Littafi Mai Tsarki. Hannatu wadda ta zama mahaifiyar Sama’ila mace ce mai bangaskiya sosai. Duk da haka, ta yi alhini sa’ad da kishiyarta take mata baƙar magana. (1 Sam. 1:7) Manzo Bulus yana da bangaskiya sosai, amma ya yi alhini don “dukan jama’ar masu bi.” (2 Kor. 11:28) Sarki Dauda yana da bangaskiya sosai kuma Jehobah ya ƙaunace shi. (A. M. 13:22) Duk da haka, Dauda ya yi kuskure da ya sa shi yin baƙin ciki sosai. (Zab. 38:4) Jehobah ya ƙarfafa da kuma sanyaya zuciyar kowannensu. Bari mu ga darussa da za mu iya koya daga labarinsu.

DARASI DAGA HANNATU

3. Ta yaya baƙar magana da wasu suka yi game da mu zai iya sa mu baƙin ciki?

3 Muna iya baƙin ciki sosai sa’ad da wasu suka yi mana baƙar magana. Hakan yana iya shafanmu sosai musamman idan abokinmu ko danginmu ne ya ɓata mana rai. Muna iya damuwa cewa hakan zai ɓata dangantakarmu da shi. A wasu lokuta, wataƙila mutumin bai so ya ɓata mana rai ba, amma abin da ya faɗa ya sa mu ji kamar ya soke mu da takobi. (K. Mag. 12:18) Ko kuma wani ya ɓata mana rai da gangan. Hakan ya faru da wata ’yar’uwa matashiya. Ta ce: “Wasu shekaru da suka shige, wata aminiyata ta yi ƙarya game da ni a shafin sada zumunta. Hakan ya ɓata mini rai kuma na yi baƙin ciki. Ban san abin da zai sa aminiyata ta ɓata sunana ba.” Kana iya koyan darasi daga Hannatu idan wani amininka ko danginka ya ɓata maka rai.

4. Waɗanne matsaloli masu wuya ne Hannatu ta fuskanta?

4 Hannatu ta fuskanci wani mawuyacin yanayi. Ta yi shekaru da yawa ba ta iya haihuwa ba. (1 Sam. 1:2) Isra’ilawa da yawa suna ganin cewa macen da ba ta iya haihuwa ba, ba ta da albarkar Allah. Hakan ya sa ta jin kunya sosai. (Far. 30:​1, 2) Ban da haka, akwai wani abu da ya daɗa sa Hannatu baƙin ciki. Tana da wata kishiya mai suna Peninnah da ta haifi yara. Peninnah tana kishin Hannatu sosai kuma tana tsokanarta “kullum domin ta ba ta haushi.” (1 Sam. 1:6) Da farko Hannatu ta yi baƙin ciki sosai game da yanayinta “har ta yi ta kuka ta ƙi cin abinci.” Kuma tana “cike da ɓacin zuciya.” (1 Sam. 1:​7, 10) Ta yaya Hannatu ta sami ƙarfafawa?

5. Ta yaya addu’a ta taimaka wa Hannatu?

5 Hannatu ta gaya wa Jehobah yadda take baƙin ciki. Bayan ta yi hakan, ta bayyana wa Babban Firist Eli yanayinta. Sai ya ce mata: “Ki sauka lafiya. Bari Allah na Isra’ila ya ba ki abin da kika roƙa a wurinsa.” Mene ne sakamakon? Hannatu “ta tafi ta ci abinci, ba ta sāke yin baƙin ciki kuma ba.” (1 Sam. 1:​17, 18) Addu’a ta taimaka mata ta kasance da kwanciyar hankali.

Kamar Hannatu, ta yaya za mu sake soma kasancewa da kwanciyar rai? (Ka duba sakin layi na 6-10)

6. Wane darasi game da addu’a ne za mu iya koya daga Hannatu da kuma Filibiyawa 4:​6, 7?

6 Za mu sake samun kwanciyar hankali idan muka nace da yin addu’a. Hannatu ta ɗauki lokaci sosai tana addu’a ga Jehobah. (1 Sam. 1:12) Mu ma muna iya yin addu’a ga Jehobah na dogon lokaci. Mu gaya masa alhininmu da abin da yake sa mu tsoro da kuma kasawarmu. Ba ma bukatar mu tsara yadda za mu yi addu’ar da manyan kalmomi. A wasu lokuta, muna iya yin kuka sa’ad da muke gaya wa Jehobah matsalolinmu. Duk da haka, Jehobah ba zai taɓa gajiya da saurarar mu ba. Ƙari ga haka, muna bukatar mu tuna da shawarar da ke littafin Filibiyawa 4:​6, 7. (Karanta.) Bulus ya bayyana cewa muna bukatar mu riƙa gode wa Jehobah a addu’a. Da akwai abubuwa da yawa da za mu iya gode wa Jehobah dominsu. Alal misali, muna iya gode masa don halittunsa da rai da ya ba mu da ƙaunarsa gare mu da kuma begenmu. Wane abu ne kuma za mu iya koya daga Hannatu?

