Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 43

Jehobah Yana Yi wa Kungiyarsa Ja-goranci

Jehobah Yana Yi wa Kungiyarsa Ja-goranci

“‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ba ta wurin iko ba, amma ta wurin ruhuna ne,’ in ji Yahweh Mai Runduna.”​—ZAK. 4:6.

WAƘA TA 40 Waye ne Allahnka?

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne ya kamata Kiristoci su ci gaba da yi?

KA RIGA ka yi baftisma ne? Idan haka ne, ka nuna wa kowa cewa ka yi imani ga Jehobah kuma kana so ka bauta masa cikin ƙungiyarsa. * Amma, wajibi ne ka ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarka cewa Jehobah yana wa ƙungiyarsa ja-goranci a yau.

2-3. A wace hanya ce Jehobah yake yi wa ƙungiyarsa ja-goranci a yau? Ka ba da misali.

2 A yau, yadda Jehobah yake wa ƙungiyarsa ja-goranci ya nuna halayensa da abin da yake so ya cim ma da kuma ƙa’idodinsa. Bari mu tattauna halaye uku na Jehobah da ke bayyane a ƙungiyarsa.

3 Na farko, “Allah ba ya nuna bambanci.” (A. M. 10:34) Ƙauna ce ta motsa Jehobah ya aiko da Ɗansa don “ya fanshi mutane duka.” (1 Tim. 2:6; Yoh. 3:16) Jehobah yana amfani da mutanensa domin ya yaɗa bishara ga mutane da za su saurara kuma hakan yana sa su amfana daga fansar Yesu. Na biyu, Jehobah, Allah ne mai tsari da kuma salama. (1 Kor. 14:​33, 40) Saboda haka, ya kamata bayinsa su kasance da tsari da kuma salama. Na uku, Jehobah ‘Malaminmu’ ne mafi girma. (Isha. 30:​20, 21) Shi ya sa ƙungiyarsa take aiki tuƙuru don ta koya wa mutane game da Kalmarsa. Ta yaya Kiristoci a ƙarni na farko suka nuna waɗannan halaye guda uku? Ta yaya bayin Allah a yau suke nuna waɗannan halayen? Ta yaya ruhu mai tsarki zai taimaka maka a yau yayin da kake bauta wa Jehobah a ƙungiyarsa?

ALLAH BA YA NUNA BAMBANCI

4. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 1:8 ta nuna, me Yesu ya ce mabiyansa su riƙa yi, kuma wane taimako ne za su samu?

4 A ƙarni na farko. Wa’azin da Yesu ya yi ya sa mutane su kasance da bege. (Luk. 4:43) Ya ba mabiyansa umurni su ci gaba da wa’azi “har zuwa iyakar duniya.” (Karanta Ayyukan Manzanni 1:8.) Ba da ƙarfinsu suka yi wannan aikin ba. Suna bukatar ‘taimakon’ ruhu mai tsarki da Yesu ya yi musu alkawarin sa.​—Yoh. 14:26; Zak. 4:6.

5-6. A waɗanne hanyoyi ne ruhu mai tsarki ya taimaka wa mabiyan Yesu?

5 An saukar wa mabiyan Yesu da ruhu mai tsarki a ranar Fentakos ta 33. Nan da nan, suka soma wa’azi da taimakon ruhu mai tsarki, kuma ba da daɗewa ba, mutane da yawa suka zama mabiyan Yesu. (A. M. 2:41; 4:4) Sa’ad da aka soma tsananta wa mabiyan Yesu, ba su ji tsoro ba amma sun nemi taimakon Allah. Sun yi addu’a cewa: “Ka ba bayinka ƙarfin halin faɗin kalmarka babu tsoro.” Sai aka cika su da ruhu mai tsarki kuma suka ci gaba da “faɗin kalmar Allah babu tsoro.”​—A. M. 4:​18-20, 29, 31.

6 Mabiyan Yesu sun fuskanci wasu matsaloli. Alal misali, babu Littafi Mai Tsarki da yawa a lokacin. Babu littattafan nazari kamar yadda muke da su a yau. Kuma mabiyan Yesu za su yi wa mutane da ke yare dabam-dabam wa’azi. Duk da waɗannan ƙalubalen, waɗannan almajirai masu ƙwazo sun cim ma abin da ake gani ba zai yiwu ba, wato sun yi wa’azi “ga kowace halitta a ƙarƙashin sama.”​—Kol. 1:​6, 23.

7. Fiye da shekaru ɗari da suka shige, ta yaya bayin Jehobah suka san abin da Allah yake bukata a gare su, kuma mene ne suka yi?

