Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 39

Ka Rika Karfafa ʼYan’uwa Mata

Ka Rika Karfafa ʼYan’uwa Mata

“Ƙungiyar mata masu baza [bishara] babba ce.”​—ZAB. 68:11.

WAƘA TA 137 Mata Masu Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

ʼYan’uwanmu mata masu ƙwazo suna halartan taro, suna yin wa’azi, suna gyara da tsabtace Majami’ar Mulki kuma suna kula da ʼyan’uwa (Ka duba sakin layi na 1)

1. Ta yaya ʼyan’uwa mata suke taimakawa a ƙungiyar Jehobah, kuma waɗanne matsaloli ne suke fuskanta? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

MUNA farin ciki cewa akwai ʼyan’uwa mata da yawa a ikilisiya da suke aiki tuƙuru! Alal misali, suna yin kalami da ayyuka a taro, kuma suna yin wa’azi. Wasu suna kula da Majami’ar Mulki kuma suna nuna cewa sun damu da ʼyan’uwa maza da mata. Babu shakka, suna fuskantar matsaloli. Wasu suna kula da iyayensu tsofaffi. Wasu suna jimre tsanantawa daga iyalinsu. Wasu kuma su kaɗai ne suke kula da yaransu.

2. Me ya sa ya kamata mu ƙarfafa ʼyan’uwa mata?

2 Me ya sa ya kamata mu riƙa taimaka wa ʼyan’uwa mata? Domin mutane da yawa suna yawan rena su. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu riƙa taimaka musu. Alal misali, manzo Bulus ya gaya wa ikilisiyar da ke Roma cewa su marabci Fibi kuma su “ba ta kowane irin taimakon da take bukata.” (Rom. 16:​1, 2) Akwai lokacin da Bulus ba ya daraja mata domin shi Bafarisi ne, kuma Farisawa sun rena mata. Amma sa’ad da ya zama Kirista, ya soma daraja mata da yi musu alheri yadda Yesu ma ya yi.​—1 Kor. 11:1.

3. Ta yaya Yesu ya bi da mata, kuma yaya ya ɗauki matan da suka yi nufin Allah?

3 Yesu ya daraja dukan mata. (Yoh. 4:27) Ba ya ɗaukan mata yadda shugabannin addinai na zamaninsa suke yi. Wani littafi da ke bayyana Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yesu bai taɓa faɗin abin da ya nuna cewa ya rena mata ba.” Yesu ya fi daraja mata da suka yi nufin Jehobah. Ya kira su ’yan’uwansa kuma ya ambata su tare da mazan da ya ɗauka a matsayin iyalinsa.​—Mat. 12:50.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 A koyaushe, Yesu yana shirye ya taimaka wa matan da suka bauta wa Allah. Ya nuna suna da muhimmanci a gare shi kuma ya kāre su. Bari mu tattauna yadda za mu koyi yin la’akari da ʼyan’uwa mata daga Yesu.

KA RIƘA LA’AKARI DA ’YAN’UWA MATA

5. Me ya sa yake wa wasu ʼyan’uwa mata wuya su sami abokan kirki?

5 Dukanmu muna bukatar mu riƙa cuɗanya da abokan kirki. Amma, a wasu lokuta yakan yi wa ’yan’uwa mata wuya su sami abokan kirki. Me ya sa? Ga wasu misalai. Wata ’yar’uwa mai suna Jordan * ta ce: “Tun da yake ba ni da aure, sau da yawa ina ganin ba ni da aiki da kuma amfani a ikilisiya.” Wata ’yar’uwa majagaba mai suna Kristen da ta ƙaura don ta ƙara ƙwazo a wa’azi ta ce: “Idan ka koma sabuwar ikilisiya, za ka ji kamar ka kaɗaita.” Wasu ’yan’uwa maza ma suna jin hakan. Zai yi wa ʼyan’uwan da iyalinsu ba Shaidu ba wuya su kusace su, kuma suna iya jin kaɗaici domin ba sa kusa da ʼyan’uwansu a ikilisiya. Wasu ’yan’uwa mata sun kaɗaita domin suna rashin lafiya, ba sa iya fita, ko kuma suna kula da wani a iyalinsu da ke rashin lafiya. Wata ’yar’uwa mai suna Annette ta ce, “Idan ’yan’uwa suka gayyace ni liyafa, ba na iya halarta domin ni ce nake kula da mahaifiyata.”

