Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 28

Ka Tabbata da Abin da Ka Yi Imani da Shi?

Ka Tabbata da Abin da Ka Yi Imani da Shi?

“Ka ci gaba da abin da ka koya, ka kuma tabbatar da gaskiyar koyarwar.”​—2 TIM. 3:14.

WAƘA TA 56 Ka Riƙe Gaskiya

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mece ce kalmar nan “gaskiya” take nufi?

“TA YAYA ka koyi gaskiya?” “Iyayenka Shaidun Jehobah ne?” “Yaushe ne ka soma bauta wa Jehobah?” Wataƙila an taɓa yi maka irin waɗannan tambayoyin. Amma mece ce kalmar nan “gaskiya” take nufi? A yawancin lokuta, tana nufin abubuwan da muka yi imani da su da yadda muke bauta wa Allah da kuma salon rayuwarmu. Mutane da suke cikin “gaskiya” sun san koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma suna bin ƙa’idodinsa. Saboda haka, ba sa amincewa da koyarwar ƙarya kuma suna jin daɗin rayuwa, duk da cewa akwai mugunta a ko’ina.​—Yoh. 8:32.

2. Kamar yadda Yohanna 13:​34, 35 suka nuna, me zai iya sa mutane su soma bauta wa Allah?

2 Me ya sa ka soma bauta wa Jehobah? Wataƙila halin kirki na Shaidun Jehobah ne ya sa ka soma yin hakan. (1 Bit. 2:12) Ko kuma wataƙila yadda suke nuna ƙauna ne. Mutane da yawa sun lura da hakan a lokaci na farko da suka halarci taronmu. Kuma ƙaunar ce suka fi tunawa da ita ba jawabin da aka yi ba. Wannan ba abin mamaki ba ne domin Yesu ya ce za a san almajiransa ta ƙauna da suke nuna wa juna. (Karanta Yohanna 13:​34, 35.) Amma akwai ƙarin abubuwa da muke bukatar mu yi don mu ƙarfafa bangaskiyarmu.

3. Me zai faru idan mun kasance da bangaskiya kawai don ƙauna da mutanen Allah suke nuna wa juna?

3 Bai kamata mu kasance da bangaskiya don ƙaunar da mutanen Allah suke nuna wa juna kawai ba. Me ya sa? Don muna iya daina bauta wa Jehobah idan wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa, wataƙila dattijo ko majagaba ya yi zunubi mai tsanani. Muna kuma iya yin hakan idan wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ɓata mana rai, ko wani ya yi ridda, kuma ya ce muna koyar da ƙarya. Saboda haka, idan kana so ka kasance da bangaskiya sosai, wajibi ne ka ƙulla abota na kud da kud da Jehobah. Idan bangaskiyarka ga Allah ta dangana ga abin da wasu suke yi ba don kana da dangantaka da Jehobah ba, bangaskiyarka ba za ta yi ƙarfi ba. Ra’ayinka game da Jehobah da mutanensa zai taimaka maka ka kasance da bangaskiya. Amma yana da muhimmanci ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, ka fahimci abin da kake koya kuma ka yi bincike. Yin hakan zai sa ka tabbatar wa kanka cewa abin da kake koya game da Jehobah gaskiya ne.​—Rom. 12:2.

4. Kamar yadda Matiyu 13:​3-6, 20, 21 suka nuna, mene ne wasu suka yi sa’ad da aka jarraba bangaskiyarsu?

4 Yesu ya ce wasu za su yi “farin ciki” don sun koyi gaskiya, amma bangaskiyarsu za ta yi yaushi sa’ad da aka jarraba su. (Karanta Matiyu 13:​3-6, 20, 21.) Wataƙila ba su san cewa za su fuskanci ƙalubale idan sun zama mabiyan Yesu ba. (Mat. 16:24) Ko kuwa suna ganin cewa ba za su taɓa fuskantar matsaloli ba idan sun suna bauta wa Jehobah. Amma dole ne mu fuskanci matsaloli a wannan rayuwar. Yanayinmu zai iya canjawa, kuma hakan zai sa mu soma baƙin ciki.​—Zab. 6:6; M. Wa. 9:11.

