Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Furucin manzo Bulus da ke 1 Korintiyawa 15:29 yana nufin cewa wasu Kiristoci a zamanin dā sun yi baftisma ne a madadin matattu?

A’a, Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan tahiri ba su nuna cewa Kiristoci a dā sun yi baftisma a madadin matattu ba.

Yadda aka fassara wannan ayar a juyin Littafi Mai Tsarki da yawa ya sa wasu mutane tunani cewa an yi baftisma a madadin matattu a zamanin Bulus. Alal misali, ayar a juyin New International Version ta ce: “Idan ba za a ta da matattu ba, mene ne waɗanda aka yi musu baftisma a madadin matattu za su yi?”

Wani masani mai suna Dokta Gregory Lockwood ya ce babu wata aya a Littafi Mai Tsarki ko kuma a littafin tarihi da ya tabbatar cewa an yi wa wani baftisma a madadin wani mutumin da ya mutu. Ƙari ga haka, Farfesa Gordon D. Fee ya ce: “Babu wani misali a Littafi Mai Tsarki ko kuma a littafin tarihi cewa an yi irin wannan baftismar. Ba a ambata hakan a Sabuwar Alkawari ba, babu abin da ya tabbatar da cewa Kiristoci a dā sun yi haka ko kuma an yi hakan a cocin da aka kafa jim kaɗan bayan manzannin Yesu sun mutu.”

Yesu ya umurci mabiyansa cewa: “Ku je ku faɗa wa dukan al’umman duniya su bi ni, ku sa su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma . . . , ku kuma koya musu su yi biyayya da dukan abubuwan da na umarce ku.” (Mat. 28:​19, 20) Kafin mutum ya zama mabiyin Yesu da ya yi baftisma, yana bukatar ya koya game da Jehobah da Yesu, ya yi imani da su kuma ya riƙa yi musu biyayya. Mutumin da ya mutu ba zai iya yin waɗannan abubuwan ba, kuma Kirista da ke raye ba zai iya yin su a madadinsa ba.​—M. Wa. 9:​5, 10; Yoh. 4:1; 1 Kor. 1:​14-16.

To, mene ne Bulus yake nufi?

Wasu mutane a Koranti sun ce ba za a ta da matattu ba. (1 Kor. 15:12) Bulus ya ƙaryata wannan ra’ayin. Ya bayyana musu cewa a kullum, ya fuskanci yanayoyin da za su iya sa ya rasa ransa. Amma duk da matsalolin da ya fuskanta, ya kasance da tabbaci cewa bayan ya mutu, za a ta da shi da jiki na ruhu kuma zai yi rayuwa a sama.​—1 Kor. 15:​30-32, 42-44.

’Yan’uwa a Koranti suna bukatar su fahimci cewa ko da yake su shafaffu ne, za su fuskanci matsaloli sosai a rayuwa kuma su mutu kafin a ta da su. Saboda haka, sa’ad da aka yi musu “baftisma zuwa cikin Almasihu Yesu,” hakan yana nufin cewa sun yi baftisma zuwa “cikin mutuwarsa.” (Rom. 6:3) Kamar Yesu, za su fuskanci matsaloli kuma su mutu kafin a ta da su.

Fiye da shekara biyu bayan an yi wa Yesu baftisma, ya gaya wa mabiyansa cewa: “Za a yi muku baftisma kuma da baftismar da za a yi mini.” (Mar. 10:​38, 39) A lokacin, ba a yi wa Yesu baftisma a ruwa ba tukun. Yana nufin cewa kasancewa da aminci ga Allah zai sa a kashe shi. Bulus ya rubuta cewa shafaffu za su ‘sha wahala tare da Almasihu, domin kuma a ɗaukaka su tare.’ (Rom. 8:​16, 17; 2 Kor. 4:17) Saboda haka, su ma za su mutu kafin a ta da su zuwa sama.

Don haka, ga ainihin abin da Bulus yake nufi: “In ba haka ba, mene ne waɗanda ake yi wa baftisma don su zama matattu za su yi? Idan ba za a ta da matattu ba sam, don me ake yi musu irin wannan baftismar?”