Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 22

Ka Taimaka wa Dalibinka Ya Cancanci Yin Baftisma

Ka Taimaka wa Dalibinka Ya Cancanci Yin Baftisma

“A yi wa kowannenku baftisma.”​—A. M. 2:38.

WAƘA TA 72 Mu Yaɗa Gaskiya Game da Mulkin Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne manzannin Yesu suka gaya wa taron jama’a su yi?

JAMA’A da yawa sun taru a Urushalima. Sun fito ne daga ƙasashe dabam-dabam kuma suna yin yaruka dabam-dabam. Sai wani abin mamaki ya faru a ranar. Kwatsam, sai wasu Yahudawa suka soma yin magana a yarukan mutanen nan! Hakan ya ba mutanen mamaki sosai, amma abin da Yahudawan da kuma manzo Bitrus suka faɗa ne ya fi ba su mamaki. Mutanen sun ji cewa za su sami ceto idan suka ba da gaskiya ga Yesu Kristi. Saƙon ya ratsa zuciyarsu sosai har suka yi tambaya suka ce: “Mene ne za mu yi?” Sai Bitrus ya ce musu: “A yi wa kowannenku baftisma.”​—A. M. 2:​37, 38.

Wani ɗan’uwa tare da matarsa suna nazarin Littafi Mai Tsarki da wani matashi kuma yana riƙe da littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! (Ka duba sakin layi na 2)

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

2 Wani abin ban mamaki ya faru bayan haka. Wajen mutane 3,000 sun yi baftisma a ranar kuma suka zama mabiyan Kristi. Yadda aka fara yin wa’azin da Yesu ya umurci mabiyansa su yi ke nan. Mabiyansa suna yin wannan aikin har a yau. A zamaninmu, ba za mu iya tattaunawa da mutane na ’yan sa’o’i sa’an nan su yi baftisma nan da nan ba. Yana iya ɗaukan watanni ko shekara ko kuma fiye da hakan kafin ɗalibi ya cancanci yin baftisma. Taimaka wa mutane su zama mabiyan Yesu ba ƙaramin aiki ba ne. Idan kana nazari da wani yanzu, za ka fahimci hakan. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za ka taimaka wa ɗalibinka ya cancanci yin baftisma.

KA TAIMAKA WA ƊALIBINKA YA RIƘA BIN ABIN DA YAKE KOYA

3. Kamar yadda Matiyu 28:​19, 20 suka nuna, mene ne ɗalibi yake bukatar ya yi don ya cancanci yin baftisma?

3 Kafin ɗalibi ya cancanci yin baftisma, yana bukatar ya riƙa bin abin da yake koya. (Karanta Matiyu 28:​19, 20.) Idan ɗalibi yana yin abin da yake koya, zai zama kamar mutum “mai hikima” a kwatancin Yesu, wanda ya gina gidansa a kan dutse. (Mat. 7:​24, 25; Luk. 6:​47, 48) Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibi ya riƙa yin abin da yake koya? Bari mu tattauna abubuwa uku da za mu iya yi.

4. Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibi ya ci gaba da ƙoƙari don ya cancanci yin baftisma? (Ka duba akwatin nan “ Ka Taimaka wa Ɗalibinka Ya Kafa Maƙasudai Kuma Ya Cim ma Maƙasudan.”)

