Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 33

Tashin Matattu na Nuna Kauna da Hikima da Kuma Hakurin Allah

Tashin Matattu na Nuna Kauna da Hikima da Kuma Hakurin Allah

“Za a tā da matattu.”​—A. M. 24:15.

WAƘA TA 151 Zai Kira Su

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa Jehobah ya halicci abubuwa?

AKWAI lokacin da Jehobah ne kaɗai yake wanzuwa. Duk da haka, bai kaɗaita ba. Jehobah ba ya bukatar ya kasance da kowa don ya yi farin ciki. Amma Allah yana son wasu ma su ji daɗin rayuwa. Domin Jehobah mai ƙauna ne, sai ya soma halittan abubuwa.​—Zab. 36:9; 1 Yoh. 4:19.

2. Ta yaya Yesu da mala’iku suka nuna cewa suna farin ciki don abubuwan da Jehobah ya halitta?

2 Da farko, Jehobah ya halicci Ɗansa Yesu. Bayan haka, ya yi amfani da Yesu don ya halicci “kome da kome” har da miliyoyin mala’iku. (Kol. 1:16) Yesu ya yi farin ciki sosai don wannan dama da ya samu na yin aiki tare da Ubansa. (K. Mag. 8:30) Ban da haka, mala’iku ma sun yi farin ciki. Suna wurin sa’ad da Jehobah da Yesu suka halicci sammai da duniya. Mene ne mala’iku suka yi? Sun yi “farin ciki” a lokacin da aka halicci duniya kuma sun ci gaba da yin farin ciki sa’ad da Jehobah ya halicci sauran abubuwa har da ’yan Adam. (Ayu. 38:7; K. Mag. 8:31) Duk abubuwan da Jehobah ya halitta sun nuna cewa shi mai ƙauna ne da hikima.​—Zab. 104:24; Rom. 1:20.

3. Kamar yadda 1 Korintiyawa 15:​21, 22 suka nuna, mene ne hadayar Yesu ta sa ya yiwu?

3 Jehobah yana so ’yan Adam su ji daɗin rayuwa har abada a wannan kyakkyawar duniya da ya halitta. Amma sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi tawaye ga Allah, hakan ya jawo wa yaransu zunubi da mutuwa. (Rom. 5:12) Mene ne Jehobah ya yi? Nan da nan Jehobah ya shirya yadda zai ceto ’yan Adam. (Far. 3:15) Jehobah zai ba da Ɗansa hadaya don ’ya’yan Adamu da Hauwa’u su sami ceto daga zunubi da mutuwa. Bayan haka, zai ba duk wanda ya zaɓi ya bauta masa rai na har abada.​—Yoh. 3:16; Rom. 6:23; karanta 1 Korintiyawa 15:​21, 22.

4. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Alkawarin da Allah ya yi cewa zai ta da matattu ya ta da tambayoyi da yawa. Alal misali, ta yaya za a ta da matattu? Za mu iya gane ’yan’uwanmu idan aka ta da su daga matattu? Ta yaya tashin matattu zai sa mu farin ciki? Kuma mene ne tashin matattu zai koya mana game da ƙaunar Jehobah da hikimarsa da kuma haƙurinsa? Bari mu tattauna waɗannan tambayoyin.

TA YAYA ZA A TA DA MATATTU?

5. Me ya sa zai dace mu gaskata cewa ba za a ta da mutane a lokaci ɗaya ba?

5 Sa’ad da Jehobah ya yi amfani da Ɗansa don ya ta da mutane da yawa daga matattu, ba dukansu ba ne za a ta da a lokaci ɗaya ba. Me ya sa? Domin idan mutane suka yi yawa a duniya nan take, hakan zai jawo rashin tsari. Jehobah ba ya yin abu da hargitsi da rashin tsari. Ya san cewa ana bukatar a kasance da tsari idan za a yi zaman lafiya. (1 Kor. 14:33) Jehobah ya nuna hikima da haƙuri a lokacin da yake aiki tare da Yesu don su halicci duniya domin ’yan Adam su zauna a ciki. Yesu ma zai nuna hikima da haƙuri a lokacin sarautarsa na shekara dubu, yayin da yake aiki tare da waɗanda suka tsira a Armageddon don su gyara duniya domin waɗanda za a ta da daga matattu.