Za mu iya nuna cewa mun damu da mata yadda Yesu ya yi (Ka duba sakin layi na 6-9) *

6. Kamar yadda Luka 10:​38-42 suka nuna, ta yaya Yesu ya taimaka wa Marta da Maryamu?

6 Yesu ya yi cuɗanya da ’yan’uwa mata kuma shi abokinsu ne na ƙwarai. Bari mu tattauna abokantakarsa da Maryamu da Marta da ba su yi aure ba. (Karanta Luka 10:​38-42.) Yesu ya sa sun saki jiki ta ayyukansa da kuma kalamansa. Alal misali, Maryamu ta saki jiki kuma ta zauna don Yesu ya koyar da ita kamar sauran mabiyansa. * Sa’ad da Marta ta yi fushi domin Maryamu ta ƙi ta taimaka mata, Marta ta gaya wa Yesu abin da ke zuciyarta. A wannan lokacin, Yesu ya koya wa mata biyun darasi mai muhimmanci. Ya nuna cewa ya damu da su da kuma ɗan’uwansu Li’azaru sa’ad da ya ci gaba da ziyartar su. (Yoh. 12:​1-3) Don haka, sa’ad da Li’azaru ya soma rashin lafiya sosai, Maryamu da Marta sun nemi taimakon Yesu.​—Yoh. 11:​3, 5.

7. A wace hanya ce za mu iya ƙarfafa ’yan’uwa mata?

7 A taron ikilisiya ne wasu ’yan’uwa mata suke samun zarafin kasancewa da ’yan’uwansu. Don haka, zai dace mu yi amfani da wannan zarafin don mu marabce su, mu tattauna da su, kuma mu nuna musu cewa mun damu da su. Jordan wadda aka ambata ɗazu ta ce: “Ina samun ƙarfafawa sosai sa’ad da ’yan’uwa suka yaba mini don kalamina, suka shirya fita wa’azi tare da ni ko kuma suka nuna sun damu da ni.” Wajibi ne mu nuna wa ’yan’uwa mata cewa suna da daraja. Wata mai suna Kia ta ce: “Idan ban halarci taro ba, na san cewa ’yan’uwa maza da mata za su turo mini saƙo don su san ko ina lafiya, kuma hakan ya sa na san cewa sun damu da ni.”

8. A waɗanne hanyoyi ne kuma za mu iya yin koyi da Yesu?

8 Za mu iya keɓe lokaci don yin cuɗanya da ’yan’uwa mata kamar yadda Yesu ya yi. Muna iya gayyatar su don mu ci abinci tare ko kuma mu je shaƙatawa. Sa’ad da muka yi hakan, ya kamata abin da muka tattauna ya ƙarfafa su. (Rom. 1:​11, 12) Ya kamata dattawa su kasance da irin halin Yesu. Ya san cewa kasancewa marasa aure zai iya zama da ƙalubale ga wasu, ya nuna sarai cewa yin aure ko kuma haifan yara ba shi ne ke sa mutum farin ciki ba. (Luk. 11:​27, 28) A maimakon haka, idan muka saka bautar Jehobah farko a rayuwarmu, za mu yi farin ciki da gaske.​—Mat. 19:12.

9. Mene ne dattawa za su yi don su taimaki ’yan’uwa mata?

9 Dattawa musamman suna bukatar su riƙa bi da ’yan’uwa mata a matsayin ’yan’uwansu da kuma iyayensu. (1 Tim. 5:​1, 2) Zai dace dattawa su riƙa keɓe lokaci kafin taro ko kuma bayan taro don su tattauna da ’yan’uwa mata. Wata ’yar’uwa mai suna Kristen ta ce: “Wani dattijo ya lura cewa ina da ayyuka da yawa kuma ya tambaye ni yadda na tsara ayyukana. Na yi farin ciki cewa ya damu da ni.” Idan dattawa suna keɓe lokaci don su tattauna da ’yan’uwa mata, hakan zai nuna cewa sun damu da su. * Annette wadda aka ambata ɗazu ta bayyana amfani tattaunawa da dattawa a kai a kai. Ta ce: “Hakan ya sa mun wayi juna. Idan ina da matsala, yana yi mini sauƙi in nemi taimako daga wurinsu.”

