Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 11

Ka Shirya Yin Baftisma Kuwa?

Ka Shirya Yin Baftisma Kuwa?

“Baftisma kuwa, . . . ta cece ku a yanzu.”​—1 BIT. 3:21.

WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne mutum yake bukatar yi kafin ya soma gina gida?

A CE wani mutum ya yi shirin gina gida. Ya san irin gidan da yake so ya gina. Shin zai dace ya fita ya soma sayan kayan gina gidan kuma ya soma ginin? A’a. Kafin ya soma ginin, akwai abu mai muhimmanci da yake bukatar ya yi. Yana bukatar ya lissafta adadin kuɗin da zai kashe. Me ya sa? Domin yana bukatar ya san ko yana da isasshen kuɗin kammala ginin. Idan ya yi hakan, zai kasance masa da sauƙi ya kammala ginin.

2. Kamar yadda Luka 14:​27-30 suka nuna, mene ne kake bukatar ka yi tunani a kai kafin ka yi baftisma?

2 Ƙaunarka ga Jehobah da kuma yadda kake daraja shi ya motsa ka ka soma tunanin yin baftisma kuwa? Idan haka ne, kana bukatar ka yanke irin shawarar da wannan mai gina gida ya yanke. Me ya sa muka ce hakan? Ka yi la’akari da abin da Yesu ya ce a Luka 14:​28-30. (Karanta.) A ayoyin, Yesu yana magana ne game da abin da zama mabiyinsa ya ƙunsa. Don mu zama mabiyan Yesu, muna bukatar mu kasance da jimiri kuma mu yi sadaukarwa sosai. (Luk. 9:​23-26; 12:​51-53) Don haka, kafin ka yi baftisma, kana bukatar ka yi tunani sosai a kan abin da yin hakan ya ƙunsa. Wannan zai taimaka maka ka ci gaba da bauta wa Allah da aminci bayan ka yi baftisma.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Shin yin baftisma yana da muhimmanci ne? Ƙwarai kuwa! Yin baftisma zai sa ka sami albarka a yanzu da kuma a nan gaba. Bari mu tattauna wasu tambayoyi masu muhimmanci game da baftisma. Hakan zai taimaka maka ka amsa wannan tambayar: “Na yi shirin yin baftisma kuwa?”

ABIN DA YA KAMATA KA SANI

4. (a) Mene ne yin alkawarin bauta wa Allah yake nufi? (b) Kamar yadda Romawa 14:8 ta nuna, mene ne furucin nan “mu na Ubangiji ne” yake nufi?

4 Mene ne alkawarin bauta wa Allah yake nufi? Kafin a yi maka baftisma, dole sai ka yi alkawarin bauta wa Allah. Yin hakan ya ƙunshi yin addu’a ga Jehobah da kuma gaya masa cewa za ka bauta masa har abada. A lokacin da ka yi alkawarin bauta wa Allah, ka ‘ƙi kanka.’ Yanzu kai na Jehobah ne kuma wannan gata ce babba. (Karanta Romawa 14:8.) Ka gaya wa Jehobah cewa daga wannan ranar, za ka mai da hankali ga faranta masa rai ba kanka ba. Yin alkawarin bauta wa Allah yana da muhimmanci sosai. Jehobah ba ya tilasta mana mu yi alkawarin bauta masa. Amma idan muka yi alkawarin, yana so mu cika shi.​—Zab. 116:​12, 14.

5. Wace alaƙa ce ke tsakanin yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma?

5 Wace alaƙa ce ke tsakanin baftisma da kuma alkawarin bauta wa Jehobah? Babu wanda ya san lokacin da ka yi wa Allah alkawarin bauta masa. Amma za a yi maka baftisma a gaban jama’a, wataƙila a taron da’ira ko kuma a taron yanki. Sa’ad da aka yi maka baftisma, ka nuna wa mutane cewa ka riga da ka yi alkawarin bauta wa Jehobah. * Baftismar da ka yi za ta nuna wa mutane cewa kana ƙauna Jehobah da dukan zuciyarka da ranka da hankalinka da kuma ƙarfinka, kuma kana a shirye ka bauta masa har abada.​—Mar. 12:30.

6-7. Kamar yadda 1 Bitrus 3:​18-22 suka nuna, waɗanne dalilai biyu ne suka sa yin baftisma yake da muhimmanci?

