Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ra’ayoyin Mutane Game da Yin Addu’a

Ra’ayoyin Mutane Game da Yin Addu’a

“Idan ina yin addu’a, ina ji kamar Allah yana tare da ni, yana yi mini ja-gora a duk lokacin da na rasa na yi.”​—MARÍA.

“Matata ta rasu bayan ta yi shekaru 13 tana fama da cutar kansa. Na tuna yadda na yi ta addu’a ga Allah kowace rana kuma nakan ji a zuciyata cewa yana sauraro na. Hakan ya kwantar mini da hankali.”​—RAÚL.

“Yin addu’a babban gata ne da Allah ya ba wa ’yan Adam.”​—ARNE.

María da Raúl da Arne da ma wasu mutane da yawa suna ganin addu’a kyauta ce mai daraja da Allah ya ba mu. Ta wajen addu’a ne suke iya magana da Allah, su gode masa kuma su roƙe shi ya taimaka musu. Sun yi imani cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da addu’a gaskiya ne. Ya ce: “Wannan ne tabbacin da muke da shi a gaban Allah, wato, idan mun roƙi kome bisa ga nufinsa, zai saurare mu.”​—1 Yohanna 5:14.

Amma akwai wasu mutane da yawa da ba su amince da hakan ba. Steve ya bayyana ra’ayinsa game da addu’a. Ya ce: “Sa’ad da nake shekara 17, abokaina guda uku sun rasu, ɗaya ta sanadiyyar hatsarin mota, biyu kuma sun nitse a teku kuma suka mutu.” Mene ne Steve ya yi? Ya ce, “Na yi addu’a ga Allah kuma na tambaye shi me ya sa hakan ya faru? Amma na ji shiru. Sai na ce wa kaina, ‘Me amfanin yin addu’a ma?’ ” Mutane da yawa suna ganin tun da ba a amsa addu’arsu, gwamma su daina yin addu’ar.

Akwai wasu dalilai kuma da suka sa mutane suke ganin addu’a ba ta da amfani. Wasu sun ce tun da Allah yana ganin matsalolin da muke fuskanta kuma ya san bukatunmu, ba sai mun gaya masa game da su ba.

Wasu kuma suna ganin cewa Allah yana ƙin amsa addu’arsu ne saboda kurakuren da suka yi a baya. Jenny ta ce: “Matsalata ita ce ina yawan ji kamar ba ni da daraja. Na yi abubuwa da yawa da na yi da-na-saninsu, don haka nakan gaya wa kaina cewa ban cancanci Allah ya ji addu’ata ba.”

Kai fa, kana ganin addu’a tana da amfani? Idan kana shakkar amfanin yin addu’a, abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wannan batun zai taimaka maka. Littafi Mai Tsarki ya faɗi gaskiya game da yin addu’a, * kuma zai taimaka maka ka sami amsoshin tambayoyin nan:

  • Allah yana jin addu’o’inmu kuwa?

  • Me ya sa Allah ba ya amsa wasu addu’o’i?

  • Ta yaya za ka yi addu’a kuma Allah ya amsa?

  • Ta yaya yin addu’a zai amfane ka?

^ sakin layi na 9 A cikin Littafi Mai Tsarki, an ambata addu’o’in da bayin Allah suka yi har da Yesu Almasihu. An ambata addu’o’i fiye da 150 a Nassosin Ibrananci wanda ake yawan kira Tsohon Alkawari.