Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Yi Aikin da Aka Ba Ka da Ƙwazo!

Ka Yi Aikin da Aka Ba Ka da Ƙwazo!

YAYA kake ji sa’ad da abokinka ya turo maka wasiƙa mai ban-ƙarfafa? Timoti ya sami irin wannan wasiƙa daga manzo Bulus, kuma wasiƙar ita ce littafin 2 Timoti. Babu shakka, Timoti ya nemi wurin da babu surutu don ya karanta wasiƙar da abokinsa ya turo masa. Wataƙila ya yi tunani cewa: ‘Bulus yana nan lafiya kuwa?’ Shin yana da shawarar da zai ba ni game da hidimata? Wasiƙar nan za ta iya taimaka mini in yi nasara a hidimata kuma in taimaka wa mutane? Kamar yadda za mu gani, Timoti ya sami amsoshin waɗannan tambayoyin da kuma wasu a wannan wasiƙa mai muhimmanci. A wannan talifin, za mu mai da hankali ga wasu shawarwari masu muhimmanci da ke wannan wasiƙar.

“NA JIMRE DA KOME”

A lokacin da Timoti ya soma karanta wasiƙar da Bulus ya aiko masa, ya lura cewa dangantakarsu tana da danƙo. Bulus ya kira Timoti “ɗana wanda nake ƙauna.” (2 Tim. 1:2) A lokacin da aka tura wa Timoti wannan wasiƙa a shekara ta 65, shi ɗan shekara 30 da wani abu ne, kuma shi dattijo ne da ya manyanta. Ya riga ya yi fiye da shekara goma yana hidima da Bulus kuma ya koyi abubuwa da dama.

Sanin cewa Bulus yana jimre matsalolin da yake fuskanta ya ƙarfafa Timoti. An saka Bulus a kurkuku a Roma, kuma ba da daɗewa ba za a kashe shi. (2 Tim. 1:​15, 16; 4:​6-8) Timoti ya san cewa Bulus yana da ƙarfin zuciya domin ya ce: “Na jimre da kome.” (2 Tim. 2:​8-13) Kamar Timoti, yadda Bulus ya jimre zai iya ƙarfafa mu.

“KA RURA BAIWAN”

Bulus ya ƙarfafa Timoti ya ɗauki hidimarsa ga Allah da muhimmanci. Bulus yana so Timoti ya ‘rura baiwar’ da Allah ya ba shi, yadda ake rura wuta. (2 Tim. 1:​6, Littafi Mai Tsarki.) Bulus ya yi amfani da kalmar Helenancin nan khaʹri·sma sa’ad da yake magana game da “baiwa.” Wannan kalmar tana nufin baiwar da aka ba mutum kuma bai cancanci samun baiwar ba. Timoti ya samu wannan baiwar sa’ad da aka ba shi aiki na musamman a ikilisiya.​—1 Tim. 4:14.

Mene ne Timoti zai yi da wannan baiwar? Sa’ad da yake karanta furucin nan ‘ka rura baiwar,’ wataƙila ya yi tunanin yadda a wasu lokuta wutar da muke dafa abinci da ita take mutuwa ta zama garwashi. Wajibi ne a rura wannan garwashin don ya sake kama wuta. Wani ƙamus ya ce kalmar Helenancin nan a·na·zo·py·reʹo da Bulus ya yi amfani da ita tana nufin “rura wuta ko sa abu ya farfaɗo.” Don haka, furucinsa yana nufin mutum ya yi farin ciki da kuma saka ƙwazo a aikinsa. A taƙaice, Bulus yana ƙarfafa Timoti cewa: “Ka yi aikin da aka ba ka da ƙwazo!” Mu ma a yau muna bukatar mu saka ƙwazo a hidimarmu.

KA KULA DA AMANAR NAN DA AKA BA KA

A wannan wasiƙar, Bulus ya sake faɗan wani abu da zai taimaka wa Timoti ya yi nasara a hidimarsa. Bulus ya ce: “Ta wurin taimakon ruhu mai tsarkin da yake zaune a cikinmu, ka kula da wannan koyarwa ta gaskiyar da aka ba ka amanarta.” (2 Tim. 1:14) Mece ce wannan amanar? Wane abu ne aka ba Timoti amana? A ayar da ta gabata, Bulus ya yi magana game da ‘koyarwa ta gaskiya’ da ke cikin kalmar Allah. (2 Tim. 1:13) Tun da yake Timoti mai shela ne, wajibi ne ya koya wa ’yan’uwa a ikilisiya da kuma mutane a yankinsu gaskiya. (2 Tim. 4:​1-5) Ƙari ga haka, an naɗa Timoti dattijo don ya kula da tumakin Allah. (1 Bit. 5:2) Timoti zai kula da wannan amanar da aka ba shi ta wajen dogara ga ruhun Jehobah da kuma Kalmarsa.​—2 Tim. 3:​14-17.

A yau, mu ma an ba mu amanar koya wa mutane gaskiya. (Mat. 28:​19, 20) Za mu nuna godiya don wannan amanar ta wajen yin addu’a da kuma yin nazarin Kalmar Allah a kai a kai. (Rom. 12:​11, 12; 1 Tim. 4:​13, 15, 16) Ƙari ga haka, muna iya samun ƙarin aiki na yin hidima a matsayin dattijo ko kuma yin hidima ta cikakken lokaci. Ya kamata irin wannan aikin ya sa mu kasance da sauƙin kai kuma mu dogara ga Allah. Saboda haka, za mu iya kula da wannan amanar da aka ba mu da kuma daraja ta idan mun dogara ga Jehobah don ya taimaka mana.

“KA DANƘA WA MUTANE MASU AMINCI”

Aikin Timoti ya ƙunshi horar da wasu su yi irin ayyukan da yake yi. Shi ya sa Bulus ya umurce shi cewa: “Duk koyarwar da ka ji daga gare ni . . . , sai ka danƙa wa mutane masu aminci, waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu.” (2 Tim. 2:2) Bulus ya gaya wa Timoti ya koya wa wasu ’yan’uwa dukan abubuwan da ya koya. Yana da muhimmanci kowane dattijo a ikilisiya ya yi abin da Timoti ya yi. Dattijo nagari ba zai ɓoye abubuwan da ya sani game da wani aiki ba. A maimakon haka, zai koya wa wasu don su ma su iya yin aikin da yake yi. Ba ya jin tsoro cewa za su fi shi iya yin aikin. Saboda haka, dattijo ba zai koyar da wasu abubuwa game da aikin da yake yi kaɗai ba. Ya kamata ya taimaka wa waɗanda yake horarwa su san abin da ya wajaba su yi kuma su manyanta. Ta yin hakan, “mutane masu aminci” da ya horar za su sami ci gaba kuma su taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya.

Babu shakka, Timoti ya daraja wasiƙar da Bulus ya tura masa. Wataƙila ya karanta wannan wasiƙa a kai a kai kuma ya yi tunani a kan yadda zai bi shawarwarin masu kyau a hidimarsa.

Ya kamata mu riƙa bin wannan shawarar. Ta yaya za mu yi hakan? Mu yi iya ƙoƙarinmu don mu rura baiwar da aka ba mu, mu kula da baiwar kuma mu koya wa mutane dukan abubuwan da muka sani. Ta yin hakan, kamar yadda Bulus ya gaya wa Timoti, za mu ‘cika hidimarmu.’​—2 Tim. 4:5.