Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 46

Ka Yi Ƙarfin Zuciya, Jehobah Zai Taimake Ka

Ka Yi Ƙarfin Zuciya, Jehobah Zai Taimake Ka

“Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.”​—IBRAN. 13:5.

WAƘA TA 55 Kada Ku Ji Tsoron Su!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne zai ƙarfafa mu sa’ad da muke fuskantar matsaloli? (Zabura 118:​5-7)

KA TAƁA ji kamar babu wanda zai taimaka maka ka jimre matsalolin da kake fuskanta? Mutane da yawa sun taɓa jin hakan, har da bayin Jehobah masu aminci. (1 Sar. 19:14) Idan hakan ya faru da kai, ka tuna alkawarin da Jehobah ya yi. Ya ce: “Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.” Shi ya sa, ba tare da shakka ba, muna iya cewa, “Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba. Me ɗan Adam zai iya yi mini?” (Ibran. 13:​5, 6) Manzo Bulus ya rubuta waɗannan kalmomi ga Kiristocin da ke Yahudiya a wajen shekara ta 61 bayan haihuwar Yesu. Kalmominsa sun tuna mana da abin wani marubucin zabura ya ce a Zabura 118:​5-7.​—Karanta.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin, kuma me ya sa?

2 Kamar wannan marubucin zabura, Bulus ya san cewa Jehobah zai taimaka masa domin ya yi hakan a dā. Alal misali, shekaru biyu kafin ya rubuta wasiƙa ga Ibraniyawa, Bulus ya tsira daga muguwar guguwa sa’ad da yake tafiya a jirgin ruwa. (A. M. 27:​4, 15, 20) Shekaru da yawa kafin wannan tafiyar, Jehobah ya taimaka masa a hanyoyi da yawa. Za mu tattauna uku daga cikinsu. Jehobah ya yi amfani da Yesu da mala’iku da hukumomi da kuma Kiristoci don ya taimaka wa Bulus. Yin bitar abubuwan da suka faru a rayuwar Bulus zai sa mu daɗa kasancewa da tabbaci cewa Allah zai ji addu’o’inmu kuma ya taimaka mana.

TAIMAKO DAGA YESU DA KUMA MALA’IKU

3. Mene ne wataƙila Bulus ya yi tunaninsa, kuma me ya sa?

3 Bulus yana bukatar taimako. A wajen shekara ta 56, taron ’yan iska sun fitar da Bulus daga haikali kuma suka yi ƙoƙarin su kashe shi. Washegari, sa’ad da aka kai shi gaban majalisa, maƙiyansa sun kusan kashe shi. (A. M. 21:​30-32; 22:30; 23:​6-10) A lokacin, wataƙila Bulus ya yi tunani, ‘Har tsawon wane lokaci ne zan jimre da wannan cin mutuncin?’

4. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da Yesu don ya taimaka wa Bulus?

4 Ta yaya aka taimaka wa Bulus? A daren da aka kama Bulus, “Ubangiji” Yesu, ya tsaya kusa da shi ya ce: “Ka ci gaba da ƙarfin zuciyarka, domin kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lallai ne za ka shaide ni a Roma.” (A. M. 23:11) Wannan alkawarin ya ƙarfafa Bulus sosai! Yesu ya yaba masa don wa’azin da ya yi a Urushalima. Kuma ya yi masa alkawari cewa zai kai Roma don ya daɗa yin wa’azi sosai. Bayan wannan ƙarfafawa da Bulus ya samu, hakika, ya ji kamar yaron da ya riƙe hannun mahaifinsa don ya samu kāriya.

Sa’ad da ake wata guguwa mai tsanani, wani mala’ika ya tabbatar wa Bulus da cewa dukansu da ke cikin jirgin za su tsira (Ka duba sakin layi na 5)

5. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da mala’ika don ya taimaka wa Bulus? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

5 Waɗanne matsaloli ne kuma Bulus ya fuskanta? Wajen shekara biyu bayan abubuwan da Bulus ya fuskanta a Urushalima, ya shiga jirgin ruwa zuwa Italiya. Sai aka soma muguwar guguwa, hakan ya sa ma’aikatan jirgin da kuma fasinjoji suka ji kamar ba za su iya tsira ba. Amma Bulus bai ji tsoro ba. Me ya sa? Ya gaya wa waɗanda ke jirgin cewa: “A daren jiya wani mala’ikan Allah wanda nake nasa, wanda nake kuma bauta masa, ya tsaya kusa da ni, ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lallai za ka tsaya a gaban Kaisar. Ga shi kuma ta dalilinka Allah cikin alherinsa zai ceci abokan tafiyarka.’ ” Jehobah ya sake yin amfani da mala’ika don ya maimaita alkawarin da Yesu ya yi wa Bulus. Kuma da gaske, Bulus ya kai Roma.​—A. M. 27:​20-25; 28:16.