5. Ta yaya yawancin ’yan’uwanmu suke nuna cewa abin da suka yi imani da shi gaskiya ne?

5 Yawancin ’yan’uwanmu suna da tabbaci cewa abin da suka yi imani da shi gaskiya ne. Me ya sa muka ce hakan? Domin suna ci gaba da bauta wa Jehobah ko da wani ɗan’uwa a ikilisiya ya yi zunubi. (Zab. 119:165) A duk lokacin da suka fuskanci ƙalubale, bangaskiyarsu tana daɗa ƙarfi. (Yaƙ. 1:​2-4) Ta yaya za ka kasance da irin wannan bangaskiyar?

KA SAN ALLAH SOSAI

6. Bangaskiyar Kiristoci a dā ta dangana a kan me?

6 Kiristoci a ƙarni na farko suna da bangaskiya sosai don sun san Nassosi da kuma koyarwar Yesu Kristi, wanda shi ne “labarin nan mai daɗi dominku.” (Gal. 2:5) Wannan gaskiyar ita ce dukan abubuwan da muka yi imani da su. Abubuwan nan sun haɗa da gaskiya game da fansar da Yesu ya yi da kuma tashinsa daga matattu. Manzo Bulus ya kasance da tabbaci cewa waɗannan koyarwar gaskiya ne. Me ya sa? Domin ya yi amfani da Nassosi don ya yi “musu bayani, yana kuma tabbatar musu cewa [ya wajaba] Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu.” (A. M. 17:​2, 3) Kiristoci a ƙarni na farko sun amince da wannan koyarwar kuma sun dogara ga ruhu mai tsarki ya taimaka musu su fahimci Kalmar Allah. Sun yi bincike don su tabbatar wa kansu cewa koyarwar daga Littafi Mai Tsarki ne. (A. M. 17:​11, 12; Ibran. 5:14) Bangaskiyarsu ba ta dangana ga yadda suke ji ba kawai ko kuma don suna farin ciki sa’ad da suka yi cuɗanya da ’yan’uwansu. Maimakon haka, sun kasance da bangaskiya don sun ‘san Allah’ sosai.​—Kol. 1:​9, 10.

7. Ta yaya bangaskiyarmu za ta taimaka mana?

7 Gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah ba ta canjawa. (Zab. 119:160) Alal misali, ba ta canjawa idan wani ɗan’uwa ya ɓata mana rai ko kuma ya yi zunubi mai tsanani. Kuma ba ta canjawa sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Saboda haka, ya kamata mu san koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai, kuma mu tabbatar wa kanmu cewa koyarwar gaskiya ce. Idan muna da bangaskiya sosai, za mu kasance da aminci ga Jehobah sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Me za ka yi don ka ci gaba da bauta wa Jehobah?

KA TABBATAR DA GASKIYA

8. Kamar yadda 2 Timoti 3:​14, 15 suka nuna, me ya taimaka wa Timoti ya san cewa abin da ke Littafi Mai Tsarki gaskiya ne?

Timoti ya kasance da tabbaci cewa abin da ya yi imani da shi gaskiya ne. Ta yaya? (Karanta 2 Timoti 3:​14, 15.) Mahaifiyarsa da kakarsa ce suka fara koya masa “kalmomin Allah masu tsarki.” Amma babu shakka, shi ma ya keɓe lokaci don ya yi nazarin waɗannan kalmomin Allah. Saboda haka, ya “tabbatar da gaskiyar koyarwar.” Daga baya, Timoti da mahaifiyarsa da kakarsa suka zama Kiristoci. Babu shakka, abin da ya taimaka wa Timoti shi ne ƙauna da mabiyan Yesu suka nuna masa. Ban da haka, yana son yin cuɗanya da ’yan’uwan da ke ikilisiya, ya kuma taimaka musu. (Filib. 2:​19, 20) Ba don yana ƙaunar mutane ba ne ya sa ya kasance da bangaskiya ba, amma ya amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma hakan ya sa ya zama abokin Jehobah. Wajibi ne kai ma ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ka amince cewa koyarwar gaskiya ce.

