Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 5

“Almasihu Ne Shugaban Kowane” Namiji

“Almasihu Ne Shugaban Kowane” Namiji

“Almasihu ne shugaban kowane” namiji.—1 KOR. 11:3.

WAƘA TA 12 Jehobah, Allah Mafi Iko

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne zai iya shafan yadda miji yake bi da matarsa da yaransa?

MENE NE kalmar nan ‘shugabanci’ take nufi a gare ka? Wasu maza suna barin al’ada ko yadda aka rene su ya shafi yadda suke bi da matarsu da kuma yaransu. Ka yi la’akari da abin da wata mai suna Yanita da take zama a Turai ta faɗa. Ta ce: “A wurin da nake zama, mutane sun gaskata cewa maza sun fi mata amfani. Ya kamata a ɗauki mata a matsayin bayi.” Wani ɗan’uwa mai suna Luke da ke zama a Amirka ya ce: “Wasu maza suna koya wa yaransu maza cewa duk abin da mata suka ce bai da amfani don haka bai kamata a saurare su ba.” Amma ba haka Jehobah yake so maza su yi sha’ani da mata ba. (Gwada Markus 7:13.) Ta yaya namiji zai zama shugaba nagari?

2. Mene ne ya wajaba magidanta su sani, kuma me ya sa?

2 Kafin namiji ya zama shugaba nagari, yana bukatar ya san abin da Jehobah yake so ya yi. Ƙari ga haka, yana bukatar ya san dalilin da ya sa Jehobah ya kafa wannan tsarin da kuma yadda zai bi misalin Jehobah da Yesu. Me ya sa namiji yake bukatar ya san waɗannan abubuwan? Domin Jehobah ya ba magidanta iko kuma yana so su yi amfani da shi yadda ya kamata.—Luk. 12:48b.

MENE NE SHUGABANCI?

3. Mene ne muka koya game da shugabanci daga 1 Korintiyawa 11:3?

3 Karanta 1 Korintiyawa 11:3. Wannan ayar ta bayyana yadda Jehobah ya tsara iyalinsa a sama da kuma duniya. Tun da yake shi ne ‘shugaba,’ ya fi kowa iko. Ta wannan tsarin, ya ba wasu iko, amma za su ba da lissafin yadda suka yi amfani da shi. (Rom. 14:10; Afis. 3:14, 15) Jehobah ya ba Yesu iko a kan ikilisiya, amma Yesu zai ba da lissafin yadda yake bi da mu ga Jehobah. (1 Kor. 15:27) Jehobah ya ba magidanta iko a kan matansu da kuma yaransu, amma za su ba da lissafi ga Jehobah da Yesu a kan yadda suka yi sha’ani da iyalinsu.—1 Bit. 3:7.

4. Wane iko ne Jehobah da Yesu suke da shi?

4 Da yake Jehobah ne Maɗaukaki, yana da ikon kafa wa ’ya’yansa dokoki, kuma ya tabbatar cewa sun bi dokokin. (Isha. 33:22) Yesu wanda shi ne shugaban ikilisiyar Kirista yana da ikon kafa dokoki.—Gal. 6:2; Kol. 1:18-20.

5. Wane iko ne magidanci yake da shi, kuma mene ne ba zai iya yi ba?

5 Kamar Jehobah da Yesu, maigida Kirista yana da ikon tsai da shawarwari don iyalinsa. (Rom. 7:2; Afis. 6:4) Amma ikonsa yana da iyaka. Alal misali, ya kamata ya kafa dokoki da suka jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (K. Mag. 3:5, 6) Kuma maigida bai da ikon kafa wa mutanen da ba ’yan iyalinsa ba dokoki. (Rom. 14:4) Ƙari ga haka, sa’ad da yaransa suka girma kuma suka bar gida, za su riƙa daraja shi amma ba shi da iko a kansu.—Mat. 19:5.

ME YA SA JEHOBAH YA BA WASU IKO?

6. Me ya sa Jehobah ya ba wasu iko?

6 Jehobah ya kafa tsarin shugabanci domin yana ƙaunar iyalinsa. Kyauta ce daga gare shi. Shugabanci yana sa iyalin Jehobah su kasance da tsari da kuma kwanciyar hankali. (1 Kor. 14:33, 40) Da a ce Jehobah bai ba wasu iko ba, da iyalinsa ba za ta kasance da tsari ba kuma ba za ta riƙa farin ciki ba. Alal misali, da ba za a san ko wane ne zai riƙa tsai da shawarwari da kuma tabbatar da cewa an bi shawarwarin ba.

