Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 28

Kada Ku Yi Gasa da Juna, Ku Bidi Zaman Lafiya

Kada Ku Yi Gasa da Juna, Ku Bidi Zaman Lafiya

“Kada mu zama masu girman kai ko masu [“gasa da,” NW] juna ko masu kishin juna.”​GAL. 5:26.

WAƘA TA 101 Mu Riƙa Hidima da Haɗin Kai

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me zai iya faruwa idan wasu suna ƙoƙari su nuna cewa sun fi wasu?

A YAU, mutane da yawa suna yin ƙoƙari su nuna cewa sun fi wasu, kuma ba sa damuwa da yadda hakan yake shafan wasu. Alal misali, ɗan kasuwa zai iya yin maguɗi don ya fi sauran ’yan kasuwa ci gaba. Ɗan ƙwallo na iya ji wa abokin gasarsa rauni da gangan don ƙungiyarsu ta yi nasara a wasan. Ɗan makaranta na iya satar amsoshi a lokacin jarrabawa don ya samu ya shiga wani sanannen jami’a. A matsayinmu na Kiristoci, mun san cewa waɗannan halayen ba su da kyau domin suna cikin “ayyukan da halin mutuntaka yake haifar.” (Gal. 5:19-21) Shin, zai yiwu wasu a cikin ikilisiya su soma nuna halin gasa kuma su sa wasu su yi koyi da halin ba tare da saninsu ba? Wannan muhimmiyar tambaya ce domin halin gasa zai iya kawo rashin haɗin kai a cikin ikilisiya.

2. Me za mu tattauna a wannan talifin?

2 A wannan talifin, za mu tattauna halaye marasa kyau da za su iya jawo gasa a cikin ikilisiya. Za mu kuma tattauna misalin bayin Allah na dā waɗanda ba su yi ƙoƙari su nuna cewa sun fi wasu ba. Da farko, bari mu tattauna yadda za mu bincika dalilin da ya sa muke yin wasu abubuwa.

KA BINCIKA DALILIN DA YA SA KAKE YIN WASU ABUBUWA

3. Waɗanne irin tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

3 Yana da kyau mu riƙa bincika dalilin da ya sa muke yin wasu abubuwa. Za mu iya yi wa kanmu tambayoyi kamar haka: ‘Tunanin cewa na fi wani ne ya fi sa ni farin ciki? Ina aiki tuƙuru a ikilisiya don a ce ni nake kan gaba ko kuma don in fi wasu? Ko kuma ina aiki da dukan ƙarfina ne don in faranta ran Jehobah?’ Me ya sa ya kamata mu yi waɗannan tambayoyin? Ka yi la’akari da abin da Kalmar Allah ta faɗa.

4. Kamar yadda aka rubuta a Galatiyawa 6:3, 4, me ya sa bai kamata mu gwada kanmu da wasu ba?

4 Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu gwada kanmu da wasu. (Karanta Galatiyawa 6:3, 4.) Me ya sa? Idan mun ɗauka cewa mun fi wasu, za mu soma girman kai. Idan kuma mun ɗauka cewa ba mu iya kome ba, za mu iya yin sanyin gwiwa. Irin ra’ayoyin nan ba su dace ba. (Rom. 12:3) Wata ’yar’uwa mai suna Katerina, * da ke zama a ƙasar Girka ta ce: “Nakan gwada kaina da wasu ’yan’uwa da nake ganin sun fi ni kyau, sun fi ni iya wa’azi kuma suna da abokai fiye da ni. Hakan ya sa na ɗauka kamar ba ni da daraja.” Ya kamata mu tuna cewa Jehobah ya jawo mu wurinsa domin muna ƙaunar sa kuma muna saurarar Ɗansa ne, ba domin muna da kyau ko don mun iya magana ko kuma don mutane da yawa suna son mu ba.​—Yoh. 6:44; 1 Kor. 1:26-31.

5. Mene ne ka koya daga labarin wani ɗan’uwa mai suna Hyun?

5 Wata tambaya kuma da ya kamata mu yi wa kanmu ita ce, ‘An san ni a matsayin mai son zaman lafiya ko kuma mai yawan faɗa da mutane?’ Ga abin da ya faru da wani dattijo mai suna Hyun, da ke ƙasar Koriya ta Kudu. Akwai lokacin da ya soma tunanin cewa ’yan’uwa da ke da ayyuka a cikin ikilisiya suna ƙoƙarin su nuna cewa sun fi shi. Ya ce, “Nakan yi gunaguni a kan ’yan’uwan kuma in ƙi amincewa da abin da suka faɗa.” Mene ne sakamakon hakan? Ya ce, “Halina ya raba kan ikilisiyar.” Wasu abokansa sun taimaka masa ya ga cewa yana da matsala. Ɗan’uwa Hyun ya canja halinsa kuma yanzu yana hidimarsa da kyau. Idan mun lura cewa mun soma zama masu gasa maimakon masu neman zaman lafiya, dole ne mu canja halinmu nan da nan.

