Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 17

Jehobah Yana Kaunarka Sosai!

Jehobah Yana Kaunarka Sosai!

Jehobah “yana ƙaunar mutanensa.”​—2 TAR. 2:11.

WAƘA TA 108 Ƙauna ta Gaskiya Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

Ubanmu da ke sama “yana ƙaunar” kowanenmu (Ka duba sakin layi na 1)

1. Mene ne Jehobah yake gani game da mutanensa?

JEHOBAH “yana ƙaunar mutanensa.” (2 Tar. 2:11) Hakan yana sa mu farin ciki! Jehobah yana ganin halayenmu masu kyau kuma yana taimaka mana mu zama abokansa. Idan muka kasance da aminci a gare shi, shi ma zai kusace mu!​—Yoh. 6:44.

2. Me ya sa yake wa wasu wuya su gaskata cewa Jehobah yana ƙaunar su?

2 Wasu za su iya cewa, ‘Na san cewa Jehobah yana ƙaunar mutanensa gabaki ɗaya, amma yaya zan san cewa yana ƙauna ta?’ Mene ne zai iya sa mutum ya yi wannan tambayar? Wata mai suna Oksana, * wadda ta sha wahala sosai sa’ad da take ƙarama ta ce: “Na yi farin ciki sosai sa’ad da na yi baftisma kuma na soma hidimar majagaba. Amma bayan shekara 15, na soma tuna mugayen abubuwan da suka faru da ni sa’ad da nake ƙarama. Sai na soma tunani cewa Jehobah ya daina amincewa da ni.” Wata majagaba mai suna Yua, wadda ta fuskanci matsaloli sosai sa’ad da take ƙarama ta ce: “Na yi alkawarin bauta wa Jehobah domin ina so in sa shi farin ciki. Amma na tabbatar wa kaina cewa ba ya ƙaunata.”

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Kamar waɗannan Kiristoci masu aminci da aka ambata, kai ma kana ƙaunar Jehobah amma wataƙila kana shakkar ko yana ƙaunar ka. Me ya sa kake bukatar ka kasance da tabbaci cewa yana ƙaunar ka sosai? Kuma me zai taimaka maka ka jimre sa’ad da kake tunanin cewa Jehobah ba ya ƙaunar ka? Bari mu tattauna amsoshin waɗannan tambayoyin.

YIN SHAKKAR ƘAUNAR JEHOBAH YANA DA LAHANI

4. Me ya sa yake da lahani mu riƙa shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu?

4 Ƙauna tana da iko sosai. Idan mun tabbata cewa Jehobah yana ƙaunar mu da kuma taimaka mana, hakan zai motsa mu mu bauta masa da zuciya ɗaya ko da muna fuskantar matsaloli. Amma, idan muna shakka cewa Allah yana ƙaunar mu, ba za mu kasance da “ƙarfi” ba. (K. Mag. 24:10) Idan muka yi sanyin gwiwa kuma muka soma ganin cewa Allah ba ya ƙaunar mu, ba za mu iya yin tsayayya da Shaiɗan ba.​—Afis. 6:16.

5. Me ya faru da wasu da suke shakka cewa Allah yana ƙaunar su?

5 Wasu ’yan’uwanmu sun soma shakka cewa Jehobah yana ƙaunar su kuma hakan ya raunana bangaskiyarsu. Wani dattijo mai suna James ya ce: “Ko da yake ina hidima a Bethel kuma ina jin daɗin yin wa’azi a ikilisiyar da ake wani yare, ban tabbata ko Jehobah ya amince da hidimar da nake masa ba. Har na soma shakka ko Jehobah yana jin addu’o’ina.” Wata mai suna Eva wadda take hidima ta cikakken lokaci ta ce: “Na koyi cewa bai dace mu riƙa shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu ba, domin hakan zai shafi kome da muke yi a bautarmu. Zai sa ka daina marmarin yin nufin Allah kuma ka daina farin cikin bauta masa.” Wani dattijo mai suna Michael da ke hidimar majagaba na kullum ya ce: “Idan ba ka gaskata cewa Allah yana ƙaunar ka ba, hakan zai sa ka daina bauta masa.”

