Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 15

Darussa Daga Kalmomin Yesu na Karshe

Darussa Daga Kalmomin Yesu na Karshe

“Wannan shi ne Ɗana, wanda nake ƙauna, ina jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”​—MAT. 17:5.

WAƘA TA 17 “Na Yarda”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Mene ne ya faru kafin Yesu ya furta kalmominsa na ƙarshe?

A RANAR 14 ga Nisan a shekara ta 33, an tuhume Yesu da laifin da bai yi ba, aka gana masa azaba kuma aka rataye shi a kan gungume. An kafa ƙusa a hannayensa da ƙafafunsa kuma yana shan azaba sosai. Duk da haka, wajibi ne ya yi magana domin yana da abubuwa masu muhimmanci da zai faɗa.

2 Bari mu tattauna kalmomin da Yesu ya faɗa sa’ad da yake gab da mutuwa a kan gungumen azaba da kuma darussan da muka koya. Yin hakan zai sa mu “saurare shi.”​—Mat. 17:5.

“UBA . . . KA GAFARTA MUSU”

3. Su waye ne wataƙila Yesu yake magana game da su sa’ad da ya ce: ‘Uba, ka gafarta musu’?

3 Mene ne Yesu ya ce? Sa’ad da Yesu yake kan gungumen azaba sai ya yi addu’a cewa: “Uba . . . ka gafarta musu.” Su waye ne Yesu yake so a gafarta ma? Kalmominsa na gaba sun nuna waɗanda yake magana game da su. Ya ce: “Ba su san abin da suke yi ba.” (Luk. 23:​33, 34) Wataƙila Yesu yana magana ne game da sojojin Roma da suka rataye shi domin ba su san shi sosai ba. Ban da haka, mai yiwuwa yana magana ne game da wasu mutane da suka ce a kashe shi amma daga baya za su yi imani da shi. (A. M. 2:​36-38) Yesu bai bar rashin adalci da aka yi masa ya sa ya riƙa fushi da kuma ƙiyayya da waɗanda suke tsananta masa ba. (1 Bit. 2:23) Maimakon haka, ya roƙi Jehobah ya gafarta wa waɗanda suke gab da kashe shi.

4. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Yesu ya kasance a shirya ya gafarta wa masu tsananta masa?

4 Wane darasi ne za mu iya koya daga kalmomin Yesu? Kamar Yesu, muna bukatar mu riƙa gafarta wa mutane. (Kol. 3:13) Wasu mutane, har da danginmu za su iya tsananta mana domin ba su amince da imaninmu ba da kuma salon rayuwarmu. Za su iya yin ƙarya game da mu ko su wulaƙanta mu a gaban mutane ko su yayyaga littattafanmu ko kuma su yi barazanar yi mana lahani. Maimakon mu riƙa fushi da su, muna iya roƙon Jehobah ya taimaka wa waɗanda suke tsananta mana su koyi gaskiya. (Mat. 5:​44, 45) A wasu lokuta, yana iya yi mana wuya mu gafarta wa mutane, musamman idan an yi mana rashin adalci. Amma za mu riƙa baƙin ciki idan muka ci gaba da fushi da kuma ƙin gafartawa. Wata ’yar’uwa ta ce: “Na fahimci cewa gafarta wa mutane ba ya nufin cewa ina so abin da suka yi mini ko kuma na bar su su wulaƙanta ni. Amma, yana nufin cewa ba na so in ci gaba da yin fushi ne.” (Zab. 37:8) Idan muka gafarta wa mutane, muna nuna cewa ba ma so abin da ya faru da mu ya ci gaba da ɓata mana rai.​—Afis. 4:​31, 32.

“ZA KA ZAUNA TARE DA NI” A ALJANNA

5. Wane alkawari ne Yesu ya yi wa ɗaya daga cikin masu laifin da aka rataye kusa da shi, kuma me ya sa ya yi wannan alkawarin?

5 Mene ne Yesu ya ce? An rataye mutane biyu kusa da Yesu a kan gungumen azaba. Da farko, mutanen sun yi wa Yesu ba’a. (Mat. 27:44) Amma daga baya, ɗaya cikinsu ya daina yin hakan domin ya fahimci cewa Yesu bai yi “laifi” ba. (Luk. 23:​40, 41) Ban da haka, ya zo ya yi imani cewa za a ta da Yesu daga mutuwa kuma zai zama sarki. Sai ya gaya wa Yesu: “Ya Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka!” (Luk. 23:42) Mutumin yana da bangaskiya sosai! Sai Yesu ya ce masa: ‘Hakika ina gaya maka yau ɗin nan, za ka zauna tare da ni’ a Aljanna. (Luk. 23:43) Ka lura cewa Yesu ya yi amfani da kalmomin nan “ina” da “ka” da kuma “ni” sa’ad da yake wannan alkawarin. Yesu ya sa ɗaya cikin masu laifin ya kasance da bege domin ya san cewa Ubansa mai jinƙai ne.​—Zab. 103:8.