7. Mene ne Hannatu da mijinta suke yawan yi?

7 Duk da matsalolin da Hannatu ta fuskanta, tana bin maigidanta a kai a kai zuwa Shiloh don yin ibada. (1 Sam. 1:​1-5) A lokacin da Hannatu ta je mazauni don ibada ne Eli, Babban Firist ya ƙarfafa ta sa’ad da ya ce yana fatan Jehobah ya amsa addu’arta.​—1 Sam. 1:​9, 17.

8. Ta yaya halartan taro zai taimaka mana? Ka bayyana.

8 Muna iya samun kwanciyar hankali idan muka ci gaba da halartan taro. Kafin a soma taro, ana addu’a cewa Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki. Salama tana cikin halayen da ruhu mai tsarki yake sa mu kasance da su. (Gal. 5:22) Idan muka halarci taro duk da cewa muna cikin damuwa, Jehobah da kuma ’yan’uwanmu za su ƙarfafa mu kuma su taimaka mana mu sami kwanciyar rai. Addu’a da kuma halartan taro su ne abubuwa mafi muhimmanci da Jehobah yake amfani da su don ya sanyaya mana zuciya. (Ibran. 10:​24, 25) Ka yi la’akari da wani darasi da za mu iya koya daga labarin Hannatu.

9. Mene ne bai canja ba a yanayin da Hannatu take ciki, amma me ya taimaka mata?

9 Hannatu ba ta daina fuskantar matsaloli nan da nan ba. Sa’ad da ta dawo daga mazauni, ta ci gaba da zama a gidansu tare da kishiyarta Peninnah. Kuma Littafi Mai Tsarki bai ce Peninnah ta canja halinta ba. Don haka, wataƙila Hannatu ta ci gaba da jimre baƙar maganganun Peninnah. Amma Hannatu ta sami kwanciyar hankali. Ka tuna cewa bayan Hannatu ta miƙa matsalarta ga Jehobah, ba ta sake damuwa ba. Ta bar Jehobah ya sanyaya mata zuciya. Daga baya, Jehobah ya amsa addu’ar Hannatu kuma ta haifi yara!​—1 Sam. 1:​19, 20; 2:21.

10. Wane darasi muka koya daga Hannatu?

10 Muna iya kasancewa da kwanciyar rai duk da cewa muna fama da matsaloli. Ko da muna yin addu’a sosai kuma muna halartan taro a kai a kai, ba za mu daina fuskantar wasu matsaloli ba. Amma misalin Hannatu ya koya mana cewa babu abin da zai iya hana Jehobah sanyaya mana zuciya. Jehobah ba zai taɓa mantawa da mu ba, kuma tabbas, zai albarkace mu don amincinmu.​—Ibran. 11:6.

DARASI DAGA MANZO BULUS

11. Waɗanne abubuwa ne za su iya sa Bulus damuwa?

11 Akwai abubuwa da yawa da za su iya sa Bulus alhini. Alal misali, domin yana ƙaunar ’yan’uwansa, ya damu sosai don matsalolin da suke fuskanta. (2 Kor. 2:4; 11:28) Ƙari ga haka, sa’ad da yake wa’azi, mutanen da suke tsananta masa sun yi masa dūka kuma suka saka shi a kurkuku. Ban da haka, ya jimre matsaloli kamar su “talauci.” (Filib. 4:12) Kuma da yake ya fuskanci hatsarin jirgin ruwa aƙalla sau uku, wataƙila hakan ya daɗa sa shi alhini. (2 Kor. 11:​23-27) Me ya taimaka wa Bulus ya daina damuwa?

