Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 47

Kana a Shirye Ka Rika Bin Shawara?

Kana a Shirye Ka Rika Bin Shawara?

“A ƙarshe dai, ’yan’uwana, ku riƙa farin ciki, kuna yin canje-canje.”​—2 KOR. 13:​11, New World Translation.

WAƘA TA 54 ‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Kamar yadda Matiyu 7:​13, 14 suka nuna, me ya sa za mu iya cewa muna cikin tafiya?

DUKANMU muna cikin tafiya. Muna ƙoƙari mu bauta wa Jehobah don mu yi rayuwa a sabuwar duniya a mulkin Allah. A kowace rana, muna ƙoƙarin bin hanyar da za ta sa mu sami rai. Amma, kamar yadda Yesu ya ce, hanyar ƙarama ce kuma a wasu lokuta tana da wuyar bi. (Karanta Matiyu 7:​13, 14.) Domin mu ajizai ne, yana da sauƙi mu bijire daga wannan hanyar.​—Gal. 6:1.

2. Me za mu tattauna a wannan talifin? (Ka kuma duba akwatin nan “ Sauƙin Kai Yana Sa Mu Yi Canje-Canje.”)

2 Idan muna so mu kasance a ƙaramar hanyar rai, wajibi ne mu yarda mu canja tunaninmu da halinmu da kuma ayyukanmu. Manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristocin da ke Korinti su ci gaba da “yin canje-canje.” (2 Kor. 13:11) Wannan shawara ta shafe mu. A wannan talifin, za mu tattauna yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu yi canje-canje da kuma yadda abokai da suka manyanta za su taimaka mana mu ci gaba a hanyar rai. Za mu kuma tattauna lokacin da zai yi mana wuya mu bi shawarar da ƙungiyar Jehobah ta ba da. Ƙari ga haka, za mu ga yadda zama masu sauƙin kai zai taimaka mana mu yi canje-canje kuma mu ci gaba da farin ciki a bautarmu ga Jehobah.

KA BI SHAWARAR KALMAR ALLAH

3. Ta yaya Kalmar Allah za ta taimaka mana?

3 Ba shi da sauƙi mu bincika tunaninmu da yadda muke ji. Me ya sa? Domin zuciyarmu ta fi kome ruɗu, saboda haka, zai yi wuya mu san abin da zuciyarmu za ta sa mu yi. (Irm. 17:9) Yana da sauƙi mu ‘ruɗi kanmu’ da tunanin ƙarya. (Yaƙ. 1:22) Saboda haka, wajibi ne mu yi amfani da Kalmar Allah don mu bincika duk “tunani da nufin da suke cikin” zuciyarmu. (Ibran. 4:​12, 13) Kalmar Allah tana aiki kamar na’urar ɗaukan hoton jiki, don tana taimaka mana mu ga abin da ke cikin zuciyarmu. Amma, wajibi ne mu zama masu tawali’u idan muna so mu amfana daga shawarar da ke cikin Kalmar Allah ko kuma da dattawa suke ba mu.

4. Me ya nuna cewa Sarki Saul ya zama mai fahariya?

4 Abin da Sarki Saul ya yi ya nuna abin da zai faru idan ba mu da tawali’u. Saul ya zama mai fahariya sosai, har ya ƙi ya amince cewa yana bukatar ya yi canje-canje a tunaninsa da ayyukansa. (Zab. 36:​1, 2; Hab. 2:4) Jehobah ya ba Saul umurnin abin da zai yi bayan ya ci Amalakawa a yaƙi. Amma, Saul bai yi abin da Jehobah ya gaya masa ba. Kuma sa’ad da annabi Sama’ila ya yi masa magana a kan batun, Saul ya ƙi amincewa da kuskurensa. Maimakon haka, ya ba da hujja cewa abin da ya yi ba laifi ba ne kuma mutane ne suka sa ya yi hakan. (1 Sam. 15:​13-24) Saul ya taɓa nuna irin wannan halin a dā. (1 Sam. 13:​10-14) Abin baƙin ciki, ya zama mai fahariya. Bai canja tunaninsa ba, saboda haka, Jehobah ya yi masa horo kuma ya tsige shi daga sarauta.

5. Wane darasi ne muka koya daga abin da ya faru da Saul?

5 Bai kamata mu yi koyi da Saul ba, saboda haka, ya kamata mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Sa’ad da na karanta Kalmar Allah, nakan nemi hujja na ƙin bin abin da na karanta? Ina ganin cewa abin da nake yi ba laifi ba ne? Ina ɗora wa wasu laifi don abubuwan da na yi?’ Idan muna yin waɗannan abubuwa, wajibi ne mu canja tunaninmu da halinmu. Idan ba haka, za mu zama masu girman kai kuma hakan zai sa Jehobah ya ƙi mu a matsayin abokansa.​—Yaƙ. 4:6.

