Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 20

Wane ne “Sarkin Arewa” a Yau?

Wane ne “Sarkin Arewa” a Yau?

“Zai mutu ba mai taimakonsa.”​—DAN. 11:45.

WAƘA TA 95 Muna Samun Ƙarin Haske

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

A YAU, muna da tabbaci sosai cewa muna rayuwa a ƙarshen kwanaki na ƙarshe. Nan ba da jimawa ba, Jehobah da kuma Ɗansa, Yesu za su hallaka dukan mulkokin da ke gāba da Mulkin Allah. Kafin wannan lokacin, sarkin arewa da sarkin kudu za su ci gaba da yaƙi da juna da kuma bayin Allah.

2 A wannan talifin, za mu tattauna annabcin da ke littafin Daniyel 11:40–12:1. Za mu san ko waye ne sarkin arewa, kuma za mu tattauna yadda za mu dogara ga Jehobah duk da ƙalubalen da za mu fuskanta.

SABON SARKIN AREWA

3-4. Waye ne sarkin arewa? Ka bayyana.

3 Bayan da Tarayyar Soviet ta rugurguje a shekara ta 1991, bayin Allah da ke zama a waɗannan yankunan sun “ɗan sami ƙarfafawa,” wato sun ɗan sami ’yanci. (Dan. 11:34) A sakamakon haka, sun sami zarafin yin wa’azi a sake, kuma ba da daɗewa ba, adadin masu shela ya ƙaru sosai a yankunan. Amma bayan ʼyan shekaru, Rasha da magoya bayanta sun zama sarkin arewa. Kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, kafin wata gwamnati ta zama sarkin arewa ko sarkin kudu, dole ta yi abubuwan nan uku: (1) sarakunan za su sarauci ƙasashen da mutanen Allah suke zama ko kuma su tsananta musu. (2) yadda za su bi da mutanen zai nuna cewa sun tsani Allah, kuma (3) za su riƙa yin jayayya da juna.

4 Ga wasu dalilai da suka sa muka ce Rasha da magoya bayanta ne sarkin arewa. (1) Sun kai wa bayin Allah hari ta wajen saka wa aikinsu takunkumi da kuma tsananta wa dubban ʼyan’uwa da ke zama a ƙasashen da suke mulki. (2) Waɗannan abubuwa sun nuna cewa sun tsani Jehobah da mutanensa. (3) Suna yin jayayya da sarkin kudu, wato Amirka da Birtaniya. Yanzu, bari mu tattauna abubuwan da Rasha da magoya bayanta suka yi da suka nuna cewa su ne sarkin arewa.

SARKIN AREWA DA SARKIN KUDU SUN CI GABA DA YAƘAN JUNA

5. Mene ne Daniyel 11:​40-43 yake magana a kai, kuma mene ne ya faru a lokacin?

5 Karanta Daniyel 11:​40-43. Wannan annabcin ya nuna abubuwan da za su faru a kwanaki na ƙarshe. Wannan ayar ta nuna jayayyar da za ta kasance tsakanin sarkin arewa da sarkin kudu. Kamar yadda Daniyel ya annabta, a kwanaki na ƙarshe, sarkin kudu zai yi “yaƙi” da sarkin arewa.​—Dan. 11:40.

6. Mene ne ya nuna cewa sarkin arewa da sarkin kudu suna yaƙan juna?

6 Sarkin arewa da sarkin kudu sun ci gaba da yin yaƙi da juna domin suna so su zama ƙasa mafi iko a duniya. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru bayan Yaƙin Duniya na Biyu, Tarayyar Soviet, wato sarkin arewa da magoya bayanta sun sami iko a kan ƙasashe da yawa a Turai. Hakan ya sa sarkin kudu ya haɗa kai da ƙasashe da yawa, kuma suka kafa Ƙungiyar Ƙawance ta Ƙasashen Yammaci (NATO). Sarkin arewa da sarkin kudu sun ci gaba da kashe kuɗaɗe sosai don sayan manyan makamai. Suna kuma yaƙan juna ta wajen goyon bayan maƙiyan juna a Afirka da Asiya da kuma Amirka ta Tsakiya. A kwana-kwanan nan, Rasha da magoya bayanta sun zama masu iko sosai a duniya. Suna kuma yin amfani da kwamfuta wajen yaƙan sarkin kudu. Sarkin arewa da sarkin kudu suna yin amfani da manhajar kwamfuta don ɓata tattalin arzikin juna da kuma mulkinsu. Kuma kamar yadda Daniyel ya annabta, sarkin arewa ya ci gaba da tsananta wa mutanen Allah.​—Dan. 11:41.