7. Kamar yadda Afisawa 5:25, 28 suka nuna, ta yaya Jehobah yake so maza su bi da mata?

7 Idan tsarin shugabanci da Jehobah ya kafa yana da kyau, me ya sa mata da yawa suke ganin cewa mazansu na wulaƙanta su? Hakan yana faruwa ne domin maza da yawa ba sa bin ƙa’idodin da Jehobah ya kafa wa iyali, amma suna bin al’adu. Ƙari ga haka, suna iya wulaƙanta matansu don su biya bukatunsu. Alal misali, magidanci yana iya wulaƙanta matarsa domin ya nuna cewa shi namijin ƙwarai ne. Yana iya tunanin cewa ba zai iya tilasta wa matarsa ta ƙaunace shi ba, amma yana iya sa ta riƙa jin tsoron sa. Yana iya yin hakan don ya riƙa jujjuya ta kamar waina. * Irin wannan ra’ayin bai dace ba. Mazan da ke da irin wannan ra’ayin ba sa daraja mata yadda ya kamata, kuma ba sa yin abin da Jehobah yake so.—Karanta Afisawa 5:25, 28.

TA YAYA MAGIDANCI ZAI ZAMA SHUGABA NAGARI?

8. Ta yaya magidanci zai iya zama shugaba nagari?

8 Magidanci yana iya zama shugaba nagari idan ya yi koyi da yadda Jehobah da Yesu suke nuna iko. Ka yi la’akari da halaye biyu da Jehobah da Yesu suka nuna, kuma ka lura da yadda magidanci zai iya nuna waɗannan halayen yayin da yake sha’ani da matarsa da yaransa.

9. Ta yaya Jehobah yake nuna sauƙin kai?

9 Sauƙin kai. Jehobah ne ya fi kowa hikima, duk da haka, yana saurarar ra’ayin bayinsa. (Far. 18:23, 24, 32) Ya ba mutane damar furta ra’ayinsu. (1 Sar. 22:19-22) Jehobah kamiltacce ne, amma a yanzu ba ya bukatar mu riƙa yin abubuwa kamar kamiltattu. A maimakon haka, yana taimaka wa mutane ajizai da suke bauta masa su yi nasara. (Zab. 113:6, 7) Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ‘mai taimako’ ne. (Zab. 27:9; Ibran. 13:6) Sarki Dauda ya ce ya cim ma abubuwa da yawa ne domin Jehobah mai sauƙin kai ne kuma ya taimaka masa.—2 Sam. 22:36.

10. Ta yaya Yesu ya nuna sauƙin kai?

10 Ka yi la’akari da misalin Yesu. Ko da yake shi ne Ubangiji da kuma Shugaban mabiyansa, ya wanke ƙafafunsu. Me ya sa Jehobah ya sa aka rubuta wannan labarin a Littafi Mai Tsarki? Domin yana so kowa har da magidanta su ga misali mai kyau da za su iya bi. Yesu ya ce: “Na nuna muku misali ne domin ku ma ku yi yadda na yi muku.” (Yoh. 13:12-17) Ko da yake Yesu yana da iko sosai, bai so mutane su riƙa yi masa hidima ba. A maimakon haka, ya yi wa mutane hidima.—Mat. 20:28.

Magidanci yana iya nuna sauƙin kai da ƙauna ta wajen yin ayyuka a gida da kuma taimaka wa iyalinsa su ƙulla dangantaka da Allah (Ka duba sakin layi na 11, 13)

11. Ta yaya magidanci zai yi koyi da Jehobah da Yesu?

11 Darussan da muka koya. Magidanci zai iya nuna sauƙin kai a hanyoyi da yawa. Alal misali, ba zai bukaci matarsa da yaransa su riƙa yin abubuwa ba tare da yin kuskure ba. Yana saurarar ra’ayin iyalinsa ko da ra’ayinsu bai jitu da nasa ba. Wata mai suna Marley da ke zama a Amirka ta ce: “A wasu lokuta, ra’ayina da na mijina yana bambanta. Amma yadda yake neman ra’ayina kafin ya yanke shawara yana sa in ga cewa yana daraja ni.” Ƙari ga haka, magidanci mai sauƙin kai yana shirye ya yi ayyuka a gida ko da a yankinsu mutane suna ganin cewa aikin na mata ne. Hakan yana iya yin wuya sosai. Me ya sa? Wata ’yar’uwa mai suna Rachel ta ce: “A ƙasarmu, idan miji ya taya matarsa yin wanke-wanke ko kuma shara a gida, maƙwabta za su ce bai cika namiji ba. Suna iya ɗauka cewa matar ta fi ƙarfinsa.” Idan mutane suna da irin wannan ra’ayin a wurin da kake zama, ka tuna cewa Yesu ya wanke ƙafafun almajiransa, ko da yake mutane suna ganin cewa wannan aikin bayi ne. Magidanci nagari ba ya damuwa da yadda mutane suke ɗaukansa, amma yana so matarsa da yaransa su yi farin ciki. Ban da sauƙin kai, wane hali ne kuma yake da muhimmanci magidanci ya kasance da shi?