KU RIƘA GODE WA ’YAN’UWA MATA

10. Mene ne zai taimaka wa ’yan’uwa mata su riƙa farin ciki?

10 Dukanmu muna daɗa ƙwazo idan mutane suka yaba mana don ayyukanmu. Amma mukan yi sanyin gwiwa idan ba wanda ya yaba mana don ayyukan da muka yi. Wata ’yar’uwa marar aure mai suna Abigail ta bayyana cewa a wasu lokuta tana ji kamar babu wanda ya san da ita. Ta ce: “Sun san cewa ni ’yar wane-da-wace ce, amma ba su taɓa tattaunawa da ni ba. Hakan yakan sa na ji cewa babu wanda ya damu da ni.” Wata mai suna Pam ta yi shekaru da yawa tana hidima a ƙasar waje, daga baya ta dawo gida don ta kula da iyayenta. Yanzu ta ba shekara 70 baya kuma har ila tana hidimar majagaba. Pam ta ce: “Abin da ya taimaka mini sosai shi ne sa’ad da mutane suka nuna godiya don ayyukan da nake yi.”

11. Ta yaya Yesu ya nuna godiya ga matan da suka bi shi wa’azi?

11 Yesu ya nuna godiya don yadda mata masu aminci suka yi masa “hidima da kayansu.” (Luk. 8:​1-3) Ya ba su gatar yi masa hidima kuma ya koya musu muhimman abubuwa game da Allah. Alal misali, ya gaya musu cewa za a kashe shi kuma a ta da shi daga mutuwa. (Luk. 24:​5-8) Ya shirya waɗannan mata don tsanantawar da za su fuskanta, yadda ya shirya manzanninsa. (Mar. 9:​30-32; 10:​32-34) Kuma sa’ad da manzannin suka gudu a lokacin da aka kama Yesu, wasu cikin matan sun kasance tare da shi a lokacin da yake kan gungumen azaba.​—Mat. 26:56; Mar. 15:​40, 41.

12. Wane aiki ne Yesu ya ba mata?

12 Yesu ya ba mata aiki mai muhimmanci. Alal misali, mata masu aminci ne suka fara ganin Yesu a lokacin da aka ta da shi. Ya tura matan su gaya wa almajiransa cewa an ta da shi daga matattu. (Mat. 28:​5, 9, 10) A ranar Fentakos na 33, wataƙila mata suna wurin sa’ad da aka sauko wa almajiran Yesu da ruhu mai tsarki. Idan haka ne, waɗannan mata ma sun yi magana cikin harsuna kuma sun gaya wa mutane “manyan abubuwan da Allah ya yi.”​—A. M. 1:14; 2:​2-4, 11.

13. Waɗanne ayyuka ne ’yan’uwa mata suke yi a yau, kuma ta yaya za mu nuna godiya don ayyukansu?

13 Ya kamata mu riƙa yaba wa ’yan’uwa mata saboda ayyukan da suke yi a ƙungiyar Jehobah. Waɗannan ayyukan sun haɗa da gine-gine da kula da su, da taimaka wa rukunin da ake wani yare da kuma aiki a Bethel. Suna taimakawa a aikin ba da agaji, da fassara littattafai da yin hidimar majagaba da kuma hidima a ƙasar waje. Mata ma suna halartan makarantar majagaba da Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki da kuma Makarantar Gilead. Ƙari ga haka, mata suna taimaka wa mazajensu su cim ma aikinsu a ikilisiya da kuma ƙungiyar Jehobah. Waɗannan ’yan’uwan suna cim ma ayyukansu ne domin matansu suna taimaka musu. (Afis. 4:8) Za ka iya taimaka wa waɗannan ’yan’uwa mata a ayyukan da suke yi?