SARKIN AREWA YA SHIGA “ƘASA MAI DARAJA”

7. Mene ne “Ƙasa Mai Daraja”?

7 Littafin Daniyel 11:41 ya ce sarkin arewa zai shiga “Ƙasa Mai Daraja.” Wace ƙasa ke nan? A zamanin dā, ƙasar Isra’ila ce ta fi “dukan ƙasashe albarka.” (Ezek. 20:6) Abin da ya sa ƙasar take da albarka shi ne domin a wurin ne ake bauta ta gaskiya. Tun ranar Fentakos ta 33, “ƙasar” nan ba ƙasar Isra’ila ba ce kuma. Me ya sa? Domin akwai bayin Jehobah a dukan duniya. A maimakon haka, “Ƙasa Mai Daraja” a yau tana nufin ayyukan ibada da mutanen Jehobah suke yi. Alal misali, taronsu da kuma wa’azin bishara.

8. Ta yaya sarkin arewa ya shiga “Ƙasa Mai Daraja”?

8 A kwanaki na ƙarshe, sarkin arewa ya shiga “Ƙasa Mai Daraja” sau da yawa. Alal misali, a lokacin da ƙasar Jamus ce sarkin arewa, musamman a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, sarkin ya shiga “Ƙasa Mai Daraja” ta wajen tsananta wa bayin Allah da kuma kashe su. A lokacin da Tarayyar Soviet ta zama sarkin arewa, wato bayan Yaƙin Duniya na Biyu, sarkin nan ya shiga “Ƙasa Mai Daraja” ta wajen tsananta wa bayin Allah da kuma tilasta musu su bar gidajensu.

9. Ta yaya Rasha da magoya bayanta suka shiga “Ƙasa Mai Daraja” a kwana-kwanan nan?

9 A kwana-kwanan nan, Rasha da magoya bayanta ma sun shiga “Ƙasa Mai Daraja.” A wace hanya ce suka yi hakan? A shekara ta 2017, ƙasar Rasha ta saka wa aikin mutanen Allah takunkumi kuma ta jefa wasu ʼyan’uwanmu cikin kurkuku. Ta kuma haramta yin amfani da littattafanmu, har da juyin Littafi Mai Tsarki na New World Translation. Ƙari ga haka, ta ƙwace Reshen Ofishinmu da wasu Majami’un Mulki da kuma Majami’un Manyan Taro. Bayan da abubuwan nan suka faru ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta faɗa a 2018 cewa Rasha da magoya bayanta ne sarkin arewa. Amma, Shaidun Jehobah ba za su yi adawa da kowace gwamnati ba, kuma ba za su nemi a canja ta ba ko da tana tsananta musu. A maimakon haka, suna bin shawarar da ke Littafi Mai Tsarki da ta ce su riƙa addu’a a madadin “dukan waɗanda suke da manyan matsayi,” musamman sa’ad da suke so su yanke shawarwarin da za su iya shafar ibadarsu.​—1 Tim. 2:​1, 2.

SARKIN AREWA ZAI HALLAKA SARKIN KUDU KUWA?

