Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 34

Ta Yaya Za Mu “Dandana” Alherin Jehobah?

Ta Yaya Za Mu “Dandana” Alherin Jehobah?

“Ku ɗanɗana ku ga Yahweh mai alheri ne, mai albarka ne wanda ya sami wurin ɓuya a cikinsa.”​—ZAB. 34:8.

WAƘA TA 117 Mu Riƙa Yin Alheri Kamar Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Kamar yadda Zabura 34:8 ta nuna, mene ne za mu yi don mu ga alherin Jehobah?

A CE wani ya ba ka abincin da ba ka taɓa ci ba. Za ka iya koyan wani abu game da abincin ta wajen kallon abincin ko sansanawa ko sanin abubuwan da aka yi abincin da su, ko kuma ta wajen tambayar mutane ra’ayinsu game da abincin. Amma abin da za ka iya yi don ka san ko abincin yana da daɗi shi ne, ɗanɗana abincin.

2 Za mu iya koyan wani abu game da alherin Jehobah ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki da littattafanmu da kuma saurarar bayin Jehobah sa’ad da suke ba da labarin yadda Jehobah ya yi musu alheri. Amma sai mun “ɗanɗana” alherin Allah da kanmu ne za mu san yadda Jehobah yake. (Karanta Zabura 34:8.) Ga wani misalin yadda za mu yi hakan. A ce muna so mu soma wani fannin hidima ta cikakken lokaci, amma kafin mu yi hakan, muna bukatar mu sauƙaƙa rayuwarmu. Mai yiwuwa mun daɗe muna karanta alkawarin da Yesu ya yi cewa idan mun saka Mulkin Allah farko a rayuwarmu, Jehobah zai ba mu abubuwan da muke bukata, amma ba mu taɓa ganin hakan ya faru da mu ba. (Mat. 6:33) Duk da haka, mun ba da gaskiya ga abin da Yesu ya faɗa. Sai muka rage kashe kuɗi kuma muka yi wasu canje-canje a aikin da muke yi domin mu mai da hankali ga yin wa’azi. Yayin da muke hakan, mun ga cewa da gaske Jehobah yana kula da bukatunmu. Hakan ya sa mun “ɗanɗana” alherin Jehobah da kanmu.

3. Kamar yadda Zabura 31:19 ta nuna, su waye ne Jehobah yake ma alheri?

3 Jehobah “mai alheri ne ga kowa,” har da waɗanda ba su san shi ba. (Zab. 145:9; Mat. 5:45) Amma Jehobah yana yin alheri musamman ga waɗanda suke ƙaunar sa kuma suke bauta masa da zuciya ɗaya. (Karanta Zabura 31:19.) Ka yi la’akari da wasu hanyoyin da muke amfana daga alherin Jehobah.

4. Ta yaya Jehobah yake nuna alheri ga waɗanda suka soma kusantar shi?

4 A duk lokacin da muka bi abin da muka koya daga wurin Jehobah, za mu amfana. Alal misali, a lokacin da muka koya game da shi kuma muka soma ƙaunar shi, ya taimaka mana mu daina tunani da kuma yin abubuwan da ba ya so. (Kol. 1:21) Kuma sa’ad da muka yi alkawarin bauta masa kuma muka yi baftisma, ya ƙara yi mana alheri ta wajen ba mu zuciya mai tsabta kuma ya ƙulla dangantaka da mu.​—1 Bit. 3:21.

5. Ta yaya Jehobah yake yi mana alheri yayin da muke yin wa’azi?

5 Jehobah yana nuna mana alheri yayin da muke yin wa’azi. Kai mai jin kunya ne? Bayin Jehobah da yawa suna jin kunya. Wataƙila kafin ka zama Mashaidin Jehobah ba ka taɓa tsammani cewa za ka iya zuwa gidan wani da ba ka sani ba ka yi masa wa’azi. Amma yau kana yin hakan sosai. Kuma Jehobah yana taimaka maka ka ji daɗin wa’azi yanzu! Ban da wannan ma, Jehobah yana taimaka maka a wasu hanyoyi dabam. Ya taimaka maka ka kasance a natse a lokacin da kake fuskantar hamayya. Ƙari ga haka, ya taimaka maka ka tuna nassin da za ka yi amfani da shi a lokacin da mutane suka saurare ka. Kuma ya ba ka ƙarfin ci gaba da yin wa’azi duk da cewa mutane a yankinku ba sa saurarar wa’azi.​—Irm. 20:7-9.