KADA KA ZAMA MAI GIRMAN KAI DA KISHI

6. Bisa ga Galatiyawa 5:26, waɗanne halaye marasa kyau ne suke sa mutane su yi gasa da juna?

6 Karanta Galatiyawa 5:26. Waɗanne halaye marasa kyau ne za su iya sa mutane su soma gasa da juna? Ɗaya daga cikinsu shi ne girman kai. Mutum mai girman kai bai damu da kowa ba, sai kansa. Wani halin kuma shi ne kishi. Mutum mai kishi yakan so abin wani kuma yakan so ya raba mutumin da abin da yake da shi. Gaskiyar ita ce, duk mutumin da yake kishin wani, ya tsane mutumin ke nan. Don haka, ya kamata mu guji waɗannan halaye marasa kyau.

7. Wane misali ne ya nuna cewa girman kai da kishi ba su da kyau?

7 Idan gara ya ci katakan da aka yi rufin gida da su, kome kyaun rufin, da shigewar lokaci zai rushe. Haka ma, mutum zai iya daɗe yana bauta ma Jehobah, amma in yana da girman kai da kishi, a ƙarshe, hakan zai kai shi ga hallaka. (K. Mag. 16:18) A hankali zai daina bauta ma Jehobah kuma zai jawo wa kansa da kuma wasu masifa. To me za mu yi don mu guji girman kai da kuma kishi?

8. Ta yaya za mu guji girman kai?

8 Za mu iya guji girman kai idan muka bi shawarar da manzo Bulus ya ba wa ’yan’uwan da ke Filibi, cewa: “Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai da sauƙin kai. Amma cikin sauƙin kai kuma bari kowa ya ɗauka ɗan’uwansa da muhimmanci fiye da kansa.” (Filib. 2:3) Idan muna ɗaukan ’yan’uwanmu da muhimmanci fiye da kanmu, ba za mu riƙa gwada kanmu da waɗanda suke da wata baiwa fiye da mu ba. A maimakon haka, za mu taya su murna, musamman idan suna amfani da baiwar wajen ɗaukaka sunan Jehobah. Kuma idan ’yan’uwanmu da suke da baiwa suka bi shawarar Bulus, su ma za su mai da hankali ga halayenmu masu kyau. Hakan zai kawo salama da haɗin kai a cikin ikilisiya.

9. Ta yaya za mu guji yin kishi?

9 Za mu iya mu guji yin kishin ’yan’uwanmu idan mun tuna cewa akwai wasu abubuwa da ba za mu iya yin su da kyau ba. Idan muna da sauƙin kai, ba za mu yi ƙoƙari mu nuna cewa mun fi ’yan’uwanmu ba. A maimakon haka, za mu yi ƙoƙari mu koyi abubuwa daga waɗanda suka fi mu. Alal misali, idan muka ga wani ɗan’uwa da ya iya ba da jawabi sosai, za mu iya tambayarsa ya gaya mana yadda yake shirya jawabansa. Idan mun ga wata ’yar’uwa da ta iya dahuwa sosai, za mu iya gaya mata ta koya mana yadda mu ma za mu iya dahuwa da kyau. Kuma idan yana yi ma wani matashi wuya ya sami abokai, zai iya tambayar wani da yake da abokai da yawa ya taimaka masa don ya iya samun abokai. Idan muka yi hakan, za mu guji yin kishi kuma za mu daɗa ƙwarewa.

KA BI MISALAI MASU KYAU DAGA LITTAFI MAI TSARKI

Sauƙin kai ya sa Gideyon ya yi zaman lafiya da mutanen Ifrayim (Ka duba sakin layi na 10-12)

10. Wace matsala ce Gideyon ya fuskanta?

10 Ka yi tunani a kan abin da ya faru tsakanin Gideyon, wanda ya fito daga zuriyar Manasse, da mutanen zuriyar Ifrayim. Jehobah ya taimaka wa Gideyon da sojojinsa 300 su ci nasara a yaƙi. Hakan zai iya sa su yin fahariya. Mutanen Ifrayim sun je sun sami Gideyon domin su yi faɗa da shi, maimakon su yabe shi. Sun yi fushi ne domin Gideyon bai gayyace su su je su yi faɗa tare a lokacin da suka fara faɗan ba. Damuwarsu ita ce a ɗaukaka zuriyarsu. Sun manta cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda Gideyon ya ɗaukaka sunan Jehobah da kuma kāre mutanen Jehobah.​—Alƙa. 8:1.

