Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 16

Ku Rika Nuna Godiya don Yesu Ya Fanshe Mu

Ku Rika Nuna Godiya don Yesu Ya Fanshe Mu

“Ɗan Mutum ya zo . . . domin ya . . . ba da ransa domin ceton mutane da yawa.”​—MAR. 10:45.

WAƘA TA 18 Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Mece ce fansa, kuma me ya sa muke bukatar fansar?

A LOKACIN da Adamu ya yi zunubi, ya yi hasarar yin rayuwa har abada. Ƙari ga haka, ya hana yaran da zai haifa a nan gaba samun zarafin yin rayuwa har abada. Adamu ba shi da hujjar yin zunubi. Ya yi hakan ne da gangan. Yaransa fa? Ba su yi wani laifi ba. (Rom. 5:​12, 14) Adamu ya cancanci ya mutu don zunubinsa. Amma da yake yaransa ba su yi laifi ba, shin Jehobah zai iya taimaka musu su rayu har abada? Ƙwarai kuwa! Ba da daɗewa ba bayan Adamu ya yi zunubi, Jehobah ya bayyana shirin da yake yi don ya ceci ’ya’yan Adamu daga zunubi da kuma mutuwa. (Far. 3:15) A lokacin da Jehobah ya ƙayyade, zai aiko da Ɗansa daga sama don ya “ba da ransa domin ceton mutane da yawa.”​—Mar. 10:45; Yoh. 6:51.

2 Mece ce fansa? A Nassosin Helenanci, kalmar nan tana nufin abin da Yesu ya biya don ya ceci ’yan Adam. (1 Kor. 15:22) Me ya sa muke bukatar fansar? Domin a Dokar da Jehobah ya bayar, ya ce a ba da rai a maimakon rai. (Fit. 21:​23, 24) Adamu ya yi hasarar kamiltaccen rai da yake da shi. Domin a cika dokar Allah, Yesu ya ba da kamiltaccen ransa. (Rom. 5:17) Hakan ya sa ya zama “Uba Madawwami” ga dukan mutanen da suka yi imani da fansar.​—Isha. 9:6; Rom. 3:​23, 24.

3. Kamar yadda Yohanna 14:31 da 15:13 suka nuna, me ya sa Yesu ya yarda ya mutu?

3 Yesu yana a shirye ya sadaukar da ransa domin yana matuƙar ƙaunar mu da kuma Ubansa. (Karanta Yohanna 14:31; 15:13.) Ƙaunar nan ta motsa shi ya riƙe amincinsa har ƙarshe kuma ya cika nufin Ubansa. A sakamakon haka, nufin Jehobah ga mutane da kuma duniya zai cika. A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale Yesu ya sha wahala sosai kafin ya mutu. Za mu kuma tattauna labarin wani marubucin Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa yana daraja fansar Yesu sosai. Bayan haka, za mu tattauna yadda za mu nuna godiya don fansar da Jehobah da kuma Yesu suka tanada mana.

ME YA SA YESU YA SHA WAHALA?

Ku yi tunanin irin wulaƙancin da Yesu ya jimre domin ya tanada mana fansar! (Ka duba sakin layi na 4)

4. Ka kwatanta yadda Yesu ya mutu.

4 Ka yi tunanin abin da ya faru a rana ta ƙarshe kafin a kashe Yesu. Ko da yake zai iya neman taimakon rundunar mala’iku a sama, ya ƙyale sojojin Roma su kama shi kuma su yi masa dūkan tsiya. (Mat. 26:​52-54; Yoh. 18:3; 19:1) Sun yi masa dūka da bulalar da ta ji masa rauni sosai. Daga baya, sun sa ya ɗauki gungume a bayansa da ke cike da rauni. Sai Yesu ya soma jan gungumen zuwa wurin da za a kashe shi. Amma da ya gāji, sai sojojin suka gaya wa wani mutum ya ɗauki gungumen. (Mat. 27:32) Sa’ad da Yesu ya kai inda za a kashe shi, sai sojojin suka buga ƙusa a hannuwansa da ƙafafunsa a jikin gungumen. Nauyin jikinsa yana ta yaga inda suka buga ƙusar. Abokansa da mahaifiyarsa suna ta yin kuka, amma shugabannin Yahudawa suna ta yi masa dariya. (Luk. 23:​32-38; Yoh. 19:25) Yesu ya yi sa’o’i da yawa yana ta shan azaba. Sannu a hankali, sai yin numfashi ya soma yi masa wuya. Kafin ya mutu, ya yi addu’a ta ƙarshe ga Jehobah. Sai ya sunkuyar da kansa kuma ya daina numfashi. (Mar. 15:37; Luk. 23:46; Yoh. 10:​17, 18; 19:30) Babu shakka, Yesu ya sha wahala sosai kafin ya mutu!