Waɗanda suka tsira daga Armageddon za su koya wa waɗanda aka ta da daga mutuwa game da Mulkin Allah da kuma ƙa’idodinsa (Ka duba sakin layi na 6) *

6. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 24:15 ta nuna, su waye ne za su kasance cikin waɗanda Jehobah zai ta da daga mutuwa?

6 Hanya mafi muhimmanci da waɗanda suka tsira a Armageddon za su taimaka wa waɗanda aka ta da, shi ne koyar da su game da Mulkin Allah da kuma dokokinsa. Me ya sa? Domin yawancin waɗanda za a ta da “marasa adalci” ne. (Karanta Ayyukan Manzanni 24:15.) Suna bukatar su yi canje-canje don su amfana daga fansar Yesu. Ka yi tunanin irin aikin da za mu yi don koyar da miliyoyin mutane da ba su san game da Jehobah ba. Za a koyar da kowane mutum kamar yadda muke nazari da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a yau ne? Shin za a tura sabbin nan zuwa ikilisiyoyi don a horar da su kuma su ma su koyar da waɗanda za a ta da bayan su ne? Muna bukatar mu jira mu ga abin da zai faru. Amma mun san cewa a ƙarshen sarauta Yesu na shekara dubu, duniya “za ta cika da sanin Yahweh.” (Isha. 11:9) Za mu yi farin ciki sosai a wannan lokaci kuma za mu yi aiki mai kyau har shekara dubu!

7. Me ya sa bayin Allah za su nuna ƙauna sa’ad da suke koyar da waɗanda aka ta da daga matattu?

7 A lokacin sarautar Yesu na shekara dubu, dukan mutanen Jehobah za su bukaci yin canje-canje don su faranta masa rai. Dukansu za su riƙa nuna ƙauna yayin da suke taimaka wa waɗanda aka ta da su kasance da halaye masu kyau kuma su riƙa bin ƙa’idodin Jehobah. (1 Bit. 3:8) Waɗanda aka ta da daga mutuwa za su ga cewa bayin Jehobah suna da sauƙin kai kuma suna yin canje-canje don su bauta wa Jehobah. Hakan zai sa waɗanda aka ta da su so bauta wa Jehobah tare da mutanensa.​—Filib. 2:12.

ZA MU GANE WAƊANDA AKA TA DA DAGA MUTUWA?

8. Me ya sa za mu gane ’yan’uwanmu da abokanmu da za a ta da daga matattu?

8 Akwai dalilai da yawa da suka sa muka san cewa waɗanda za su marabci mutanen da aka ta da daga matattu za su gane ’yan’uwansu. Alal misali, tashin matattu da aka yi a dā ya nuna cewa Jehobah zai sa mutanen da suka tashi su sake kasancewa da siffarsu da muryarsu da kuma tunaninsu. Ka tuna cewa Yesu ya kamanta mutuwa da barci, tashin matattu kuma da ta da mutum daga barci. (Mat. 9:​18, 24; Yoh. 11:​11-13) Idan mutum ya tashi daga barci, siffarsa da muryarsa da kuma tunaninsa ba sa canjawa. Ka yi la’akari da misalin La’azaru. Ya yi kwana huɗu a mace, saboda haka, jikinsa ya soma ruɓewa. Duk da haka, Yesu ya ta da shi daga mutuwa, kuma nan take ’yan’uwansa suka gane shi, hakika La’azaru ma ya tuna da su.​—Yoh. 11:​38-44; 12:​1, 2.

