Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Za ka iya yin shiri tun yanzu domin sabuwar duniya da ta yi kusan zuwa

Aljannar da Ta Kusan Zuwa!

Aljannar da Ta Kusan Zuwa!

Allah ya halicci duniya don masu adalci su yi rayuwa har abada a cikinta. (Zabura 37:29) Ya saka mata da miji na farko a cikin lambun Adnin, kuma ya ba su aiki da hakkin kula da duniya.​—Farawa 1:28; 2:15.

A yau duniya ba aljanna ba ce. Amma Allah bai canja nufinsa ba. Ta yaya Allah zai mai da duniya aljanna? Kamar yadda muka gani a talifofin da suka gabata, Allah ba zai hallaka doron ƙasa ba. Amma zai bar mutane masu adalci su yi rayuwa a cikinta. Yaya duniya za ta zama, bayan Allah ya cika alkawarinsa?

Gwamnati ɗaya da za ta yi mulkin duniya

Sa’ad da gwamnatin Allah ta soma mulkin duniya nan ba da jimawa ba, mutane za su riƙa yin farin ciki, za su sami zaman lafiya kuma za su yi ayyuka masu kyau tare. Allah ya naɗa Yesu ya yi mulki a kan duniya. A yau, masu mulki da yawa ba su damu da mutane ba. Amma ba haka Yesu yake ba, domin a kowane lokaci yana yin abin da zai taimaka wa mutane. Zai nuna ƙauna da alheri da jinƙai da adalci yayin da yake sarauta.​—Ishaya 11:4.

Dukan mutane a duniya za su zama da haɗin kai

Mutane ba za su nuna bambancin ƙabila ko ƙasa ba. Duka ’yan Adam za su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:9, 10) Dukan mutanen da suke rayuwa a duniya za su ƙaunaci Allah da maƙwabtansu, kuma za su yi aiki tare cikin salama don su cika nufin Allah, wato kula da duniya.​—Zabura 115:16.

Ba za a riƙa yin bala’i ba

Idan Mulkin Allah ya soma sarauta, Mahaliccinmu zai kawar da bala’o’i. (Zabura 24:1, 2) A lokacin da Yesu ya dakatar da wata mahaukaciyar guguwa, ya nuna abin da zai yi da ikon da Allah ya ba shi. (Markus 4:39, 41) Sa’ad da Yesu ya soma sarauta, babu wanda zai sake jin tsoron bala’i. Mutane za su yi zaman lafiya da dabbobi kuma ba za a riƙa gurɓata mahalli ba.​—Hosiya 2:18.

Ƙoshin lafiya da isasshen abinci

Kowa zai sami ƙoshin lafiya. Babu wanda zai yi rashin lafiya ko ya tsufa ko ya mutu. (Ishaya 35:5, 6) Mutane za su yi rayuwa a wuri mai tsabta kamar yadda Adamu da Hauwa’u suka yi a cikin lambun Adnin. A sabuwar duniya, ƙasa za ta ba da amfani sosai kamar yadda yake a lambun Adnin, kuma mutane za su sami abinci a yalwace. (Farawa 2:9) Kamar yadda yake da al’ummar Allah, wato Isra’ila ta dā, kowa zai ‘ci abinci ya ƙoshi.’​—Littafin Firistoci 26:4, 5.

Salama da kwanciyar hankali na ƙwarai

A Mulkin Allah, mutane a dukan duniya za su zauna lafiya da juna, su daraja juna kuma su yi wa juna adalci. Ba za a yi yaƙi ba, babu wanda zai danne wani kuma kowa zai sami abin da yake bukata. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa: “Kowane mutum zai zauna cikin salama a ƙarƙashin itacen inabinsa da na ɓaurensa. Ba wanda zai tsoratar da shi.”​—Mika 4:3, 4.

Kowa zai sami gida da kuma aikin yi mai kyau

Kowace iyali za ta sami gida ba tare da jin tsoro cewa wata rana za ta rasa gidan ba, kuma za mu ji daɗin kowane aikin da muke yi. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗa, waɗanda suka shiga sabuwar duniya “ba za su yi aiki a banza ba.”​—Ishaya 65:21-23.

Koyarwa mafi kyau

Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa: “Ƙasar za ta cika da sanin Yahweh.” (Ishaya 11:9) Mutane da za su yi rayuwa a sabuwar duniya za su ci gaba da koyan hikima daga wurin Jehobah, mai hikima marar iyaka, kuma za su koyi abubuwa daga halittunsa. Ba za su yi amfani da iliminsu su ƙera makamai ko su cutar da wasu ba. (Ishaya 2:4) Maimakon haka, za su koyi yadda za su yi zaman lafiya da juna kuma su kula da duniya.​—Zabura 37:11.

Rayuwa har abada

Allah ya ɗauki lokaci ya yi duniya da kyau domin mu ji daɗin rayuwa a ciki kowace rana. Nufinsa shi ne ’yan Adam su yi rayuwa a duniya har abada. (Zabura 37:29; Ishaya 45:18) Jehobah “zai halaka mutuwa har abada” don ya cim ma abin da ya nufa wa duniya tun farko. (Ishaya 25:8) Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa ba za a sake “mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba” ba. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4) Jehobah zai ba da damar yin rayuwa har abada ga waɗanda ya cece su a ƙarshen duniya, da miliyoyin mutane da zai tayar da su daga matattu.​—Yohanna 5:28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15.

A yanzu ma, miliyoyin mutane suna shirin yin rayuwa a ƙarƙashin Mulkin Allah da ya yi kusan zuwa. Ko da yake su ajizai ne, suna ƙoƙari su yi irin rayuwar da Jehobah yake so mutane su yi a sabuwar duniya da zai kawo. Me ke taimaka musu? Koya game da Jehobah Allah da kuma wanda ya aiko Yesu Kristi.​—Yohanna 17:3.

Ka nemi ƙarin bayani a kan yadda za ka tsira wa ƙarshen wannan duniyar, don ka yi rayuwa a sabuwar duniya da ta yi kusan zuwa. Ka gaya ma wani Mashaidin Jehobah ya yi nazari da kai kyauta.