14. Mene ne abin da aka faɗa a Zabura 68:11 zai sa dattawa su yi?

14 Dattawa masu hikima sun san cewa ’yan’uwa mata suna yin ayyuka da yawa kuma sun iya wa’azi sosai. (Karanta Zabura 68:11.) Saboda haka, dattawa suna yin koyi da misalinsu. Abigail da aka ambata ɗazu ta ce tana farin ciki sa’ad da ’yan’uwa maza suka tambaye ta hanyoyin da ya dace na soma tattaunawa da mutane a yankin. Ta ce: “Hakan yana taimaka mini in ga cewa ina da amfani a ƙungiyar Jehobah.” Ƙari ga haka, dattawa sun san cewa ’yan’uwa mata da suka manyanta suna taimaka wa ’yan mata da suke fuskantar matsaloli. (Tit. 2:​3-5) Hakika, ’yan’uwa mata sun cancanci mu riƙa nuna musu ƙauna da kuma godiya!

KA KĀRE ’YAN’UWA MATA KUMA KA TAIMAKA MUSU

15. A wane lokaci ne ’yan’uwa mata za su bukaci wani ya kāre su?

15 A wasu lokuta, ’yan’uwa mata za su bukaci wanda zai kāre su sa’ad da suke cikin wata matsala. (Isha. 1:17) Alal misali, wata gwauruwa ko wadda aurenta ya mutu tana iya bukatar wani da zai taimaka mata ta yi wasu abubuwa da mijinta yake yi a dā. ’Yar’uwa da ta tsufa tana iya bukatar taimako don tattaunawa da likita. Ko kuma ’yar’uwa majagaba da take wasu ayyuka a ƙungiyar Jehobah za ta bukaci wani ya kāre ta idan aka ce ba ta fita wa’azi kamar yadda sauran majagaba suke yi. A wace hanya ce kuma za mu iya taimaka wa ’yan’uwa mata? Bari mu sake tattauna misalin Yesu.

16. Kamar yadda Markus 14:​3-9 suka nuna, ta yaya Yesu ya kāre Maryamu?

16 Yesu ya yi saurin kāre mata a lokacin da mutane ba su fahimce su ba. Alal misali, ya kāre Maryamu sa’ad da Marta ta yi gunaguni game da ita. (Luk. 10:​38-42) Yesu ya sake kāre ta sa’ad da wasu suka ce ta yi abin da bai dace ba. (Karanta Markus 14:​3-9.) Yesu ya fahimci Maryamu kuma ya yaba mata, ya ce: “Ai, abu mai kyau ne ta yi mini. . . . Ta yi iyakacin ƙoƙarinta.” Ya ma annabta cewa za a riƙa faɗin abin da ta yi a “duk inda za a yi shelar labarin nan mai daɗi a duniya duka,” kamar yadda ake yi a wannan talifin. Abin ban-sha’awa ne cewa a lokacin da Yesu yake yaba wa Maryamu don abin da ta yi ne ya ambata cewa za a yi wa’azi a dukan faɗin duniya! Babu shakka, wannan furucin ya ƙarfafa Maryamu sosai bayan wasu sun kushe ta!

17. Ka ba da misalin da ya nuna lokacin da za mu bukaci kāre ʼyan’uwa mata.

17 Kana kāre ’yan’uwa mata sa’ad da bukata ta taso? Ka yi la’akari da misalin nan. Wasu masu shela sun lura cewa wata ’yar’uwa da mijinta ba Mashaidi ba ne tana yawan zuwa taro a makare kuma ta koma gida nan da nan bayan taron. Kuma sun lura cewa ba ta yawan kawo yaranta taro. Don haka, sai suka soma kushe ta domin suna ganin cewa tana bukatar ta yi tsayin daka don mijinta ya bar ta ta riƙa zuwa da yaransu taro. Amma ba su san cewa ’yar’uwar tana yin iya ƙoƙarinta ba. Maigidanta ne yake da ikon yanke wa iyalinsa shawara. Saboda haka, mene ne za ka iya yi? Idan ka yaba wa ’yar’uwar kuma ka faɗi abubuwa masu kyau da take yi, hakan zai sa ’yan’uwan su daina kushe ta.