6. Wane alkawari da Yesu ya yi ne zai ƙarfafa mu, kuma me ya sa?

6 Ta yaya Yesu yake taimaka mana? Yesu zai taimaka mana yadda ya taimaka wa Bulus. Alal misali, Yesu ya yi wa dukan mabiyansa alkawari cewa: ‘Ga shi kuwa, ina tare da ku kullum har ƙarshen zamani.’ (Mat. 28:20) Abin da Yesu ya faɗa zai iya ƙarfafa mu. Me ya sa? Domin a wasu lokuta, muna baƙin ciki sosai. Alal misali, sa’ad da aka yi mana rasuwa, muna iya yin shekaru muna baƙin ciki. Wasu suna fama da matsalolin da ke tattare da tsufa. Wasu kuma suna yin kwanaki da yawa suna fama da ciwon baƙin ciki. Duk da haka, muna jimrewa domin mun san cewa Yesu yana tare da mu “kullum,” har a lokacin da muka fi baƙin ciki.​—Mat. 11:​28-30.

Mala’iku suna yi mana ja-goranci da kuma taimaka mana a wa’azi (Ka duba sakin layi na 7)

7. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:6 ta nuna, ta yaya Jehobah yake taimaka mana a yau?

7 Kalmar Allah ta tabbatar mana da cewa Jehobah zai yi amfani da mala’ikunsa ya taimaka mana. (Ibran. 1:​7, 14) Alal misali, mala’iku suna taimaka mana da kuma yi mana ja-goranci sa’ad da muke yin wa’azin “labari mai daɗi na mulkin sama” ga “kowace al’umma, da zuriya, da yare, da kabila.”​—Mat. 24:​13, 14; karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:6.

TAIMAKO DAGA HUKUMOMI

8. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da kwamandan sojoji don ya taimaka wa Bulus?

8 Ta yaya aka taimaka wa Bulus? A shekara ta 56, Yesu ya tabbatar wa Bulus cewa zai isa Roma. Amma wasu Yahudawa suna so su yi masa ƙwantan-ɓauna kuma su kashe shi. Sa’ad da kwamandan sojojin Roma mai suna Kalaudiyus Lisiyas ya ji abin da mutanen suka ƙulla, sai ya taimaka wa Bulus. Nan da nan, Kalaudiyus ya tura sojoji da yawa su kāre Bulus, su kai shi Kaisariya, kuma sun bi hanyar da ke da nisar kilomita 105 daga Urushalima. A Kaisariya, gwamna mai suna Filikus ya ba da umurni a “tsare shi a fādar da Sarki Hirudus ya gina.” Hakan ya sa Yahudawan sun kasa kashe Bulus.​—A. M. 23:​12-35.

9. Ta yaya gwamna Festus ya taimaka wa Bulus?

9 Shekaru biyu bayan haka, ba a sako Bulus daga kurkuku a Kaisariya ba. Kuma Festus ya zama gwamna maimakon Filikus. Yahudawa sun roƙi Festus ya sa a dawo da Bulus Urushalima don a yi masa shari’a, amma Festus ya ƙi. Wataƙila gwamnan ya san cewa Yahudawa sun “shirya waɗansu su jira su kashe [Bulus] a hanya.”​—A. M. 24:​27–25:5.

10. Mene ne gwamna Festus ya yi sa’ad da Bulus ya ɗaukaka ƙara gaban Kaisar?

10 Daga baya, an yi wa Bulus shari’a a Kaisariya. Da yake Festus “yana so ya faranta wa Yahudawa rai,” ya tambayi Bulus cewa: “Ko ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a gabana a can game da waɗannan abubuwa?” Bulus ya san cewa za a iya kashe shi a Urushalima, kuma ya san abin da ya kamata ya yi don kada hakan ya faru, amma ya isa Roma kuma ya ci gaba da wa’azi. Ya ce: A kai ni “gaban kotun Kaisar!” Bayan Festus ya tattauna da masu ba shi shawara, sai ya ce wa Bulus: “To, ka roƙa a ɗaukaka ƙararka zuwa gaban Kaisar, wurin Kaisar kuwa za ka tafi.” Shawarar da Festus ya yanke ta ceci Bulus daga hannun maƙiyansa. Ba da daɗewa ba, Bulus ya isa Roma kuma ya yi nesa da Yahudawan da suke so su kashe shi.​—A. M. 25:​6-12.