9. Me ya sa ba za a ta da matattu da kamiltaccen jiki ba?

9 Jehobah ya yi alkawari cewa a Mulkinsa, babu mutumin da zai ce: “Ina ciwo.” (Isha. 33:24; Rom. 6:7) Saboda haka, waɗanda aka ta da daga matattu za a sake halittar su da lafiyayyen jiki. Amma ba za su zama kamilai nan da nan ba. Idan hakan ya faru, abokansu da iyalansu ba za su iya gane su ba. Kamar dai dukan ’yan Adam za su zama kamilai a hankali a sarautar Yesu na shekara dubu. A ƙarshen sarautar Yesu na shekara dubu ne zai miƙa wa Ubansa sarautar. Yesu zai kammala aikinsa kuma zai sa ’yan Adam su zama kamiltattu.​—1 Kor. 15:​24-28; R. Yar. 20:​1-3.

TA YAYA TASHIN MATATTU ZAI SA MU FARIN CIKI?

10. Yaya tashin matattu zai sa ka ji?

10 Ka yi tunanin yadda za mu ji yayin da muke marabtar ’yan’uwanmu da aka ta da daga matattu. Za ka yi dariya ne ko kuwa za ka zub da hawaye don farin ciki? Ko kuwa za ka soma rera waƙa don ka yabi Jehobah? Muna da tabbaci cewa za ka ƙaunaci Jehobah da Ɗansa Yesu don yadda suka ta da matattu.

11. Kamar yadda Yesu ya ce a Yohanna 5:​28, 29, wane amfani ne mutanen da ke bin ƙa’idodin Jehobah za su samu?

11 Ka yi tunanin irin farin cikin da waɗanda aka ta da daga matattu za su yi yayin da suke gyara halayensu kuma suke bin ƙa’idodin Jehobah. Mutanen da suka yi waɗannan canje-canje za su yi rayuwa har abada. Amma Jehobah ba zai yarda mutanen da suka ƙi bin ƙa’idodinsa su kasance a cikin Aljanna ba.​—Isha. 65:20; karanta Yohanna 5:​28, 29.

12. Ta yaya Jehobah zai albarkaci mutanen da ke duniya?

12 A Mulkin Allah, bayin Jehobah za su ga cikar abin da ke Karin Magana 10:22. Ta ce: “Albarkar Ubangiji takan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙin ciki ba.” (Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.) Da yake ruhun Jehobah na tare da mutanensa, za su kyautata halayensu sosai kuma su zama kamiltattu. (Yoh. 13:​15-17; Afis. 4:​23, 24) A kowace rana, za su kasance da ƙoshin lafiya. Hakika rayuwa za ta yi daɗi a lokacin! (Ayu. 33:25) Ta yaya yin tunani a kan tashin matattu zai taimaka maka yanzu?

DARASI DAGA ƘAUNAR JEHOBAH

13. Kamar yadda Zabura 139:​1-4 suka nuna, ta yaya tashin matattu zai nuna cewa Jehobah ya san mu sosai?

13 Kamar yadda muka tattauna ɗazu, idan Jehobah ya ta da matattu, zai dawo musu da tunaninsu da kuma halayensu. Ka yi tunanin abin da hakan yake nufi. Jehobah yana ƙaunar ka sosai shi ya sa yake lura da tunaninka da yadda kake ji da furucinka da kuma ayyukanka. Saboda haka, idan ya ta da kai, za ka kasance daidai yadda kake kafin ka rasu. Sarki Dauda ya san cewa Jehobah ya san kowannenmu. (Karanta Zabura 139:​1-4.) Yaya za mu ji idan muka fahimci yadda Jehobah ya san mu?

