Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 31

Kana Shirye Ka Jira Abin da Jehobah Zai Yi?

Kana Shirye Ka Jira Abin da Jehobah Zai Yi?

“Zan jira.”​—MIK. 7:7.

WAƘA TA 128 Mu Jimre Har Ƙarshe

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

YAYA kake ji idan wani abu da kake bukata da gaggawa bai zo a lokacin da kake tsammani ba? Ka damu ne? Littafin Karin Magana 13:12 ta ce: “Sa rai wanda ba ta biya bukata ba, takan sa zuciya ta ɓace.” Amma yaya za ka ji idan ka gano cewa akwai dalilai masu kyau da suka sa abin bai zo a lokacin da kake tsammani ba? Mai yiwuwa za ka yi haƙuri ka jira.

2 A wannan talifin, za mu tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da dama da za su taimaka mana mu zama masu haƙuri yayin da muke “jira.” (Mik. 7:7) Sa’an nan, za mu tattauna fannoni biyu da muke bukatar mu jira Jehobah ya ɗauki mataki. A ƙarshe, za mu tattauna albarkun da waɗanda suka zama masu haƙuri za su samu.

ƘA’IDODIN LITTAFI MAI TSARKI DA ZA SU TAIMAKE MU MU ZAMA MASU HAƘURI

3. Mene ne Yakub 5:7 ta koya mana?

3 Littafin Yakub 5:7 ta nuna mana dalilin da ya sa muke bukatar mu zama masu haƙuri. Ayar ta ce: “Ku dubi irin haƙurin da manomi yakan yi lokacin da yake jira gonarsa ta ba da amfani mai kyau. Da yawan haƙuri yakan jira ruwan shuka da ruwan ƙarshe.” Mene ne ka koya daga wannan ayar? Mai hikima yakan yi abubuwa da kyau a hankali, kuma ya sami sakamako mai kyau.

4. Mene ne muka koya daga Karin Magana 4:18?

4 Littafin Karin Magana 4:18 ta ce, “hanyar masu adalci kamar ɓullowar hasken rana take, hasken da yakan yi ta ƙaruwa har ya haskaka cikakke iri na tsakar rana.” Wannan ayar ta nuna mana cewa Jehobah yana taimaka wa mutanensa su fahimci nufinsa a hankali a hankali. Ƙari ga haka, ayar za ta iya taimaka mana mu fahimci yadda Kirista yake yin canje-canje a rayuwarsa don ya kusaci Jehobah. Yakan ɗauki lokaci kafin mutum ya kusaci Jehobah. Idan muna nazari da kyau kuma muna bin shawarwarin da ke Kalmar Allah da kuma waɗanda ƙungiyarsa take ba mu, a hankali za mu kasance da halayen Kristi. Ban da haka, za mu daɗa sanin Allah. Bari mu tattauna misalin da Yesu ya bayar a kan wannan batun.

Kamar yadda iri yake girma a hankali a hankali, haka ma mutumin da ya saurari saƙon Mulkin Allah yake samun ci gaba a hankali a hankali (Ka duba sakin layi na 5)

5. Wane misali ne Yesu ya bayar don ya nuna cewa yana ɗaukan lokaci kafin mutum ya yi canje-canje?

5 Yesu ya yi amfani da misali don ya bayyana yadda saƙon Mulkin Allah yake girma kamar iri a zuciyar masu son gaskiya. Ya ce: “Irin ya tsira ya yi girma, mutumin [manomin] bai ma san yadda aka yi ba. Ƙasa tana ba da amfani da kanta, da farko takan fitar da kara, sa’an nan kai, sai kuma kan ya fitar da ƙwaya.” (Mar. 4:27, 28) Mene ne Yesu yake nufi? Yana nufin cewa kamar yadda iri take girma a hankali a hankali, haka ma mutumin da ya saurari saƙon Mulkin Allah yake samun ci gaba a hankali a hankali. Alal misali, yayin da ɗalibanmu suka soma kusantar Jehobah, za mu soma ganin canje-canje masu kyau da suke yi a rayuwarsu. (Afis. 4:22-24) Amma muna bukatar mu tuna cewa Jehobah ne yake sa wannan ƙaramin irin ya yi girma.​—1 Kor. 3:7.

6-7. Mene ne muka koya daga yadda Jehobah ya halicci duniya?

6 A duk abubuwan da yake yi, Jehobah yana ɗaukan iya lokacin da yake bukata don ya kammala aikinsa. Yana yin hakan don ya ɗaukaka sunansa kuma halittunsa su amfana. Alal misali, ka yi la’akari da yadda Jehobah ya shirya duniya kafin ya halicci ’yan Adam.

