Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 32

Ka Karfafa Bangaskiyarka Cewa Akwai Mahalicci

Ka Karfafa Bangaskiyarka Cewa Akwai Mahalicci

“Bangaskiya ita ce kasancewa da tabbaci a kan . . . abin da ba a iya gani.”​—IBRAN. 11:1.

WAƘA TA 11 Halittun Allah Suna Yabon Sa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne aka koya maka game da Mahaliccinmu?

IDAN iyayenka Shaidun Jehobah ne, wataƙila ka koya game da Jehobah tun kana ƙarami. Ka koyi cewa shi ne Mahalicci, yana da halaye masu kyau kuma yana so ya mai da duniya ta zama aljanna.​—Far. 1:1; A. M. 17:24-27.

2. Yaya wasu suke ɗaukan mutanen da suka yi imani da wanzuwar Mahalicci?

2 Amma mutane da yawa ba su yarda cewa Allah yana wanzuwa ba, balle ma su gaskata cewa shi ne ya halicci abubuwa. A maimakon haka, sun ce rayuwa ta soma ne haka kawai, sa’an nan ƙananan abubuwa masu rai suka yi ta canjawa zuwa manya ta wurin juyin halitta. Wasu daga cikin mutanen da suka gaskata da hakan sun yi makaranta sosai. A cewarsu, kimiyya ta ƙaryata Littafi Mai Tsarki, kuma marasa ilimi ne suke gaskatawa da wanzuwar Mahalicci.

3. Me ya sa yake da muhimmanci mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

3 Shin za mu bar ra’ayin mutanen da suka yi makaranta sosai ya sa mu yi shakka cewa Jehobah ne Mahaliccinmu mai ƙauna? Hakan ya dangana ga abin da ya sa muka yarda cewa Jehobah ne Mahalicci. Shin mun gaskata da hakan ne domin abin da aka gaya mana, ko kuma domin mun ɗauki lokaci mun yi nazari da kanmu? (1 Kor. 3:12-15) Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. Idan muka yi hakan, ba za mu bar wani ya ruɗe mu da “ilimin duniyar nan da kuma ilimin ruɗu na banza” ba. (Kol. 2:8; Ibran. 11:6) Wannan talifin zai taimaka mana ta wajen tattauna, (1) abin da ya sa mutane da yawa ba su amince cewa akwai Mahalicci ba, (2) yadda za mu kasance da bangaskiya cewa Jehobah ne Mahaliccinmu da kuma (3) yadda za mu ƙarfafa bangaskiyarmu.

ABIN DA YA SA MUTANE DA YAWA BA SU AMINCE CEWA AKWAI MAHALICCI BA

4. Kamar yadda Ibraniyawa 11:1 ta nuna, mece ce bangaskiya?

4 Wasu mutane suna ganin bangaskiya tana nufin mutum ya yi imani da abin da bai tabbata ba. Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa hakan ba bangaskiya ta ƙwarai ba ce. (Karanta Ibraniyawa 11:1.) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tabbaci ne yake sa mutum ya kasance da bangaskiya. Saboda haka, ko da yake ba ma iya ganin Jehobah da Yesu da kuma Mulkin Allah, muna da tabbaci cewa suna wanzuwa. (Ibran. 11:3) Wani ɗan kimiyya da ya zama Mashaidi, ya ce: “Shaidun Jehobah suna da tabbaci a kan abin da suka yi imani da shi, kuma ba sa yin watsi da bayanan kimiyya.”

5. Me ya sa mutane da yawa suke ɗauka cewa babu Mahalicci?

5 Me ya sa mutane da yawa suka ƙi su amince cewa akwai Mahalicci, duk da cewa akwai tabbacin hakan? Wasu ba su taɓa bincika tabbacin nan da kansu ba. Wani mai suna Robert da yanzu Mashaidi ne, ya ce: “Da yake malamaina ba su taɓa ambata batun halitta a makaranta ba, na ɗauka cewa ba halittar abubuwa aka yi ba. Sai da na kai shekara 22 kafin na tattauna da Shaidun Jehobah kuma suka nuna mini tabbaci daga Littafi Mai Tsarki cewa Allah ne ya halicci kome.” *​—Ka duba akwatin nan “ Saƙo Mai Muhimmanci ga Iyaye.”

