Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 52

Yadda Za Ka Daina Yin Sanyin Gwiwa

Yadda Za Ka Daina Yin Sanyin Gwiwa

Ka “danƙa wa Yahweh damuwarka, shi kuwa zai lura da kai.”​—ZAB. 55:22.

WAƘA TA 33 Mu Miƙa Dukan Damuwarmu ga Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Ta yaya yin sanyin gwiwa zai shafe mu?

A KOWACE rana, muna fuskantar matsaloli kuma muna yin iya ƙoƙarinmu don mu jimre da su. Amma zai yi mana wuya mu magance matsalolinmu sa’ad da muke sanyin gwiwa. Saboda haka, ya kamata mu san cewa sanyin gwiwa zai iya sa mu ji kamar ba mu da amfani kuma ya hana mu farin ciki. Littafin Karin Magana 24:​10, ta ce: “In ka nuna jikinka ya mutu a ranar wahala, to, lallai ba ka da ƙarfi ke nan.” Hakika, yin sanyin gwiwa yana iya sa mu kasa jimre da matsaloli.

2. Waɗanne abubuwa ne za su sa mu sanyin gwiwa, kuma mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Abubuwa da yawa suna iya sa mu sanyin gwiwa. Waɗannan abubuwa sun ƙunshi ajizancinmu ko kasawarmu ko kuma rashin lafiya. Muna iya yin sanyin gwiwa don ba a ba mu aikin da muke so a hidimar Jehobah ba ko kuma muna wa’azi a yankin da yawancin mutane ba sa saurarar mu. A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwan da za mu iya yi don mu daina sanyin gwiwa.

SA’AD DA MUKE FAMA DA AJIZANCINMU DA KASAWARMU

3. Me zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kurakuranmu?

3 Yana da sauƙi mu kasance da ra’ayin da bai dace game da ajizancinmu da kuma kasawarmu. Saboda haka, muna iya ganin cewa Jehobah ba zai sa mu shiga Aljanna ba domin kurakuranmu. Kasancewa da irin wannan ra’ayin yana da lahani. Yaya ya kamata mu riƙa ɗaukan kurakuranmu? Littafi Mai Tsarki ya ce, ban da Yesu dukan ’yan Adam sun “yi zunubi.” (Rom. 3:23) Jehobah ba ya mai da hankali ga kurakuranmu ko kuma ya riƙa ganin cewa ya kamata mu riƙa yin abubuwa kamar kamiltattu. Maimakon haka, shi Uba ne mai ƙauna da yake so ya taimaka mana. Kuma yana haƙuri da mu. Ƙari ga haka, ya san irin famar da muke yi da kasawarmu da kuma yadda kurakurenmu sake sa mu baƙin ciki, kuma yana a shirye ya taimaka mana.​—Rom. 7:​18, 19.

Jehobah yana daraja abubuwa masu kyau da muka yi a dā da waɗanda muke yi yanzu (Ka duba sakin layi na 5) *

4-5. Kamar yadda littafin 1 Yohanna 3:​19, 20 suka nuna, me ya taimaka wa wasu ’yan’uwa mata biyu su daina sanyin gwiwa?

4 Ka yi la’akari da labarin Deborah da Maria. * Sa’ad da Deborah take ƙarama, iyalinta sun wulaƙanta ta, kuma da ƙyar suke yaba mata. Saboda haka, sa’ad da ta yi girma sai ta soma ganin ba ta da amfani. A lokacin da ta ɗan yi kuskure, tana ganin ba za ta iya yin kome daidai ba. Ita ma Maria tana da irin wannan matsala. Danginta sun wulaƙanta ta. Saboda haka, tana ganin ba ta da amfani. Har ma bayan da ta yi baftisma, ta ɗauka cewa ba ta cancanci zama Mashaidiyar Jehobah ba!