14. Yaya ya kamata mu ji idan muka yi tunanin yadda Jehobah ya san mu?

14 Bai kamata hankalinmu ya tashi ba idan mun yi tunani a kan yadda Jehobah ya san mu sosai. Me ya sa? Ka tuna cewa Jehobah ya damu da mu sosai. Yana daraja kowannenmu. Yana lura da abubuwan da muke fuskanta a rayuwa. Hakan na da ban-ƙarfafa sosai! Kada mu taɓa yin tunanin cewa ba mu da mai taimako. A kowace rana, Jehobah yana tare da mu kuma yana so ya taimaka mana.​—2 Tar. 16:9.

KA NUNA GODIYA DON HIKIMAR JEHOBAH

15. Me ya sa tashin matattu yake nuna cewa Jehobah mai hikima ne?

15 Idan mutum yana tsoron mutuwa, maƙiyansa za su iya tilasta masa ya yi abin da ba ya son yi. Abin da waɗanda ke goyon bayan Shaiɗan ke amfani da shi ke nan don su sa mutane su ci amana abokansu ko kuma su yi abin da bai dace ba. Amma ba za su iya tilasta mana mu yi abin da suke so ba. Mun san cewa idan maƙiyanmu suka kashe mu, Jehobah zai ta da mu. (R. Yar. 2:10) Muna da tabbaci cewa ba su isa su hana mu bauta wa Jehobah ba. (Rom. 8:​35-39) Jehobah ya nuna cewa yana da hikima don yadda ya ba mu begen tashin matattu! Begen tashin matattu ya kuɓutar da mu daga tarkon da Shaiɗan yake amfani da shi don ya tsorata mutane. Kuma ya sa mu kasance da ƙarfin zuciya don mu riƙe aminci ga Jehobah.

Shawarwarinmu suna nuna cewa mun dogara ga Jehobah ya biya bukatunmu kuwa? (Ka duba sakin layi na 16) *

16. Waɗanne tambayoyi ne kake bukatar ka yi wa kanka, kuma ta yaya amsoshin za su taimaka maka ka san ko kana dogara ga Jehobah?

16 Idan maƙiya suka yi barazanar kashe ka, za ka dogara ga Jehobah cewa zai ta da kai daga mutuwa? Me zai taimaka maka ka san cewa za ka iya dogara ga Jehobah? Hanya ɗaya ita ce ta tambayar kanka, ‘Shawarwarin da nake tsai da wa a kowace rana suna nuna cewa na dogara ga Jehobah kuwa?’ (Luk. 16:10) Wata tambaya kuma ita ce, ‘Salon rayuwata yana nuna cewa na dogara ga Jehobah cewa zai biya bukatuna idan na saka Mulkinsa farko a rayuwata?’ (Mat. 6:​31-33) Za mu nuna cewa mun dogara ga Jehobah kuma muna shirye mu jimre kowace matsala idan amsar waɗannan tambayoyin e ce.​—K. Mag. 3:​5, 6.

JEHOBAH YANA DA HAƘURI

17. (a) Ta yaya tashin matattu yake nuna cewa Jehobah yana da haƙuri? (b) Ta yaya za mu nuna godiya don haƙurin Jehobah?

17 Jehobah ya riga ya ƙayyade lokacin da zai halaka mugaye. (Mat. 24:36) Ba zai ɗauki mataki kafin lokacin da ya ƙayyade ba don rashin haƙuri. Ya ƙosa ya ta da matattu amma yana haƙuri. (Ayu. 14:​14, 15) Yana jiran lokacin da ya dace don ya ta da su. (Yoh. 5:28) Muna da dalilai masu kyau da suka sa ya kamata mu nuna godiya don yadda Jehobah yake haƙuri. Domin Jehobah yana da haƙuri, mutane da yawa har da mu ma muna da zarafin “tuba.” (2 Bit. 3:9) Jehobah yana so mutane da yawa su sami zarafin yin rayuwa har abada. Don haka, bari mu riƙa godiya don yadda yake nuna haƙuri. Ta yaya? Ta wajen yin iya ƙoƙarinmu don mu taimaka ma “waɗanda suke da zuciya ta samun rai na har abada” su bauta wa Jehobah. (A. M. 13:​48, New World Translation) Hakan zai sa su amfana daga haƙurin Jehobah, yadda mu ma muka amfana.