6 Shin zai dace ka yi baftisma? Ka yi la’akari da abin da ke 1 Bitrus 3:​18-22. (Karanta.) Jirgin da Nuhu ya gina ya nuna wa mutane cewa yana da bangaskiya. Hakazalika, baftismarka tana nuna wa mutane cewa ka yi alkawarin bauta wa Jehobah. Amma kana bukatar yin baftisma kuwa? E. Bitrus ya faɗi dalilin. Da farko, baftisma tana ‘cetan ku.’ Baftisma za ta iya cetan mu idan muka nuna cewa mun yi imani da Yesu, mun gaskata cewa ya mutu dominmu, ya tashi daga matattu kuma yanzu yana zaune a hannun dama na Allah.

7 Na biyu, yin baftisma zai sa mu kasance da kwanciyar hankali. Idan muka yi alkawarin bauta wa Allah kuma muka yi baftisma, mun ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. Da yake mun tuba da gaske kuma mun yi imani da fansar Yesu, Allah zai gafarta zunubanmu. Hakan zai sa mu kasance da kwanciyar hankali.

8. Mene ne ya kamata ya sa ka yanke shawarar yin baftisma?

8 Me ya kamata ya motsa ka ka yanke shawarar yin baftisma? Yayin da kake yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ka koyi abubuwa da yawa game da Jehobah da abubuwan da yake so da kuma ayyukansa. Abubuwan da ka koya game da shi sun sa ka soma ƙaunar sa sosai. Ƙaunarka ga Jehobah ce za ta motsa ka ka yanke shawarar yin baftisma.

9. Kamar yadda Matiyu 28:​19, 20 suka nuna, mene ne yin baftisma a cikin sunan Uba da Ɗa da kuma ruhu mai tsarki yake nufi?

9 Wani dalili kuma da zai sa ka yanke shawarar yin baftisma shi ne domin ka san abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar kuma ka gaskata da hakan. Ka yi la’akari da abin da Yesu ya faɗa sa’ad da ya umurci mabiyansa su yi wa’azi. (Karanta Matiyu 28:19, 20.) Yesu ya ce waɗanda suke so su yi baftisma za su yi hakan “cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na ruhu mai tsarki.” Mene ne hakan yake nufi? Yana nufin cewa za ka gaskata da abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da Jehobah da Ɗansa Yesu da kuma ruhu mai tsarki da dukan zuciyarka. Wannan gaskiya tana da iko sosai kuma za ta iya ratsa zuciyarka. (Ibran. 4:12) Bari mu tattauna wasu daga cikinsu.

10-11. Waɗanne gaskiya game da Jehobah ne ka koya?

10 Ka yi tunanin lokaci na farko da ka koyi gaskiya game da Allah: Ka koyi cewa sunan Allah ‘Jehobah’ ne. Shi ne “Mafi Ɗaukaka a dukan duniya,” kuma shi ne Allah na gaskiya. (Zab. 83:18; Irm. 10:10) Shi ne Mahalicci kuma “ceto daga wurin Yahweh yake.” (Zab. 3:8; 36:9) Jehobah ya yi shiri don ya cece mu daga zunubi da mutuwa, kuma ya ba mu begen yin rayuwa har abada. (Yoh. 17:3) Alkawarin bauta wa Allah da kuma baftismar da za ka yi zai nuna wa kowa cewa kai Mashaidin Jehobah ne. (Isha. 43:​10-12) Za ka shiga iyalin da ke alfahari cewa suna amsa sunan Allah kuma suna koya wa mutane sunan.​—Zab. 86:12.

11 Hakika, fahimtar abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da Jehobah gata ce babba! Sa’ad da ka amince da wannan gaskiyar, hakan ya motsa ka ka yi alkawarin bauta wa Allah da kuma baftisma.

12-13. Waɗanne gaskiya game da Yesu ne ka koya kuma ka amince da ita?

