Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Littafin Karin Magana 24:​16, ta ce: “Ko da mai adalci ya fāɗi sau bakwai, zai tashi.” Shin wannan furucin yana magana ne game da mutum da ya yi zunubi a kai a kai, kuma Allah ya gafarta masa?

Ba abin da wannan ayar take nufi ke nan ba. Maimakon haka, wannan ayar tana magana ne game da mutumin da yake fuskantar matsaloli da yawa, amma ya ci gaba da jimrewa.

Bari mu duba ayoyin da ke kusa da wannan ayar. Sun ce: ‘Kada ka zama kamar mugu, kana yi wa gidan mai adalci kwanton ɓauna, kada ka ɓata gidan masu adalci. Gama ko da mai adalci ya fāɗi sau bakwai, zai tashi sau bakwai kuma, amma masifa ɗaya takan halaka mugaye. Kada ka yi farin ciki sa’ad da abokin gābanka ya fāɗi, sa’ad da kuma ya yi tuntuɓe, kada ka yi murna a zuciyarka.’​—K. Mag. 24:​15-17.

Wasu mutane suna tunanin cewa aya ta 16 tana magana game da mutum da ya yi zunubi, amma ya tuba kuma ya sake ƙulla dangantaka da Allah. Wasu limamai biyu ’yan Birtaniya sun ce “masu wa’azi a dā da kuma a zamani sun ce abin da ayar take nufi ke nan.” Limaman sun daɗa cewa kasancewa da wannan ra’ayin yana nufin cewa “mutumin kirki yana iya yin . . . zunubai masu tsanani, har ila yana ƙaunar Allah kuma yakan tuba a kowane lokaci da ya yi zunubin.” Mutumin da ba ya so ya daina yin zunubi zai so wannan bayanin. Yana iya yin tunani cewa ko da ya yi zunubi a kai a kai, Allah zai gafarta masa.

Amma ba abin da aya ta 16 take nufi ke nan ba.

A Ibrananci, ana yin amfani da kalmar nan “faɗi” da ke ayoyi 16 da 17 a hanyoyi dabam-dabam. Kalmar tana iya nufin faɗuwa a zahiri. Alal misali, wata dabba ta faɗi a hanya ko mutum ya faɗi daga rufin gida ko kuma dutse ya faɗo ƙasa. (M. Sha. 22:​4, 8; Amos 9:9) Amma kalmar tana iya kasancewa da wata ma’ana dabam. Alal misali, a alamance ana iya cewa: “Idan Yahweh yana farin ciki da hanyar rayuwar mutum yakan kiyaye tafiyarsa da tabbaci. Ko da ma ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Yahweh yakan riƙe shi da hannunsa.”​—Zab. 37:​23, 24; K. Mag. 11:5; 13:17; 17:20.

Wani Farfesa mai suna Edward H. Plumptre ya ce: “A Ibrananci, ba a yin amfani da kalmar nan [“faɗi”] sa’ad da ake magana game da yin zunubi.” Saboda haka, wani masani ya ce aya ta 16 tana nufin: “Ba shi da amfani a wulaƙanta mutanen Allah domin za su yi nasara, amma mugaye ba za su yi nasara ba!”

Saboda haka, waɗannan bayanan sun nuna cewa Karin Magana 24:16 ba ta magana game da yin zunubi, amma game da fuskantar matsaloli a kai a kai. A wannan zamani, mai adalci yana iya yin rashin lafiya ko kuma ya fuskanci wasu matsaloli. Ban da haka, hukumomi suna iya tsananta masa don imaninsa. Amma ya san cewa Allah zai taimaka masa ya jimre da yanayin kuma ya yi nasara. Babu shakka, kana yawan ganin yadda Allah ya taimaka wa bayinsa su yi nasara. Muna da tabbaci cewa Jehobah yana ‘riƙe dukan waɗanda suke fāɗuwa, yakan tā da dukan waɗanda suke ƙarƙashin danniya.’​—Zab. 41:​1-3; 145:​14-19.

Don haka, “mai adalci” ba ya farin ciki domin wasu suna fuskantar matsaloli. Maimakon haka, yana samun ƙarfafa domin ya san cewa “idan mutum yana tsoron Allah, yana kuma girmama shi, kome zai tafi daidai.”​—M. Wa. 8:​11-13; Ayu. 31:​3-6; Zab. 27:​5, 6.