6. Ka bayyana abin da ya sa Sarki Saul da Sarki Dauda suka bambanta.

6 Sarki Saul da Sarki Dauda sun bambanta, Dauda mutum ne da yake son “koyarwar Yahweh.” (Zab. 1:​1-3) Dauda ya san cewa Jehobah yakan ceci masu sauƙin kai amma yana ƙasƙantar da masu ɗaga kai. (2 Sam. 22:28) Shi ya sa Dauda ya bar dokar Allah ta canja tunaninsa. Ya ce: “Na yabi Yahweh wanda yake bi da ni, ko da dare zuciyata tana yi mini gargaɗi.”​—Zab. 16:7.

KALMAR ALLAH

Kalmar Allah tana mana gargaɗi sa’ad da muka bijire. Idan mu masu sauƙin kai ne, za mu bar Kalmar Allah ta daidaita tunaninmu (Ka duba sakin layi na 7)

7. Me za mu yi idan mu masu sauƙin kai ne?

7 Idan mu masu sauƙin kai ne, za mu bar Kalmar Allah ta daidaita tunaninmu don kada mu yi abin da bai dace ba. Kalmar Allah za ta zama kamar murya da take gaya mana cewa: “Ga hanyar, yi tafiya a cikinta.” (Isha. 30:21) Idan muka saurari Jehobah, za mu amfana sosai. (Isha. 48:17) Alal misali, ba za mu sha kunya ba domin wani ya yi mana gyara. Ban da haka, za mu kusaci Jehobah domin mun san cewa ya damu da mu kamar yadda mahaifi yake damuwa da yaransa.​—Ibran. 12:7.

8. Kamar yadda aka ambata a Yaƙub 1:​22-25, ta yaya Kalmar Allah za ta zama kamar madubi a gare mu?

8 Kalmar Allah tana iya zama kamar madubi a gare mu. (Karanta Yaƙub 1:​22-25.) Kafin mu bar gida kowane safe, yawancinmu muna kallon kanmu a madubi. Ta yin hakan, muna ganin gyarar da muke bukatar yi kafin wasu su gan mu. Hakazalika, idan muna karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, za mu ga hanyoyin da za mu gyara tunaninmu da halinmu. Mutane da yawa sun lura cewa karanta nassin yini kowane safe kafin su bar gida yana taimaka musu. Suna barin abin da suka karanta ya shafi yadda suke tunani. Sai su nemi hanyoyin bin shawarar Kalmar Allah a ranar. Ƙari ga haka, wajibi ne kowace rana mu riƙa nazari da kuma bimbini a kan Kalmar Allah. Muna iya yin tunani cewa yin hakan yana da sauƙi, amma yana cikin abubuwa masu muhimmanci da za su taimaka mana mu ci gaba da bin ƙaramar hanya da za ta sa mu sami rai.

KA SAURARI ABOKAI DA SUKA MANYANTA

ABOKAI DA SUKA MANYANTA

Wani ɗan’uwa da ya manyanta yana iya yi mana gargaɗi. Shin muna farin ciki cewa abokinmu yana da ƙarfin zuciya yi mana gargaɗi? (Ka duba sakin layi na 9)

9. A wane lokaci ne abokinka zai yi maka gyara?

9 Shin ka taɓa yin wani abu da ya soma ɓata dangantakarka da Jehobah? (Zab. 73:​2, 3) Idan wani abokinka da ya manyanta ya yi maka gyara, ka saurare shi ne kuma ka bi shawararsa? Idan haka ne, ka yi abin da ya dace, kuma babu shakka ka yi farin ciki cewa abokinka ya yi maka gargaɗi.​—K. Mag. 1:5.

10. Me ya kamata ka yi idan abokinka ya yi maka gyara?

10 Kalmar Allah ta ce: “Aboki aboki ne ko da ya ɓata maka rai.” (K. Mag. 27:6) Mene ne wannan furucin yake nufi? Alal misali: A ce kana son ka tsallake wata hanya sai wayarka ta soma ƙara. Hakan ya sa ka shiga hanyar ba tare da dubawa ba. Nan take, sai abokinka ya riƙe hannunka ya jawo ka. Ya riƙe ka sosai har ya ji maka rauni, amma matakin da ya ɗauka ne ya sa mota ba ta buge ka ba. Duk da cewa raunin da ya ji maka yana maka zafi, ba za ka yi fushi don yadda abokinka ya jawo ka ba. Maimakon haka, za ka nuna godiya don yadda ya taimaka maka. Hakazalika, kana iya yin fushi domin abokinka ya yi maka gargaɗi cewa furucinka ko ayyukanka ba su jitu da ƙa’idodin Allah ba. Amma kada ka ƙi shawararsa ko kuma ka yi fushi. Yin hakan zai sa ka zama wawa. (M. Wa. 7:9) Maimakon haka, ka yi farin ciki cewa abokinka yana da ƙarfin zuciyar yi maka magana.