6. Mene ne za mu yi idan muka soma shakka cewa Allah yana ƙaunar mu?

6 Misalan nan sun nuna cewa idan muna shakkar ƙaunar Jehobah a gare mu, za mu ɓata dangantakarmu da shi. Amma, me ya kamata mu yi idan muka soma irin wannan tunanin? Wajibi ne mu daina yin irin wannan tunanin nan da nan! Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka sauya ‘tunanin’ nan da salama ta Allah da za ta ‘tsare zuciyarka da tunaninka.’ (Zab. 139:23; Filib. 4:​6, 7) Kuma ka tuna cewa ba kai kaɗai ba ne ke yin irin wannan tunanin. Akwai ’yan’uwa masu aminci da suke fama da irin wannan tunanin. Har bayin Jehobah a dā sun yi fama da irin wannan tunanin. Ka yi la’akari da abin da za mu koya daga manzo Bulus.

DARASI DAGA LABARIN MANZO BULUS

7. Waɗanne matsaloli ne Bulus ya jimre da su?

7 Kana yin tunani a wasu lokuta cewa ayyukan da kake da su sun fi ƙarfinka? Idan haka ne, za ka fahimci abin da Bulus ya fuskanta. Ya damu da “dukan jama’ar masu bi” sosai. (2 Kor. 11:​23-28) Kana rashin lafiya mai tsanani da ke hana ka farin ciki? Bulus ya yi fama da “ƙaya a jiki,” kuma wataƙila rashin lafiya mai tsanani ne da yake so ya daina damunsa. (2 Kor. 12:​7-10) Ajizancinka yana sa ka baƙin ciki? Hakan ya faru da Bulus. Ya ce shi “abin tausayi ne” domin ya yi fama don ya yi abin da ya dace.​—Rom. 7:​21-24.

8. Mene ne ya taimaka wa Bulus ya jimre da matsalolinsa?

8 Duk da cewa Bulus ya fuskanci waɗannan matsalolin, ya ci gaba da bauta wa Jehobah. Mene ne ya ƙarfafa shi ya yi hakan? Ko da yake Bulus ya san kasawarsa, ya kasance da bangaskiya ga fansar da Yesu ya ba da. Kuma ya san alkawarin da Yesu ya yi cewa ‘dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi [Yesu] . . . zai sami rai na har abada.’ (Yoh. 3:16; Rom. 6:23) Bulus yana cikin waɗanda suka ba da gaskiya ga hadayar Yesu. Yana da tabbaci cewa Jehobah yana so ya gafarta wa mutane har da waɗanda suka yi zunubi mai tsanani idan suka tuba.​—Zab. 86:5.

9. Mene ne muka koya daga kalmomin Bulus da ke Galatiyawa 2:20?

9 Bulus yana da bangaskiya cewa Allah yana ƙaunarsa sosai domin ya san cewa Allah ya turo Yesu ya mutu a madadinsa. (Karanta Galatiyawa 2:20.) Bulus ya faɗi kalmomi masu ban-ƙarfafa a ƙarshen wannan ayar, ya ce: ‘Ɗan Allah, . . . ya ƙaunace ni har ya ba da ransa domina.’ Bulus bai yi tunanin cewa zunubansa sun yi yawa har Allah ba zai ƙaunace shi ba. Bai ce, ‘Na fahimci dalilin da ya sa Jehobah yake ƙaunar ’yan’uwana amma ba ya ƙauna ta.’ Maimakon Bulus ya yi tunanin haka, ya gaya wa Romawa cewa: ‘Tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu saboda mu.’ (Rom. 5:8) Ƙaunar Jehobah a gare mu ba ta da iyaka!

10. Me muka koya daga Romawa 8:​38, 39?

10 Karanta Romawa 8:​38, 39. Bulus ya san cewa Allah yana ƙaunar mu sosai. Ya ce babu abin da zai “raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana.” Bulus ya san cewa Jehobah ya yi haƙuri sosai da al’ummar Isra’ila. Ƙari ga haka, ya san cewa Jehobah ya nuna masa jinƙai sosai. To mene ne yake nufi? Bulus yana nufin cewa, ‘Tun da Jehobah ya turo Ɗansa ya mutu a madadina, bai kamata in yi shakka cewa yana ƙauna ta ba.’​—Rom. 8:32.