5 Duk da haka, waɗannan ’yan’uwa mata biyu sun ci gaba da bauta wa Jehobah. Me ya sa? Domin sun yi addu’a ga Jehobah kuma suka gaya masa yadda suke ji. (Zab. 55:22) Sun koyi cewa Jehobah ya san cewa abubuwan da suka faru da mu suna iya sa mu riƙa ganin ba mu da amfani. Amma, Jehobah yana ganin halayenmu masu kyau, ko da ba ma ganin hakan.​—Karanta 1 Yohanna 3:​19, 20.

6. Mene ne mutum zai iya yi idan ya sake yin kuskure da ya yi a dā?

6 Wani yana iya fama sosai don ya daina wani mugun hali. Amma yana iya sake yin kuskure kuma hakan yana iya sa shi sanyin gwiwa. Hakika, mukan yi baƙin ciki sa’ad da muka yi zunubi. (2 Kor. 7:10) Duk da haka, bai kamata mu riƙa baƙin ciki ainun kuma mu riƙa tunanin cewa ‘Ba ni da amfani kuma Jehobah ba zai taɓa gafarta mini ba.’ Hakan ba gaskiya ba ne, kuma irin wannan ra’ayin na iya sa mu daina bauta wa Jehobah. Ka tuna cewa littafin Karin Magana 24:10 ya ce ba za mu kasance da ƙarfi ba idan mun yi sanyin gwiwa. Maimakon haka, ka “shirya” da Jehobah ta wajen roƙon sa ya gafarta maka. (Isha. 1:18) Jehobah zai gafarta maka idan ya ga cewa ka yi da-na-sani don zunubinka kuma kana ƙoƙari sosai don ka tuba. Ƙari ga haka, ka nemi taimakon dattawa, don za su taimaka maka ka magance matsalarka.​—Yaƙ. 5:​14, 15.

7. Me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa ba idan muna fama mu yi abin da ya dace?

7 Wani dattijo mai suna Jean-Luc a ƙasar Faransa ya gaya wa waɗanda suke fama da kasawarsu cewa: “A gaban Jehobah, mai adalci ba wanda bai taɓa yin kuskure ba ne, amma wanda ya yi da-na-sani kuma yana ƙoƙari ya tuba.” (Rom. 7:​21-25) Saboda haka, kada ka ɗauka cewa ba ka da amfani idan kana fama da wata kasawa. Domin dukanmu muna yin kuskure, muna bukatar alherin da Jehobah yake mana don hadayar Yesu.​—Afis. 1:7; 1 Yoh. 4:10.

8. Wane ne zai iya taimaka mana sa’ad da muke sanyin gwiwa?

8 ’Yan’uwanmu za su ƙarfafa mu! Za su saurare mu sa’ad da muke gaya musu abin da ke damunmu, kuma za su ƙarfafa mu. (K. Mag. 12:25; 1 Tas. 5:14) Wata ’yar’uwa a Nijeriya mai suna Joy da ta yi fama da sanyin gwiwa ta ce: “’Yan’uwa sun taimaka mini sosai. Sun tabbatar mini cewa Jehobah yana amsa addu’o’ina. Na koyi yadda ake ƙarfafa waɗanda suka yi sanyin gwiwa daga wajensu.” Amma, ya kamata mu riƙa tuna cewa ba a kowane lokaci ba ne ’yan’uwanmu za su san cewa muna bukatar ƙarfafa ba. Saboda haka, zai dace mu nemi taimakon wani ɗan’uwa ko ’yar’uwar da ta manyanta idan bukata ta taso.

SA’AD DA MUKE FAMA DA RASHIN LAFIYA

9. Ta yaya Zabura 41:3 da 94:19 suke ƙarfafa mu?

9 Ka nemi taimakon Jehobah. Sa’ad da muka jima muna rashin lafiya, zai yi mana wuya mu kasance da ra’ayin da ya dace. Jehobah ba zai warkar da mu ta hanyar mu’ujiza ba, amma zai ƙarfafa mu kuma ya ba mu ƙarfin jimre da yanayin. (Karanta Zabura 41:3; 94:19.) Alal misali, Jehobah zai iya sa ’yan’uwa su taimaka mana da aikace-aikacen gida ko kuma cefane. Zai iya sa ’yan’uwa su yi addu’a da mu ko kuma ya sa mu tuna da kalmomi masu ban-ƙarfafa da ke cikin Kalmarsa. Waɗannan kalmomin sun ƙunshi begen yin rayuwa ba tare da rashin lafiya da azaba ba a sabuwar duniya da ke nan tafe.​—Rom. 15:4.