12. Mene ne ƙauna ta sa Jehobah da Yesu su yi?

12 Ƙauna. Ƙauna ce ke sa Jehobah ya yi dukan abubuwan da yake yi. (1 Yoh. 4:7, 8) Ya tanada mana Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa don yana ƙaunar mu kuma yana so mu zama abokansa. Yana taimaka mana mu kasance da kwanciyar hankali ta wajen tabbatar mana cewa yana ƙaunar mu. Yana biyan bukatunmu kuwa? Ƙwarai kuwa. Jehobah yana “tanada mana kome a yalwace domin jin daɗinmu.” (1 Tim. 6:17) Sa’ad da muka yi kuskure, yana yi mana gyara, amma hakan ba ya sa ya daina ƙaunar mu. Domin Jehobah yana ƙaunar mu, ya yi shiri don a fanshe mu. Yesu ma yana ƙaunar mu sosai, shi ya sa ya ba da ransa dominmu. (Yoh. 3:16; 15:13) Babu abin da zai iya hana Jehobah da Yesu ƙaunar mutane masu aminci.—Yoh. 13:1; Rom. 8:35, 38, 39.

13. Me ya sa yake da muhimmanci magidanci ya riƙa nuna ƙauna ga iyalinsa? (Ka duba akwatin nan “ Ta Yaya Ango Zai Sa Amaryarsa Ta Riƙa Daraja Shi?”)

13 Darussan da muka koya. Ƙauna ce ya kamata ta motsa magidanci ya yi dukan abubuwan da yake yi. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Manzo Yohanna ya ba da amsar, ya ce: “Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa wanda yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda bai taɓa gani ba.” (1 Yoh. 4:11, 20) Magidanci da yake ƙaunar iyalinsa kuma yake so ya yi koyi da Jehobah da Yesu, zai taimaka wa iyalin ta kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, ya sa su kasance da kwanciyar hankali kuma ya riƙa biyan bukatunsu. (1 Tim. 5:8) Zai yi renon yaransa, ya kuma horar da su. Zai ci gaba da tsai da shawarwarin da za su ɗaukaka Jehobah kuma iyalinsa su amfana. Bari mu tattauna kowanne cikinsu kuma mu ga yadda magidanci zai yi koyi da Jehobah da Yesu.

ABIN DA MAGIDANCI YAKE BUKATAR YI

14. Ta yaya magidanci zai taimaka wa iyalinsa su ƙarfafa dangantakarsu da Allah?

14 Yana taimaka wa iyalinsa su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Yesu ya yi koyi da Jehobah, domin yana so ya taimaka wa mabiyansa su ƙarfafa bangaskiyarsu. (Mat. 5:3, 6; Mar. 6:34) Hakazalika, abu mafi muhimmanci da magidanci zai yi, shi ne ya taimaka wa iyalinsa ta kusaci Jehobah. (M. Sha. 6:6-9) Zai yi hakan ta wajen tabbata cewa shi da iyalinsa suna karanta Kalmar Allah, da halartan taro, da yin wa’azi da kuma kyautata dangantakarsu da Jehobah.

15. Ta yaya magidanci zai taimaka wa iyalinsa su kasance da kwanciyar hankali?

15 Yana taimaka wa iyalinsa su kasance da kwanciyar hankali. Jehobah ya nuna wa kowa cewa yana ƙaunar Yesu. (Mat. 3:17) Yesu ya nuna wa mabiyansa cewa yana ƙaunar su ta furucinsa da kuma ayyukansa. Mabiyansa ma sun nuna suna ƙaunar sa. (Yoh. 15:9, 12, 13; 21:16) Magidanci yana iya nuna cewa yana ƙaunar matarsa da yaransa ta abubuwan da yake yi, kamar yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Yana bukatar ya riƙa gaya musu cewa yana ƙaunar su kuma suna da muhimmanci a gare shi. A lokacin da ya dace, zai iya faɗin hakan a gaban mutane.—K. Mag. 31:28, 29.

Magidanci yana bukatar ya riƙa biyan bukatun iyalinsa don ya faranta ran Jehobah (Ka duba sakin layi na 16)

16. Mene ne ya wajaba magidanta su yi, kuma mene ne bai kamata su yi ba?

16 Yana biyan bukatun iyalinsa. Jehobah ya biya bukatun Isra’ilawa duk da cewa ya yi musu horo don rashin biyayya. (M. Sha. 2:7; 29:5) A yau ma, yana biyan bukatunmu. (Mat. 6:31-33; 7:11) Hakazalika, Yesu ya ciyar da mabiyansa. (Mat. 14:17-20) Ya kuma warƙar da marasa lafiya. (Mat. 4:24) Wajibi ne magidanci ya biya bukatun iyalinsa don ya faranta ran Jehobah. Amma akwai abubuwan da yake bukatar ya guje wa. Bai kamata ya shagala da ayyukansa har ya kasa taimaka wa iyalinsa su ƙarfafa dangantakarsu da Allah kuma su kasa kasancewa da kwanciyar rai ba.