11. Waɗanne kalmomin Ishaya masu ban-ƙarfafa ne wataƙila Bulus ya yi tunani a kai?

11 Yayin da Bulus yake shirin tafiya zuwa Italiya, wataƙila ya yi tunani a kan abin da annabi Ishaya ya ce game da maƙiyan Jehobah. Ya ce: “Ku yi shawara tare, amma zai zama banza, ku yi shiri, amma ba zai zaunu ba. Gama mu, Allah yana tare da mu!” (Isha. 8:10) Bulus ya san cewa Allah zai taimaka masa, kuma hakan ya ƙarfafa shi yayin da zai fuskanci matsaloli a nan gaba.

Kamar yadda Jehobah ya yi a dā, zai iya sa hukumomi su kāre bayinsa (Ka duba sakin layi na 12)

12. Ta yaya Yuliyus ya bi da Bulus, kuma mene ne hakan ya nuna wa Bulus?

12 A shekara ta 58, Bulus ya soma tafiyarsa zuwa Italiya. Wani sojan Roma mai suna Yuliyus ne ke kula da Bulus domin shi fursuna ne. Yuliyus yana da ikon ƙuntata wa Bulus ko kuma ya yi masa alheri. Mene ne ya yi? Washegari da suka isa gaɓa teku, “Yuliyus kuwa ya yi wa Bulus alheri, ya bar shi ya je ya ga abokansa su biya masa bukatarsa.” Bayan haka, Yuliyus ya ceci Bulus. Ta yaya? Sojojin sun so su kashe dukan fursunonin da ke jirgin ruwan, amma Yuliyus ya hana su yin hakan. Me ya sa? Domin “ya so ya ceci Bulus.” Hakika, Bulus ya lura cewa Jehobah yana amfani da wannan soja don ya taimaka masa, kuma ya kāre shi.​—A. M. 27:​1-3, 42-44.

Ka duba sakin layi na 13

13. Ta yaya Jehobah yake amfani da hukumomi?

13 Ta yaya hukumomi suke taimaka mana? Idan wani abu ya jitu da nufin Jehobah, yana amfani da ruhunsa mai tsarki don ya sa hukumomi yin abin da yake so. Ka yi la’akari da abin da Sarki Sulemanu ya ce: “Zuciyar sarki tana kama da ruwan rafi a hannun Yahweh, Yahweh yakan juya shi duk inda yake so.” (K. Mag. 21:1) Mene ne wannan karin magana yake nufi? ’Yan Adam za su iya yi wa ruwan rafi hanya don ruwan ya bi hanyar da suke so. Hakazalika, Jehobah yana iya yin amfani da ruhunsa don ya sa hukumomi su yi abin da yake so don a cika nufinsa. Hakan yana sa hukumomi su tsai da shawarwarin da za su amfani mutanen Allah.​—Gwada Ezra 7:​21, 25, 26.

14. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 12:5 ta nuna, su waye ne za mu iya yin addu’a dominsu?

14 Abin da za mu iya yi. Muna iya yin addu’a domin “dukan sarakunan da dukan waɗanda suke da manyan matsayi” su yanke shawarwarin da za su sa mu ci gaba da hidimarmu. (1 Tim. 2:​1, 2; Neh. 1:11) Kamar yadda Kiristoci a ƙarni na farko suka yi, mu ma muna yi wa ’yan’uwanmu Kiristoci da ke kurkuku addu’a. (Karanta Ayyukan Manzanni 12:5; Ibran. 13:3) Ƙari ga haka, muna iya yin addu’a domin masu gadin ’yan’uwanmu da ke kurkuku. Muna iya roƙan Jehobah ya motsa su su bi da ’yan’uwanmu kamar Yuliyus da ya nuna wa Bulus “alheri.”​—A. M. 27:3.

TAIMAKO DAGA ’YAN’UWA

15-16. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da Arastarkus da Luka don ya taimaka wa Bulus?

15 Ta yaya aka taimaka wa Bulus? Sa’ad da Bulus yake tafiya zuwa Roma, Jehobah ya yi amfani da ’yan’uwa sau da yawa don su taimaka masa. Bari mu tattauna wasu daga cikin misalan.

16 Abokan Bulus masu aminci, wato Arastarkus da Luka sun bi shi zuwa Roma. * Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa Yesu ya yi wa Arastarkus da Luka alkawari cewa za su isa Roma lafiya ba. Saboda haka, sun sadaukar da rayukansu don su kasance tare da Bulus. Sa’ad da suka fuskanci matsaloli a jirgin ne suka san cewa za a cece su. A lokacin da Arastarkus da Luka suka shiga jirgi a Kaisariya, babu shakka, Bulus ya yi addu’a kuma ya gode wa Jehobah don waɗannan ’yan’uwa biyu masu ƙarfin zuciya da ya tura su taimaka masa.​—A. M. 27:​1, 2, 20-25.

17. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da ’yan’uwa don ya taimaka wa Bulus?