6. Wane darasi ne muka koya daga kalmomin Yesu ga wani mai laifi?

6 Wane darasi ne za mu iya koya daga kalmomin Yesu? Yesu yana kamar Ubansa. (Ibran. 1:3) Jehobah yana so ya gafarta mana kuma ya nuna mana jinƙai. Amma zai yi hakan ne idan muka tuba da gaske kuma muka yi imani da hadayar da Yesu ya yi. (1 Yoh. 1:7) Yana wa wasu wuya su gaskata cewa Jehobah zai gafarta musu don abubuwan da suka yi a dā. Idan a wasu lokuta kana jin hakan, ka tuna cewa sa’ad da Yesu yake gab da mutuwa, ya nuna jinƙai ga ɗaya daga cikin masu laifin da ya soma imani ga Allah. Idan Jehobah ya nuna jinƙai ga wannan mutum mai laifi da ya ɗan soma nuna imani, babu shakka, zai fi yin hakan ga bayinsa masu aminci da suke yin iya ƙoƙarinsu don su yi masa biyayya!​—Zab. 51:1; 1 Yoh. 2:​1, 2.

“GA ƊANKI! . . . WANNAN TA ZAMA MAMARKA!”

7. Kamar yadda aka nuna a Yohanna 19:​26, 27, mene ne Yesu ya gaya wa Maryamu da Yohanna, kuma me ya sa ya ce hakan?

7 Mene ne Yesu ya ce? (Karanta Yohanna 19:​26, 27.) Yesu yana so ya kula da mahaifiyarsa wadda gwauruwa ce. Wataƙila ƙannensa za su biya bukatunta, amma wane ne zai taimaka mata ta ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah? Babu abin da ya nuna cewa ’yan’uwan Yesu sun soma bauta wa Jehobah a lokacin. Amma, Yohanna almajirin Yesu ne mai aminci kuma shi amininsa ne. Yesu yana ɗaukan waɗanda suke bauta wa Jehobah tare da shi a matsayin iyalinsa. (Mat. 12:​46-50) Domin Yesu yana ƙaunar mahaifiyarsa, sai ya sa Yohanna ya kula da ita don Yesu ya san zai taimaka mata ta ci gaba da bauta wa Jehobah. Yesu ya gaya wa mahaifiyarsa cewa: “Ga ɗanki!” Kuma ya gaya wa Yohanna cewa: Ga “mamarka.” Tun daga ranar Yohanna ya zama kamar ɗa ga Maryamu kuma ya kula da ita kamar ita ce mahaifiyarsa. Babu shakka, Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar wannan matar da ta kula da shi sa’ad da yake jariri kuma ba ta yasar da shi sa’ad da yake gab da mutuwa ba!

8. Wane darasi ne za mu iya koya daga abin da Yesu ya gaya wa Maryamu da Yohanna?

8 Wane darasi ne za mu iya koya daga kalmomin Yesu? Dangantakarmu da ’yan’uwanmu Kiristoci za ta yi danƙo sosai fiye da ta ’yan iyalinmu. ’Yan iyalinmu za su iya tsananta mana ko su yasar da mu. Amma kamar yadda Yesu ya yi mana alkawari, idan mun kasance da aminci ga Jehobah da ƙungiyarsa, albarkun da za mu samu za su ninka abubuwan da muka rasa “sau ɗari.” ’Yan’uwa da yawa za su zama kamar ’ya’yanmu ko kuma iyayenmu. (Mar. 10:​29, 30) Ya kamata sanin cewa kana da ’yan’uwa maza da mata masu haɗin kai da suke da bangaskiya da kuma ƙauna ga Jehobah ya sa ka farin ciki.​—Kol. 3:14; 1 Bit. 2:17.

“YA ALLAHNA, DON ME KA YASHE NI?”

9. Wane darasi ne za mu iya koya daga furucin Yesu da ke Matiyu 27:46?

9 Mene ne Yesu ya ce? Jim kaɗan kafin Yesu mutu, ya ɗaga muryarsa, ya ce: “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” (Mat. 27:46) Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dalilin da ya sa Yesu ya yi wannan furucin ba. Amma wane darasi ne za mu iya koya daga furucin? Na ɗaya, furucin nan da Yesu ya yi ya cika annabcin da ke Zabura 22:1. * Ƙari ga haka, furucin ya nuna cewa Jehobah bai “kewaye shi da katanga” ba. (Ayu. 1:10) Yesu ya fahimci cewa Ubansa ya bari a jarraba bangaskiyarsa sosai har a kashe shi. Babu wani ɗan Adam da aka taɓa jarrabawa kamar Yesu. Bugu da ƙari, furucin ya nuna cewa Yesu bai yi wani laifin da ya isa a kashe shi ba.