18. A waɗanne hanyoyi ne kuma za mu taimaka wa ’yan’uwa mata?

18 Za mu nuna wa ’yan’uwanmu mata cewa mun damu da su ta wajen taimaka musu. (1 Yoh. 3:18) Annette, wadda take kula da mahaifiyarta ta ce: “Wasu ’yan’uwa sukan zo gidanmu don su taya ni kula da mahaifiyata ko kuma su kawo mana abinci. Hakan ya sa na ji cewa ana ƙauna ta kuma ina da daraja a ikilisiya.” An taimaka wa Jordan ma. Wani ɗan’uwa ya koya mata yadda za ta riƙa kula da motarta. Ta ce: “Sanin cewa ’yan’uwa sun damu da ni kuma ba sa so wani abu ya faru da ni ya sa ni farin ciki.”

19. A waɗanne hanyoyi ne kuma dattawa za su iya taimaka wa ’yan’uwa mata?

19 Dattawa ma suna yin iya ƙoƙarinsu don su nuna sun damu da ’yan’uwa mata. Sun san cewa Jehobah yana so a riƙa bi da waɗannan ’yan’uwa yadda ya dace. (Yaƙ. 1:27) Saboda haka, suna yin koyi da Yesu kuma suna nuna sanin yakamata. Suna yin alheri maimakon nace wa bin dokoki. (Mat. 15:​22-28) Idan dattawa suka yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka wa ’yan’uwa mata, hakan zai sa ’yan’uwan su ga cewa Jehobah yana ƙaunar su. Sa’ad da ɗan’uwan da ke kula da rukunin masu wa’azi da Kia take ya ji cewa za ta ƙaura zuwa wani gida, nan da nan ya yi shiri don a taimaka mata. Kia ta ce: “Hakan ya rage mini gajiya sosai. Don sun ƙarfafa ni da kuma taimaka mini, dattawan sun nuna mini cewa ina da daraja a ikilisiya kuma suna nan a shirye su taimaka mini a lokacin matsala.”

DUKA ’YAN’UWA MATA SUNA BUKATAR TAIMAKO

20-21. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja duka ’yan’uwa mata?

20 A dukan ikilisiyoyi a yau, da akwai ’yan’uwa mata da yawa da suke hidima da ƙwazo kuma ya kamata mu tallafa musu. Kamar yadda muka koya daga misalin Yesu, muna iya taimaka musu ta wajen keɓe lokaci don yin cuɗanya da su da kuma sanin su sosai. Za mu iya gode musu don abubuwan da suke yi a hidimarsu ga Allah. Kuma mu riƙa kāre su a lokacin da muke bukatar yin hakan.

21 Sa’ad da manzo Bulus yake kammala wasiƙarsa ga ’yan’uwan da ke Roma, ya ambata ’yan’uwa mata guda tara. (Rom. 16:​1, 3, 6, 12, 13, 15) Hakika, yadda aka yaba musu da kuma gai da su ya ƙarfafa waɗannan ’yan’uwa mata. Bari mu ma mu riƙa taimaka wa ’yan’uwa mata a ƙungiyar Jehobah. Idan muka yi hakan, za mu nuna cewa muna ƙaunar su a matsayin ’yan’uwanmu.

WAƘA TA 136 Jehobah Zai Ba Ka “Cikakkiyar Lada”

^ sakin layi na 5 ʼYan’uwa mata Kiristoci suna fuskantar ƙalubale sosai. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya ƙarfafa su kamar yadda Yesu ya yi. Za mu ga yadda Yesu ya kasance tare da mata, ya nuna ya damu da su, kuma ya kāre su.

^ sakin layi na 5 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 6 Wani littafi ya ce: “Ɗalibai suna zama kusa da malamansu don a koyar da su. Sukan yi hakan idan suna so su zama malamai, amma ba a barin mata su zama malamai. . . . Don haka, yawanci maza Yahudawa sun yi mamaki da suka ga Maryamu ta zauna kusa da Yesu kuma yana koyar da ita.”

^ sakin layi na 9 Ya kamata dattawa su yi hankali sa’ad da suke taimaka wa ’yan’uwa mata. Alal misali, kada su kaɗai su ziyarce su.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa yana yin koyi da yadda Yesu ya nuna ya damu da mata masu aminci. Yana canja wa wasu mata biyu tayar motarsu, wani ya kai ziyara wurin wata ’yar’uwa tsohuwa, wani kuma ya kai matarsa wurin wata ’yar’uwa da ’yarta don su yi ibada ta iyali tare.