6. Ta yaya yadda Jehobah yake horar da mu ya nuna cewa shi mai alheri ne?

6 Jehobah ya kuma nuna mana alheri ta wajen koya mana yadda za mu yi wa’azi. (Yoh. 6:45) A taron tsakiyar mako, ana nuna mana yadda za mu yi wa’azi kuma ana ƙarfafa mu mu bi shawarwarin nan yayin da muke wa’azi. Da farko, za mu iya jin tsoron yin abin da ba mu saba ba, amma idan muka yi hakan, za mu ga amfanin bin wannan shawarar a yankinmu. A taron ikilisiya da kuma taron yanki, ana ƙarfafa mu mu gwada yin amfani da hanyoyin yin wa’azi da ba mu taɓa gwadawa ba. Za mu iya jin tsoron bin wannan shawarar, amma idan muka yi hakan, Jehobah zai yi mana albarka. Bari mu tattauna yadda za mu iya cim ma maƙasudinmu.

JEHOBAH YANA YI MA WAƊANDA SUKA DOGARA GARE SHI ALBARKA

7. Wace albarka ce za mu samu idan muka faɗaɗa hidimarmu?

7 Za mu daɗa kusantar Jehobah. Ka yi la’akari da misalin wani dattijo mai suna Samuel * wanda yake hidima da matarsa a Kolombiya. Ma’auratan nan sun daɗe suna jin daɗin hidimar majagaba a ikilisiyarsu, amma sun so su faɗaɗa hidimarsu ta wajen taimaka ma wata ikilisiya da ke bukatar masu shela sosai. Sai suka yi sadaukarwa don su samu su cim ma wannan maƙasudin. Samuel ya ce: “Mun bi shawarar da ke Matiyu 6:33 kuma muka daina sayan abubuwan da ba ma bukata. Amma abin da ya fi mana wuya shi ne barin gidanmu, domin an gina shi daidai yadda muke so, kuma ba a bin mu bashi a kan gidan.” Bayan sun ƙaura zuwa sabuwar ikilisiyar, sai suka gano cewa ba sa bukatar kuɗi da yawa. Samuel ya ƙara cewa: “Mun ga yadda Jehobah ya yi mana ja-goranci kuma ya amsa addu’o’inmu. Mun ga cewa Jehobah yana farin ciki da mu kuma yana ƙaunar mu.” Za ka iya faɗaɗa hidimarka? Idan ka yi hakan, ka tabbata cewa za ka daɗa kusantar Jehobah kuma zai kula da kai.​—Zab. 18:25.

8. Mene ne ka koya daga abin da Ivan da Viktoria suka ce?

8 Za mu yi farin ciki a hidimarmu. Ka yi la’akari da abin da wasu ma’aurata masu suna Ivan da Viktoria da suke hidima a ƙasar Kyrgyzstan suka faɗa. Sun sauƙaƙa rayuwarsu don su taimaka a aikin gina wuraren ibada. Ivan ya ce: “Mun yi kowane aiki da ƙwazo sosai. Ko da yake mukan gaji da yamma, mukan yi farin ciki domin mun san cewa muna yin amfani da ƙarfinmu mu yi wa Jehobah aiki. Ƙari ga haka, mun yi farin ciki domin mun yi sabbin abokai kuma mun yi cuɗanya da su.”​—Mar. 10:29, 30.

9. Mene ne wata ’yar’uwa da take fama da yanayi mai wuya ta yi don ta faɗaɗa hidimarta, kuma wane sakamako ne ta samu?

9 Za mu iya yin farin ciki a hidimarmu ga Jehobah ko da muna cikin yanayi mai wuya. Alal misali, Mirreh wata gwauruwa a Yammacin Afirka ta yi aiki a matsayin likita. Amma da ta yi ritaya, sai ta soma hidimar majagaba. Mirreh tana fama da wani ciwo mai tsananin zafi da ke sa tafiya ya yi mata wuya. Saboda haka, awa ɗaya take iya yi a wa’azi gida-gida. Amma ta fi yin wa’azi ta wajen amfani da amalanke. Tana da ɗalibai da waɗanda take koma ziyara wurin su, wasu kuma ta waya ne take kiran su. Me ya sa Mirreh ta daɗa ƙwazo a hidima? Mirreh ta ce: “Ina ƙaunar Jehobah da Yesu sosai. Kuma a koyaushe ina addu’a Jehobah ya taimaka mini in yi iya ƙoƙarina a hidimarsa.”​—Mat. 22:36, 37.

