Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 20

Kada Ka Gaji da Yin Wa’azi

Kada Ka Gaji da Yin Wa’azi

“Ka shuka hatsinka, . . . kada ka naɗa hannuwanka.”​—M. WA. 11:6.

WAƘA TA 70 Ku Nemi Masu Zuciyar Kirki

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

Bayan Yesu ya koma sama, mabiyansa sun ci gaba da yin ƙwazo a wa’azi a Urushalima da kuma wasu wurare (Ka duba sakin layi na 1)

1. Wane misali ne Yesu ya kafa wa mabiyansa, kuma mene ne suka yi? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

YESU ya yi wa’azi da farin ciki a lokacin da yake duniya, kuma yana so mabiyansa ma su yi hakan. (Yoh. 4:​35, 36) Sa’ad da Yesu yake tare da almajiransa, sun yi wa’azi da ƙwazo sosai. (Luk. 10:​1, 5-11, 17) Amma da aka kama Yesu kuma aka kashe shi, almajiransa sun ɗan yi sanyin gwiwa. (Yoh. 16:32) Bayan ya tashi daga matattu, Yesu ya ƙarfafa su su mai da hankali ga yin wa’azi. Bayan ya koma sama, almajiransa sun yi wa’azi da ƙwazo sosai har hakan ya sa maƙiyansu suka ce: “Kun cika Urushalima duk da koyarwarku.”​—A. M. 5:28.

2. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa bayinsa su yi nasara a yin wa’azi?

2 Yesu ya yi wa Kiristoci na farko ja-goranci yayin da suke wa’azi kuma Jehobah ya taimaka musu su sami ƙaruwa. Alal misali, a ranar Fentakos ta shekara ta 33, mutane wajen 3,000 sun yi baftisma. (A. M. 2:41) Kuma adadin mabiyan Yesu ya ci gaba da ƙaruwa sosai. (A. M. 6:7) Duk da haka, Yesu ya annabta cewa za a sami ƙarin mutane da za su soma bauta wa Jehobah a kwanaki na ƙarshe.​—Yoh. 14:12; A. M. 1:8.

3-4. Me ya sa wa’azi yake yi wa wasu wuya, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Dukanmu muna bukata mu kasance da ra’ayin da ya dace game da yin wa’azi. A wasu ƙasashe, yin wa’azi yana da sauƙi. Me ya sa? Domin mutane da yawa suna son nazarin Littafi Mai Tsarki. Wasu a cikinsu ma sai sun jira kafin a sami Mashaidin da zai yi nazari da su! Amma a wasu wurare, yana da wuya masu shela su yi wa’azi, domin ba sa samun mutane a gida, kuma waɗanda suke gida ba sa son jin wa’azi.

4 Idan kana zama a yankin da yin wa’azi yake da wuya, shawarwarin da ke wannan talifin za su iya taimaka maka. Za mu tattauna abubuwan da wasu suka yi don su iya samun mutanen da za su yi musu wa’azi. Ƙari ga haka, za mu tattauna dalilin da ya sa ya kamata mu kasance da ra’ayin da ya dace ko da mutane sun saurare mu ko ba su saurare mu ba.

KA CI GABA DA YIN WA’AZI DA MURNA KO DA BA KA SAMUN MUTANE

5. Wane ƙalubale ne Shaidu da yawa suke fuskanta?

5 Yana yi wa Shaidun Jehobah da yawa wuya su sami mutane a gidajensu. Wasu masu shela suna zama a yankunan da gidajen suke da tsaro sosai ko kuma manyan ƙofofi. A irin waɗannan gidaje ko unguwa, wataƙila akwai mai gadi da zai hana ka shiga idan wani bai gayyace ka ba. Wasu masu shela kuma suna iya zuwa gida-gida yin wa’azi, amma ba sa samun mutane sosai a gida. Wasu kuma, suna wa’azi a ƙauyuka da ba mutane sosai. Masu shelar suna iya yin tafiya mai nisa don su nemi mutumin da wataƙila ba ya gida! Kada mu yi sanyin gwiwa idan muna yin wa’azi a irin waɗannan yankuna. Mene ne za mu yi don mu magance wannan ƙalubalen kuma mu yi wa mutane da yawa wa’azi?