7 A zamaninmu. Jehobah ya ci gaba da yi wa bayinsa ja-goranci da kuma ƙarfafa su. Yana yin hakan ta yin amfani da Kalmarsa da aka rubuta da taimakon ruhu mai tsarki. A cikin Littafi Mai Tsarki, za mu iya karanta game da hidimar Yesu da umurnin da ya ba mabiyansa cewa su ci gaba da yin wa’azi. (Mat. 28:​19, 20) Hasumiyar Tsaro ta watan Yuli, 1881 ta ce: “Jehobah bai zaɓe mu don mutane su ɗaukaka mu ko mu zama masu arziki ba, amma domin mu yi amfani da abubuwan da muke da su don mu yi wa’azi.” Wata ƙasida mai jigo To Whom the Work Is Entrusted da aka wallafa a 1919, ta ce: “Aikin yana da yawa, amma aikin Ubangiji ne, kuma zai ba mu ƙarfin yin sa.” Kamar Kiristoci na farko, waɗannan ’yan’uwan suna da gaba gaɗi kuma sun yi wannan aikin da ƙwazo domin sun tabbata cewa ruhu mai tsarki zai taimaka musu su yi wa dukan mutane wa’azi. Mu ma muna da irin wannan tabbaci a yau.

Ƙungiyar Jehobah ta yi amfani da kayan aiki mafi kyau don yaɗa bishara (Ka duba sakin layi na 8-9)

8-9. Waɗanne hanyoyi ne ƙungiyar Jehobah ta yi amfani da su don yin wa’azi?

8 Ƙungiyar Jehobah ta yi amfani da kayan aiki mafi kyau don ta yaɗa bishara. Waɗannan abubuwa sun haɗa da littattafai, da fim ɗin “Photo-Drama of Creation” da garmaho da motoci masu lasifika da shirye-shiryen rediyo, kuma a kwanan nan muna amfani da Intane. Ƙungiyar Jehobah tana kuma fassara littattafai cikin harsuna dabam-dabam a hanyar da ba a taɓa yi ba! Me ya sa? Domin tana so dukan mutane su koyi gaskiya a yarensu. Jehobah ba ya nuna bambanci kuma ya annabta cewa za a yi wa’azi a “kowace al’umma, da zuriya, da yare, da kabila.” (R. Yar. 14:​6, 7) Jehobah yana so kowa ya ji wa’azi.

9 Mutane da ke zama a manyan gidaje masu tsaro sosai kuma fa? Domin a yi wa waɗannan mutanen wa’azi, ƙungiyar Jehobah ta soma amfani da hanyoyi dabam-dabam na yin wa’azi ga jama’a. Alal misali, a shekara ta 2001, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta ba ’yan’uwa a Faransa izinin soma wa’azi da amalanke kuma daga baya, ʼyan’uwa a wasu ƙasashe ma sun soma wa’azi a wannan hanyar. Hakan ya sa an sami sakamako mai kyau. A shekara ta 2011, an soma wani sabon tsarin yin wa’azi a wuraren da aka fi jama’a a birnin New York kuma ana kiran tsarin special metropolitan public witnessing. A shekarar, an ba da littattafai 102,129 da kuma mujallu 68,911. Kuma mutane 4,701 sun ce a riƙa nazari da su! Wannan ya nuna mana cewa ruhun Jehobah yana taimaka mana a wannan aikin. Hakan ya sa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta ba da izinin yin amfani da wannan amalanken yin wa’azi a faɗin duniya.

10. Mene ne za mu yi don mu kyautata yadda muke wa’azi?

10 Abin da za ka iya yi. A taron ikilisiya, Jehobah yana koya mana yadda za mu yi wa’azi. Ka riƙa fita wa’azi da ’yan’uwa da ke rukunin wa’azinku. ’Yan’uwa da ke rukunin za su taimaka maka ka ƙware a wa’azi da koyarwa kuma su ƙarfafa ka ta halayensu masu kyau. Kamar yadda Zakariya 4:6 ta nuna, muna yin nufin Allah ba da ƙarfinmu ba, amma don ruhu mai tsarki yana taimaka mana. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ba mu ƙarfi domin aikin da muke yi nasa ne.

JEHOBAH ALLAH NE MAI TSARI DA SALAMA

11. Ta yaya Hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci ta yi aiki da haɗin kai don ta sa mutanen Allah su kasance da tsari?

