Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

“Ga Mu Nan Ka Aike Mu!”

“Ga Mu Nan Ka Aike Mu!”

KANA so ka daɗa ƙwazo a hidimarka ga Jehobah ta wajen ƙaura zuwa wurin da ake bukatar masu shela ne? Idan haka, za ka amfana daga labarin Ɗan’uwa Bergame da matarsa.

Jack da matarsa Marie-Line sun soma hidima ta cikakken lokaci tun shekara ta 1988. Ma’auratan nan suna saurin sabawa da sabon yankinsu, kuma sun amince su je wurare da yawa da aka tura su a yankin Guadeloupe da French Guiana. Reshen ofishinmu na Faransa ne ke kula da yankunan nan. Bari mu yi masu wasu tambayoyi.

Me ya sa kuka soma hidima ta cikakken lokaci?

Marie-Line: A lokacin da nake ƙarama, ni da mahaifiyata da take da ƙwazo sosai muna yawan fita wa’azi a Guadeloupe daga safe har yamma. Ina ƙaunar mutane sosai. Saboda haka, sa’ad da na kammala makaranta a shekara ta 1985, na soma hidimar majagaba.

Jack: Sa’ad da nake matashi, ina yawan cuɗanya da ’yan’uwan da ke hidima ta cikakken lokaci. A lokacin ina yin hidimar majagaba na ɗan lokaci sa’ad da muka sami hutu daga makaranta. A ƙarshen mako, mukan shiga mota mu je yankin da ’yan’uwa majagaba ke wa’azi don yin wa’azi tare da su. Mukan yi wa’azi daga safe har yamma, bayan haka sai mu je kogi mu yi iyo. Mun ji daɗin yin haka sosai!

Bayan da muka yi aure a shekara ta 1988, sai na yi tunani, “Babu wanda muke kula da shi, don haka, za mu iya daɗa ƙwazo a hidimar Jehobah.” Sai ni da matata muka soma hidimar majagaba. Bayan shekara ɗaya da muka halarci makarantar majagaba, mun soma hidimar majagaba ta musamman. Mun ji daɗin yin hidimomi da yawa a Guadeloupe kafin aka tura mu yankin French Guiana.

Kun yi hidima a wurare dabam-dabam shekaru da yawa. Me ya taimaka muku ku saba da hidimar? 

Marie-Line: ’Yan’uwan da ke hidima a Bethel a Guiana sun san cewa muna son furucin da ke Ishaya 6:8. Don haka, a duk lokacin da suka kira mu, sai su ce mana da wasa, “Kun tuna ayar nan da kuka fi so?” Hakan yana sa mu san cewa za a tura mu wani wuri kuma sai mu ce, ‘Ga Mu Nan Ka Aike Mu!’

Ba ma gwada wurin da muka yi hidima a dā da sabon wurin da aka tura mu domin yin hakan zai hana mu jin daɗin hidimarmu. Ƙari ga haka, muna ƙoƙari sosai don mu san ’yan’uwanmu.

Jack: A dā, wasu abokanmu sun yi ƙoƙarin hana mu ƙaura domin suna so mu ci gaba da zama kusa da su. Amma da muka bar Guadeloupe, wani ɗan’uwa ya tuna mana abin da Yesu ya ce a Matiyu 13:38: “Gonar kuma ita ce duniya.” Saboda haka, a duk lokacin da aka tura mu wani wuri, muna tunawa cewa har yanzu muna yin hidima a gonar ko da a ina ne aka tura mu. Ballantana ma, yi wa mutane wa’azi a duk inda suke ita ce ta fi muhimmanci!

Sa’ad da muka isa yankin da aka tura mu, mukan lura cewa ’yan’uwa suna jin daɗin rayuwa. Don haka, muna ƙoƙarin yin rayuwa a wurin yadda suke yi. Gaskiya ne cewa abincin ya bambanta, amma muna cin abincin da mutanen wurin ke ci da ruwan da suke sha kuma muna ɗaukan matakan da suka dace don mu kasance da ƙoshin lafiya. Muna yin iya ƙoƙarinmu mu mai da hankali ga abubuwa masu kyau a sabon yankin da aka tura mu.

Marie-Line: Ƙari ga haka, muna koyan abubuwa da yawa daga ’yan’uwan da ke yankin. Na tuna wani abin da ya faru lokacin da muka isa French Guiana. Ana ruwan sama sosai, don haka, mun so mu jira a daina ruwan kafin mu fita wa’azi. Amma wata ’yar’uwa ta ce mini, “Ba ki yi shirin fita wa’azi ba ne?” Na yi mamaki, sai na ce “Ta yaya za mu fita?” Sai ta ce, “Ki ɗauki laimarki, za mu fita wa’azi da keke.” Ta hakan na koyi riƙe laima sa’ad da nake tuƙa keke. Da a ce ban koyi hakan ba, da ba zan iya wa’azi a lokacin damina ba.