6. Ta yaya masu wa’azi suke kama da masu kamun kifi?

6 Yesu ya kwatanta yin wa’azi da kamun kifi. (Mar. 1:17) Wasu masu kamun kifi suna iya yin kwanaki ba su kama kifi ba. Amma ba sa yin sanyin gwiwa, sai dai su canja yadda suke yin aikin. Sukan canja lokaci da wuri da kuma yadda suke kama kifin. Muna iya yin hakan a hidimarmu. Ka yi la’akari da waɗannan shawarwarin.

Idan muna wa’azi a wuraren da ba a yawan samun mutane a gida, zai dace mu yi ƙoƙari mu je a wasu lokuta dabam, mu neme su a wurare dabam-dabam ko kuma mu yi amfani da hanyoyi dabam-dabam (Ka duba sakin layi na 7-10) *

7. Wane sakamako ne za mu iya samu idan muka je wa’azi a lokaci dabam-dabam?

7 Ka ziyarci mutane a wani lokaci dabam. Idan muka je wa’azi a lokacin da mutane suke gida, za mu same su. Dole ne mutane su koma gidansu bayan sun tashi a aiki. ’Yan’uwa da yawa suna wa’azi da rana ko kuma da yamma domin lokacin da suka fi samun mutane a gida ke nan. Ƙari ga haka, a lokacin ne mutanen suke sake jiki kuma suke a shirye su saurari wa’azi. Ko kuma za ka iya bin shawarar da wani dattijo mai suna David ya bayar. Ya ce bayan ya yi wa’azi na ɗan lokaci a yankinsu, shi da abokin wa’azinsa suna komawa gidajen da ba su sami mutane ba. David ya ce: “Nakan yi mamaki don yawan mutane da muke samu sa’ad da muka koma gidajensu.” *

Idan muna wa’azi a wuraren da ba a yawan samun mutane a gida, zai dace mu yi ƙoƙari mu je a wasu lokuta dabam (Ka duba sakin layi na 7-8)

8. Ta yaya za mu bi shawarar da ke Mai-Wa’azi 11:6 yayin da muke wa’azi?

8 Kada mu yi sanyin gwiwa. Nassin da aka ɗauko jigon wannan talifin ya tuna mana halin da ya kamata mu kasance da shi. (Karanta Mai-Wa’azi 11:6.) David wanda aka ambata ɗazu bai yi sanyin gwiwa ba. Ya haɗu da wani mai gida bayan ya je gidan sau da yawa bai same shi ba. Mutumin yana son tattauna Littafi Mai Tsarki kuma ya ce: “Na yi wajen shekara takwas ina zama a wannan gidan, amma Shaidun Jehobah ba su taɓa zuwa wa’azi ba.” David ya ce: “Na lura cewa mutane sukan saurari wa’azinmu idan daga baya mun same su a gida.”

Idan muna wa’azi a wuraren da ba a yawan samun mutane a gida, mu neme su a wurare dabam-dabam (Ka duba sakin layi na 9)

9. Mene ne wasu Shaidu suka yi don su sami mutane a gida?

9 Ka je wani wuri dabam. Don su sami mutanen da ba sa zama a gida, wasu masu shela sun canja wurin da suke wa’azi. Alal misali, wa’azi a kan titi da yin amfani da amalanke hanyoyi ne masu kyau na haɗuwa da mutanen da suke zama a manyan gidaje da ba a yarda a yi wa’azi. Hakan yana ba Shaidun Jehobah damar tattaunawa da mutanen da suke zama a waɗannan gidajen da yake wuya a yi musu wa’azi. Ƙari ga haka, masu shela da yawa sun lura cewa mutane sun fi son tattaunawa ko kuma karɓan littattafanmu a tasha ko kasuwa ko kuma wuraren sana’a. Wani mai kula da da’ira mai suna Floiran a ƙasar Bolibiya ya ce: “Muna zuwa wa’azi a kasuwa da kuma wuraren sana’a tsakanin ƙarfe ɗaya da kuma uku na rana sa’ad da ’yan kasuwar ba sa ciniki sosai. Muna samun mutanen da za mu tattauna da su sosai har mu soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wasu.”