11 A ƙarni na farko. Hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a Urushalima ta yi aiki da haɗin kai domin mutanen Allah su kasance da tsari da kuma salama. (A. M. 2:42) Alal misali, a shekara ta 49 da batun kaciya ya taso, hukumar ta tattauna batun kuma ruhu mai tsarki ya taimaka musu. Da a ce Kiristocin sun bar wannan batun ya raba kansu, da ba su yi wannan wa’azin ba. Ko da yake ’yan’uwan Yahudawa ne, ba su bar al’adarsu ta shafi shawarar da suka yanke ba. Sun bincika Kalmar Allah kuma sun nemi taimakon ruhu mai tsarki don su yanke shawara mai kyau. (A. M. 15:​1, 2, 5-20, 28) Mene ne sakamakon? Jehobah ya albarkace su, ikilisiyar ta kasance da salama da haɗin kai, kuma suka ci gaba da wa’azi.​—A. M. 15:​30, 31; 16:​4, 5.

12. Mene ne ya nuna cewa ƙungiyar Jehobah tana da tsari da kuma salama a yau?

12 A zamaninmu. Ƙungiyar Jehobah ta taimaka wa bayin Jehobah su kasance da tsari da kuma salama. A Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 1895, an wallafa wani talifi mai jigo “Decently and in Order,” (Kasancewa da Tsari) kuma an ɗauko jigon daga 1 Korintiyawa 14:40. Talifin ya ce: “Manzanni sun rubuta abubuwa da yawa ga ikilisiya game da kasancewa da tsari . . . Yana da muhimmanci mu ci gaba da bin ‘abin da aka rubuta tun dā’ don a gargaɗar da mu.” (Rom. 15:4) Ƙungiyar Jehobah a yau tana ƙoƙartawa don ta sa kowa ya kasance da tsari da salama. Alal misali, idan ka halarci taro a wata ikilisiya a ƙasarku ko kuma a wata ƙasa kuma ana nazarin Hasumiyar Tsaro, ka san yadda za a gudanar da nazarin da talifin da za a tattauna. Nan da nan za ka saki jiki! Ruhun Allah ne kawai ke sa a kasance da wannan haɗin kai.​—Zaf. 3:9.

13. Kamar yadda Yaƙub 3:17 ta nuna, waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

13 Abin da za ka iya yi. Jehobah yana so bayinsa su ‘kiyaye ɗayantuwar nan da ruhu ya ba su, ta wurin salamar da ta ɗaure su tare.’ (Afis. 4:​1-3) Saboda haka, ka tambayi kanka: ‘Ina sa ikilisiyarmu ta kasance da haɗin kai da salama? Ina yin biyayya ga waɗanda suke ja-goranci ne? Shin wasu za su iya dogara da ni, musamman idan ina da damar yin wasu ayyuka a ikilisiya? Ina yin abu a kan lokaci? Ina taimaka wa mutane? Kuma ina ɗokin yi wa mutane hidima?’ (Karanta Yaƙub 3:17.) Idan ka ga cewa kana bukatar ka yi gyara, ka nemi taimakon ruhu mai tsarki. Idan ka bar ruhu mai tsarki ya riƙa maka ja-goranci, ’yan’uwa a ikilisiya za su ƙaunace ka kuma su riƙa daraja ka.

JEHOBAH YANA KOYAR DA MU KUMA YANA BA MU ABIN DA MUKE BUKATA

14. Kamar yadda aka nuna a Kolosiyawa 1:​9, 10, ta yaya Jehobah ya koyar da bayinsa a ƙarni na farko?

14 A ƙarni na farko. Jehobah yana so ya koyar da mutanensa. (Zab. 32:8) Yana so su san shi, su ƙaunace shi kuma su yi rayuwa har abada a matsayin yara da yake ƙauna sosai. Ba za a iya cim ma waɗannan abubuwa ba idan Jehobah bai koyar da mu ba. (Yoh. 17:3) Jehobah ya yi amfani da ikilisiya a ƙarni na farko don ya koyar da bayinsa. (Karanta Kolosiyawa 1:​9, 10.) Ruhu mai tsarki, wato “mai taimako” da Yesu ya yi alkawarinsa ne ya taimaki mabiyansa. (Yoh. 14:16) Ruhu mai tsarki ya taimaki mabiyan su fahimci Kalmar Allah kuma su tuna dukan abubuwan da Yesu ya faɗa kuma ya yi da aka rubuta a Linjila. Hakan ya ƙarfafa bangaskiyar Kiristoci a ƙarni na farko kuma ya sa su daɗa ƙaunar Jehobah da Ɗansa da kuma juna.