4 Ka taimaka wa ɗalibinka ya kafa maƙasudai. Me ya sa kake bukatar ka yi hakan? Ga wani misali: A ce za ka yi wata doguwar tafiya da motarka, za ka iya yanke shawarar tsayawa a wasu wurare masu ban sha’awa. Yin hakan zai sa ba za ka gaji da tafiyar ba. Hakazalika, idan ɗalibi ya kafa maƙasudai da zai iya cim ma a cikin ƙanƙanin lokaci kuma ya yi hakan, zai ga cewa zai iya cim ma maƙasudinsa na yin baftisma. Ka yi amfani da sashen “Maƙasudi” da ke littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! don ka taimaka wa ɗalibinka ya sami ci gaba. Bayan kun tattauna kowane darasi, ka taimaka wa ɗalibinka ya ga yadda maƙasudin da ya kafa zai taimaka masa ya yi abin da ya koya. Idan kana da wani maƙasudi dabam da kake so ɗalibinka ya cim ma, ka faɗa masa ya rubuta a sashen nan “Sauran maƙasudai.” Ka riƙa yin amfani da wannan sashen don ka nuna wa ɗalibinka maƙasudai da zai iya cim ma a cikin ƙanƙanin lokaci, da kuma waɗanda za su ɗauki lokaci.

5. Kamar yadda aka rubuta a Markus 10:​17-22, mene ne Yesu ya gaya wa wani mai arziki ya yi, kuma me ya sa?

5 Ka taimaka wa ɗalibinka ya yi gyara a rayuwarsa. (Karanta Markus 10:​17-22.) Yesu ya san cewa zai yi wa mai arziki wuya ya sayar da dukan abin da ya mallaka. (Mar. 10:23) Duk da haka, Yesu ya gaya wa mai arzikin nan ya ɗauki wannan mataki mai wuya. Me ya sa? Domin Yesu yana ƙaunar shi. A wasu lokuta, za mu iya yin jinkirin ƙarfafa ɗalibinmu ya yi abin da yake koya, domin muna ganin ba zai yi masa sauƙi ya yi gyara masu wuya a rayuwarsa da farko ba. Yana iya ɗaukan lokaci kafin mutane su canja rayuwarsu kuma su koyi sabon hali. (Kol. 3:​9, 10) Amma idan ka gaya masa gyarar da yake bukatar ya yi tun da wuri, hakan zai taimaka masa ya soma yin gyarar. Wannan shawarar za ta taimaka masa ya ga cewa ka damu da shi.​—Zab. 141:5; K. Mag. 27:17.

6. Me ya sa yake da kyau mu san ra’ayin ɗalibinmu?

6 Yana da muhimmanci ka tambayi ɗalibinka ra’ayinsa a kan batutuwan da kake tattaunawa da shi. Yin hakan zai taimaka maka ka san abin da ɗalibinka ya fahimta da kuma abubuwan da ya yi imani da su. Idan kana yin hakan a kai a kai, zai yi maka sauƙi idan a nan gaba kana so ka tattauna batutuwa da mai yiwuwa za su yi masa wuya ya amince. A littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! akwai irin tambayoyin nan da yawa. Alal misali, a darasi na 4 akwai tambayar nan: “Yaya kake ganin Jehobah yake ji sa’ad da ka yi amfani da sunansa?” A darasi na 9 kuma tambayar ta ce: “Waɗanne abubuwa ne za ka so ka yi addu’a a kai?” Da farko, yana iya yi wa ɗalibinka wuya ya amsa waɗannan tambayoyin. Za ka iya taimaka masa ta wajen koya masa yadda zai yi tunani a kan nassosi da kuma hotuna da ke littafin.

7. Ta yaya za mu yi amfani da labaran ’yan’uwa mu taimaka wa ɗalibanmu?

7 Bayan da ɗalibinka ya fahimci abin da yake bukatar ya yi, ka ba shi labarin wasu da zai taimaka masa ya yi hakan. Alal misali, idan yana yi wa ɗalibinka wuya ya halarci taro, ka nuna masa bidiyon nan, Jehobah Ya Kula Da Ni. Za ka iya samun shi a sashen “Ka Bincika,” a darasi na 14. A darussan da ke littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, za ka iya samun irin labaran nan a sashen “Ka Yi Bincike Sosai” ko kuma “Ka Bincika.” * Ka guji kwatanta ɗalibinka da wani ta wajen ce masa, “Idan har wane ya yi, kai ma za ka iya yi.” Ka bar ɗalibinka ya faɗi hakan da kansa. Maimakon ka kwatanta shi da wani, ka tattauna abubuwan da suka taimaka wa mutumin da ke bidiyon. Mai yiwuwa za ka iya ambata wani nassi ko kuma wani matakin da mutumin ya ɗauka. Idan zai yiwu, ka nanata yadda Jehobah ya taimaka masa.

8. Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibinmu ya soma ƙaunar Jehobah?

8 Ka taimaka wa ɗalibinka ya soma ƙaunar Jehobah. Ta yaya za ka yi hakan? Ka nemi zarafin tattauna halaye masu kyau na Jehobah tare da ɗalibinka. Ka taimaka wa ɗalibinka ya ga cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna kuma yana taimaka wa waɗanda suke ƙaunar shi. (1 Tim. 1:11; Ibran. 11:6) Ka taimaka wa ɗalibinka ya san cewa zai sami albarka idan ya bi abin da yake koya, kuma hakan zai nuna masa cewa Jehobah yana ƙaunar sa. (Isha. 48:​17, 18) Idan ɗalibinka ya soma ƙaunar Jehobah, zai soma yin gyara a rayuwarsa.​—1 Yoh. 5:3.

KA TAIMAKA WA ƊALIBINKA YA SAN ’YAN’UWA A IKILISIYA

9. Bisa ga Markus 10:​29, 30, me zai taimaka wa mutum ya yi sadaukarwa don ya cancanci yin baftisma?

9 Kafin ɗalibinka ya cancanci yin baftisma, yana bukatar ya yi wasu sadaukarwa. Kamar mai arzikin da aka ambata ɗazu, wasu ɗalibai za su bukaci su sadaukar da dukiyarsu. Idan aikin da suke yi ya saɓa wa ƙa’idar Littafi Mai Tsarki, za su bukaci su canja aikin. Ɗalibai da yawa za su bukaci su daina abokantaka da mutanen da ba sa ƙaunar Jehobah. Wasu da iyalinsu ba sa son Shaidun Jehobah, za su iya yin watsi da su. Yesu ya san cewa yin irin waɗannan sadaukarwa zai iya yi ma wasu wuya. Amma ya yi alkawari cewa waɗanda suka bi shi ba za su yi da-na-sani ba domin mutanen Jehobah za su zama iyalinsu. (Karanta Markus 10:​29, 30.) Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibinka ya sami iyali a ƙungiyar Jehobah?

10. Mene ne ka koya daga labarin Manuel?

10 Ka zama abokin ɗalibinka. Yana da muhimmanci ka nuna wa ɗalibinka cewa ka damu da shi. Me ya sa? Wani ɗan’uwa mai suna Manuel da ke zama a Meziko ya bayyana yadda malaminsa ya taimaka masa a lokacin da yake nazari. Ya ce: “Kafin mu soma kowane nazari, yakan tambaye ni, ‘Ya kake?’ Ya taimaka mini in saki jiki kuma in gaya masa abubuwan da ke damu na. Hakan ya nuna mini cewa ya damu da ni sosai.”

11. Ta yaya ɗalibanmu za su amfana idan muna shaƙatawa da su?

11 Kamar yadda Yesu yakan shaƙata da mabiyansa a wasu lokuta, kai ma ka yi hakan da ɗalibinka. (Yoh. 3:22) Idan ɗalibinka yana samun ci gaba, za ka iya gayyatar shi gidanka don ku ci abinci tare ko kuma ku kalli shirin JW. Ɗalibinka zai ji daɗin hakan musamman a lokacin da ake bukukuwan da suka saɓa wa Littafi Mai Tsarki. Hakan zai taimaka masa kada ya kaɗaita. Wani ɗan’uwa mai suna Kazibwe da ke zama a Yuganda ya ce: “Nakan koyi abubuwa da yawa game da Jehobah sa’ad da nake shaƙatawa da malamina kamar yadda nakan yi sa’ad da muke nazari. Na ga yadda Jehobah yake kula da mutanensa, da yadda suke farin ciki. Kuma abin da nake so a rayuwata ke nan.”