Idan muna wa’azi a wuraren da ba a yawan samun mutane a gida, zai dace mu yi ƙoƙari mu yi amfani da hanyoyi dabam-dabam (Ka duba sakin layi na 10)

10. Waɗanne abubuwa ne za ka iya yi don ka yi wa mutane wa’azi a yankinku?

10 Ka canja yadda kake yin wa’azi. A ce ka yi ta zuwa gidan wani don ka yi masa wa’azi amma ba ka gan shi ba. Ka je gidan a lokuta dabam-dabam amma duk da haka, ba ka same shi ba. Waɗanne matakai ne kuma za ka iya ɗaukawa don ka same shi? Wata mai suna Katarína ta ce: “Ina rubuta wasiƙu ga mutanen da ba na samun su a gida, kuma ina rubuta abin da zan gaya musu da a ce na haɗu da su.” Mene ne wannan ya koya mana? Ka gwada hanyoyi dabam-dabam da za ka iya yi wa kowa wa’azi a yankinku.

KA CI GABA DA YIN WA’AZI DA MURNA KO DA MUTANE BA SA SAURARA

11. Me ya sa wasu ba sa saurarar wa’azinmu?

11 Wasu mutane ba sa son saurarar wa’azinmu. Suna ganin ba sa bukatar su san game da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki. Ba su yi imani da Allah ba domin suna ganin mutane suna shan wahala sosai a duniya. Ba sa son Littafi Mai Tsarki domin suna ganin munafuncin limaman addinai da suke da’awar yin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Wasu kuma sun shagala da aikinsu ko iyalinsu ko suna fama da matsaloli kuma ba su san ko Littafi Mai Tsarki zai taimaka musu ba. Ta yaya za mu ci gaba da farin ciki ko da mutane suna ganin wa’azin da muke yi ba shi da amfani?

12. Ta yaya bin shawarar da ke Filibiyawa 2:4 za ta taimaka mana a hidimarmu?

12 Ka nuna ka damu da mutane. Mutane da yawa da a dā ba sa saurarar wa’azinmu sun soma saurara domin sun ga cewa mun damu su. (Karanta Filibiyawa 2:4.) Alal misali, David wanda aka ambata ɗazu ya ce: “Idan wani ya ce ba ya so ya ji wa’azi, muna tambayar sa: ‘Me ya sa ka ce hakan?’ ” Idan ka damu da mutane, za su iya gane hakan. Suna iya manta abin da muka faɗa, amma za su tuna yadda muka sa su ji. Ko da masu gidan ba su bari mu yi wa’azi ba, za mu iya nunawa ta halinmu da kuma fuskarmu cewa mun damu da su.

13. Mene ne za mu yi don mutane su saurari wa’azinmu?

13 Za mu nuna cewa mun damu da mutane sa’ad da muka canja batun da muke so mu tattauna da wani don ya jitu da yanayinsa. Alal misali, shin akwai abubuwan da suka nuna cewa mutumin yana da yara? Wataƙila zai so ya ji shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki game da renon yara ko kuma yadda iyalinsa za ta riƙa farin ciki. Shin akwai makulli da yawa a ƙofarsa? Muna iya zaɓa mu tattauna game da mugunta da ake yi a ko’ina da kuma yadda hakan yake sa mutane tsoro. Wataƙila mutumin zai ji daɗin sanin cewa za a kawo ƙarshen waɗannan abubuwan. A duk lokacin da ka sami mutanen da suke so su saurari wa’azinmu, ka taimaka musu su fahimci yadda shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki za su taimaka musu. Katarína wadda aka ambata ɗazu ta ce: “Na tuna yadda Littafi Mai Tsarki ya gyara rayuwata.” A sakamakon haka, Katarína ta gaskata da abin da take wa’azi a kai kuma mutanen sun ga hakan.