9. Waɗanne koyarwa uku masu muhimmanci ne kake bukatar ka tabbatar wa kanka?

9 Kana bukatar ka tabbatar wa kanka da gaskiyar nan guda uku. Na farko, kana bukatar ka amince cewa Jehobah ne ya halicci dukan abubuwa. (Fit. 3:​14, 15; Ibran. 3:4; R. Yar. 4:11) Na biyu, wajibi ne ka tabbatar wa kanka cewa Littafi Mai Tsarki saƙon Allah ne ga ’yan Adam. (2 Tim. 3:​16, 17) Na uku, kana bukatar ka tabbatar wa kanka cewa Jehobah yana da rukunin mutane masu bauta masa da Yesu ke yi wa ja-goranci. Kuma Shaidun Jehobah ne wannan rukunin. (Isha. 43:​10-12; Yoh. 14:6; A. M. 15:14) Ba ka bukatar ka san kome game da Littafi Mai Tsarki kafin ka tabbatar wa kanka waɗannan abubuwa. Maƙasudinka shi ne ka yi amfani da “hankalinka” don ka tabbatar wa kanka cewa abin da ka yi imani da shi gaskiya ne.​—Rom. 12:​1, New World Translation.

KA TAIMAKA WA MUTANE SU KASANCE DA TABBACI

10. Ban da sanin gaskiya, me muke bukatar mu yi?

10 Muddin ka tabbatar wa kanka cewa waɗannan koyarwa uku gaskiya ne, ya kamata ka yi amfani da Nassosi don ka sa mutane su amince da koyarwar. Me ya sa? Da yake mu mabiyan Yesu ne, muna da hakkin koya wa mutanen da za su saurare mu gaskiyar Kalmar Allah. * (1 Tim. 4:16) Muna ƙarfafa bangaskiyarmu yayin da muke koya wa mutane wannan gaskiyar.

11. Ta yaya za mu iya yin koyi da manzo Bulus?

11 Sa’ad da manzo Bulus yake koyar da mutane yana ƙoƙarin sa su yi imani game da “Yesu ta hanyar Koyarwar Musa da littattafan annabawa.” (A. M. 28:23) Ta yaya za mu iya yin koyi da Bulus sa’ad da muke koyar da mutane? Bai kamata mu riƙa gaya musu abubuwan da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa kawai ba. Wajibi ne mu taimaka wa ɗalibanmu su yi nazari kuma su yi tunani sosai game da abin da suka koya daga Littafi Mai Tsarki. Muna so su bauta wa Jehobah ba don suna daraja mu ba, amma domin sun tabbatar wa kansu cewa abin da suke koya game da Allah gaskiya ne.

Iyaye, ku taimaka wa yaranku su kasance da bangaskiya ta wajen koya musu “abubuwan Allah masu wuyar ganewa” (Ka duba sakin layi na 12-13) *

12-13. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su ci gaba da bauta wa Jehobah?

12 Iyaye, babu shakka kuna son yaranku su ci gaba da bauta wa Jehobah. Kuna iya tunani cewa idan suna da abokan kirki a ikilisiya, suna iya kasancewa da bangaskiya sosai. Amma, idan kuna son yaranku su tabbata cewa abin da suke koya gaskiya ne, ba abokan kirki kawai suke bukata ba. Suna bukatar su ƙulla abota da Allah kuma su tabbatar wa kansu cewa abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne.