Idan ’yan’uwa dabam-dabam suna bin ka yin nazari da ɗalibinka, zai yi wa ɗalibin sauƙi ya soma halartan taro (Ka duba sakin layi na 12) *

12. Me ya sa ya kamata mu gayyaci ’yan’uwa dabam-dabam su bi mu yin nazari da ɗalibinmu?

12 Ka gayyaci ’yan’uwa dabam-dabam su bi ka yin nazari da ɗalibinka. A wasu lokuta, za mu iya gani kamar zuwa mu kaɗai ko kuma da mutum ɗaya a kowane lokaci ya fi sauƙi. Ko da yake yin hakan yana da sauƙi, ɗalibinmu zai fi amfana idan muna zuwa yin nazari da shi da tare da ’yan’uwa dabam-dabam. Wani ɗan’uwa mai suna Dmitrii da ke zama a Moldova ya ce: “ ’Yan’uwa dabam-dabam da suke zuwa tare da mai yin nazari da ni sukan bayyana abubuwa a hanyoyi dabam-dabam. Hakan ya taimaka mini in ga hanyoyin da zan iya bi in yi abin da nake koya. Ban ji kunya sosai ba a rana ta farko da na halarci taro, domin na riga na wayi ’yan’uwa da yawa.”

13. Me ya sa ya kamata mu taimaka wa ɗalibinmu ya halarci taro?

13 Ka taimaka wa ɗalibinka ya soma halartan taro. Me ya sa? Domin Jehobah ya umurci bayinsa su riƙa bauta masa tare. (Ibran. 10:​24, 25) Ban da haka, ’yan’uwa a ikilisiya suna kamar iyalinmu ne. A duk lokacin da muka halarci taro, kamar dai muna cin abinci mai daɗi tare da su ne. Ƙarfafa ɗalibinka ya soma halartan taro zai taimaka masa sosai ya cancanci yin baftisma. Amma zai iya yi masa wuya ya soma halartan taro. Ta yaya littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! zai taimaka wa ɗalibinka ya magance matsalolin da ke hana shi halartan taro?

14. Ta yaya za mu iya ƙarfafa ɗalibinmu ya halarci taro?

14 Ka yi amfani da darasi na 10 na littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! don ka ƙarfafa ɗalibinka. Ƙwararrun masu shela da suka gwada yin amfani da wannan littafin kafin a fitar da shi, sun yi nasarar taimaka wa ɗalibansu su soma halartan taro. Amma ba sai ka jira har kun kai darasi na 10 kafin ka gayyaci ɗalibinka zuwa taro ba. Ka gayyace shi tun da wuri, kuma ka ci gaba da yin hakan. Ƙalubalen da ɗalibai suke fuskanta ya bambanta. Don haka, ka yi tunanin ƙalubalen da ɗalibinka yake fuskanta don ka san yadda za ka taimaka masa. Amma kada ka yi sanyin gwiwa idan ya ɗau dogon lokaci kafin ya soma halartan taro. Ka dai ci gaba da gayyatar shi.

KA TAIMAKA WA ƊALIBINKA YA DAINA JIN TSORO

15. Mene ne zai iya ba ɗalibinka tsoro?

15 Yaya ka ji sa’ad da ka soma bauta wa Jehobah? Wataƙila ka ɗauka cewa ba za ka iya yin wa’azi gida-gida ba. Ko kuma ka ji tsoro cewa iyalinka da abokanka za su ƙi amincewa da matakin da ka ɗauka. Idan haka ne, za ka fahimci yanayin ɗalibinka. Yesu ya ce wasu za su iya jin tsoro. Amma ya ƙarfafa mabiyansa kada su bar tsoro ya hana su bauta wa Jehobah. (Mat. 10:​16, 17, 27, 28) Ta yaya Yesu ya taimaka wa mabiyansa su daina jin tsoro? Kuma ta yaya za mu bi misalinsa?