15. A waɗanne hanyoyi ne ka ga yadda Jehobah ya cika alkawarinsa da ke Ishaya 2:​2, 3?

15 A zamaninmu. Jehobah ya annabta cewa “a kwanaki” na ƙarshe, mutane daga dukan al’ummai za su haura tudun Jehobah don ya koyar da su. (Karanta Ishaya 2:​2, 3.) A yau wannan annabcin yana cika. Bauta ta gaskiya ta fi kowane irin addinin ƙarya a duniya. Kuma Jehobah yana koya wa mutanensa Littafi Mai Tsarki sosai! (Isha. 25:6) Yana amfani da “bawan nan mai aminci, mai hikima,” don ya koyar da mu a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, muna iya karanta talifofi dabam-dabam daga littattafanmu, mu saurari jawabai kuma mu kalli bidiyon katoon. (Mat. 24:45) Muna ji kamar Elihu abokin Ayuba wanda ya ce: “Wane ne me iya koyarwa kamar [Allah]?”​—Ayu. 36:22.

Ka tabbatar wa kanka da cewa ka koyi gaskiya kuma ka yi amfani da ita a rayuwarka (Ka duba sakin layi na 16) *

16. Mene ne za ka yi don ka amfana daga koyarwar Jehobah?

16 Abin da za ka iya yi. Ruhun Allah zai taimaka maka ka yi amfani da abin da ka karanta da kuma yi nazarinsa a Kalmar Allah. Ka yi addu’a kamar wani marubucin zabura da ya ce: “Ya Yahweh, koya mini hanyarka, domin in yi tafiya cikin amincinka. Ba ni zuciya ɗaya, domin in girmama Sunanka.” (Zab. 86:11) Saboda haka, ka ci gaba da karanta da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafan da ƙungiyar Jehobah take tanadarwa. Hakika, maƙasudinka ba kawai samun ilimi ba. Kana bukatar ka tabbata cewa abin da kake koya gaskiya ne kuma ka riƙa amfani da shi a rayuwarka. Ruhu mai tsarki zai taimaka maka ka yi hakan. Ban da haka, ya kamata ka ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya. (Ibran. 10:​24, 25) Me ya sa? Domin kuna bauta wa Jehobah tare. Ka roƙi Allah ya taimaka maka ka yi kalami daga zuciyarka a taro kuma ka yi iya ƙoƙarinka sa’ad da kake da jawabi a taro. Ta yin waɗannan abubuwan, za ka nuna wa Jehobah da Ɗansa cewa kana ƙaunar ‘tumakinsu’ masu tamani.​—Yoh. 21:​15-17.

17. A waɗanne hanyoyi ne za ka nuna cewa kana goyon bayan ƙungiyar Jehobah?

17 Ba da daɗewa ba, ƙungiyar da ruhun Allah ke yi wa ja-goranci ne za ta rage a duniya. Saboda haka, ka haɗa kai da ƙungiyar Jehobah. Ka nuna cewa kana ƙaunar dukan mutane yadda Allah yake yi ta wajen yi wa dukan mutane da ka haɗu da su wa’azi. Ka yi koyi da yadda Jehobah yake da tsari da kuma salama ta wajen taimaka wa ’yan’uwa su kasance da haɗin kai. Ka saurari Jehobah Malaminka Mafi Girma ta wajen yin amfani da dukan abubuwan da yake tanadinsu. Idan ka yi hakan, ba za ka ji tsoro ba sa’ad da wannan duniyar ta zo ƙarshe. Maimakon haka, za ka yi ƙarfin zuciya kuma ka kasance tare da waɗanda suke bauta wa Jehobah da aminci a ƙungiyarsa.

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu

^ sakin layi na 5 Ka tabbata cewa Jehobah ne ke yi wa ƙungiyarsa ja-goranci a yau? A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah ya yi wa Kiristoci a ƙarni na farko ja-goranci da yadda yake wa bayinsa hakan a yau.

^ sakin layi na 1 MA’ANAR WASU KALMOMI: Ƙungiyar Jehobah tana da sassa biyu. Akwai wadda ke sama da kuma duniya. A wannan talifin, kalmar nan “ƙungiya” tana nufin sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya.

^ sakin layi na 52 BAYANI A KAN HOTUNA: Bayan wata ’yar’uwa majagaba ta kalli bidiyoyi kuma ta ga ’yan’uwa da suke hidima a ƙasashen da ake bukatar masu shela sosai, hakan ya motsa ta ta yi koyi da su. Daga baya ta cim ma maƙasudinta na yin hidima a inda ake bukatar masu shela sosai.