13 Idan iyaye suna so su koya wa yaransu game da Allah, wajibi ne su ma su riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. Kuma su riƙa bimbini a kan abin da suka koya. Sa’an nan za su iya koya yaransu su yi hakan. Suna bukatar su koya wa yaransu yadda za su riƙa yin amfani da littattafan bincike kamar yadda suke koya wa ɗalibansu. Idan suka yi hakan, za su taimaka wa yaransu su ƙaunaci Jehobah kuma su amince cewa yana amfani da “bawan nan mai aminci, mai hikima” don ya taimaka mana mu fahimci Kalmarsa. (Mat. 24:​45-47) Iyaye, kada ku riƙa koya wa yaranku abubuwa masu sauƙi kawai a Littafi Mai Tsarki. Ku taimaka musu su kasance da bangaskiya sosai ta wajen koya musu “abubuwan Allah masu wuyar ganewa” daidai da shekarunsu da iyawarsu.​—1 Kor. 2:10.

KU RIƘA NAZARIN ANNABCIN DA KE LITTAFI MAI TSARKI

14. Me ya sa ya kamata mu yi nazarin annabcin da ke Littafi Mai Tsarki? (Ka duba akwatin nan “Za Ka Iya Bayyana Waɗannan Annabci Ne?”)

14 Annabcin da ke Kalmar Allah yana da muhimmanci don yana taimaka mana mu kasance da bangaskiya ga Jehobah. Wane annabci ne ya ƙarfafa bangaskiyarka? Kana iya ambata annabci game da ‘kwanaki na ƙarshe.’ (2 Tim. 3:​1-5; Mat. 24:​3, 7) Amma wane annabci ne kuma da ya cika ya ƙarfafa ka? Alal misali, kana iya bayyana yadda annabcin da ke Daniyel sura 2 ko Daniyel sura 11 ya cika kuma yake cika yanzu? * Idan abubuwan da ka koya daga Littafi Mai Tsarki ne suka sa ka kasance da bangaskiya, ba abin da zai sa ka karaya. Ka yi la’akari da ’yan’uwan da aka tsananta musu a Jamus a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu. Sun kasance da bangaskiya sosai, duk da cewa ba su fahimci annabcin Littafi Mai Tsarki game da kwanaki na ƙarshe ba.

Yin nazarin Kalmar Allah, har da annabcin da ke cikinta, zai sa mu kasance da aminci sa’ad da muke fuskantar matsaloli (Ka duba sakin layi na 15-17) *

15-17. Ta yaya nazarin Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa ’yan’uwanmu da ’yan Nazi suka tsananta wa?

15 Sa’ad da ’yan Nazi suke mulki a Jamus, an saka ’yan’uwanmu da yawa a kurkuku. Hitler da kuma wani babban ma’aikacin gwamnati mai suna Heinrich Himmler sun tsani Shaidun Jehobah sosai. Wata ’yar’uwa ta faɗi abin da Himmler ya gaya wa wasu ’yan’uwa mata Shaidu da aka saka a kurkuku. Ya ce: “Jehobahnku yana iya yin sarauta a sama, amma mu ne muke mulki a nan duniya! Za mu ga waɗanda za su fi jimrewa, mu ʼyan Nazi ko ku Shaidu!” Me ya taimaka wa bayin Jehobah su kasance da aminci?

16 Waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun san cewa Mulkin Allah ya soma sarauta a shekara ta 1914. Ba su yi mamaki cewa ana tsananta musu sosai ba. Duk da haka, bayin Jehobah sun tabbata cewa babu gwamnatin ɗan Adam da za ta iya hana Allah cika nufinsa ba. Hitler bai iya kawar da bauta ta gaskiya ba ko kuma ya kafa gwamnati da ta fi Mulkin Allah ba. ’Yan’uwanmu sun kasance da tabbaci cewa Hitler zai daina mulki.