10. Wane darasi ne za mu iya koya daga furucin Yesu ga Ubansa?

10 Wane darasi ne za mu iya koya daga kalmomin Yesu? Darasi na farko shi ne: Kada mu sa rai cewa Jehobah zai kāre mu daga abubuwan da za su iya jarraba imaninmu. Kamar yadda aka jarraba Yesu sosai, ya wajaba mu ma mu kasance a shirye don mu riƙe aminci ko da za a kashe mu ne. (Mat. 16:​24, 25) Amma muna da tabbaci cewa Jehobah ba zai yarda a jarraba mu a hanyar da ba za mu iya jimrewa ba. (1 Kor. 10:13) Wani darasi kuma shi ne cewa za mu iya shan wahala ko da ba mu yi wani laifi ba. (1 Bit. 2:​19, 20) Ba domin mun yi wani laifi ba ne ya sa ake tsananta mana ba, amma domin mu ba na duniya ba ne kuma muna ba da shaida ga gaskiya. (Yoh. 17:14; 1 Bit. 4:​15, 16) Yesu ya fahimci dalilan da suka sa Jehobah ya ƙyale shi ya sha wahala. Amma a wasu lokuta, wasu bayin Jehobah ba su fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale su su sha wahala ba. (Hab. 1:3) Allahnmu mai jinƙai ya fahimci cewa ba rashin bangaskiya ba ne ya sa waɗannan bayinsa suke tunanin nan ba. Amma suna bukatar ƙarfafawar da Jehobah kaɗai yake iya bayarwa.​—2 Kor. 1:​3, 4.

“INA JIN ƘISHIN RUWA”

11. Me ya sa Yesu ya yi furucin da ke Yohanna 19:28?

11 Mene ne Yesu ya ce? (Karanta Yohanna 19:28.) Me ya sa Yesu ya ce: “Ina jin ƙishin ruwa”? Ya yi hakan ne domin ya “cika abin da yake a cikin Rubutacciyar Maganar Allah,” wato annabcin da ke Zabura 22:15. Ayar ta ce: “Ƙarfina ya shanye kamar kasko, harshena ya manne a bakina.” Babu shakka, Yesu ya ji ƙishin ruwa sosai domin wahalar da ya sha da kuma rataye shi da aka yi a kan gungume. Don haka, ya so a ba shi ruwa.

12. Mene ne muka koya daga kalmomin Yesu “ina jin ƙishin ruwa”?

12 Wane darasi ne za mu iya koya daga kalmomin Yesu? Yesu bai yi tunani cewa bai dace ya faɗi yadda yake ji ba, mu ma ya kamata mu riƙa faɗin yadda muke ji. Wataƙila ba ma iya gaya wa mutane bukatunmu. Amma idan muna bukatar taimako, kada mu yi jinkirin gaya wa mutane su taimaka mana. Alal misali, idan mu tsofaffi ne ko muna rashin lafiya, za mu iya gaya wa wani abokinmu ya kai mu kanti ko kuma asibiti a motarsa. Idan muna sanyin gwiwa, muna iya gaya wa dattijo ko Kirista da ya manyanta matsalolinmu ko kuma ya ‘ƙarfafa’ mu. (K. Mag. 12:25) Bari mu tuna cewa ’yan’uwanmu suna ƙaunar mu, kuma suna so su taimaka mana a “kwanakin masifa.” (K. Mag. 17:17) Amma ba su san abin da muke tunaninsa ko kuma yadda muke ji ba. Ba za su san ko muna bukatar taimako ba sai mun gaya musu.

“AN GAMA!”

13. Mene ne Yesu ya cim ma don ya kasance da aminci har mutuwa?

13 Mene ne Yesu ya ce? A misalin ƙarfe uku na rana a ranar 14 ga Nisan, sai Yesu ya ɗaga murya ya ce: “An gama!” (Yoh. 19:30) Furucin Yesu ya koya mana cewa sa’ad da yake gab da mutuwa ya yi dukan abubuwan da Jehobah ya ce ya yi. Yesu ya cim ma abubuwa da yawa domin ya kasance da aminci har mutuwa. Da farko, Yesu ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Kuma cewa kamiltacce zai iya kasancewa da aminci kome jarrabawar Shaiɗan. Na biyu, Yesu ya ba da ransa hadaya. Hadayarsa ta sa ya yiwu ’yan Adam ajizai su ƙulla dangantaka na kud da kud da Allah kuma su sami zarafin yin rayuwa har abada. Na uku, Yesu ya nuna cewa Jehobah sarki ne mai adalci. Ƙari ga haka, Yesu ya tsarkake sunan Ubansa.