7 Yayin da Littafi Mai Tsarki yake magana a kan yadda Jehobah ya halicci duniya, ya ambata abubuwa kamar yadda Jehobah ya “shirya iyakarta,” ya “kafa tushenta,” kuma ya “kafa dutse mafi amfani na gininta.” (Ayu. 38:5, 6) Jehobah ya ɗauki lokaci don ya dudduba aikin da ya yi. (Far. 1:10, 12) Ka yi tunanin yadda mala’iku suka ji sa’ad da suka ga abubuwan da Jehobah ya halitta. Hakika sun yi farin ciki sosai! Shi ya sa suka “tā da muryar farin ciki.” (Ayu. 38:7) Mene ne muka koya? Jehobah ya ɗauki dubban shekaru yana halittar duniya, da taurari da kuma halittu masu rai, amma sa’ad da ya gama halitta kuma ya kalli abubuwan da ya yi, sai ya ce suna “da kyau sosai.”​—Far. 1:31.

8. Mene ne za mu tattauna yanzu?

8 Waɗannan misalan sun nuna mana cewa akwai ƙa’idodi da yawa a Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu ga cewa muna bukatar mu zama masu haƙuri. Yanzu za mu tattauna fannoni biyu da muke bukata mu jira Jehobah ya ɗauki mataki.

A WANE LOKACI NE MUKE BUKATAR MU JIRA JEHOBAH YA ƊAUKI MATAKI?

9. Wane yanayi ne zai bukace mu mu jira Jehobah ya ɗauki mataki?

9 A wasu lokuta, za mu bukaci mu jira Jehobah ya amsa addu’o’inmu. A wasu lokuta, idan mun daɗe muna fama da wata matsala ko muna ƙoƙari mu daina yin wani abin da Jehobah ba ya so, kuma muka roƙi Jehobah ya taimaka mana, za mu iya ɗauka cewa yana jinkirin amsa addu’armu. Me ya sa Jehobah ba ya amsa dukan addu’o’inmu nan da nan?

10. Me ya sa muke bukatar mu yi haƙuri yayin da muke jira Jehobah ya amsa addu’o’inmu?

10 Jehobah yana jin addu’o’inmu. (Zab. 65:2) Addu’o’inmu suna nuna masa cewa muna da bangaskiya. (Ibran. 11:6) Idan mun yi addu’a cewa Jehobah ya taimaka mana mu riƙa yin abin da zai faranta masa rai, zai yi farin ciki in ya ga cewa muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi hakan. (1 Yoh. 3:22) Don haka, idan muka roƙi Jehobah ya taimaka mana mu daina yin abubuwan da ba ya so, muna bukatar mu yi haƙuri kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu daina abin. Yesu ya taimaka mana mu fahimci cewa Jehobah ba zai amsa wasu addu’o’inmu nan take ba. Ya ce: “Ku yi ta roƙo za a ba ku, ku yi ta nema za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa kuma za a buɗe muku. Gama duk wanda ya roƙa za a ba shi, duk wanda ya nema zai samu, kuma duk wanda ya ƙwanƙwasa za a buɗe masa.” (Mat. 7:7, 8) Idan muka bi wannan shawarar kuma muka “nace cikin addu’a,” za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Ubanmu na sama zai amsa addu’o’inmu.​—Kol. 4:2.

Yayin da muke jira Jehobah ya ɗauki mataki, ya kamata mu ci gaba da yin addu’a kuma mu gaskata cewa zai amsa addu’ar (Ka duba sakin layi na 11) *

11. Ta yaya 1 Bitrus 5:6 za ta taimaka mana idan muna ganin kamar Allah yana jinkirin amsa addu’armu?

11 Ko da yake za mu iya ji kamar Jehobah yana jinkirin amsa addu’armu, ya yi alkawari cewa zai amsa a “lokacin da ya ga ya dace.” (Karanta 1 Bitrus 5:6.) Don haka, kada mu ɗauka cewa Jehobah ya yi kuskure idan bai amsa addu’armu a lokacin da muke so ba. Alal misali, mutane da yawa sun yi shekaru suna addu’a Mulkin Allah ya zo don ya kawar da mugunta a duniya. Yesu da kansa ma ya ce mu yi addu’a don Mulkin ya zo. (Mat. 6:10) Zai zama wauta idan mutum ya daina bauta wa Jehobah domin ƙarshen bai zo a lokacin da mutane suke zato ba! (Hab. 2:3; Mat. 24:44) Idan muka ci gaba da jira kuma muka yi imani cewa Jehobah zai ji addu’armu, za mu nuna cewa mu masu hikima ne. Ƙarshe zai zo a daidai lokacin da ya kamata, domin Jehobah ya riga ya saka ‘rana’ da kuma lokacin da hakan zai faru. Kuma wannan ranar ce za ta fi dacewa da kowa.​—Mat. 24:36; 2 Bit. 3:15.