11. Me zai sa wani ya ƙi bin shawarar abokinsa?

11 Me zai sa wani ya ƙi bin shawara mai kyau da abokinsa ya ba shi? Fahariya ce. Masu fahariya suna son jin abin da kunnensu ke “marmarin ji.” Saboda haka, suna “toshe kunnensu ga jin koyarwar gaskiya.” (2 Tim. 4:​3, 4) A ganinsu, ba sa bukatar shawara domin suna ganin sun fi kowa hikima ko daraja. Amma manzo Bulus ya ce: “In wani yana tsammani shi wani abu ne, amma kuwa shi ba kome ba ne, ruɗin kansa yake yi.” (Gal. 6:3) Sarki Sulemanu ya bayyana hakan da kyau. Ya ce: “Gwamma saurayi mai hikima wanda shi talaka ne, da tsohon sarki mai wawanci wanda ba ya karɓar shawara.”​—M. Wa. 4:13.

12. Kamar yadda aka nuna a Galatiyawa 2:​11-14, wane darasi muka koya daga abin da manzo Bitrus ya yi?

12 Ka yi tunanin abin da Bitrus ya yi sa’ad da Bulus ya yi masa gyara a gaban mutane. (Karanta Galatiyawa 2:​11-14.) Da Bitrus ya yi fushi don yadda Bulus ya yi masa gyara a gaban mutane, amma shi mai hikima ne. Ya amince da gyarar kuma bai riƙe Bulus a zuciya ba. Maimakon haka, daga baya ya kira Bulus “ɗan’uwanmu Bulus wanda muke ƙauna.”​—2 Bit. 3:15.

13. Mene ne ya kamata mu yi tunani a kai kafin mu ba mutum shawara?

13 Idan kana ganin kana bukatar ka ba abokinka shawara, me ya kamata ka tuna? Kafin ka yi wa abokinka magana, ka tambayi kanka, ‘Shin ina ɗaukan kaina a matsayin “mai adalci ne sosai”?’ (M. Wa. 7:16) Mai adalci sosai yana shari’anta mutane bisa nasa ƙa’idodi ba da ƙa’idodin Jehobah ba, kuma wataƙila shi ba mai jin tausayin mutane ba ne. Idan bayan ka bincika kanka, ka ga cewa har ila kana bukatar ka yi wa abokinka gargaɗi, ka gaya masa matsalar kuma ka yi amfani da tambayoyi da za su taimaka masa ya fahimci kuskurensa. Ka tabbata cewa abin da ka faɗa masa ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, kuma ka tuna cewa ba kai ke da hakkin shari’anta abokinka ba, amma kana so ya san ra’ayin Jehobah game da ayyukansa. (Rom. 14:10) Ka yi amfani da abin da ke cikin Kalmar Allah, kuma ka zama mai juyayi kamar Yesu sa’ad da kake ba wani shawara. (K. Mag. 3:5; Mat. 12:20) Me ya sa? Domin Jehobah zai bi da mu yadda muke bi da mutane.​—Yaƙ. 2:13.

KA BI JA-GORANCIN ƘUNGIYAR JEHOBAH

ƘUNGIYAR JEHOBAH

Ƙungiyar Jehobah tana tanada mana littattafai da bidiyoyi da kuma taro da ke taimaka mana mu bi shawarwarin da ke Kalmar Allah. A wasu lokuta, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu tana yin canje-canje a yadda ake gudanar da ayyukanmu (Ka duba sakin layi na 14)

14. Mene ne ƙungiyar Jehobah take mana tanadinsa?

14 Jehobah yana amfani da sashen ƙungiyarsa da ke duniya don ya yi mana ja-goranci. Wannan ƙungiyar tana mana tanadin bidiyoyi da littattafai da kuma shirya taro da ke taimaka mana mu bi shawarwari da ke Kalmar Allah. Muna iya tabbata da waɗannan abubuwan don an ɗauko su daga Littafi Mai Tsarki. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu tana dogara da ruhu mai tsarki don tsai da shawarwari game da hanyar da ta fi kyau na yin wa’azi. Duk da haka, hukumar tana duba waɗannan shawarwari a kai a kai don ta ga ko ya dace a yi gyara. Me ya sa? Domin yanayin “duniyar nan” yana canjawa, kuma wajibi ne ƙungiyar Allah ta bi sabon salo.​—1 Kor. 7:31.