An tura ku hidima a wasu yankuna kusan sau 15. Shin kuna da shawarar da za ku ba waɗanda suke son ƙaura?

Marie-Line: Ƙaura bai da sauƙi. Yana da muhimmanci mutum ya sami wurin da zai iya hutawa bayan ya dawo daga wa’azi.

Jack: Ina yawan yin fenti a ɗakinmu a sabon yankin da muka je. Idan ’yan’uwan da ke hidima a Bethel sun san cewa ba za mu daɗe a wurin ba, sukan ce mini “Ɗan’uwa Jack, kada ka yi wa ɗakinku fenti!”

Matata ta iya kwashe kaya sosai! Tana tsara kome da kyau kuma ta rubuta a kwalin cewa “na ɗaki,” “na bayan gida,” “na kicin” da dai sauransu. Don haka, sa’ad da muka isa sabon gidanmu, yana kasance mana da sauƙi mu saka kayayyakin a wurin da ya dace. Takan rubuta abubuwan da ke cikin kowane kwali don ya yi mana sauƙi mu sami abin da muke bukata.

Marie-Line: Domin mun koyi yadda za mu riƙa tsara abubuwa, hakan ya taimaka mana mu soma yin hidimarmu ba tare da ɓata lokaci ba.

Ta yaya kuke tsara lokacinku don ku sami damar ‘cika hidimarku’?​—2 Tim. 4:5.

Marie-Line: A ranar Litinin mukan huta kuma mu shirya taro. Daga ranar Talata sai mu soma fita wa’azi.

Jack: Ko da yake muna bukatar mu ba da rahoton sa’o’in da muka yi a wa’azi, ba ma mai da hankali ga hakan. Mun fi mai da hankali ga hidimarmu. Idan muka fita wa’azi, muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi wa dukan mutanen da muka haɗu da su wa’azi.

Marie-Line: Alal misali, a duk lokacin da muka je hutu, nakan je da warƙa. Wasu mutane sukan ce mu ba su littattafai, duk da cewa ba mu gaya musu mu Shaidun Jehobah ne ba. Saboda haka, muna mai da hankali sosai ga irin suturar da muke sakawa da kuma halinmu. Domin mutane suna lura da abubuwan da muke yi.

Jack: Ƙari ga haka, mukan kyautata wa maƙwabtanmu. Nakan tsinci datti a ƙasa, na zubar da shara, kuma na share ganyaye da suka faɗo kewaye da gidan. Maƙwabtanmu suna lura da waɗannan abubuwan kuma sukan tambaye ni “Kana da Littafi Mai Tsarki da za ka ba ni?”

Kuna zuwa wa’azi a wuraren da ke da nisa sosai. Shin za ku iya tuna wani abu mai muhimmanci da ya faru da ku?

Jack: A yankin Guiana, wasu wuraren suna da wuyan zuwa sosai. A yawanci lokaci, mukan yi tafiyar mil 370 a cikin mako ɗaya a hanyoyin da ba su da kyau. Mun tuna lokacin da muka je yankin St. Élie da ke Amazon. Mun je yankin a jirgin ruwa da mota mai babban taya kuma mu yi sa’o’i da yawa kafin mu isa yankin. Yawancin mutanen da suke zama a yankin masu haƙa zinariya ne. Don su nuna godiyarsu saboda littattafan da muka ba su, wasu sun ba da gudummawar zinariya! Da yamma, mun nuna musu ɗaya cikin bidiyoyinmu. Mutane da yawa sun zo kallon bidiyon.

Marie-Line: An ba Jack jawabi a taron Tuna da Mutuwar Yesu a yankin Camopi. Don mu je wurin, mun yi tafiyar awa huɗu a jirgin ruwa a Kogin Oyapock. Ba za mu manta da wannan tafiyar ba.

Jack: Wuri marar zurfi a kogin yana da haɗari sosai. Amma ganin yadda ruwan ke gangara yana da kyau. Matuƙin jirgin yana bukatar ya ƙware sosai kafin ya iya bin wurin. Amma mun ji daɗin wannan tafiyar. Ko da yake Shaidun Jehobah guda 6 ne a taron, mutane wajen 50 sun halarci taron har ma da ’yan asalin ƙasar!

Marie-Line: Matasa suna iya moran abubuwan da muka mora a hidimar Jehobah idan suka ƙara ƙwazo. A irin wannan yanayin mutum yana bukatar ya dogara ga Jehobah kuma hakan zai taimaka masa ya kasance da bangaskiya sosai. Muna yawan ganin yadda Jehobah yake taimaka mana.

Kun koyi yaruka da yawa. Kuna da baiwar koyan yaruka ne?