5. Mene ne ya fi sa Yesu baƙin ciki?

5 Ba yadda aka kashe Yesu ba ne ya fi damun sa ba. Amma ƙarairayin da aka yi a kansa kafin a kashe shi ne. An yi ƙarya a kansa cewa shi mai yin saɓo ne, wato ba ya daraja Allah. (Mat. 26:​64-66) Ganin cewa mutane za su iya yin ƙarya a kansa cewa ba ya daraja Allah ya sa shi baƙin ciki sosai kuma ya so Ubansa ya kāre shi don kada ya fuskanci jarrabawar. (Mat. 26:​38, 39, 42) Me ya sa Jehobah ya ƙyale Ɗansa ƙaunatacce ya sha wahala kuma ya mutu? Bari mu tattauna dalilai uku.

6. Me ya sa aka rataye Yesu a kan gungume?

6 Da farko, an rataye Yesu a kan gungume domin a kuɓutar da Yahudawa daga wata la’ana. (Gal. 3:​10, 13) Suna da wannan la’anar ne domin sun yi alkawarin bin Dokokin Allah, amma ba su yi hakan ba. Ƙari ga haka, sun cancanci su mutu domin su ’ya’yan Adamu ne. (Rom. 5:12) Allah ya faɗa a Dokar da ya ba Isra’ilawa cewa a kashe duk mutumin da ya yi zunubi mai tsanani. Bayan haka, a wasu lokuta ana iya rataye gawarsa a kan gungume. * (M. Sha. 21:​22, 23; 27:26) Da yake an rataye Yesu a kan gungume, ya ceci Yahudawa daga wannan la’anar, kuma hadayarsa za ta taimaka musu duk da cewa sun ƙi shi.

7. Wane dalili na biyu ne ya sa Allah ya ƙyale Ɗansa ya sha wahala?

7 Ga dalili na biyu da ya sa Allah ya ƙyale Ɗansa ya sha wahala. Yana horar da Yesu ne don aikin da zai yi a nan gaba a matsayin Babban Firist. Yesu ya ga cewa yana da wuya mutum ya riƙe aminci sa’ad da yake fuskantar jarrabawa mai tsanani. Ya fuskanci jarrabawa sosai har ya nemi taimako, yana “kuka mai tsanani da hawaye.” Babu shakka, domin Yesu ya sha wahala, ya fahimci bukatunmu kuma ‘ya isa ya taimake’ mu sa’ad da ‘ake gwada mu.’ Muna farin ciki sosai cewa Jehobah ya naɗa mana Babban Firist, wanda ya “damu da kāsawarmu”!​—Ibran. 2:​17, 18; 4:​14-16; 5:​7-10.

8. Wane dalili na uku ne ya sa Allah ya bari Yesu ya sha wahala?

8 Na uku, Jehobah ya ƙyale Ɗansa ya sha wahala domin ya ba da amsa ga wata muhimmiyar tambaya cewa: ’Yan Adam za su iya riƙe amincinsu sa’ad da suke fuskantar jarrabawa mai tsanani? Shaiɗan ya ce ba zai yiwu ba! Ya ce ’yan Adam suna bauta wa Allah ne domin alherin da yake musu. Kuma yana ganin cewa ’yan Adam ba sa ƙaunar Jehobah yadda Adamu ma bai ƙaunaci Jehobah ba. (Ayu. 1:​9-11; 2:​4, 5) Da yake Jehobah ya amince da Ɗansa, ya bari a jarraba shi fiye da yadda kowane ɗan Adam zai iya jimrewa. Yesu ya riƙe amincinsa kuma ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne.