12. Mene ne ya taimaka wa Bulus ya rage damuwa?

12 Bulus ya damu sosai sa’ad da ’yan’uwansa suka fuskanci matsaloli, amma bai yi ƙoƙarin magance matsalolin da kansa ba. Ya san kasawarsa. Ya shirya don wasu su kula da ikilisiya. Alal misali, ya ba mutane masu aminci kamar Timoti da Titus wannan hakkin. Hakika, aikin da waɗannan ’yan’uwan suka yi ya sa Bulus ya rage damuwa.​—Filib. 2:​19, 20; Tit. 1:​1, 4, 5.

Kamar yadda muka koya daga misalin manzo Bulus, me za mu yi don mu guji yin alhini? (Ka duba sakin layi na 13-15)

13. Ta yaya dattawa za su yi koyi da Bulus?

13 Ka roƙi wasu su taimaka maka. Kamar Bulus, dattawa a yau suna iya damuwa domin matsalolin da ’yan’uwa a ikilisiya ke fuskanta. Amma dattijo ba zai iya taimaka wa dukan ’yan’uwa a ikilisiya ba. Idan ya fahimci cewa ba zai iya taimaka wa dukan ’yan’uwa a ikilisiya ba, hakan zai sa ya nemi taimakon wasu dattawa da suka ƙware kuma zai koyar da matasa su kula da ikilisiya.​—2 Tim. 2:2.

14. Wane abu ne Bulus bai damu da shi ba, kuma me za mu iya koya daga misalinsa?

14 Ka amince cewa kana bukatar ƙarfafawa. Bulus yana da sauƙin kai, don haka, ya nemi taimakon abokansa. Domin abokansa sun ƙarfafa shi, bai damu cewa wasu mutane za su ɗauka cewa ya yi sanyi gwiwa ba. A wasiƙarsa ga Filimon, Bulus ya ce: “Ƙaunarka ta kawo mini farin ciki ainun da kuma ƙarfafawa sosai.” (Fil. 7) Bulus ya ambata ’yan’uwa da yawa da suka ƙarfafa shi sosai sa’ad da yake fama da matsaloli. (Kol. 4:​7-11) Idan muka amince cewa muna bukatar ƙarfafawa, ’yan’uwanmu za su yi farin cikin taimaka mana.

15. Mene ne Bulus ya yi sa’ad da yake fuskantar mawuyacin yanayi?

15 Ka dogara ga Kalmar Allah. Bulus ya san cewa Kalmar Allah za ta ƙarfafa shi. (Rom. 15:4) Za ta kuma taimaka masa ya sami hikimar bi da tsanantawa. (2 Tim. 3:​15, 16) Sa’ad da aka saka shi a kurkuku a karo na biyu a Roma, ya ga cewa mutuwarsa ta kusa. Mene ne ya yi yayin da yake fuskantar wannan mawuyacin yanayi? Ya ce Timoti ya zo wurinsa ba tare da ɓata lokaci ba kuma ya kawo masa ‘littattafai.’ (2 Tim. 4:​6, 7, 9, 13) Me ya sa? Domin wataƙila littattafan sassan Nassosin Ibrananci ne da Bulus zai riƙa yin nazari da su. Idan muka yi koyi da Bulus ta wajen yin nazarin Kalmar Allah a kai a kai, Jehobah zai yi amfani da Kalmarsa don ya sanyaya mana zuciya ko da wace irin matsala ce muke fuskanta.

DARASI DAGA SARKI DAUDA

Kamar Sarki Dauda, me zai taimaka mana idan muka yi zunubi mai tsanani? (Ka duba sakin layi na 16-19)

16. Wace matsala ce Dauda ya jawo wa kansa?

16 Dauda ya damu sosai domin ya yi abin da bai dace ba. Ya yi zina da Bath-sheba, ya sa a kashe mijinta kuma ya yi ƙoƙarin ɓoye laifin da ya yi. (2 Sam. 12:9) Da farko, Dauda bai damu ba sa’ad da zuciyarsa take damunsa don laifin da ya aikata. A sakamakon haka, ya ɓata dangantakarsa da Jehobah, ya yi baƙin ciki sosai har ma da rashin lafiya. (Zab. 32:​3, 4) Mene ne ya taimaka wa Dauda ya magance matsalolin da ya jawo wa kansa, kuma mene ne zai iya taimaka mana idan muka yi zunubi mai tsanani?