14. Ta yaya ya kamata mu ƙuduri niyyar yin rayuwa a kowace rana? Ka bayyana.

14 Wane darasi ne za mu iya koya daga kalmomin Yesu? Wajibi ne mu riƙe amincinmu a kowace rana. Ka yi la’akari da furucin Ɗan’uwa Maxwell Friend wanda shi malami ne a Makarantar Gilead. Sa’ad da yake yin jawabi game da aminci a wani taron ƙasashe, ya ce: “Kada ka yi shiririta a kan abin da ya kamata ka yi yau. Ka san ko za ka rayu har gobe? Ka yi rayuwa kowace rana a hanyar da za ta cancanci yin rayuwa har abada.” Bari mu yi rayuwa kowace rana kamar ita ce rana na ƙarshe na kasancewa da aminci! Idan muna gab da mutuwa, za mu iya cewa, “Jehobah, na yi iya ƙoƙarina in kasance da aminci, na nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne, na tsarkake sunanka kuma na goyi bayan Mulkinka!”

“A CIKIN HANNUWANKA NAKE BA DA RUHUNA”

15. Kamar yadda aka nuna a Luka 23:​46, wane tabbaci ne Yesu yake da shi?

15 Mene ne Yesu ya ce? (Karanta Luka 23:46.) Yesu ya ce da tabbaci: “Uba! A cikin hannuwanka nake ba da ruhuna.” Yesu ya san cewa rayuwarsa a nan gaba ya dangana da Jehobah kuma ya tabbata cewa Ubansa zai tuna da shi.

16. Wane darasi ka koya daga labarin wani Mashaidi ɗan shekara 15?

16 Wane darasi ne za mu iya koya daga kalmomin Yesu? Ka kasance da aminci ga Jehobah ko da rayuwarka tana cikin haɗari. Don ka yi hakan, wajibi ne ka “dogara ga Yahweh da dukan zuciyarka.” (K. Mag. 3:5) Ka yi la’akari da labarin wani matashi ɗan shekara 15 mai suna Joshua da ke ciwon ajali. Ya ƙi ya yi jinyar da za ta sa ya taka dokar Allah. Kafin ya mutu, ya gaya wa mahaifiyarsa cewa: “Mama, Jehobah zai kula da ni. . . . Ina da tabbaci cewa Jehobah zai ta da ni daga mutuwa a nan gaba. Ya san zuciyata da yadda nake ji, kuma ina ƙaunar sa sosai.” * Ya dace kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Idan na fuskanci yanayi da zai iya sa in mutu, zan kasance da aminci ga Jehobah cewa zai tuna da ni?’

17-18. Waɗanne darussa muka koya? (Ka kuma duba akwatin nan “ Abin da Muka Koya Daga Kalmomin Yesu na Ƙarshe.”)

17 Mun koyi darussa masu muhimmanci daga kalmomin Yesu na ƙarshe! An tunasar mana cewa muna bukatar mu riƙa gafarta wa mutane kuma mu kasance da tabbaci cewa zai gafarta mana. Muna da ’yan’uwa maza da mata a cikin ikilisiya da suke a shirye su taimaka mana a duk lokacin da muke da bukata. Amma wajibi ne mu nemi taimako. Mun san cewa Jehobah zai taimaka mana mu jimre duk jarrabawar da muke fuskanta. Kuma mun ga muhimmancin yin rayuwa kullum kamar ranarmu ce ta ƙarshe. Muna yin hakan da tabbaci cewa Jehobah zai ta da mu idan muka mutu.

18 Hakika, kalmomin Yesu sa’ad da yake gab da mutuwa suna iya koya mana abubuwa da yawa! Ta wajen yin amfani da darussan da muka koya, muna yin biyayya da kalmomin Jehobah game da Ɗansa cewa: “Ku saurare shi!”​—Mat. 17:5.

WAƘA TA 126 Mu Yi Tsaro, Mu Riƙe Aminci, Mu Yi Ƙarfi

^ sakin layi na 5 Kamar yadda aka ambata a Matiyu 17:​5, Jehobah yana so mu saurari Ɗansa. A wannan talifin, za mu tattauna darussa da yawa da muka koya daga kalmomin Yesu sa’ad da yake gab da mutuwa a kan gungumen azaba.

^ sakin layi na 9 Idan kana so ka san ƙarin dalilan da suka sa Yesu ya yi ƙaulin abin da ke Zabura 22:​1, ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a fitowar nan.

^ sakin layi na 16 Ka duba talifin nan “Joshua’s Faith​—A Victory for Children’s Rights” a fitowar Awake! na 22 ga Janairu, 1995.