Wane darasi game da haƙuri ne za mu iya koya daga Yusufu? (Ka duba sakin layi na 12-14)

12. A wane lokaci ne zai iya yi mana wuya mu yi haƙuri?

12 Muna bukatar mu yi haƙuri yayin da muke jira a yi mana adalci. A yawancin lokuta, mutane a duniya suna wulaƙanta waɗanda jinsinsu ko launin fatarsu ko yarensu ko al’adarsu ko kuma ƙasarsu ba ɗaya ba. Wasu kuma ana wulaƙanta su domin suna da naƙasa ko wani irin rashin lafiya dabam. Bayin Jehobah da yawa suna jimre rashin adalci da ake yi musu domin imaninsu. Idan aka wulaƙanta mu, muna bukatar mu tuna abin da Yesu ya faɗa. Ya ce: “Wanda ya jimre har zuwa ƙarshe, zai tsira.” (Mat. 24:13) Amma mene ne za ka yi idan wani a ikilisiya ya yi zunubi mai tsanani kuma ka san da hakan? Bayan an sanar da dattawa, shin za ka yi haƙuri ka ƙyale su su daidaita batun? Mene ne dattawa suke bukatar su yi idan wani ya yi zunubi mai tsanani?

13. Mene ne Jehobah yake so dattawa su yi idan wani ya yi zunubi mai tsanani?

13 Idan dattawa suka san cewa wani ya yi zunubi mai tsanani, za su roƙi Jehobah ya ba su “hikimar da take daga” wurinsa don su fahimci batun yadda yake so. (Yak. 3:17) Maƙasudinsu shi ne su taimaka su ‘dawo da mai zunubi kan hanya,’ idan zai yiwu. (Yak. 5:19, 20) Suna yin iya ƙoƙarinsu don su kāre ’yan’uwa a ikilisiya kuma su ƙarfafa waɗanda aka yi musu laifin. (2 Kor. 1:3, 4) Abu na farko da dattawa suke yi idan suka ji cewa wani ya yi zunubi mai tsanani shi ne, suna bincike domin su san asalin abin da ya faru. Hakan zai iya ɗaukan lokaci. Sai su yi addu’a kuma su ba da horo “yadda ya kamata,” bisa ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. (Irm. 30:11, New World Translation) Ko da yake dattawa ba za su zauna su jira har sai lokaci ya ƙure ba, bai kamata su yi hanzarin yanke hukunci ba. Idan dattawa suka bi ja-gorancin Jehobah, kowa a ikilisiya zai amfana. Amma ko da dattawa sun yanke hukuncin da ya dace, waɗanda aka yi musu laifin za su iya ci gaba da fushi. Idan kana wannan yanayin, mene ne za ka yi don ka sami kwanciyar hankali?

14. Wane misali a Littafi Mai Tsarki ne zai taimaka maka ka jimre idan wani Kirista ya yi maka laifi mai tsanani?

14 Wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ko kuma mutumin da ba Mashaidi ba, ya taɓa maka wani laifi mai tsanani? Akwai misalai da yawa a Kalmar Allah da za su taimaka mana mu koyi yadda za mu bar kome a hannun Allah. Alal misali, ’yan’uwan Yusufu sun yi masa rashin adalci, amma bai bar hakan ya sa shi ya zama mai zafin rai ba. Maimakon haka, ya mai da hankali ga ibadarsa, kuma Jehobah ya albarkace shi don yadda ya jimre kuma ya yi haƙuri. (Far. 39:21) Da shigewar lokaci, Yusufu ya manta da abin da aka yi masa kuma ya mai da hankali ga yadda Jehobah ya albarkace shi. (Far. 45:5) Mu ma za mu sami kwanciyar hankali kamar Yusufu idan muka kusaci Jehobah kuma muka bar kome a hannunsa.​—Zab. 7:17; 73:28.

15. Mene ne ya taimaka ma wata ’yar’uwa ta jimre rashin adalci da aka yi mata?

15 Hakika, ba a kowane lokaci ba ne za a yi mana rashin adalci irin wanda aka yi wa Yusufu. Amma ko da wane irin wulaƙanci ne aka yi mana, za mu iya yin baƙin ciki. Idan muka sami matsala da wani, ko da Mashaidi ne ko a’a, za mu amfana idan muka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Filib. 2:3, 4) Ga wani misali. Wata ’yar’uwa ta yi baƙin ciki sa’ad da ta ji cewa wata abokiyar aikinta ta yi ƙarya a kanta. Maimakon ta ɗauki mataki nan da nan, ’yar’uwar ta yi tunani a kan misalin Yesu. Sa’ad da mutane suka zage shi, bai rama ba. (1 Bit. 2:21, 23) Hakan ya sa ta yanke shawara cewa za ta mance da batun. Daga baya, ta gano cewa abokiyar aikinta tana fama da rashin lafiya da kuma matsaloli. Saboda haka, ’yar’uwar ta gaya wa kanta cewa mai yiwuwa abokiyar aikinta ba ta yi maganar da mummunan nufi ba. ’Yar’uwar ta gode wa Allah cewa ta jimre, kuma hakan ya sa ta kasance da kwanciyar hankali.

