Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sakamakon Yin Murmushi!

Sakamakon Yin Murmushi!

WASU ’yan mata biyu suna tafiya a wurin da mutane ke kasuwanci a birnin Baguio, a ƙasar Filifin. Sun ga ’yan’uwa da suke wa’azi da amalanke, amma ba su yi musu magana ba. Wata ’yar’uwa mai suna Helen da ta tsaya kusa da amalanken ta yi musu murmushi. ’Yan matan sun ci gaba da tafiya, amma yadda Helen ta yi musu murmushi ya burge su.

Sa’ad da ’yan matan suke mota suna komawa gida, sai suka ga babbar alamar jw.org da ke gaban wata Majami’ar Mulki. Sun tuna cewa sun ga irin wannan alamar a kan wani amalanken wa’azi a ranar. Sai suka sauka daga motar kuma suka je Majami’ar. Sun ga an rubuta lokacin da ikilisiyoyi suke yin taro a ƙofar Majami’ar.

’Yan matan sun halarci taro na gaba da aka yi a Majami’ar. Sun yi mamaki sa’ad da suka ga Helen yayin da suka shiga Majami’ar Mulkin. Nan da nan sun tuna cewa ita ce ta yi musu murmushi. Helen ta ce: “Na ji tsoro da suka zo suka same ni, domin ban san dalilin da ya sa suka zo wurina ba.” Amma sun gaya wa Helen cewa sun taɓa ganin ta tana wa’azi da amalanke.

’Yan matan sun ji daɗin taron, kuma sun saki jiki sosai sa’ad da suke tare da ’yan’uwan. Sa’ad da suka ga ’yan’uwa suna shara bayan taro, sai su ma suka bi su yin shara. Ɗaya cikinsu ta bar ƙasar Filifin, amma ɗayan ta soma halartan taro kuma ana nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Hakan ya faru don ’yar’uwarmu ta yi murmushi sa’ad da take wa’azi!