10. Sarkin arewa zai hallaka sarkin kudu kuwa? Ka bayyana.

10 Annabcin da ke littafin Daniyel 11:​40-45 ya mai da hankali ne musamman a kan abubuwan da sarkin arewa zai yi. Shin hakan yana nufin cewa zai hallaka sarkin kudu? A’a. Sarkin kudu zai kasance “da rai” a lokacin da Jehobah da Yesu za su yi amfani da yaƙin Armageddon don su hallaka dukan gwamnatocin ʼyan Adam. (R. Yar. 19:20) Me ya sa muka tabbata da hakan? Ka yi la’akari da abin da annabcin da ke littafin Daniyel da kuma Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna suka nuna.

A lokacin Armageddon, Mulkin Allah da aka kamanta da dutse, zai kawo ƙarshen sarautar ’yan Adam da aka kamanta da babban gunki (Ka duba sakin layi na 11)

11. Mene ne Daniyel 2:​43-45 yake nufi? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

11 Karanta Daniyel 2:​43-45. Annabi Daniyel ya kwatanta gwamnatoci dabam-dabam na ʼyan Adam waɗanda abubuwan da suka yi ya shafi bayin Allah. Ya kwatanta su da sassa dabam-dabam na wani babban gunki. Ƙafafun gunkin na baƙin ƙarfe ne da aka gauraye da laƙa. Kuma ƙafafun na wakiltar mulkin Amirka da Birtaniya. Annabcin ya nuna cewa Amirka da Birtaniya za su ci gaba da mulki har lokacin da Allah zai hallaka dukan gwamnatocin ʼyan Adam.

12. Wane ne kai na bakwai na dabbar yake wakilta, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?

12 Manzo Yohanna ya kuma kwatanta gwamnatoci dabam-dabam waɗanda mulkinsu ya shafi mutanen Allah. A annabcin Yohanna, gwamnatocin nan suna kamar dabba mai kawuna bakwai. Kai na bakwai na dabbar yana wakiltar mulkin Amirka da Birtaniya. Hakan yana da muhimmanci domin wannan kai shi ne na ƙarshe. Kai na bakwai na dabbar ne zai riƙa mulki a lokacin da Yesu da rundunarsa na sama za su zo su hallaka shi da dabbar gabaki ɗaya. *​—R. Yar. 13:​1, 2; 17:​13, 14.

MENE NE SARKIN AREWA ZAI YI NAN BA DA DAƊEWA BA?

13-14. Wane ne Gog na “yankin Magog,” kuma me zai sa ya kai wa bayin Allah hari?

13 Annabcin da Ezekiyel ya yi ya nuna abin da zai iya faruwa kafin a hallaka sarkin arewa da sarkin kudu. Idan annabcin da ke Ezekiyel 38:​10-23 da Daniyel 2:​43-45; 11:44–12:1 da kuma Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 16:​13-16, 21 suna magana ne game da abu guda, to ga abubuwan da za su iya faruwa.

14 Bayan an soma ƙunci mai girma, “dukan sarakunan duniya” za su haɗa kai. (R. Yar. 16:​13, 14; 19:19) Littafi Mai Tsarki ya kira sarakunan nan da suka haɗa kai Gog na “yankin Magog.” (Ezek. 38:2) Za su kai wa mutanen Allah hari na ƙarshe, suna sa rai cewa za su hallaka su. Me zai sa su kai wannan harin? A wahayin da manzo Yohanna ya gani game da wannan lokaci, ya ce manya-manyan ƙanƙara za su faɗo a kan magabtan Allah. Ƙanƙarar nan za ta iya wakiltar saƙon hukunci da bayin Allah za su riƙa sanarwa. Mai yiwuwa wannan saƙon zai sa Gog na yankin Magog ya kai wa mutanen Allah hari da nufin hallaka su.​—R. Yar. 16:21.

15-16. (a) Wane abu ne ake kwatantawa a littafin Daniyel 11:​44, 45? (b) Me zai faru da sarkin arewa da kuma sauran sarakunan duniya?

15 Wataƙila wannan saƙon hukunci da kuma hari na ƙarshe da za a kai wa bayin Allah ne aka kwatanta a Daniyel 11:​44, 45. (Karanta.) A annabcin, Daniyel ya ce labari “daga gabas da arewa” zai firgita sarkin arewa kuma zai sa shi “fushi.” Sarkin arewa yana so ya “kakkashe” mutane da yawa. Da alama cewa mutane da yawa da aka ambata bayin Jehobah ne. * Wataƙila Daniyel yana kwatanta hari na ƙarshe da za a kai wa bayin Allah.