14. Kamar yadda Karin Magana 27:17 ta nuna, ta yaya abokan wa’azi za su iya taimaka wa juna?

14 Ka nemi taimakon wasu. A ƙarni na farko, Bulus ya koya wa Timoti yadda yake wa’azi da koyarwa kuma ya ƙarfafa shi ya yi amfani da abubuwan da ya koya yayin da yake wa’azi. (1 Kor. 4:17) Kamar Timoti, za mu iya samun taimako daga ’yan’uwan da suka ƙware a ikilisiya. (Karanta Karin Magana 27:17.) Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa majagaba mai suna Shawn. Ya yi hidima na ɗan lokaci a wani ƙauye da yawancin mutane ba sa son su canja addininsu. Ta yaya ya ci gaba da farin ciki? Ya ce: “A duk lokacin da na sami dama, ina fita wa’azi da wani. Muna taimaka wa juna don mu inganta yadda muke koyarwa sa’ad da muke ziyartar gidajen mutane. Alal misali, muna tattauna abin da mai gidan ya ce da kuma amsar da muka ba shi. Sai mu faɗi abin da za mu yi idan hakan ya sake faruwa.”

15. Me ya sa addu’a take da muhimmanci a hidimarmu?

15 Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka a duk lokacin da ka fita wa’azi. Ba za mu cim ma kome ba, idan ba tare da taimakon ruhu mai tsarki ba. (Zab. 127:1; Luk. 11:13) Ka faɗa wa Jehobah taimakon da kake bukata daga gare shi. Alal misali, ka roƙe shi ya taimaka maka ka haɗu da mutumin da yake so ya koya game da shi, kuma yana shirye ya saurari wa’azinka. Bayan haka, sai ka yi ƙoƙari ka yi wa kowa da ka haɗu da shi wa’azi.

16. Me ya sa yin nazari yake da muhimmanci a hidimarmu?

16 Ka keɓe lokacin yin nazari. Kalmar Allah ta ce ka “tabbatar da abin da yake nufin Allah, wato abin da yake mai kyau, abin karɓa ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.” (Rom. 12:2) Idan muka yi nazari, za mu san Allah sosai. Kuma idan muna yi wa mutane wa’azi game da shi, za su ga cewa mun gaskata da abin da muke faɗa. Katarína wadda aka ambata ɗazu ta ce: “A kwanan nan, na ga cewa ina bukata in ƙarfafa bangaskiyata game da wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki. Don haka, na yi nazarin abubuwan da za su tabbatar mini cewa akwai Mahalicci, da cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce, da kuma tabbaci cewa Allah yana da ƙungiya da yake amfani da ita a yau.” Katarína ta ce nazarin da ta yi ya ƙarfafa bangaskiyarta kuma ta daɗa farin ciki a hidimarta.

ABIN DA YA SA MUKE CI GABA DA FARIN CIKI A HIDIMARMU

17. Me ya taimaki Yesu ya kasance da ra’ayin da ya dace?

17 Yesu ya kasance da ra’ayin da ya dace kuma ya ci gaba da wa’azi duk da cewa wasu sun ƙi saurararsa. Me ya taimaka masa? Ya san cewa mutane suna bukatar su san gaskiya, kuma yana so ya taimaka wa mutane da yawa su san Allah. Ya kuma san cewa wasu da ba su saurare shi da farko ba, za su iya saurarar shi daga baya. Ka yi tunanin abin da ya faru a iyalinsa. A cikin shekaru uku da rabi da Yesu ya yi yana hidima a duniya, babu ɗan’uwansa da ya bi shi. (Yoh. 7:5) Amma bayan da ya tashi daga mutuwa, sai suka zama Kiristoci.​—A. M. 1:14.