17 A lokacin da Bulus yake tafiya, ’yan’uwa sun taimaka masa sau da yawa. Alal misali, sa’ad da suka tsaya a tashar jirgin ruwan da ke Sida, Yuliyus ya bar Bulus ya “je ya ga abokansa” don “su biya masa bukata.” Daga baya, a birnin Butiyoli, Bulus da abokansa sun haɗu da waɗansu ’yan’uwa kuma suka roƙe su su “yi kwana bakwai tare da su.” ’Yan’uwan da ke waɗannan wuraren sun biya bukatun Bulus da abokansa, kuma Bulus ya ba su labarin abubuwan da suka fuskanta kuma hakan ya ƙarfafa ’yan’uwan. (Gwada Ayyukan Manzanni 15:​2, 3.) Bayan wannan ziyara mai ban ƙarfafa, Bulus da abokansa sun ci gaba da tafiyarsu.​—A. M. 27:3; 28:​13, 14.

Kamar Bulus, Jehobah yana yin amfani da ’yan’uwa don ya taimaka mana (Ka duba sakin layi na 18)

18. Mene ne ya sa Bulus ya gode wa Allah kuma ya yi ƙarfin gwiwa?

18 Yayin da Bulus yake gab da shiga Roma, wataƙila ya tuna wasiƙar da ya rubuta ga ’yan’uwan da ke birnin shekaru uku da suka shige. Ya ce: “Tun shekaru masu yawa ina marmarin zuwa wurinku domin in gan ku.” (Rom. 15:23) Amma bai san cewa zai isa Roma a matsayin fursuna ba. Da ya ga cewa ’yan’uwa da ke Roma sun tsaya a bakin hanya domin su gaishe shi yayin da yake shiga birnin, hakan ya ƙarfafa shi sosai! Kalmar Allah ta ce: “Da Bulus ya gan su kuwa ya yi godiya ga Allah, ya kuma ƙara samun ƙarfin gwiwa.” (A. M. 28:15) Ka lura cewa Bulus ya gode wa Allah sa’ad da ya ga ’yan’uwan. Me ya sa? Domin ya ga cewa Jehobah ne ya yi amfani da ’yan’uwan don ya taimaka masa.

Ka duba sakin layi na 19

19. Kamar yadda 1 Bitrus 4:10 ta nuna, ta yaya Jehobah zai iya yin amfani da mu don ya taimaka wa mabukata?

19 Abin da za mu iya yi. Ka san wasu ’yan’uwa a ikilisiyarku da suke baƙin ciki domin suna fama da rashin lafiya ko an yi musu rasuwa ko kuma suna fuskantar wasu matsaloli dabam? Idan mun san wani ɗan’uwa da yake bukatar taimako, muna iya roƙan Jehobah ya taimaka mana mu faɗi wani abin da zai ƙarfafa shi ko kuma mu yi masa alheri. Furucinmu da ayyukanmu suna iya zama abin da ɗan’uwan yake bukata don ya sami ƙarfafawa. (Karanta 1 Bitrus 4:10.) * Idan muka taimaka musu, suna iya gaskata cewa alkawarin da Jehobah ya yi cewa “har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba” gaskiya ne. Hakika, hakan zai sa ka farin ciki.

20. Me ya sa za mu iya cewa da tabbaci: “Ubangiji mai taimakona ne”?

20 Mu ma muna iya fuskantar matsaloli a rayuwa, kamar yadda Bulus da abokansa suka fuskanta. Amma ya kamata mu kasance da ƙarfin zuciya domin Jehobah yana tare da mu. Zai yi amfani da Yesu da mala’iku don ya taimaka mana. Kuma idan yin wani abu ya jitu da nufinsa, Jehobah yana iya yin amfani da hukumomi don ya taimaka mana. Ƙari ga haka, Jehobah yana yin amfani da ruhunsa don ya motsa bayinsa su taimaka wa ’yan’uwansu. Saboda haka, kamar Bulus, muna da dalilin furtawa da tabbaci cewa: “Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba. Me ɗan Adam zai iya yi mini?”​—Ibran. 13:6.

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

^ sakin layi na 5 A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da Jehobah ya taimaka wa Bulus sa’ad da yake fuskantar matsaloli. Yin bitar yadda Jehobah ya taimaka wa bayinsa a dā, zai tabbatar mana da cewa zai taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli a rayuwa.

^ sakin layi na 16 A dā, Arastarkus da Luka abokan tafiyar Bulus ne. Waɗannan maza masu aminci sun kasance da Bulus sa’ad da yake kurkuku a Roma.​—A. M. 16:​10-12; 20:4; Kol. 4:​10, 14.

^ sakin layi na 19 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2009, shafuffuka na 13-14, sakin layi na 5-9.