16. Mene ne zai iya ƙarfafa ka idan kana fama da rashin adalci? (1 Bitrus 3:12)

16 Idan kana shan wahala domin rashin adalci da aka yi maka ko kuma don wani abu dabam, ka tuna cewa Jehobah yana kusa da “waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa.” (Zab. 34:18) Yana ƙaunar ka domin yadda kake jimrewa da kuma yadda ka bar kome a hannunsa. (Zab. 55:22) Shi ne mai shari’ar dukan duniya, kuma yana ganin kome da ke faruwa. (Karanta 1 Bitrus 3:12.) Saboda haka, idan kana fama da wata matsala da ba za ka iya magancewa ba, ka tuna cewa zai fi dacewa ka jira Jehobah ya ɗauki mataki.

ALBARKUN DA WAƊANDA SUKA JIRA JEHOBAH YA DAUƘI MATAKI ZA SU SAMU

17. Kamar yadda Ishaya 30:18 ta nuna, wane alkawari ne Jehobah ya yi mana?

17 Nan ba da daɗewa ba, Ubanmu na sama zai yi mana albarka sosai sa’ad da Mulkinsa ya zo. Littafin Ishaya 30:18 ta ce: “Yahweh yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai. Gama Yahweh Allah ne mai yin gaskiya. Masu albarka ne masu jiransa.” Waɗanda suka dogara ga Jehobah za su sami albarka sosai a yanzu da kuma a sabuwar duniya a nan gaba.

18. Waɗanne albarku ne za mu samu?

18 Sa’ad da mutanen Allah suka shiga sabuwar duniya, ba za su sake bukatar jimre matsalolin da suke fuskanta a yau ba. Ba za a sake yin rashin adalci ko a sha azaba ba. (R. Yar. 21:4) Ba za mu riƙa damuwa cewa za mu rasa abin da muke bukata ba, domin kome zai kasance a yalwace. (Zab. 72:16; Isha. 54:13) Hakika wannan abin farin ciki ne!

19. Mene ne Jehobah yake yi mana a yanzu?

19 Jehobah yana shirya mu a yanzu domin mu iya yin rayuwa a ƙarƙashin Mulkinsa, ta wajen taimaka mana mu daina yin abubuwan da ba ya so, kuma mu kasance da halayen da suke faranta masa rai. Kada ka yi sanyin gwiwa har ka daina bauta wa Jehobah. Za mu more rayuwa mai daɗi nan ba da daɗewa ba! Yayin da muke ɗokin ganin wannan ranar, bari mu ci gaba da farin ciki kuma mu ci gaba da jira har sai Jehobah ya yi abubuwan da ya yi alkawari cewa zai yi mana!

WAƘA TA 118 Ka “Ƙara Mana Bangaskiya”

^ sakin layi na 5 Ka taɓa jin wani da ya daɗe yana bauta wa Jehobah ya ce, ‘Ban yi tsammanin cewa zan tsufa a wannan muguwar duniya ba’? Dukanmu muna marmarin ganin lokacin da Jehobah zai kawo ƙarshen duniya, musamman wannan lokacin da abubuwa sun yi wuya. Amma dole ne mu zama masu haƙuri. A wannan talifin, za mu tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu zama masu haƙuri. Ƙari ga haka, za mu tattauna fannoni biyu da muke bukatar mu jira Jehobah ya ɗauki mataki. A ƙarshe, za mu tattauna albarkun da waɗanda suka zama masu haƙuri za su samu.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ’yar’uwa ta soma addu’a ga Jehobah tun tana ƙarama. A lokacin ne iyayenta suka koya mata yin addu’a. Sa’ad da ta zama matashiya, ta soma yin hidimar majagaba, kuma takan roƙi Jehobah ya taimaka mata a hidimarta. Bayan shekaru da yawa, mijinta ya soma rashin lafiya mai tsanani, kuma ta roƙi Jehobah ya ba su ƙarfin jimre matsalar. Yanzu da ta zama gwauruwa, ta ci gaba da yin addu’a, kuma tana da tabbaci cewa Ubanta na sama zai amsa addu’o’inta kamar yadda ya saba yi.