11. Mene ne Gideyon ya gaya wa mutanen Ifrayim?

11 A cikin sauƙin kai, Gideyon ya gaya wa mutanen Ifrayim cewa: “Me na yi fiye da ku?” Sai ya tuna wa mutanen Ifrayim yadda Jehobah ya taimaka musu su yi abubuwa masu muhimmanci. Da suka ji hakan, sai suka “daina fushi.” (Alƙa. 8:2, 3) Gideyon ya yi iya ƙoƙarinsa ya nuna sauƙin kai don a sami zaman lafiya tsakanin mutanen Allah.

12. Me muka koya daga labarin mutanen Ifrayim da kuma Gideyon?

12 Me muka koya daga labarin nan? Misalin mutanen Ifrayim ya koya mana cewa abin da ya kamata mu sa a kan gaba shi ne ɗaukaka Jehobah, ba kanmu ba. Iyaye maza da dattawa za su iya koyan darasi mai kyau daga misalin Gideyon. Idan mutum yana fushi don wani abu da muka yi masa, zai dace mu yi ƙoƙari mu fahimci dalilin da ya sa abin ya ɓata masa rai. Idan kuma akwai abin da mutumin ya yi da kyau, ya kamata mu yaba masa. Hakan zai bukaci mu kasance da sauƙin kai musamman idan mutumin ne yake da laifi. Amma zaman lafiya da ’yan’uwanmu ya fi nuna cewa ba mu da laifi.

Hannatu ta sami kwanciyar hankali domin ta bar kome a hannun Jehobah (Ka duba sakin layi na 13-14)

13. Wace matsala ce Hannatu ta fuskanta kuma me ta yi game da matsalar?

13 Misali na biyu shi ne na Hannatu. Ta auri wani Balawi mai suna Elkana, wanda yake ƙaunarta sosai. Amma Elkana yana da wata mata mai suna Feninna. Elkana ya ƙaunaci Hannatu fiye da Feninna. “Feninna tana da ’ya’ya, amma Hannatu ba ta da ’ya’ya.” Don haka, Feninna takan yi wa Hannatu dariya “kullum domin ta ba ta haushi.” Yaya Hannatu ta ji? Ta ji haushi sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce “ta yi ta kuka ta ƙi cin abinci.” (1 Sam. 1:2, 6, 7) Amma Littafi Mai Tsarki bai ce Hannatu ta yi ƙoƙari ta rama abin da Feninna ta yi mata ba. A maimakon haka, ta gaya wa Jehobah yadda take ji kuma ta bar kome a hannunsa. Shin, Feninna ta canja halinta ne? Littafi Mai Tsarki bai gaya mana ko ta canja ba. Amma mun san cewa Hannatu ta sake samun kwanciyar hankali bayan ta gaya wa Jehobah abin da ke damunta. Littafi Mai Tsarki ya ce “ba ta sāke yin baƙin ciki kuma ba.”​—1 Sam. 1:10, 18.

14. Me muka koya daga misalin Hannatu?

14 Mene ne za mu iya koya da misalin Hannatu? Idan wani yana so ya nuna maka cewa ya fi ka, ba sai ka nuna masa cewa ka fi shi ba. Maimakon mu nemi hanyar rama abin da aka yi mana, mu yi ƙoƙari mu zauna lafiya da mutumin. (Rom. 12:17-21) Ko da mutumin bai canja halinsa ba, hankalinmu zai kwanta.

Afollos da Bulus ba su yi kishin juna ba domin sun san cewa Jehobah ne yake sa musu albarka a aikinsu (Ka duba sakin layi na 15-18)

15. Wace alaƙa ce ke tsakanin Afollos da Bulus?

15 Misali na ƙarshe da za mu tattauna shi ne na Afollos da kuma manzo Bulus. Su biyun sun san Nassosi sosai, an san da su sosai kuma sun iya koyarwa. Ƙari ga haka, sun taimaka wa mutane da yawa su zama almajiran Yesu. Amma ba su yi kishin juna ba.