10. Me ya taimaka wa Ɗan’uwa Isang ya daina sanyin gwiwa?

10 Akwai wani ɗan’uwa a Nijeriya mai suna Isang da ya yi hatsari. Bayan haka, sai likitansa ya gaya masa cewa ba zai sake tafiya ba. Isang ya ce: “Hakan ya sa ni baƙin ciki da kuma sanyin gwiwa sosai.” Mene ne ya taimaka masa ya daina baƙin ciki? Isang ya ce: “Ni da matata ba mu daina yin addu’a ga Jehobah ba, kuma ba mu daina nazarin Kalmarsa ba. Kuma mun ƙuduri niyyar mu ci gaba da yin godiya don abubuwa da muke da su, da kuma begenmu na yin rayuwa a sabuwar duniya.”

Har waɗanda suke rashin lafiya da tsofaffi suna iya yin wa’azi (Ka duba sakin layi na 11-13)

11. Ta yaya Cindy ta yi farin ciki sa’ad da take rashin lafiya?

11 Likita ya gaya wa wata ’yar’uwa a ƙasar Meziko mai suna Cindy cewa tana da cutar da za ta yi ajalinta. Mene ne ya taimaka mata ta jimre? Sa’ad da take jinya, ta kafa maƙasudin yin wa’azi kowace rana. Ta ce: “Yin hakan ya taimaka min in mai da hankali ga wasu maimakon in riƙa tunanin tiyata da zan yi ko zafin da nake ji ko kuma rashin lafiyata. Ga abin da nake yi: Sa’ad da nake tattaunawa da likitoci ko nas, nakan tambaye su game da iyalansu. Sai in tambaye su dalilin da ya sa suka zaɓi wannan aiki mai wuya sosai. Hakan yana sa ya yi mini sauƙi in san batun da zan tattauna da su. Da yawa a cikinsu sun gaya mini cewa yana da wuya majiyata su tambaye su yadda suke. Kuma da yawa sun gode mini don yadda na damu da su. Wasu ma sun ba ni adireshinsu da lambar wayarsu. Saboda haka, a wannan mawuyacin lokaci a rayuwata, Jehobah ya sa in jimre kuma ya sa in yi farin ciki.”​—K. Mag. 15:15.

12-13. Ta yaya wasu da ke rashin lafiya ko tsofaffi suke wa’azi, kuma wane sakamako suke samu?

12 Marasa lafiya ko waɗanda ba sa iya fita waje saboda rashin lafiya sukan yi sanyin gwiwa domin ba sa iya yin wa’azi yadda suke so. Duk da haka, da yawa sun nemi hanyoyin yin wa’azi. An saka wata ’yar’uwa a Amirka mai suna Laurel a cikin wata na’urar yin numfashi har shekara 37! Tana da ciwon kansa, an yi mata tiyata sau da yawa kuma tana fama da cutar fata. Amma dukan waɗannan matsaloli masu tsanani ba su hana ta yin wa’azi ba. Ta yi wa’azi ga ma’aikatan kiwon lafiya da kuma wasu da suka zo gidanta. Mene ne sakamakon? Ta taimaka wa mutane 17 su koya game da Jehobah! *

13 Wani dattijo a Faransa mai suna Richard ya ba da wannan shawara ga waɗanda ba sa iya fita waje saboda rashin lafiya ko kuma waɗanda suke gidan kula da tsofaffi. Ya ce: “Ku riƙa ajiye wasu littattafanmu da mujallu a wurin da mutane za su gani. Hakan zai sa mutane da suke wucewa su gani kuma su faɗi abin da zai sa a tattauna da su. Wannan tattaunawar za ta ƙarfafa ’yan’uwanmu da ba sa iya yin wa’azi gida-gida.” Waɗanda ba sa iya fita waje suna iya yin wa’azi ta hanyar wasiƙa ko kuma waya.