18. Me ya sa muke ci gaba da yin wa’azi?

18 Ba mu san wanda zai soma bauta wa Jehobah ba. Wasu suna ɗaukan lokaci sosai kafin su soma son saƙonmu. Ko waɗanda ba sa so su saurari saƙonmu ma sukan lura cewa muna da hali da kuma ra’ayi mai kyau, kuma hakan yana iya sa su soma “ɗaukaka Allah.”​—1 Bit. 2:12.

19. Mene ne muka koya a 1 Korintiyawa 3:​6, 7 game da yin wa’azi?

19 Yayin da muke yin shuki da ban-ruwa, dole ne mu tuna cewa Allah ne yake sa irin ya yi girma. (Karanta 1 Korintiyawa 3:​6, 7.) Wani ɗan’uwa mai suna Getahun da ke hidima a Habasha ya ce: “Fiye da shekaru 20, ni kaɗai ne Mashaidi a yankinmu. Amma yanzu akwai masu shela 14 a yankin. Guda 13 a cikinsu sun yi baftisma, har da matata da yarana uku. A yawancin lokaci, mutane 32 ne suke halartan taronmu.” Getahun yana farin ciki cewa ya ci gaba da wa’azi yayin da ya yi ta jira don Jehobah ya taimaka wa mutane su san gaskiya!​—Yoh. 6:44.

20. A wace hanya ce muke kama da masu aikin ceto?

20 Jehobah yana daraja dukan mutane. Ya ba mu gatan yin aiki tare da Ɗansa don mu tattara mutane daga dukan al’ummai kafin ƙarshen wannan zamanin. (Hag. 2:7) Za mu iya kwatanta wa’azin da muke yi da aikin ceto. Muna kamar mutane da aka tura su je su ceci mutane daga ramin haƙa ma’addinai. Ko da yake ma’aikata kaɗan ne za su ceto wani daga ramin, dukan ma’aikatan sun taimaka wajen yin wannan aiki mai muhimmanci. Haka yake da aikin da muke yi a hidimarmu. Ba mu sani ko saura mutane nawa ne za a ceto daga duniyar Shaiɗan ba. Amma Jehobah zai iya yin amfani da kowannenmu don ya taimaka musu. Wani ɗan’uwa mai suna Andreas da ke zama a ƙasar Bolibiya ya ce: “Na san cewa idan mutum ya koyi gaskiya kuma ya yi baftisma, mutane da yawa ne suka yi aiki tare don su taimaka masa.” Bari mu kasance da irin wannan ra’ayi mai kyau a hidimarmu. Idan muka yi hakan, Jehobah zai albarkace mu, kuma za mu riƙa farin ciki yayin da muke yin wa’azi.

WAƘA TA 66 Mu Riƙa Yaɗa Bishara

^ sakin layi na 5 Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da yin wa’azi da farin ciki ko da ba ma haɗuwa da mutane a gida ko kuma ba sa so su saurare mu? A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi dabam-dabam da za mu iya ci gaba da yin wa’azi da farin ciki.

^ sakin layi na 7 Masu shela su bi hanyoyin yin wa’azi da aka tattauna a wannan talifin a hanyar da za ta tabbatar cewa sun bi duk wata dokar ƙasa a kan yadda za a kāre bayanan mutane.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTUNA: (daga sama zuwa ƙasa): Wani ɗan’uwa da matarsa suna wa’azi a wani yanki da ba a samun mutane a gida. Na farko yana wurin aikinsa, na biyu tana asibiti, na uku kuma ta fita yin cefane. Sun sami mutum na farko ta wajen ziyartar shi da yamma. Sun haɗu da na biyu sa’ad da suke wa’azi kusa da asibitin. Sun sami na uku ta wajen kiranta a waya.