15. Wane ƙalubale ne wasu masu shela suke fuskanta?

15 Babu shakka muna bin duk shawara da ƙungiyar Jehobah take ba mu game da sabon bayani a kan wata koyarwar Littafi Mai Tsarki ko kuma ɗabi’a. Amma me muke yi sa’ad da ta yi canje-canje da suka shafi wasu fannoni na rayuwarmu? Alal misali, a ’yan shekarun baya-bayan nan, farashin kayan gina wuraren taro da kuma gyara su ya ƙaru sosai. Saboda haka, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta ce ikilisiyoyi da yawa su riƙa amfani da Majami’ar Mulki guda. Shi ya sa aka haɗa wasu ikilisiyoyi tare kuma aka sayar da wasu Majami’un Mulki. Ana amfani da kuɗaɗen nan don gina majami’u a wuraren da aka fi bukatar su. Idan kana zama a wurin da ake sayar da majami’u kuma ana haɗa ikilisiyoyi, yana iya yi maka wuya ka saba da sabon yanayin. Yanzu wasu masu shela suna tafiya mai nisa don su halarci taro. Wasu da suka yi aiki tuƙuru don su gina ko kuma gyara wani Majami’ar Mulki ba za su fahimci dalilin da ya sa ake so a sayar da majami’ar yanzu ba. Suna iya tunanin cewa sun ɓata lokacinsu kuma sun yi aikin banza. Duk da haka, suna ba da haɗin kai ga wannan sabon umurni, kuma ya kamata a yaba musu.

16. Ta yaya bin shawarar da ke Kolosiyawa 3:​23, 24, yake taimaka mana mu ci gaba da farin ciki?

16 Za mu ci gaba da farin ciki idan muka tuna cewa Jehobah ne muke wa aiki kuma shi ne ke yi wa ƙungiyarsa ja-goranci. (Karanta Kolosiyawa 3:​23, 24.) Sarki Dauda ya kafa misali mai kyau sa’ad da ya ba da gudummawar kuɗi don gina haikali. Ya ce: “Wane ne ni? Su wane ne ma mutanena har da za mu iya kawo maka bayarwa ta yardar rai? Gama dukan abu daga gare ka suke, kuma daga cikin abin da muka karɓa daga wurinka muka ba ka.” (1 Tar. 29:14) Sa’ad da muka ba da gudummawa, muna ba Jehobah daga cikin abin da ya ba mu. Duk da haka, Jehobah yana farin ciki sosai sa’ad da muka yi amfani da lokacinmu da kuzarinmu da kuma kuɗinmu don mu yi aikinsa.​—2 Kor. 9:7.

KA CI GABA DA TAFIYA A ƘARAMAR HANYAR

17. Me ya sa bai kamata ka yi sanyin gwiwa ba idan zai dace ka yi canje-canje?

17 Wajibi ne mu yi koyi da Yesu idan muna so mu ci gaba da yin tafiya a ƙaramar hanyar da za ta sa mu sami rai. (1 Bit. 2:21) Idan zai dace ka yi canje-canje, kada ka yi sanyin gwiwa. Hakan yana nuna cewa kana so ka bi umurnin Jehobah. Kada ka manta cewa Jehobah ya san mu ajizai ne. Saboda haka, ba ya sa rai cewa za mu yi abubuwa daidai yadda Yesu ya yi.

18. Mene ne za mu yi don mu cim ma maƙasudinmu?

18 Bari dukanmu mu mai da hankali ga albarka da za mu samu a nan gaba kuma mu kasance a shirye mu canja tunaninmu da halinmu da kuma ayyukanmu. (K. Mag. 4:25; Luk. 9:62) Mu ci gaba da zama masu sauƙin kai kuma mu riƙa yin canje-canje. (2 Kor. 13:11) Idan muka yi hakan, “Allah mai ƙauna da salama zai kasance tare da [mu].” Kuma Jehobah zai taimaka mana mu riƙa farin ciki yanzu kuma ya ba mu rai a sabuwar duniya.

WAƘA TA 34 Mu Zama Masu Aminci

^ sakin layi na 5 Yana iya yi wa wasu cikinmu wuya mu canja tunaninmu da halinmu da kuma ayyukanmu. A wannan talifin, za a bayyana dalilin da ya sa muke bukatar mu yi canje-canje da kuma yadda za mu ci gaba da farin ciki sa’ad da muke yin hakan.

^ sakin layi na 76 BAYANI A KAN HOTO: Yayin da wani matashi yake faɗin abin da ya faru da shi don bai tsai da shawara mai kyau ba, ɗan’uwa da ya manyanta (a hannun dama) yana sauraransa da kyau don ya ga ko yana bukatar ya yi masa gargaɗi.