Abin da ya fi muhimmanci ga Allah shi ne abin da muke yi a yanzu da abin da za mu yi a nan gaba, ba kurakuran da muka yi a dā ba (Ka duba sakin layi na 11) *

11. Ko da yake Bulus ya yi zunubai kamar waɗanda aka ambata a 1 Timoti 1:​12-15, me ya sa ya tabbata cewa Allah yana ƙaunarsa?

11 Karanta 1 Timoti 1:​12-15. Zai yiwu cewa akwai lokutan da Bulus ya yi baƙin ciki sa’ad da ya tuna da abubuwan da ya yi kafin ya zama Kirista. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne da ya kira kansa “mafi” zunubi! Kafin Bulus ya soma bauta wa Jehobah, ya tsananta wa Kiristoci a birane da yawa, ya sa wasu a kurkuku kuma ya amince da hukuncin da kotu ta yi na kashe wasu Kiristoci. (A. M. 26:​10, 11) Babu shakka Bulus zai yi baƙin ciki idan ya haɗu da wani matashi da iyayensa suke cikin waɗanda ya amince a kashe su. Bulus ya yi da-na-sani don kurakurai da ya yi a dā amma ba zai iya canja su ba. Ya gaskata cewa Kristi ya mutu a madadinsa, kuma ya ce: “Saboda alherin Allah ne na zama yadda nake.” (1 Kor. 15:​3, 10) Wane darasi ne muka koya? Kana bukatar ka kasance da tabbaci cewa Kristi ya mutu a madadinka kuma hakan ya sa ya yiwu ka ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. (A. M. 3:19) Abin da ya fi muhimmanci ga Allah shi ne abin da muke yi a yanzu da abin da za mu yi a nan gaba, ba kurakuran da muka yi a ba, ko mu Shaidun Jehobah ne a lokacin ko a’a.​—Isha. 1:18.

12. Ta yaya kalmomin da ke 1 Yohanna 3:​19, 20 za su taimaka mana idan muna ganin ba mu da amfani ko kuma Jehobah ba ya ƙaunar mu?

12 Idan ka yi tunanin yadda Yesu ya mutu domin zunubanka, za ka iya cewa, ‘Ban cancanci samun wannan kyauta mai tamani ba.’ Me ya sa za ka ji hakan? Zuciyarmu za ta iya ruɗan mu, ta sa mu ji ba mu da amfani ko kuma Jehobah ba ya ƙaunar mu. (Karanta 1 Yohanna 3:​19, 20.) Idan muka soma irin wannan tunanin, ya kamata mu tuna cewa “Allah ya fi zuciyarmu.” Ko da muna ganin cewa Jehobah ba ya ƙaunar mu ko kuma ba zai gafarta mana ba, har ila Ubanmu yana ƙaunar mu kuma zai gafarta mana zunubanmu. Muna bukatar mu gaskata cewa Jehobah yana ƙaunar mu. Abin da zai taimaka mana mu yi hakan shi ne nazarin Kalmarsa a kai a kai da yin addu’a ba fasawa da kuma yin cuɗanya da mutanen da suke bauta masa. Me ya sa yin waɗannan abubuwan suke da muhimmanci?

NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI, ADDU’A DA KUMA AMINAI ZA SU TAIMAKA

13. Ta yaya nazarin Kalmar Allah zai taimaka mana? (Ka duba akwatin nan “ Yadda Kalmar Allah Take Taimaka Musu.”)

13 Idan kana yin nazarin Kalmar Allah a kowace rana, za ka daɗa ganin halayen Jehobah masu kyau. Za ka ga cewa yana ƙaunar ka sosai. Sa’ad da ka yi tunani sosai game da Kalmar Allah a kowace rana, hakan zai taimaka maka ka daidaita ra’ayinka. (2 Tim. 3:16) Wani dattijo mai suna Kevin da yake gani a wasu lokuta cewa ba shi da daraja ya ce: “Karanta da kuma yin bimbini a kan Zabura ta 103 ya taimaka mini in daidaita ra’ayina kuma in san yadda Jehobah yake ganina.” Eva da aka ambata ɗazu ta ce: “Abin da nake yi kafin in yi barci shi ne yin bimbini game da ra’ayin Jehobah. Hakan yana sa in kasance da kwanciyar hankali kuma in ƙarfafa bangaskiyata.”