10. Kamar yadda Ishaya 54:13 ta nuna, mene ne Jehobah yake yi ma waɗanda suka ba da kansu?

10 Jehobah zai daɗa horar da mu. Wani ɗan’uwa mai suna Kenny da ke hidimar majagaba a ƙasar Mauritius ya ga gaskiyar wannan batun. A lokacin da ya koyi gaskiya, ya bar makarantar jami’a, sai ya yi baftisma kuma ya soma hidima ta cikakken lokaci. Ya ce: “Ina iya ƙoƙarina in zama kamar annabi Ishaya wanda ya ce, ‘Ga ni nan, ka aike ni!’” (Isha. 6:8) Kenny ya taimaka a aikin gine-gine da yawa, da kuma fassara littattafanmu zuwa yarensu. Ya ce: “Na sami horarwa da ta taimaka mini in yi ayyukan da aka ba ni da kyau.” Amma ba yadda zai yi ayyukan ne kawai ya koya ba. Ya ce: “Na gano kasawata da kuma halayen da nake bukatar in koya domin in faranta ran Jehobah.” (Karanta Ishaya 54:13.) Shin za ka iya ba da kanka domin Jehobah ya horar da kai?

Wasu ma’aurata suna wa’azi a inda ake bukatar masu shela sosai; wata ’yar’uwa matashiya tana taimakawa da gina Majami’ar Mulki; wasu ma’aurata tsofaffi suna yin wa’azi ta waya. Dukansu suna jin daɗin hidimarsu (Ka duba sakin layi na 11)

11. Mene ne wasu ’yan’uwa mata a Koriya ta Kudu suka yi don su daɗa ƙwazo a wa’azi, kuma wane sakamako ne suka samu? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

11 Ko Shaidun da suka daɗe suna bauta wa Jehobah ma za su sami horarwa idan suka gwada bin wata sabuwar hanyar yin wa’azi. A lokacin annobar koronabairas, dattawa a wata ikilisiya a Koriya ta Kudu sun rubuto cewa: “Wasu da a dā suke ganin ba za su iya yin wa’azi ba saboda rashin lafiya, yanzu suna yin hakan ta waya. Wasu ’yan’uwa mata uku da suka ba shekara 80 baya sun koyi yin amfani da kwamfuta kuma yanzu suna yin wa’azi da kwamfuta kusan kowace rana.” (Zab. 92:14, 15) Za ka so ka faɗaɗa hidimarka don ka daɗa ganin alherin Jehobah? Ga wasu abubuwan da za ka iya yi don ka cim ma wannan maƙasudin.

ME ZAI TAIMAKA MAKA DON KA ƘARA ƘWAZO?

12. Wane alkawari ne Jehobah ya yi ma waɗanda suka dogara gare shi?

12 Ka dogara ga Jehobah. Ya yi alkawarin yi mana albarka idan muka dogara gare shi kuma muka yi iya ƙoƙarinmu a hidimarsa. (Mal. 3:10) Wata ’yar’uwa mai suna Fabiola da take zama a ƙasar Kolombiya ta ga yadda Jehobah ya cika wannan alkawarin. Ta so ta soma hidimar majagaba na kullum nan da nan bayan ta yi baftisma. Amma ta kasa yin hakan domin da albashinta ne take kula da maigidanta da kuma yaranta uku. A lokacin da za ta yi ritaya, ta yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mata. Ga abin da ta faɗa, ta ce: “Mutane sukan jira na dogon lokaci bayan sun yi ritaya kafin a soma biyan su fensho, amma an soma biya na fensho wata ɗaya bayan na yi ritaya. Hakan ya ba ni mamaki sosai!” Wata biyu bayan hakan, ta soma hidimar majagaba. Yanzu ta wuce shekara 70 kuma ta yi fiye da shekaru 20 tana hidimar majagaba. A cikin shekarun nan, ta taimaka wa mutane takwas su yi baftisma. Ta ce: “Ko da yake a wasu lokuta nakan ji ba ni da ƙarfi, Jehobah ya taimaka min in ci gaba da hidimar majagaba.”

Ta yaya Ibrahim da Saratu da Yakubu da kuma firistocin da suka ƙetare Kogin Urdun suka nuna cewa sun dogara ga Jehobah? (Ka duba sakin layi na 13)

13-14. Waɗanne misalai ne za su iya taimaka mana mu dogara ga Jehobah kuma mu faɗaɗa hidimarmu?