18. Me ya sa muke bukatar yin haƙuri da mutane?

18 Jehobah zai jira har sai ƙarshen sarautar Yesu na shekara dubu kafin mu zama kamiltattu. Kafin wannan lokacin, Jehobah zai ci gaba da gafarta mana zunubanmu. Saboda haka, zai dace mu ci gaba da mai da hankali ga halaye masu kyau na ʼyan’uwa kuma mu riƙa haƙuri da su. Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa wadda mijinta yake da cutar tsananin damuwa kuma ya daina halartan taro. Ta ce: “Hakan ya dame ni sosai, domin rayuwarmu ta canja farat ɗaya kuma ba mu iya yin abubuwan da muka ce za mu yi ba.” Duk da haka, wannan ’yar’uwar ta yi haƙuri da mijinta. Ta dogara ga Jehobah kuma ba ta fid da rai ba. Ta yi koyi da Jehobah kuma ba ta mai da hankali ga matsalolin ba, amma ga halaye masu kyau na mijinta. Ta ƙara cewa: “Mijina yana da halaye masu kyau, kuma yana yin iya ƙoƙarinsa don ya sami sauƙi.” Yana da muhimmanci sosai mu riƙa haƙuri da ’yan’uwa a ikilisiya da kuma ’yan iyalinmu da suke ƙoƙari su magance matsaloli!

19. Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi?

19 Yesu da mala’iku sun yi farin ciki sa’ad da aka halicci duniya. Ka yi tunanin yadda za su yi farin ciki sa’ad da duniya ta cika da mutane kamiltattu da suke ƙaunar Jehobah kuma suke bauta masa. Babu shakka, waɗanda za su yi sarauta da Yesu za su yi farin ciki yayin da suka ga cewa ’yan Adam suna amfana daga aikinsu. (R. Yar. 4:​4, 9-11; 5:​9, 10) Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance sa’ad da babu baƙin ciki ko kuka ko azaba ko rashin lafiya ko wahala, kuma an cire mutuwa har abada. (R. Yar. 21:4) Kafin wannan lokacin, ka ƙuduri niyyar yin koyi da Jehobah mai ƙauna da hikima da kuma haƙuri. Idan ka yi haka, za ka ci gaba da yin farin ciki ko da wace irin matsala ce kake fuskanta. (Yaƙ. 1:​2-4) Muna matuƙar godiya domin alkawarin da Jehobah ya yi cewa zai “tā da matattu.”​—A. M. 24:15.

WAƘA TA 141 Rai, Kyauta Ce Daga Allah

^ sakin layi na 5 Jehobah Uba ne mai hikima mai ƙauna da kuma haƙuri. Muna iya ganin waɗannan halayensa ta yadda ya halicci dukan abubuwa da kuma alkawarin da ya yi na ta da matattu. A wannan talifin, za mu tattauna wasu tambayoyi da wataƙila muke da su game da tashin matattu, kuma za mu tattauna yadda za mu nuna godiya don yadda Jehobah yake nuna ƙauna da hikima da kuma haƙuri.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani mutumin da ya yi shekaru da yawa da mutuwa ya tashi a lokacin sarautar Yesu na shekara dubu. Wani ɗan’uwa da ya tsira a Armageddon yana farin cikin koyar da mutumin abubuwan da yake bukatar yi don ya amfana daga fansar Yesu.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa yana gaya wa shugabansa cewa akwai ranakun da ba zai iya yin ƙarin ayyuka ba. Ya ce yana yin ayyukan ibada da yamma a waɗannan ranakun. Amma idan ana bukatar ya yi ƙarin ayyuka a wasu ranaku dabam, zai amince ya yi.