Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

A Ina Za Mu Sami Shawara da Za Ta Sa Mu More Rayuwa?

A Ina Za Mu Sami Shawara da Za Ta Sa Mu More Rayuwa?

Kamar yadda muka tattauna a baya, mutane sun yi ƙoƙarin more rayuwa ta wurin dogara da ilimi da kuɗi da zama mutanen kirki da kuma neman yin sa’a. Amma wanda yake bin waɗannan hanyoyin don ya more rayuwa, kama yake da mutumin da yake so ya je inda bai taɓa zuwa ba, sai ya tare wanda bai san hanya ba yana tambayarsa inda zai bi. Ba inda za mu sami shawara mai kyau da za ta taimaka mana mu more rayuwa a nan gaba ke nan? A’a!

SHAWARA DAGA WANDA YA FI MU HIKIMA

In muna son mu yi wani abu, mukan nemi shawara daga wanda ya girme mu kuma ya fi mu hikima. A yau ma, za mu sami shawara mai kyau a kan yadda za mu more rayuwa a nan gaba idan muka tuntuɓi wani da ya girme mu kuma ya fi mu hikima. Albishirin shi ne, akwai wani da ya girme mu kuma ya fi mu hikima da zai iya taimaka mana. An rubuta shawarwarin da ya ba mu a wani littafi da ake kira Littafi Mai Tsarki. Littafin nan ya yi wajen shekaru 3,500 yanzu.

Me ya sa za ka iya gaskata Littafi Mai Tsarki? Domin mawallafinsa ya fi kowa daɗewa da hikima a sama da ƙasa. An kira shi “Wanda Yake Tun Dā” da kuma “marar farko marar ƙarshe.” (Daniyel 7:9; Zabura 90:2) Shi ne “Mahaliccin sammai, Allah kaɗai, Mai siffata duniya.” (Ishaya 45:18) Ya gaya mana cewa sunansa shi ne Yahweh ko Jehobah.​—Zabura 83:18.

Littafi Mai Tsarki ba ya fifita wata kabila a kan ta wasu domin littafin ya fito ne daga wanda ya halicci dukan mutane. Shawararsa tana da amfani a koyaushe kuma ta taimaka wa mutane a ƙasashe da yawa. Akwai shi a yaruka da dama kuma yana kusan ko’ina a duniya. Ba wani littafin da aka fassara kuma ya yaɗu kamarsa. * Don haka, mutane a ko’ina za su iya karanta shi kuma ya taimaka musu. Wannan ya tabbatar mana da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa:

“Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.”​—AYYUKAN MANZANNI 10:​34, 35.

Kamar yadda iyaye suke taimaka wa yaransu domin suna ƙaunar su, Jehobah yana taimaka mana ta wurin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. (2 Timoti 3:16) Za mu iya gaskata da Kalmarsa domin shi ne ya hallice mu kuma ya san abin da ya fi dacewa da mu.

Me za ka yi don ka sami waɗannan albarkun? Za a tattauna hakan a talifi na gaba.

^ sakin layi na 6 Don ƙarin bayani a kan yadda aka fassara da kuma rarraba Littafi Mai Tsarki, ka shiga dandalinmu na www.pr418.com/ha, ka danna KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > TARIHI DA LITTAFI MAI TSARKI.

^ sakin layi na 16 Don ka sami ƙarin bayani, ka karanta littafin nan, The Bible​—God’s Word or Man’s? babi na 9, Shaidun Jehobah ne suka wallafa. Za ka iya samunsa a Turanci a dandalinmu na www.pr418.com. Ka danna LIBRARY > BOOKS & BROCHURES.