SA’AD DA BA A BA MU AIKIN DA MUKE SO BA

14. Wane misali mai kyau ne Sarki Dauda ya kafa?

14 Wataƙila ba a ba mu aikin da muke so a ƙungiyar Jehobah ba don mun tsufa sosai ko muna rashin lafiya ko kuma don wasu abubuwa. Idan muna cikin wannan yanayin, muna iya koyan darasi daga abin da ya faru da Sarki Dauda. Dauda yana so ya gina haikalin Allah, amma Jehobah ya zaɓi wani ya yi ginin. Dauda ya tallafa wa wanda aka zaɓa ya yi hakan ta wajen ba da zinariya da azurfa masu yawan gaske. Babu shakka, Dauda ya kafa mana misali mai kyau!​—2 Sam. 7:​12, 13; 1 Tar. 29:​1, 3-5.

15. Ta yaya Hugues ya daina sanyin gwiwa?

15 Wani ɗan’uwa a Faransa mai suna Hugues ya daina hidimar dattijo domin yana rashin lafiya sosai har ma ba zai iya yin ayyuka masu sauƙi a gida ba. Ya ce: “Da farko na yi sanyin gwiwa sosai, har na ɗauka ba ni da amfani. Amma da shigewar lokaci, na ga muhimmancin amincewa da kasawata, kuma na yi farin ciki cewa ina yin iya ƙoƙarina a hidimar Jehobah. Na ƙuduri niyya cewa ba zan fid da rai ba. Zan riƙa ƙoƙartawa, kamar Gidiyon da mutanensa ɗari uku da suka ci gaba da bin abokan gābansu duk da cewa sun gaji!”​—Alƙa. 8:4.

16. Mene ne za mu iya koya daga mala’iku?

16 Mala’iku sun kafa mana misali mai kyau. Alal misali, a lokacin da Sarki Ahab yake mulki, Jehobah ya gaya wa mala’iku su faɗi hanyoyin da za a iya yaudarar mugun sarkin. Wasu mala’iku sun faɗi hanyoyin da za a iya yin hakan. Amma Allah ya zaɓi mala’ika ɗaya kuma ya gaya masa cewa za a bi shawararsa. (1 Sar. 22:​19-22) Shin sauran mala’ikun sun yi sanyin gwiwa, suna tunani cewa, ‘Me ya sa na ɓata lokacina kuma na ba da shawara?’ Hakika ba su yi hakan ba don mala’ikun masu sauƙin kai ne kuma suna son a ɗaukaka Jehobah.​—Alƙa. 13:​16-18; R. Yar. 19:10.

17. Me ya kamata mu yi sa’ad da muka yi sanyin gwiwa don ba a ba mu wasu ayyuka a ƙungiyar Jehobah ba?

17 Ka mai da hankali ga gata mafi muhimmanci da kake da shi na yin wa’azi. Muna iya samun aiki, kuma za a iya karɓe aikin daga hannunmu, amma ba waɗannan ayyuka ba ne suke sa mu kasance da daraja a gaban Allah ba. Kasancewa da sauƙin kai ne yake sa Jehobah da ’yan’uwanmu su ƙaunace mu. Saboda haka, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka kasance da sauƙin kai. Ka yi tunani a kan misalai masu kyau na bayin Jehobah masu sauƙin kai da aka rubuta a cikin Kalmarsa. Ka yi iya ƙoƙarinka don ka taimaka wa ’yan’uwanka.​—Zab. 138:6; 1 Bit. 5:5.