17 Abin da waɗannan ’yan’uwa suka tabbata da shi ya faru. Bayan ’yan shekaru, gwamnatin Nazi ta rugurguje. Heinrich Himmler ya gudu duk da cewa ya ce “mu ne muke mulki a nan duniya!” Sa’ad da yake gudu, ya haɗu da Ɗan’uwa Lübke wanda yake kurkuku a dā da ya sani. Himmler da ke baƙin ciki sosai ya tambayi Ɗan’uwa Lübke: “To, Ɗalibin Littafi Mai Tsarki, me zai faru yanzu?” Ɗan’uwa Lübke ya bayyana wa Himmler cewa Shaidun Jehobah sun sani tun da daɗewa cewa Mulkin Nazi zai rugurguje kuma za su sami ’yanci. Himmler ya yi baƙar magana a dā game da Shaidun Jehobah. Amma a wannan lokacin bai san abin da zai ce ba. Ba da daɗewa ba, sai ya kashe kansa. Wane darasi muka koya? Nazarin Littafi Mai Tsarki, har da annabcin da ke cikinsa, zai ƙarfafa bangaskiyarmu kuma ya sa mu kasance da aminci sa’ad da aka tsananta mana.​—2 Bit. 1:​19-21.

18. Kamar yadda Yohanna 6:​67, 68 suka nuna, me ya sa muke bukatar “sanin Allah da kuma kowace irin ganewa” da Bulus ya ambata a Filibiyawa 1:9?

18 Muna bukata mu nuna ƙauna don a san mu Kiristoci na gaskiya ne. Ban da haka, muna bukatar “sanin Allah.” (Filib. 1:9) Idan ba haka ba, za mu zama “kamar waɗanda ake yawo da hankalinsu,” kuma “iskar kowace koyarwa tana tura su tana ɗaukar hankalinsu,” har da koyarwar ’yan ridda. (Afis. 4:14) Sa’ad da almajirai da yawa a ƙarni na farko suka daina bin Yesu, manzo Bitrus ya nuna ƙarfin bangaskiyarsa, ta wajen cewa Yesu yana da “magana mai ba da rai na har abada.” (Karanta Yohanna 6:​67, 68.) Duk da cewa Bitrus bai fahimci duk abubuwan da Yesu ya faɗa ba, ya kasance da aminci domin ya fahimci gaskiya game da Kristi. Kai ma za ka iya ƙarfafa bangaskiyarka game da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Idan ka yi hakan, bangaskiyarka za ta yi ƙarfi ko da mene ne ya faru, kuma za ka taimaka wa mutane su ƙarfafa bangaskiyarsu.​—2 Yoh. 1, 2.

WAƘA TA 72 Mu Yaɗa Gaskiya Game da Mulkin Allah

^ sakin layi na 5 Wannan talifin zai taimaka mana mu fahimci cewa koyarwar Littafi Mai Tsarki tana da muhimmanci sosai. Ƙari ga haka, zai nuna hanyoyi da za mu tabbata cewa abin da muka yi imani da shi gaskiya ne.

^ sakin layi na 10 Don ka koya wa mutane muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki, ka duba jerin talifofin nan “Tattaunawa Tsakanin Shaidun Jehobah da Mutane” da suke cikin Hasumiyar Tsaro daga shekara ta 2012 zuwa 2015. Talifofin su ne “Shin Dukan Masu Adalci Za Su Je Sama Ne?” da “Yaushe Ne Mulkin Allah Ya Soma Sarauta?” da kuma “Shaidun Jehobah Sun Yi Imani da Yesu Kuwa?

^ sakin layi na 14 Don ka ga bayanin waɗannan annabcin ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 2012, da kuma talifofin da ke Mayu 2020.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTUNA: Sa’ad da iyaye suke ibada ta iyali da yaransu suna nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki game da ƙunci mai girma.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTUNA: A lokacin ƙunci mai girma, iyalin nan ba za su yi mamaki don abin da ke faruwa ba.