Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kowa Yana So Ya More Rayuwa a Nan Gaba

Kowa Yana So Ya More Rayuwa a Nan Gaba

Wace irin rayuwa kake so? Yawancin mutane suna so su da iyalansu su ji daɗin rayuwa, su sami ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali da kuma abin biyan bukata.

Duk da haka, mutane da yawa suna ganin zai yi wuya su yi irin wannan rayuwar. Me ya sa? Don suna ganin yadda rayuwa take canjawa babu zato. Alal misali, annobar korona ta ragargaza rayuwar mutane, ta ɓata tattalin arziki, har ma ta yi sannadiyyar mutuwar mutane da yawa. Don haka, mutane suna ganin cewa rayuwa ba ta da tabbas.

Yanayin da muke ciki ya sa mutane sun duƙufa neman abubuwan da za su sa su more rayuwa a nan gaba. Wasu suna ganin cewa kome da ya same su a rayuwa sa’a ce ko rashin sa’a. Wasu mutanen kuma sun dāge neman ilimi da kuɗi, suna ganin cewa waɗannan abubuwan ne za su sa su more rayuwa. Har ila wasu suna ganin cewa idan suka zama mutanen kirki, rayuwarsu za ta yi kyau.

Da gaske abubuwan nan za su sa ka ji daɗin rayuwa? Don ka sami amsar, ka bincika tambayoyi na gaba:

  • Me Yake Shafan Yadda Rayuwarmu Za Ta Kasance?

  • Neman Kuɗi da Ilimi Ne Zai Sa Mu More Rayuwa a Nan Gaba?

  • Idan Muna da Halin Kirki, Shi Ke Nan Rayuwarmu Za Ta Yi Kyau?

  • A Ina Za Mu Sami Shawara da Za Ta Sa Mu More Rayuwa a Nan gaba?

Wannan Hasumiyar Tsaro za ta taimaka maka ka sami amsoshin tambayoyin nan.