MANZO YOHANNA YA NUNA GODIYA DON FANSAR YESU

9. Wane misali mai kyau ne manzo Yohanna ya kafa mana?

9 Koyarwa game da fansa ta ƙarfafa bangaskiyar Kiristoci da yawa. Sun ci gaba da yin wa’azi duk da tsanantawa kuma sun jimre muddar ransu. Ku yi la’akari da misalin manzo Yohanna. Ya yi wa’azi game da Yesu da kuma fansar wataƙila fiye da tsawon shekara 60. Sa’ad da ya kusan shekara 100, Romawa suna ganin cewa shi maƙiyinsu ne, don haka suka tsare shi a kurkuku a tsibirin Batmusa. Sun ce yana yin “wa’azin kalmar Allah da shaidar Yesu.” (R. Yar. 1:9) Babu shakka, Yohanna ya jimre sosai!

10. Ta yaya littattafan da Yohanna ya rubuta suka nuna cewa ya daraja fansar?

10 A littattafan da Yohanna ya rubuta, ya ambata cewa yana ƙaunar Yesu sosai kuma yana daraja hadayarsa. Ya yi magana fiye da sau 100 game da fansar ko kuma abubuwan da fansar ta cim ma. Alal misali, Yohanna ya ce: “In har wani ya yi zunubi, to, muna da mai tsaya mana a gaban Uba, wato Yesu Almasihu mai adalci.” (1 Yoh. 2:​1, 2) Yohanna ya kuma nanata muhimmancin yin ‘shaida’ game da Yesu. (R. Yar. 19:10) Babu shakka, Yohanna ya nuna godiya sosai domin fansar. Ta yaya za mu nuna cewa mun daraja fansar?

TA YAYA ZA KA NUNA GODIYA DON FANSAR YESU?

Idan mun daraja fansar sosai, za mu guji yin zunubi (Ka duba sakin layi na 11) *

11. Mene ne zai iya taimaka mana mu yi tsayayya da jarrabawa?

11 Ka guji yin zunubi. Idan muna daraja fansar Yesu sosai, ba za mu kasance da ra’ayin nan cewa: ‘Ba na bukatar in ƙoƙarta don kada in yi zunubi. Zan iya yin zunubi, kuma bayan haka, in nemi gafara.’ Maimakon haka, idan mun fuskanci jarrabawa, ya kamata mu ce: ‘A’a! Ba zai dace in yi wannan abu ba, bayan dukan alherin da Jehobah da kuma Yesu suka yi mini.’ Ƙari ga haka, za mu iya roƙan Jehobah cewa: ‘Kada ka ƙyale ni in faɗa cikin jarrabawa.’​—Mat. 6:13.

12. Ta yaya za mu bi shawarar da ke 1 Yohanna 3:​16-18?

12 Ku ƙaunaci ’yan’uwanku. Idan muna ƙaunar ’yan’uwanmu, muna nuna cewa mun daraja fansar. Me ya sa? Domin Yesu bai mutu don mu kaɗai ba, amma don ’yan’uwanmu maza da mata. Da yake ya mutu dominsu, ya nuna cewa ya daraja su sosai. (Karanta 1 Yohanna 3:​16-18.) Muna nuna ƙaunarmu ga ’yan’uwanmu ta yadda muke sha’ani da su. (Afis. 4:​29, 31–5:2) Alal misali, muna taimaka musu sa’ad da suke rashin lafiya ko fuskantar jarrabawa mai tsanani ko kuma bala’i. Amma me ya kamata mu yi idan wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ɓata mana rai?

13. Me ya sa ya dace mu riƙa gafartawa?

13 Yana maka wuya a wasu lokuta ka gafarta wa wani a ikilisiya? (L. Fir. 19:18) Idan haka ne, ka bi shawarar nan: “Kuna ta yin haƙuri da juna. Idan kuma wani a cikinku ya yi wa wani laifi, ku gafarta masa kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku zunubanku, haka ma ku ma ku gafarta wa juna.” (Kol. 3:13) A duk lokacin da muka gafarta wa ’yan’uwanmu, muna gaya wa Jehobah cewa muna daraja fansar Yesu. Ta yaya za mu ci gaba da nuna cewa mun daraja wannan kyautar?