12 Yaya ka ji sa’ad da ka koyi waɗannan gaskiya game da Yesu? Yesu shi ne mutum na biyu mafi muhimmanci. Shi ne ya ba da ransa don ya fanshe mu. Idan muka nuna ta ayyukanmu cewa mun yi imani da fansar Yesu, za a gafarta zunubanmu kuma za mu ƙulla dangantaka da Allah. Hakan zai sa mu sami rai na har abada. (Yoh. 3:16) Yesu shi ne Babban Firist. Yana so ya taimaka mana mu amfana daga fansar da ya yi kuma mu ƙulla dangantaka mai kyau da Allah. (Ibran. 4:15; 7:​24, 25) A matsayin Sarki Mulkin Allah, Jehobah zai yi amfani da shi don ya tsarkake sunansa, ya halaka mugaye kuma ya sa mutane su more rayuwa a Aljanna. (Mat. 6:​9, 10; R. Yar. 11:15) Ya kamata mu riƙa yin koyi da Yesu. (1 Bit. 2:21) Yesu ya yi amfani da rayuwarsa don yin nufin Jehobah kuma ta hakan, ya kafa misali mai kyau.​—Yoh. 4:34.

13 Idan ka amince da abin ya Littafi Mai Tsarki ya koyar game da Yesu, za ka ƙaunaci Ɗan Allah. Wannan ƙauna za ta motsa ka ka yi amfani da rayuwarka don yin nufin Allah kamar yadda Yesu ya yi. A sakamakon haka, za ka yi alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma.

14-15. Waɗanne gaskiya game da ruhu mai tsarki ne ka koya kuma ka amince da su?

14 Yaya ka ji sa’ad da ka koyi waɗannan gaskiya game da ruhu mai tsarki? Ruhu mai tsarki ba mutum ba ne, amma ikon da Allah yake amfani da shi ne. Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki don ya hure bayinsa su rubuta Littafi Mai Tsarki. Ruhun yana taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki kuma mu yi amfani da abubuwan da muka koya. (Yoh. 14:26; 2 Bit. 1:21) Ta yin amfani da ruhun, Jehobah yana ba mu ‘cikakken iko.’ (2 Kor. 4:7) Ƙari ga haka, ruhun yana ba mu ƙarfin yin wa’azi da guje wa jarrabawa da jimre tsanantawa da kuma kasancewa da ƙarfin gwiwa. Yana taimaka mana mu riƙa nuna halaye masu kyau. (Gal. 5:22) Allah yana ba da ruhunsa ga waɗanda suka dogara gare shi kuma suka roƙe shi ya ba su ruhun.​—Luk. 11:13.

15 Abin ban-ƙarfafa ne sanin cewa Jehobah yana yin amfani da ruhunsa don taimaka wa bayinsa su bauta masa! Idan ka amince da gaskiyar da ka koya game da ruhu mai tsarki a cikin Littafi Mai Tsarki, hakan zai motsa ka ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma.

16. Mene ne muka koya daga abubuwan da muka tattauna?

16 Yin alkawarin bauta wa Allah yana da muhimmanci sosai. Kamar yadda muka gani, kana bukatar ka yi sadaukarwa kuma ka jimre matsalolin da za ka iya fuskanta. Amma albarkun da za ka samu sun fi sadaukarwar da za ka yi. Baftisma za ta cece ka kuma ta sa ka kasance da dangantaka mai kyau da Allah. Ƙauna ga Jehobah ce ya kamata ta motsa ka ka yi baftisma. Kana bukatar ka amince da waɗannan gaskiya da ka koya game da Jehobah da Yesu da kuma ruhu mai tsarki da dukan zuciyarka. Bayan abubuwan da muka tattauna, mece ce amsarka ga wannan tambayar, “Na shirya yin baftisma kuwa?”

ABIN DA YA KAMATA KA YI KAFIN BAFTISMA

17. Waɗanne abubuwa ne mutum yake bukatar yi kafin a yi masa baftisma?

17 Idan kana ganin ka cancanci yin baftisma, babu shakka, ka riga da ka yi abubuwa da yawa don ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. * Da yake ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki, ka koyi abubuwa da yawa game da Jehobah da kuma Yesu. Hakan ya sa ka kasance da bangaskiya. (Ibran. 11:6) Ka amince da alkawarin da Jehobah ya yi a Littafi Mai Tsarki, kuma ka tabbata cewa domin ka yi imani da fansar Yesu, za ka sami ’yanci daga zunubi da kuma mutuwa. Ka tuba daga zunubanka, ka yi nadama domin kura-kurenka kuma ka roƙi Jehobah ya gafarta maka. Ka canja salon rayuwarka kuma ka soma yin rayuwa a hanyar da ke faranta ran Allah. (A. M. 3:19) Kana a shirye ka yi wa mutane wa’azi. Ka cancanci zama mai shela da bai yi baftisma ba kuma ka soma fita wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiya. (Mat. 24:14) Jehobah yana alfahari da kai domin waɗannan matakai da ka ɗauka, kuma kana faranta masa rai sosai.​—K. Mag. 27:11.