16 A lokacin da sarkin arewa da sauran sarakunan duniya suka kai wa bayin Allah hari, hakan zai sa Jehobah fushi sosai kuma zai sa a soma yaƙin Armageddon. (R. Yar. 16:​14, 16) A wannan lokacin, za a hallaka sarkin arewa da sauran sarakunan duniya kuma ba zai sami “mai taimako” ba.​—Dan. 11:45.

A lokacin yaƙin Armageddon, Yesu da rundunarsa za su hallaka Shaiɗan da magoya bayansa kuma za su ceci bayin Jehobah (Ka duba sakin layi na 17)

17. Waye ne Mikayel da aka ambata a Daniyel 12:​1, kuma mene ne zai yi?

17 Littafin Daniyel sura 12 ta ba da ƙarin haske a kan yadda za a hallaka sarkin arewa da sauran sarakunan duniya da kuma yadda za mu sami ceto. (Karanta Daniyel 12:1.) Mene ne ma’anar ayar nan? Mikayel ko Mika’ilu wani suna ne da ake kiran Yesu Sarkinmu. Ya soma ‘ɗaukan mataki’ don ya kāre bayin Allah tun shekara ta 1914 sa’ad da aka kafa mulkin Allah. Nan ba da jimawa ba, zai “ɗauki mataki,” wato zai hallaka maƙiyansa a yaƙin Armageddon. Wannan yaƙin zai zama abu na ƙarshe da zai faru kuma Daniyel ya kira shi “kwanakin azaba” irin wanda ba a taɓa yi ba. A annabcin da Yohanna ya yi da aka rubuta a littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna, ya kira lokacin nan lokacin “azaba . . . mai zafi,” ko ƙunci mai girma.​—R. Yar. 6:2; 7:14.

ZA A RUBUTA SUNANKA A “LITTAFIN” KUWA?

18. Me ya sa bai kamata mu ji tsoro don abubuwan da za su faru a nan gaba ba?

18 Bai kamata mu ji tsoro ba domin Daniyel da Yohanna sun tabbatar mana da cewa Jehobah da kuma Yesu za su ceci bayinsu a wannan lokacin ƙunci mai girma. Daniyel ya ce za a ‘rubuta sunan’ waɗanda suka tsira a “cikin littafin.” (Dan. 12:1) Mene ne muke bukatar mu yi don a rubuta sunayenmu a cikin littafin nan? Dole mu nuna cewa mun yi imani da Yesu wanda shi ne Ɗan Rago na Allah. (Yoh. 1:29) Muna bukatar mu yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma mu yi baftisma. (1 Bit. 3:21) Wajibi ne mu goyi bayan Mulkin Allah ta wajen taimaka wa mutane su koya game da Jehobah.

19. Me ya kamata mu yi yanzu, kuma me ya sa?

19 Yanzu ne lokacin da ya dace mu yi imani ga Jehobah kuma mu goyi bayan ƙungiyarsa. Yanzu ne lokacin da ya dace mu goyi bayan Mulkin Allah. Idan mun yi hakan, Jehobah zai cece mu a lokacin da zai yi amfani da Mulkinsa don ya hallaka sarkin arewa da sarkin kudu.

WAƘA TA 149 Waƙar Nasara

^ sakin layi na 5 Wane ne “sarkin arewa” a yau, kuma ta yaya za a hallaka shi? Amsoshin waɗannan tambayoyin za su ƙarfafa bangaskiyarmu, su kuma sa mu kasance a shirye don jarrabawar da za mu fuskanta nan ba da daɗewa ba.

^ sakin layi na 12 Domin samun cikakken bayani game da littafin Daniyel 2:​36-45 da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:​1, 2, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 2012, shafuffuka na 7-19.