6. Me ya sa wasu suka ƙi cewa akwai wanda ya halicci abubuwa?

6 Wasu ba su gaskata cewa akwai Mahalicci ba domin sun ce abin da suke iya gani ne suke gaskatawa da shi. Amma gaskiyar ita ce, akwai abubuwa da ba sa gani da suke gaskatawa da su, kamar iska. Bangaskiyar da aka ambata a Littafi Mai Tsarki ta ƙunshi “tabbaci” a kan abubuwan da “ba a iya gani.” (Ibran. 11:1) Yakan ɗauki lokaci da himma kafin mutum ya iya bincika tabbacin nan da kyau, amma mutane da yawa ba su da marmarin yin hakan. Mutumin da bai bincika abubuwan da suka tabbatar da wanzuwar Allah da kansa ba zai iya ce babu Allah.

7. Shin kowa da ya yi makaranta ne yake ƙin amince cewa Allah ne ya halicci sama da ƙasa? Ka bayyana.

7 Bayan wasu ’yan kimiyya sun bincika abubuwan da suka tabbatar cewa akwai Mahalicci, sai suka gaskata cewa Allah ne ya halicci sama da ƙasa. * Kamar Robert da aka ambata ɗazu, wasu suna iya cewa babu Mahalicci domin ba a koyar da hakan a jami’a ba. Amma akwai ’yan kimiyya da yawa da suka koya game da Jehobah kuma yanzu suna ƙaunar sa. Kamar yadda waɗannan ’yan kimiyya suka yi, mu ma muna bukatar mu ƙarfafa bangaskiyarmu, ko da mun yi makaranta ko ba mu yi ba. Babu wanda zai yi hakan a madadinmu.

YADDA ZA KA KASANCE DA BANGASKIYA CEWA JEHOBAH NE MAHALICCI

8-9. (a) Wace tambaya ce za mu tattauna? (b) Ta yaya yin nazarin halittu zai amfane ka?

8 Ta yaya za ka ƙarfafa bangaskiyarka cewa akwai Mahalicci? Ga abubuwa biyu da za ka iya yi.

9 Ka yi nazarin halittu. Idan muna lura da dabbobi da shuke-shuke da kuma taurari, za mu daɗa ba da gaskiya cewa akwai Mahalicci. (Zab. 19:1; Isha. 40:26) Yayin da kake daɗa nazarin waɗannan abubuwan, za ka daɗa kasancewa da tabbaci cewa Jehobah shi ne Mahalicci. Littattafanmu suna ɗauke da talifofi da suke bayyana abubuwa da yawa game da halittu. Kada ka ƙi karanta waɗannan talifofin ko da kana ganin suna da wuyar fahimta. Ka koyi iyakacin abin da za ka iya koya. Kuma ka riƙa kallon bidiyoyin taron yanki na shekarun baya-bayan nan game da halittu da aka saka a dandalin jw.org.

10. Ka ba da misalin da ya tabbatar cewa akwai Mahalicci. (Romawa 1:20)

10 Ka mai da hankali ga abubuwan da za ka iya koya game da Mahaliccinmu yayin da kake nazarin halittu. (Karanta Romawa 1:20.) Alal misali, rana tana ba da haske da kuma zafi da yake sa mu iya rayuwa a duniya. Amma akwai wani irin haske da rana take fitarwa da zai iya yi mana lahani. Muna bukatar kāriya daga wannan hasken. Kuma muna samun wannan kāriyar! Ta yaya? Akwai iska da ke kewaye da duniya da take kāre mu daga irin wannan haske mai haɗari. Idan wannan haske mai haɗari ya ƙaru, iskar da ke kāre mu za ta ƙaru ita ma. Shin wannan tsarin bai nuna maka cewa akwai Mahalicci mai ƙauna da kuma hikima da ya yi abubuwan nan ba?

11. A ina ne za ka sami bayanai da za su sa ka daɗa yin imani da wanzuwar Mahalicci? (Ka duba akwatin nan “ Bayanan da Za Su Iya Ƙarfafa Bangaskiyarka.”)

11 Za ka iya samun talifofi da yawa da za su daɗa tabbatar maka da cewa halittar abubuwa aka yi a littafin nan Watch Tower Publications Index da kuma ta yin bincike a dandalin jw.org. Za ka iya soma da talifofi da kuma bidiyoyin da ke ƙarƙashin jerin talifofin nan “Halittarsa Aka Yi?” a dandalin. Waɗannan ƙananan talifofi ne da suke bayyana abubuwa masu ban mamaki game da dabbobi da kuma shuke-shuke. Ƙari ga haka, suna ɗauke da misalan yadda ’yan kimiyya suke kwaikwayon halittu yayin da suke ƙera abubuwa.

12. Sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki, me muke bukatar mu lura da su?

12 Ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Ɗan kimiyyar da aka ambata a sakin layi na huɗu bai gaskata da wanzuwar Mahalicci nan da nan ba. Amma da shigewar lokaci, ya yarda cewa akwai Mahalicci. Ya ce: “Ba nazarin kimiyya da na yi ne kaɗai ya sa na kasance da bangaskiya ba. Abin da na yi nazarinsa daga Littafi Mai Tsarki ma ya taimaka mini.” Wataƙila ka riga ka san koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai. Duk da haka, kafin ka daɗa yarda da wanzuwar Mahalicci, kana bukatar ka ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah. (Yosh. 1:8; Zab. 119:97) Alal misali, ka yi tunanin yadda Littafi Mai Tsarki ya ba da bayanai na gaskiya a kan abubuwan da suka faru shekaru da yawa da suka shige. Ban da haka, ka yi tunanin abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya annabta da suka cika, da kuma yadda marubutan suka rubuta abubuwan da suka jitu da juna. Yin hakan zai sa ka daɗa yarda cewa akwai Mahalicci mai ƙauna da hikima kuma saƙonsa ne yake cikin Littafi Mai Tsarki. *​—2 Tim. 3:14; 2 Bit. 1:21.

13. Ka ba da misalin wata shawara mai kyau da ke cikin Kalmar Allah.

13 Sa’ad da kake nazarin Kalmar Allah, ka lura da yadda shawarwarin da ke ciki suke taimaka wa mutane. Alal misali, tun da daɗewa Littafi Mai Tsarki ya ce son kuɗi yana da lahani kuma yakan jawo “baƙin ciki iri-iri masu zafi.” (1 Tim. 6:9, 10; K. Mag. 28:20; Mat. 6:24) Hakan gaskiya ne a yau? Wani littafi game da halin ’yan Adam a zamaninmu ya ce: “A yawancin lokuta, mutanen da suke ganin samun kuɗi shi ne abu mafi muhimmanci a rayuwa ba sa farin ciki. Har waɗanda suke niyyar samun ƙarin kuɗi kawai ma ba sa farin ciki kuma suna ƙara wa kansu rashin lafiya.” Saboda haka, gargaɗin Littafi Mai Tsarki cewa mu guji son kuɗi yana da kyau sosai! Za ka iya tuna wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka taimaka maka? Idan muka yi tunani a kan shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki, za mu ga cewa Mahaliccinmu mai ƙauna ya san abin da ya fi dacewa da mu kuma hakan zai sa mu daɗa bin ƙa’idodinsa. (Yak. 1:5) A sakamakon haka, za mu ji daɗin rayuwa.​—Isha. 48:17, 18.

14. Mene ne nazarin Littafi Mai Tsarki zai koya maka game da Jehobah?

14 Ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da maƙasudin daɗa koya game da Jehobah. (Yoh. 17:3) Yayin da kake nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka ga irin halayen da Jehobah yake da su. Za ka kuma ga waɗannan halayen idan ka yi nazarin halittu. Sanin halayen Jehobah zai tabbatar maka da cewa yana wanzuwa. (Fit. 34:6, 7; Zab. 145:8, 9) Yayin da kake daɗa sanin Jehobah, bangaskiyarka za ta ƙaru, za ka daɗa ƙaunar sa kuma dangantakarka da shi za ta daɗa yin danƙo.

15. Ta yaya gaya wa mutane game da Allah zai taimaka maka?

15 Ka gaya wa mutane abin da ka koya game da Allah. Yayin da kake yin hakan, bangaskiyarka za ta yi ƙarfi. Idan wani da kake yi masa wa’azi yana shakkar wanzuwar Allah, mene ne za ka yi? Ka nemi bayanai daga Littafi Mai Tsarki da suke cikin littattafanmu, sai ka tattauna da mutumin. (1 Bit. 3:15) Kana iya neman taimako daga Mashaidin da ya manyanta. Ko da mutumin bai amince da amsoshin da ka ba shi ba, za ka amfana daga yin binciken. Kuma bangaskiyarka za ta yi ƙarfi. A sakamakon haka, ba za ka yarda ba idan mutanen da ake ganin suna da ilimi suka ce babu Mahalicci.

KA ƘARFAFA BANGASKIYARKA!