16. Ta yaya za mu koya wa ɗalibinmu yadda zai yi wa’azi?

16 Ka koya wa ɗalibinka yadda zai yi wa’azi. Wataƙila manzannin Yesu sun ji tsoro sa’ad da ya tura su yin wa’azi. Amma Yesu ya taimaka musu ta wajen gaya musu wurin da za su yi wa’azi da kuma abin da za su yi wa’azi a kai. (Mat. 10:​5-7) Ta yaya za mu yi koyi da Yesu? Ka taimaka wa ɗalibinka ya san waɗanda zai iya yi musu wa’azi. Alal misali, ka tambaye shi ko ya san wani da zai so ya koya game da Littafi Mai Tsarki. Sai ka taimaka masa ya shirya abin da zai faɗa a hanya mai sauƙi. Idan zai dace, kana iya taimaka wa ɗalibinka ta wajen yin amfani da sashen nan “Wasu Sun Ce,” da kuma “Wani Yana Iya Cewa,” a littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Yayin da kake hakan, ka ƙoƙarta ka koya wa ɗalibinka yadda zai yi amfani da Littafi Mai Tsarki ya amsa tambayoyin da aka yi masa a hanya mai sauƙi.

17. Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibinmu ya dogara ga Jehobah ta wajen yin amfani da Matiyu 10:​19, 20, 29-31?

17 Ka taimaka wa ɗalibinka ya dogara ga Jehobah. Yesu ya tabbatar wa mabiyansa cewa Jehobah zai taimaka musu domin Yana ƙaunar su. (Karanta Matiyu 10:​19, 20, 29-31.) Ka tuna wa ɗalibinka cewa shi ma Jehobah zai taimaka masa. Za ka iya taimaka masa ya dogara ga Jehobah ta wajen yin addu’a tare da shi game da maƙasudansa. Wani ɗan’uwa mai suna Franciszek da ke Polan ya ce: “Malamina yakan ambaci sunana sa’ad da yake yin addu’a. Da na ga yadda Jehobah ya amsa addu’ar malamina, sai ni ma na soma yin addu’a. Na ga yadda Jehobah ya taimaka mini a lokacin da na je neman izini daga oganmu a wurin sabon aikina, don in halarci taron ikilisiya da kuma taron yanki.”

18. Yaya Jehobah yake ji game da wa’azin da muke yi?

18 Jehobah ya damu da ɗalibanmu sosai. Ya san irin jan aikin da Kiristoci masu shela suke yi don su taimaka wa mutane su kusace shi, kuma yana ƙaunar su don ƙoƙarin da suke yi. (Isha. 52:7) Idan ba ka da ɗalibi a yanzu, kana iya taimaka wa ɗalibai su cancanci yin baftisma ta wajen raka wasu masu shela yin nazari da ɗalibansu.

WAƘA TA 60 Domin Su Sami Ceto

^ sakin layi na 5 A wannan talifin, za mu tattauna yadda Yesu ya taimaka wa mutane su zama mabiyansa da kuma yadda za mu yi koyi da shi. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda za mu yi amfani da sabon littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! An tsara wannan littafin yadda zai taimaka wa ɗalibanmu su sami ci gaba har su cancanci yin baftisma.

^ sakin layi na 7 Za ka kuma iya samun labaran ’yan’uwa a (1) Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah. A ciki, ka duba “Littafi Mai Tsarki,” sai ka je “Amfanin Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki,” sa’an nan ka duba “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane,” (Jerin talifofin Hasumiyar Tsaro) ko kuma a (2) manhajar JW Library® ka je “Ganawa da Labarai.”

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa tare da matarsa suna yin nazari da wani matashi. A wasu lokuta, ’yan’uwa dabam-dabam sukan bi shi yin nazarin.