14. Ta yaya yin addu’a za ta taimaka mana?

14 Ka riƙa addu’a babu fasawa. (1 Tas. 5:17) Idan kana so ka yi abokantaka da wani, dole ne ka riƙa gaya masa yadda kake ji a kowane lokaci. Haka yake da dangantakarmu da Jehobah. Sa’ad da muka gaya masa yadda muke ji da kuma ra’ayinmu a addu’a, muna nuna cewa mun dogara da shi kuma mun san cewa yana ƙaunar mu. (Zab. 94:​17-19; 1 Yoh. 5:​14, 15) Yua da aka ambata ɗazu ta ce: “Sa’ad da nake addu’a, ba na gaya wa Jehobah abin da ya faru a ranar kaɗai, amma ina gaya masa ra’ayina da kuma yadda nake ji. A hankali, na zo na ga cewa Jehobah ba manajar babban kamfani ba ne amma Uba ne da ke ƙaunar yaransa sosai.”​—Ka duba akwatin nan “ Ka Karanta Kuwa?

15. Ta yaya Jehobah yake nuna ya damu da mu?

15 Ka riƙa cuɗanya da aminai don su baiwa ne daga Jehobah. (Yak. 1:17) Ubanmu da ke sama ya nuna cewa ya damu da mu ta wajen tanadar mana ’yan’uwa a ikilisiya da suke “nuna ƙauna” a kowane lokaci. (K. Mag. 17:17) A wasiƙar da Bulus ya tura wa Kolosiyawa, ya ambata wasu Kiristoci da suka taimaka masa, kuma ya kira su “abin ta’aziyya.” (Kol. 4:​10, 11) Yesu Kristi ma ya nuna godiya don yadda mala’iku da kuma ’yan Adam suka taimaka masa.​—Luk. 22:​28, 43.

16. Ta yaya aminai za su taimaka mana mu kusaci Jehobah?

16 Kana nema da kuma karɓan taimako daga abokanka da ke ikilisiya? Gaya wa abokinmu da ya manyanta matsalolinmu ba ya nufin cewa ba mu da bangaskiya, amma hakan zai kāre mu. James da aka ambata ɗazu ya ce: “Yin abokantaka da Kiristoci da suka manyanta ya taimaka mini sosai. Sa’ad da na soma yin tunanin da bai dace ba, waɗannan abokan sukan saurare ni kuma su gaya mini cewa suna ƙaunata sosai. Sa’ad da suka yi hakan, nakan san cewa Jehobah yana ƙaunata kuma ya damu da ni.” Saboda haka, yana da muhimmanci mu ƙulla abokantaka na kud da kud da ’yan’uwanmu!

KA CI GABA DA ƘAUNAR JEHOBAH

17-18. Wa ya kamata mu saurara, kuma me ya sa?

17 Shaiɗan yana so mu daina yin abin da ya dace. Yana so mu gaskata cewa Jehobah ba ya ƙaunar mu, kuma ba mu cancanci Jehobah ya cece mu ba. Amma kamar yadda muka gani, hakan ba gaskiya ba ne.

18 Jehobah yana ƙaunar ka kuma kana da daraja a gabansa. Idan ka yi masa biyayya, za ka ‘zauna a cikin ƙaunar sa’ har abada kamar Yesu. (Yoh. 15:10) Saboda haka, kada ka gaskata da Shaiɗan ko kuma zuciyarka. A maimakon haka, ka saurari Jehobah wanda yake mai da hankali ga ayyuka masu kyau da kowannenmu yake yi. Ka kasance da tabbaci cewa yana ƙaunar “mutanensa” har da kai!

WAƘA TA 141 Rai, Kyauta Ce Daga Allah

^ sakin layi na 5 Wasu cikin ’yan’uwanmu ba su gaskata cewa Jehobah yana ƙaunar su ba. A wannan talifin za mu tattauna dalilin da ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar kowannenmu. Za mu kuma tattauna abin da za mu yi idan muna shakka cewa yana ƙaunar mu.

^ sakin layi na 2 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 67 BAYANI A KAN HOTUNA: A dā Bulus ya tsananta wa Kiristoci da yawa kuma ya tura su kurkuku. Amma ya canja sa’ad da ya amince da abin da Yesu ya yi a madadinsa, kuma ya ƙarfafa ’yan’uwansa. Wataƙila ya tsananta wa ’yan’uwan wasu a cikinsu.