16. Me zai iya faruwa idan ba mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu ba?

16 Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. Me ya sa? Domin idan ba mu mai da hankali ba, za mu iya rasa bangaskiyarmu. Ka tuna cewa bangaskiya ta ƙunshi tabbaci a kan abin da ba a iya gani. Za mu iya saurin mantawa da abin da ba ma iya gani. Shi ya sa Bulus ya kira rashin bangaskiya “zunubin da yake saurin ɗaure mu.” (Ibran. 12:1, New World Translation) Ta yaya za mu guji wannan tarkon?​—2 Tas. 1:3.

17. Me zai taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

17 Da farko, ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhu mai tsarki, kuma ka yi hakan a kai a kai. Me ya sa? Domin bangaskiya tana cikin halayen da ruhu mai tsarki yake sa mu kasance da su. (Gal. 5:22, 23, NW) Idan ruhu mai tsarki bai taimaka mana ba, ba za mu iya yin imani da Mahaliccinmu ba. Idan muka ci gaba da roƙan Jehobah ya ba mu ruhunsa mai tsarki, zai ba mu. (Luk. 11:13) Muna ma iya roƙan sa cewa: “Ka ƙara mana bangaskiya.”​—Luk. 17:5.

18. Kamar yadda Zabura 1:2, 3 suka nuna, wace kyauta ce aka ba mu?

18 Ƙari ga haka, ka riƙa yin nazarin Kalmar Allah a kai a kai. (Karanta Zabura 1:2, 3.) A lokacin da aka rubuta wannan zaburar, Isra’ilawa kaɗan ne suke da rubutacciyar Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa. Amma sarakuna da firistoci suna da rubutacciyar dokar, kuma bayan kowace shekara bakwai, sukan tara “maza, da mata, da yara,” har ma da baƙi da suke zama cikinsu don su saurari dokar. (M. Sha. 31:10-12) A zamanin Yesu ma, mutane kaɗan ne suke da Nassosi da aka kofa a naɗaɗɗen littafi, kuma ana ajiye yawancinsu a cikin majami’u. Amma a yau, yawancin mutane suna da Littafi Mai Tsarki ko kuma wani sashensa. Wannan kyauta ce mai daraja. Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don wannan kyautar?

19. Mene ne muke bukatar mu yi don mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

19 Za mu nuna godiya domin wannan kyautar ta wajen karanta Kalmar Allah a kowace rana. Muna bukatar mu keɓe lokacin karanta da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ba kawai sai lokacin da muka sami dama ba. Idan muka tsara lokacin da za mu riƙa yin nazarin Kalmar Allah a kai a kai kuma muka bi tsarin, bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi.

20. Mene ne za mu ƙuduri niyyar yi?

20 Mun bambanta da “masu hikima da masu ilimi” na duniya, domin muna da bangaskiya bisa ga abin da muka gani a Kalmar Allah. (Mat. 11:25, 26) Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana dalilin da ya sa abubuwa a duniya suke daɗa lalacewa da kuma abin da Jehobah zai yi game da hakan. Don haka, bari mu ƙudiri niyyar ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka wa mutane su gaskata cewa akwai Mahalicci. (1 Tim. 2:3, 4) Bari mu ci gaba da ɗokin ganin lokacin da dukan waɗanda suke raye a duniya za su yabi Jehobah kuma su ce: “Ya Ubangiji Allahnmu, ka cancanci ka karɓi ɗaukaka, . . . gama ka halicci kome da kome.”​—R. Yar. 4:11.

WAƘA TA 2 Jehobah Ne Sunanka

^ sakin layi na 5 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ne Mahalicci. Amma mutane da yawa ba su yarda da hakan ba. Sun gaskata cewa babu wanda ya halicci abubuwa. Idan mun gaskata da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki, abin da suke faɗa ba zai sa mu soma shakka ba. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu yi hakan.

^ sakin layi na 5 A wasu makarantu, malamai ba sa koyar da cewa Allah ne Mahalicci. Sun ce koyar da hakan zai tāke ’yancin yaran na bin addini.

^ sakin layi na 7 A cikin littafin nan Watch Tower Publications Index, akwai labaran mutane fiye da 60 da suka yi makaranta sosai kuma suka yi imani da wanzuwar Allah. A ƙarƙashin “Science,” ka duba ƙaramin jigon nan “scientists expressing belief in creation.” Za ka iya samun wasu labaran a Research Guide for Jehovah’s Witnesses. A ƙarƙashin “Science and Technology,” sai ka duba “‘Interview’ (Awake! series).”

^ sakin layi na 12 Alal misali, ka duba talifin nan “Kimiyya ta Jitu da Littafi Mai Tsarki Kuwa?” a jw.org da kuma talifin nan “Abin Da Jehobah Ya Annabta Yana Faruwa,” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 2008.