TA YAYA ZA MU NUNA GODIYARMU DON FANSAR YESU?

14. A wace hanya ce za mu nuna godiya sosai domin fansar Yesu?

14 Ka gode wa Jehobah don fansar. Wata ’yar’uwa ’yar shekara 83 a Indiya mai suna Joanna ta ce: “Ina ganin ya dace in ambata fansar kullum a addu’ata kuma in gode wa Jehobah don wannan kyautar.” Sa’ad da kake addu’a, ka gaya wa Jehobah wani laifi da ka yi, kuma ka ce ya gafarta maka. Idan zunubin da ka yi mai tsanani ne, za ka bukaci dattawa ma su taimaka maka. Za su saurare ka kuma su ba ka shawara daga Kalmar Allah. Za su yi addu’a da kai kuma su roƙi Jehobah ya gafarta maka domin ka gyara dangantakarka da shi.​—Yak. 5:​14-16.

15. Me ya sa ya dace mu yi nazari da kuma tunani game da fansar?

15 Ka yi tunani sosai game da fansar. Wata ’yar’uwa ’yar shekara 73 mai suna Rajamani ta ce: “A duk lokacin da na karanta game da irin wahalar da Yesu ya sha, ina zub da hawaye sosai.” Kai ma za ka iya yin baƙin ciki sa’ad da ka yi tunani game da yadda Ɗan Allah ya sha wahala. Amma idan kana tunani sosai game da fansar Yesu, za ka ƙaunace shi da Jehobah sosai. Domin ka iya yin tunani mai zurfi game da fansar, zai dace ka yi nazari game da batun.

Ta yin taro mai sauƙi, Yesu ya nuna wa almajiransa yadda za su riƙa tuna da hadayar da ya yi (Ka duba sakin layi na 16)

16. Ta yaya za mu amfana sa’ad da muka koya wa mutane game da fansar? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

16 Ka koya wa mutane game da fansar. Za mu daraja fansar Yesu sosai a duk lokacin da muka gaya wa mutane game da ita. Muna da littattafai da kuma bidiyoyi da yawa da za mu yin amfani da su don koya wa mutane dalilan da suka sa Yesu ya mutu dominmu. Alal misali, za ku iya yin amfani da darasi na 4 na ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! Jigon darasin shi ne “Wane Ne Yesu Kristi?” Ko kuma babi na 5 na littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? Jigon babin shi ne “Fansa, Kyauta Ce Mafi Girma Daga Allah.” Kuma a kowace shekara, muna nuna godiyarmu don fansar ta wajen halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu da kuma gayyatar mutane su halarci taron. Jehobah ya ba mu gatar koya wa mutane game da Ɗansa!

17. Me ya sa fansar Yesu ce kyauta mafi girma da Allah ya tanada mana?

17 Babu shakka, muna da dalilai masu yawa na nuna godiya domin fansar Yesu. Fansar Yesu ta sa ya yiwu mu ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah duk da cewa mu ajizai ne. Kuma fansar za ta sa a rushe ayyukan Shaiɗan gabaki ɗaya. (1 Yoh. 3:8) Ƙari ga haka, fansar za ta sa a cika nufin Jehobah ga duniyar nan. Duniyar nan gabaki ɗaya za ta zama aljanna. A lokacin, duk mutumin da ke duniyar nan zai riƙa ƙaunar Jehobah da kuma bauta masa. Saboda haka, bari mu riƙa nuna godiya kowace rana domin kyauta mafi girma da Jehobah ya tanada mana, wato fansar Yesu!

WAƘA TA 20 Ka Ba da Ɗanka Mai Daraja

^ sakin layi na 5 Me ya sa Yesu ya sha wahala kuma ya mutu? Za a amsa tambayar nan a wannan talifin. Talifin zai taimaka mana mu nuna godiya domin Yesu ya fanshe mu.

^ sakin layi na 6 Romawa suna yawan ɗaure mutum a kan gungume ko su buga masa ƙusa da ransa. Jehobah ya bari a kashe Ɗansa a wannan hanyar.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTUNA: Kowanne cikin waɗannan ’yan’uwan ya ƙi ya kalli hotunan batsa ko ya sha sigari ko kuma ya karɓi cin hanci.