SA’AD DA MUTANE BA SA SO SU JI WA’AZI

18-19. Me zai taimaka maka ka ci gaba da farin ciki idan mutanen yankinku ba sa saurarar wa’azi?

18 Ka taɓa sanyin gwiwa ne don mutane ba sa son saurarar wa’azi a yankinku ko kuma don ba ka samun su sosai a gida? Ta yaya za mu ci gaba da yin farin ciki a irin wannan yanayin? An ba da wasu shawarwari masu kyau a akwatin nan “ Hanyoyin da Za Ka Inganta Hidimarka.” Yana da muhimmanci mu kasance da ra’ayin da ya dace game da hidimarmu. Mene ne hakan yake nufi?

19 Ka mai da hankali ga yin shelar sunan Allah da Mulkinsa. Yesu ya ce mutane kaɗan ne za su bi shi. (Mat. 7:​13, 14) Muna da damar yin aiki da Jehobah da Yesu da kuma mala’iku sa’ad da muke wa’azi. (Mat. 28:​19, 20; 1 Kor. 3:9; R. Yar. 14:​6, 7) Jehobah yana neman mutanen da suke so su bauta masa. (Yoh. 6:44) Saboda haka, idan wani ba ya so ya saurari wa’azinmu yanzu, yana iya saurarar mu a wani lokaci.

20. Kamar yadda Irmiya 20:​8, 9 suka nuna, ta yaya za mu magance sanyin gwiwa?

20 Muna iya koyan darasi daga annabi Irmiya. An tura shi yin hidima a yankin da mutane ba so su saurare shi. Mutanen sun zazzage shi, kuma sun yi masa ba’a “dukan yini.” (Karanta Irmiya 20:​8, 9.) Hakan ya sa shi sanyin gwiwa sosai, har ya so ya daina yin wa’azi. Amma bai yi hakan ba. Me ya sa? Domin ‘maganar’ Jehobah ta zama kamar wuta da take ci a zuciyar Irmiya, kuma ya gaji da riƙe ta! Muna iya zama kamar Irmiya idan muna nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai kuma muka yi bimbini sosai a kansa. Idan muka yi hakan, za mu yi farin ciki sosai a hidimarmu kuma mutane suna iya saurarar mu.​—Irm. 15:16.

21. Ko da mene ne yake sa mu sanyin gwiwa, me zai taimaka mana mu daina yin hakan?

21 Deborah da aka ambata ɗazu ta ce: “Shaiɗan yana sa mu yi sanyin gwiwa.” Amma Jehobah ya fi Shaiɗan da dukan makamansa ƙarfi. Saboda haka, ko da mene ne yake so ya sa ka sanyin gwiwa, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Zai taimaka maka ka magance ajizancinka da kuma kasawarka. Ƙari ga haka, zai taimaka maka sa’ad da kake rashin lafiya. Zai taimaka maka ka kasance da ra’ayin da ya dace game da samun ayyuka a hidimarsa. Kuma zai taimaka maka ka kasance da ra’ayin da ya dace game da hidimarka. Ban da haka, ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka gaya masa ainihi yadda kake ji. Zai taimaka maka ka daina sanyin gwiwa.

WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona

^ sakin layi na 5 Dukanmu muna yin sanyin gwiwa a wasu lokuta. A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwan da za mu iya yi sa’ad da muke sanyin gwiwa. Kuma za mu ga yadda Jehobah zai iya taimaka mana mu daina sanyin gwiwa.

^ sakin layi na 4 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 12 Ka karanta labarin Laurel Nisbet a Awake! na 22 ga Janairu, 1993.

^ sakin layi na 69 BAYANI A KAN HOTUNA: Akwai lokacin da wata ’yar’uwa ta yi sanyin gwiwa, amma ta yi tunani a kan hidimar da ta yi a dā kuma ta yi addu’a ga Jehobah. Ta tabbata cewa Jehobah ya tuna da abin da ta yi a dā da kuma abin da take yi a yanzu.