18. Mene ne kake bukatar yi kafin ka yi baftisma?

18 Kafin a yi maka baftisma, akwai wasu abubuwa kuma da kake bukatar yi. Kamar yadda muka riga muka koya, kana bukatar ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka yi masa alkawari cewa za ka yi amfani da rayuwarka don yin nufinsa. (1 Bit. 4:2) Bayan haka, ka gaya wa mai tsara ayyukan rukunin dattawan ikilisiyarku cewa kana so ka yi baftisma. Zai gaya wa wasu dattawa su tattauna wasu batutuwa da kai. Kada ka ji tsoron haɗuwa da waɗannan dattawan. ’Yan’uwan sun riga sun san ka kuma suna ƙaunar ka. Za su yi maka wasu tambayoyi don su san ko ka fahimci abubuwan da ka koya a Littafi Mai Tsarki. Suna so su tabbatar da cewa ka fahimci koyarwar kuma ka san muhimmancin yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma. Idan suka ga cewa ka cancanci yin baftisma, za su gaya maka cewa za a yi maka baftisma a babban taro na gaba.

ABIN DA YA KAMATA KA YI BAYAN BAFTISMA

19-20. Mene ne kake bukatar ka yi bayan ka yi baftisma, kuma ta yaya za ka yi hakan?

19 Bayan ka yi baftisma, mene ne kake bukatar yi? * Ka tuna cewa ka yi alkawari ga Jehobah kuma yana so ka cika alkawarinka. Don haka, bayan baftismarka, kana bukatar ka cika alkawarin da ka yi. Ta yaya za ka yi hakan?

20 Ka kusaci ’yan’uwa a ikilisiya. Da yake ka yi baftisma, ka zama ɗaya cikin “ ’yan’uwa masu bin Yesu.” (1 Bit. 2:17) ’Yan’uwa maza da mata a ikilisiya ’yan’uwanka ne. Yayin da kake halartan taro, za ka ƙarfafa dangantakarka da su. Ka riƙa karanta Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kowace rana. (Zab. 1:​1, 2) Bayan ka karanta wani sashen Littafi Mai Tsarki, ka yi tunani sosai a kan abin da ka karanta. Idan ka yi hakan, abin da ka karanta zai ratsa zuciyarka. Ka riƙa yin “addu’a” a kai a kai. (Mat. 26:41) Yin addu’a zai sa ka kusaci Jehobah. Ka ‘miƙa kanka ga al’amuran mulkin’ Allah. (Mat. 6:33) Kana iya yin hakan ta wajen ɗaukan yin wa’azi da muhimmanci. Ta wajen yin wa’azi a kai a kai, bangaskiyarka za ta yi ƙarfi, kuma za ka iya taimaka wa mutane su bi hanyar rai na har abada.​—1 Tim. 4:16.

21. Wace dama ce yin baftisma za ta ba ka?

21 Yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma ita ce shawara mafi muhimmanci da za ka yanke a rayuwa. Gaskiya ne cewa yin hakan ya ƙunshi wasu abubuwa. Amma zai dace ka yi hakan ne? E! Duk matsalolin da za ka fuskanta ‘ba za su daɗe ba.’ (2 Kor. 4:17) Baftismar da ka yi za ta taimaka maka ka yi farin ciki kuma ka sami “ainihin rai” a nan gaba. (1 Tim. 6:19) Don haka, ka yi tunani sosai kuma ka yi addu’a kafin ka amsa wannan tambayar, “Na yi shirin yin baftisma kuwa?”

WAƘA TA 50 Alkawarin Bauta wa Jehobah

^ sakin layi na 5 Kana so ka yi baftisma ne? Idan haka ne, an shirya wannan talifin don ya taimaka maka. Za mu tattauna wasu tambayoyi masu muhimmanci game da yin baftisma. Amsar da za ka ba da za ta taimaka maka ka san ko ka cancanci yin baftisma.

^ sakin layi na 19 Idan ba ka kammala nazarin littattafan nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? da kuma “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah” ba, ka ci gaba da yin nazarin har sai ka kammala littattafan.