17. Wane misali ne Jehobah da Yesu suka kafa a yadda suke horar da kuma koyar da mu?

17 Yana horarwa. Jehobah yana yi mana horo da kuma koyar da mu domin yana so ya taimaka mana. (Ibran. 12:7-9) Kamar Jehobah, Yesu ma ya horar da almajiransa da ƙauna. (Yoh. 15:14, 15) Ya yi musu gargaɗi amma ya nuna musu alheri. (Mat. 20:24-28) Ya san cewa mu ajizai ne kuma muna iya yin kuskure.—Mat. 26:41.

18. Mene ne magidanci nagari yake yin la’akari da shi?

18 Magidanci da ke yin koyi da Jehobah da Yesu yana tuna cewa matarsa da yaransa ajizai ne, kuma ba ya yawan fushi da su. (Kol. 3:19) A maimakon haka, yana bin ƙa’idar da ke Galatiyawa 6:1 kuma yana ƙoƙarin ya yi musu gyara a cikin “halin tawali’u” domin shi ma ajizi ne. Kamar Yesu, ya san cewa hanya mafi muhimmanci na koyar da mutane ita ce, kafa misali mai kyau.—1 Bit. 2:21.

19-20. Ta yaya magidanci zai yi koyi da Jehobah da Yesu sa’ad da yake tsai da shawara?

19 Ka tsai da shawarwari ba tare da son kai ba. Jehobah yana tsai da shawarwarin da za su amfani wasu. Alal misali, ya halicci abubuwa masu rai, ba don amfanin kansa ba, amma don mu ji daɗin rayuwa. Babu wanda ya tilasta masa ya ba da Ɗansa ya mutu a madadinmu. Ya yi hakan domin yana so ya taimaka mana. Yesu ma ya tsai da shawarwari da suka taimaka ma wasu. (Rom. 15:3) Alal misali, ya yi amfani da lokaci da ya kamata ya huta don ya koyar da mutane.—Mar. 6:31-34.

20 Magidanci nagari ya san cewa yanke shawarwari da iyalinsa za su amfana bai da sauƙi, kuma yana ɗaukan wannan aikin da muhimmanci. Ba ya yanke shawarwari ba tare da ƙwaƙƙwarar dalili ba ko kuma bisa yadda yake ji a lokacin ba. A maimakon haka, yana barin Jehobah ya koya masa yadda zai riƙa yanke shawarwari masu kyau. * (K. Mag. 2:6, 7) Idan ya yi hakan, zai yi tunanin sa wasu su amfana ba kansa ba.—Filib. 2:4.

21. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

21 Jehobah ya ba magidanta aiki mai wuya, kuma za su ba shi lissafin yadda suka yi aikin. Idan magidanci ya yi ƙoƙari ya bi misalin da Jehobah da Yesu suka kafa, zai zama shugaba nagari. Ƙari ga haka, idan matarsa ta yi aikin da aka ba ta, za su yi farin ciki a aurensu. Ta yaya mace ya kamata ta ɗauki ikon da maigidanta yake da shi na yanke shawara a iyalin, kuma wane ƙalubale ne za ta fuskanta? A talifi na gaba, za mu tattauna waɗannan tambayoyin.

WAƘA TA 16 Mu Yabi Jehobah Domin Ɗansa

^ sakin layi na 5 Namiji yana zama shugaban iyali sa’ad da ya yi aure. A wannan talifin, za mu tattauna abin da zama shugaba yake nufi, da dalilin da ya sa Jehobah ya kafa wannan tsarin da kuma abin da mazaje za su koya daga misalin Jehobah da Yesu. A talifi na biyu a wannan jerin talifofin, za mu tattauna abin da mata da miji za su iya koya daga misalin Yesu da kuma wasu bayin Allah. A talifi na ƙarshe kuma, za mu tattauna game da shugabanci a ikilisiya.

^ sakin layi na 7 A wasu lokuta, ana nunawa a fina-finai da kuma littattafai cewa ba laifi ba ne namiji ya wulaƙanta matarsa ko kuma ya dūke ta. Irin wannan al’adar ce take sa mazaje da yawa ganin cewa ba laifi ba ne su riƙa wulaƙanta matansu.

^ sakin layi na 20 Don samun ƙarin bayani game da yadda za ka riƙa tsai da shawarwari masu kyau, ka duba talifin nan “Ka Tsai da Shawarwari da Ke Ɗaukaka Allah,” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2011, shafuffuka na 13-17.