16. Wane irin mutum ne Afollos?

16 Afollos “ɗan garin Alekzandiriya ne,” kuma a lokacin, garin ne cibiyar koyarwa. Da alama Afollos mutum ne da ya iya koyarwa kuma ya “san rubutacciyar Maganar Allah sosai-sosai.” (A. M. 18:24) A lokacin da Afollos yake hidima a Korinti, wasu ’yan’uwa sun nuna cewa sun so shi fiye da wasu ’yan’uwa, har da Bulus. (1 Kor. 1:12, 13) Shin, Afollos ya goyi bayan irin wannan halin ne? Babu abin da ya nuna cewa ya yi hakan, domin bayan wani lokaci da Afollos ya bar Korinti, Bulus ya ƙarfafa shi ya sake koma wurin. (1 Kor. 16:12) Bulus ba zai yi hakan ba da a ce ya ɗauka cewa Afollos yana raba kan ’yan’uwa a cikin ikilisiyar. A bayyane yake cewa Afollos ya yi amfani da baiwar da aka ba shi don yaɗa bishara da kuma ƙarfafa ’yan’uwansa. Mun tabbata cewa Afollos mutum ne mai sauƙin kai. Alal misali, babu abin da ya nuna cewa ya yi fushi sa’ad da Akila da Biriskila suka “ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai-sosai.”​—A. M. 18:24-28.

17. A wace hanya ce Bulus ya sa aka sami zaman lafiya?

17 Manzo Bulus ya san da ayyuka masu kyau da Afollos ya yi. Amma Bulus bai damu ko mutane za su ɗauka cewa Afollos ya fi shi ba. Abin da Bulus ya rubuta ga ’yan’uwa da ke ikilisiyar Korinti ya nuna cewa shi mai sauƙin kai ne, kuma ba ya nacewa a kan ra’ayinsa. Bulus bai so yadda ’yan’uwan suke cewa “Ni na Bulus ne” ba. A maimakon haka, ya ɗaukaka Jehobah da kuma Yesu Kristi.​—1 Kor. 3:3-6.

18. Bisa ga 1 Korintiyawa 4:6, 7, mene ne muka koya daga misalin Afollos da Bulus?

18 Mene ne za mu iya koya daga misalin Afollos da kuma Bulus? Za mu iya yin ayyuka da yawa a ƙungiyar Jehobah, har mu taimaka wa mutane da yawa su yi baftisma. Amma mun san cewa hakan ya yiwu ne domin Jehobah yana taimaka mana. Wani darasi kuma da za mu iya koya shi ne, idan muna yin ayyuka sosai a cikin ikilisiya, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don a sami zaman lafiya. Muna farin ciki sosai sa’ad da dattawa da bayi masu hidima suka taimaka mana mu yi zaman lafiya a ikilisiya. Suna yin hakan ne ta wajen ba mu shawara daga Littafi Mai Tsarki. Ba sa ƙoƙarin nuna cewa sun fi kowa muhimmanci, amma suna taimaka ma ’yan’uwa su yi koyi da Yesu.​—Karanta 1 Korintiyawa 4:6, 7.

19. Mene ne kowannenmu zai iya yi? (Ka kuma duba akwatin nan “ Kada Ku Yi Gasa da Juna.”)

19 Dukanmu muna da baiwar da Allah ya ba mu. Ya kamata mu yi amfani da baiwar wajen ‘yin hidima ga ’yan’uwanmu.’ (1 Bit. 4:10) Za mu iya ɗauka cewa abin da muke yi ba shi da muhimmanci. Amma, kamar yadda ake amfani da ƙananan bulo ne a gina gida, haka ma ƙananan abubuwan da muke yi ne suke kawo haɗin kai a ikilisiya. Ya kamata dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu don mu guji halin gasa. Bari mu ƙuduri niyyar taimaka wajen sa a yi zaman lafiya da haɗin kai a cikin ikilisiya.​—Afis. 4:3.

WAƘA TA 80 ‘Mu Dandana, Mu Gani, Ubangiji Nagari Ne’

^ sakin layi na 5 Tukunyar laƙa za ta yi saurin fashewa idan ta tsattsage a gefe. Haka ma, idan ’yan’uwa suna gasa da juna, ikilisiya za ta iya rabuwa da sauri. Idan babu haɗin kai a cikin ikilisiya, ba za a iya bauta wa Allah cikin kwanciyar hankali ba. A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa ya kamata mu guji yin gasa da juna da kuma yadda za mu biɗi zaman lafiya a ikilisiya.

^ sakin layi na 4 An canja sunayen.