17. Ta yaya Zabura 51:​1-4 suka nuna cewa Dauda ya tuba da gaske?

17 Ka nemi gafara. A ƙarshe, Dauda ya yi addu’a ga Jehobah. Ya roƙe shi ya gafarta masa kuma ya gaya masa dukan abin da ya yi. (Karanta Zabura 51:​1-4.) Hakan ya taimaka masa ya kasance da kwanciyar rai da kuma farin ciki! (Zab. 32:​1, 2, 4, 5) Idan ka yi zunubi mai tsanani, kada ka yi ƙoƙarin ɓoye shi. A maimakon haka, ka gaya wa Jehobah laifin da ka yi. Hakan zai sa ka soma samun kwanciyar hankali kuma ka daina damuwa don zunubin. Amma idan kana so ka gyara dangantakarka da Jehobah, ba addu’a kaɗai kake bukatar yi ba.

18. Mene ne Dauda ya yi sa’ad da aka yi masa horo?

18 Ka amince da horo. Jehobah ya tura annabi Nathan don ya tona asirin Dauda. Dauda bai ba da hujja don zunubin da ya yi ba. Nan da nan, ya amince cewa ya yi zunubi, ba ga mijin Bath-sheba kaɗai ba, amma ga Jehobah. Dauda ya amince da horon da Jehobah ya yi masa, kuma Jehobah ya gafarta masa. (2 Sam. 12:​10-14) Idan mun yi zunubi mai tsanani, muna bukatar mu gaya wa dattawa. (Yaƙ. 5:​14, 15) Kuma muna bukatar mu guji ba da hujja. Idan muka amince kuma muka bi horon da aka yi mana, za mu sami kwanciyar rai da kuma farin ciki.

19. Mene ne muke bukatar mu ƙuduri niyyar yi?

19 Ka ƙuduri niyyar cewa ba za ka maimaita laifin ba. Sarki Dauda ya san cewa yana bukatar taimakon Jehobah don ya guji maimaita kuskuren da ya yi. (Zab. 51:​7, 10, 12) Bayan Jehobah ya gafarta wa Dauda, ya ƙuduri niyyar daina yin tunanin da bai dace ba. A sakamakon haka, ya sake kasancewa da kwanciyar rai.

20. Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don yadda Jehobah yake gafarta mana?

20 Sa’ad da muka yi addu’a, muka amince da horo, kuma muka yi iya ƙoƙarinmu don kada mu maimaita zunubin da muka yi, muna nuna godiyarmu ga Jehobah don yadda yake gafarta mana. Idan muka ɗauki waɗannan matakan, za mu sake kasancewa da kwanciyar rai. Wani ɗan’uwa mai suna James da ya yi zunubi mai tsanani ya shaida hakan. Ya ce: “Sa’ad da na gaya wa dattawa zunubin da na yi, na ji kamar an sauƙe kaya mai nauyi daga kaina. Na sake kasancewa da kwanciyar rai.” Hakika, abin ban-ƙarfafa ne sanin cewa Jehobah ‘yana kusa da mu, yakan kuɓutar da masu fid da zuciya’!​—Zab. 34:18.

21. Ta yaya za mu bar Jehobah ya sanyaya mana zuciya?

21 Da yake muna ƙarshen wannan zamanin, za mu fuskanci matsalolin da za su sa mu damuwa. Idan kana cikin damuwa, kada ka ɓata lokaci, ka nemi taimakon Jehobah. Ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau. Ka yi koyi da Hannatu da Bulus da kuma Dauda. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka san abin da ke sa ka alhini. (Zab. 139:23) Ka bari Jehobah ya magance matsalolinka, musamman ma waɗanda suka fi ƙarfinka. Idan ka yi hakan, za ka zama kamar wani marubucin Zabura da ya rera waƙa ga Jehobah, ya ce: ‘Sa’ad da damuwoyi suka yi mini yawa, ta’aziyyarka takan ƙarfafa raina.’​—Zab. 94:19.

WAƘA TA 4 “Jehobah Makiyayina Ne”

^ sakin layi na 5 A wasu lokuta, dukanmu mukan damu don matsaloli da muke fuskanta. A wannan talifin za a tattauna misalan bayin Jehobah guda uku da suka yi fama da alhini. Za a kuma bincika yadda Jehobah ya ƙarfafa su da kuma sanyaya zuciyarsu.

^ sakin layi na 1 MA’ANAR WASU KALMOMI: Alhini yana nufin yawan damuwa ko tsoro game da wani abu. Muna iya jin hakan domin rashin kuɗi ko rashin lafiya ko matsaloli a iyali da dai sauransu. Muna iya damuwa game da kuskure da muka yi a dā ko kuma game da matsaloli da za mu fuskanta a nan gaba.