Jack: A’a. Na koyi waɗannan yarukan ne domin akwai bukata sosai. Kafin ma in soma karanta Littafi Mai Tsarki a yaren Sranantongo * a taro, na gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro! Na tambayi wani ɗan’uwa ko sun fahimci abubuwan da na faɗa. Ya ce mini, “A wasu lokuta ba mu fahimci kalmomin ba, amma ka yi ƙoƙari sosai.” Yara sun taimaka mini. A duk lokacin da na yi kuskure, sukan gaya mini, amma manya ba sa ce kome. Na koyi abubuwa da yawa daga yaran.

Marie-Line: A wani yanki, ina da ɗaliban da muke nazari a Faransanci da yaren Portuguese da kuma Sranantongo. Wata ’yar’uwa ta ba ni shawara cewa in soma nazari da yaren da ya fi wuya sai in kammala da wanda na iya sosai. Ba da daɗewa ba, na ga cewa wannan shawarar ta dace sosai.

Akwai ranar da nake so in yi nazari da ɗalibaina a yaren Sranantongo da kuma Portuguese. Sa’ad da na soma nazari da ɗaliba na biyu, ’yar’uwar da muke wa’azi tare ta ce mini, “Marie-Line, kamar akwai matsala fa!” Sai na gane cewa ina yi wa ʼyar Brazil nazari da yaren Sranantongo maimakon da yaren Portuguese!

Mutanen yankin da kuka yi hidima suna ƙaunar ku sosai. Shin kun ƙulla abota da ’yan’uwan?

Jack: Karin Magana 11:25 ta ce: “Mai bayarwa hannu sake zai ƙara yalwata.” Hakan ya sa ba ma jinkirin taimaka wa mutane. Don yadda nake ba da kai don kula da Majami’armu, wasu ’yan’uwa sun ce mini: “Ka bari masu shela a ikilisiya su yi aikin mana.” Amma sai in ce: “Ni ma mai shela ne. Saboda haka, a duk lokacin da ake aiki, ina bin su yin aikin.” Ko da yake dukanmu muna bukatar lokacin hutu, ba ma barin hakan ya hana mu taimaka wa ’yan’uwa.

Marie-Line: Muna yin iya ƙoƙarinmu don mu taimaka wa ’yan’uwanmu. Ta yin hakan, muna sanin lokacin da suke bukatar wani ya kula da yaransu ko kuma ya ɗauko yaran daga makaranta. Mukan tsara ayyukanmu don mu iya taimaka musu. Hakan yana taimaka mana mu kusaci ’yan’uwa.

Waɗanne albarku ne kuka samu don yin hidima a inda ake bukatar masu shela?

Jack: Hidima ta cikakken lokaci ta sa mu sami albarka sosai. Ƙari ga haka, muna jin daɗin kallon abubuwan da Jehobah ya halitta. Ko da yake mun fuskanci matsaloli, muna da kwanciyar hankali domin mun san cewa bayin Jehobah za su taimaka mana a duk inda muke.

Sa’ad da nake matashi, an saka ni a kurkuku a French Guiana domin na ƙi yin aikin soja. Ban taɓa yin tunanin cewa zan koma wannan yankin a matsayin mai wa’azi a ƙasar waje kuma in sami damar zuwa kurkuku don yin wa’azi ba. Babu shakka, Jehobah yana yi wa mutanensa albarka sosai!

Marie-Line: Abin da ya fi sa ni farin ciki shi ne taimaka wa mutane. Muna farin cikin yi wa Jehobah hidima. Wannan hidima ta sa mun kusaci juna a matsayin ma’aurata. A wasu lokuta, mijina yakan tambaye ni ko za mu iya gayyatar ma’aurata da suka yi sanyin gwiwa don mu ci abinci tare. Ina yawan cewa, “Abin da nake tunani ke nan!” A yawanci lokaci, muna tunani iri ɗaya.

Jack: A kwana-kwanan nan, an gano cewa ina da cutar kansa. Ko da yake matata ba ta son jin wannan batu, amma nakan ce mata: “Matata, ban tsufa ba tukun, amma in na rasu, na gamsu da rayuwa domin na yi amfani da rayuwata in yi abin da ya fi muhimmanci. Na bauta wa Jehobah kuma hakan ya sa ni farin ciki.”​—Far. 25:8.

Marie-Line: Jehobah ya ba mu ayyukan da ba mu yi tsammani ba kuma ya taimaka mana mu yi abubuwan da ba mu taɓa yin tunanin za mu iya yi ba. Mun yi abubuwa masu kyau a rayuwa. Muna dogara ga Allah, kuma za mu yi hidima a duk inda ƙungiyar Jehobah ta tura mu!

^ sakin layi na 32 Yaren Sranantongo ya ƙunshi kalmomi daga Turanci da Dutch da Portuguese da wasu yarukan Afirka, kuma bayi ne suka kirkiro yaren.