13 Ka koyi darasi daga waɗanda suka dogara ga Jehobah. A cikin Littafi Mai Tsarki, akwai misalan mutane da yawa da suka yi ƙwazo sosai a hidimarsu ga Jehobah. A yawancin lokuta, sai sun ɗauki matakin da ya nuna cewa sun dogara gare shi kafin ya yi musu albarka. Alal misali, sai da Ibrahim ya bar ƙasarsa zuwa wata ƙasa “ko da yake bai san inda za shi ba” kafin Jehobah ya albarkace shi. (Ibran. 11:8) Bayan Yakubu ya yi kokawa da mala’ika ne ya sami albarka ta musamman. (Far. 32:24-30) A lokacin da al’ummar Isra’ila take so ta shiga Ƙasar Alkawari, sai da firistoci suka saka ƙafafunsu a cikin ruwan Kogin Urdun ne al’ummar ta iya ƙetare kogin.​—Yosh. 3:14-16.

14 Za ka kuma iya amfana daga misalin Shaidun Jehobah a zamaninmu da suka dogara ga Jehobah kuma suka faɗaɗa hidimarsu. Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Payton da matarsa Diana, sun ji daɗin karanta labaran ’yan’uwa da suka faɗaɗa hidimarsu, kamar waɗanda aka ambata a jerin talifofin nan, “Sun Ba da Kansu da Yardar Rai.” * Payton ya ce: “Da muke karanta labaran, kamar dai muna kallon mutum yana cin abinci mai daɗi ne. Yayin da muka ci gaba da kallo, sai mu ma muka so mu ‘ɗanɗana mu ga’ cewa ‘Yahweh mai alheri ne.’” A ƙarshe, Payton da Diana sun ƙaura zuwa wurin da ake bukatar masu shela. Ka taɓa karanta waɗannan jerin talifofin? Ka taɓa kallon bidiyoyin nan Yin Wa’azi a Yankin da Shaidun Jehobah Ba Sa Yawan Zuwa Wa’azi​—Ostareliya da kuma Witnessing in Isolated Territory​—Ireland da ke dandalin jw.org? Talifofi da bidiyoyin nan za su taimaka maka ka ga yadda za ka iya faɗaɗa hidimarka.

15. Ta yaya cuɗanya da abokan da suka dace zai taimaka mana?

15 Ka zaɓi abokan da suka dace. Zai yi mana sauƙi mu ci abincin da ba mu taɓa ci ba idan muna tare da mutanen da suke son cin abincin. Haka ma idan muna tarayya da mutanen da suke saka Jehobah a kan gaba a rayuwarsu, za su ƙarfafa mu mu faɗaɗa hidimarmu. Abin da ya faru da wasu ma’aurata masu suna Kent da Veronica ke nan. Kent ya ce: “Abokanmu da iyalinmu sun ƙarfafa mu mu gwada sabbin hanyoyin yin wa’azi. Mun ga cewa yin cuɗanya da ’yan’uwan da suke saka Mulkin Allah farko a rayuwarsu, ya sa mun kasance da ƙarfin zuciyar gwada yin sabon abu.” Yanzu, Kent da Veronica suna yin hidimar majagaba na musamman a ƙasar Sabiya.

16. Kamar yadda kwatancin Yesu a Luka 12:​16-21 suka nuna, me ya sa muke bukatar mu yi sadaukarwa?

16 Ka yi sadaukarwa domin Jehobah. Ba ma bukatar mu sadaukar da dukan abubuwan da muke jin daɗin yi kafin mu faranta ran Jehobah. (M. Wa. 5:19, 20) Amma idan mun ƙi faɗaɗa hidimarmu domin ba ma so mu yi sadaukarwa, za mu yi kuskure kamar mutumin da Yesu ya ambata a kwatancinsa. Mutumin ya yi aiki da ƙwazo domin ya ji daɗin rayuwa amma ya manta da Allah. (Karanta Luka 12:16-21.) Wani ɗan’uwa mai suna Christian da yake zama a Faransa ya ce, “A dā ba na ba Jehobah da kuma iyalina isasshen lokaci.” Sai shi da matarsa sun yanke shawarar yin hidimar majagaba. Amma kafin su cim ma wannan maƙasudin, sun bukaci su yi murabus daga aikinsu. Don su samu abin biyan bukata, sun soma aikin shara, kuma sun koyi yadda za su lallaɓa abin da suke da shi. Shin sadaukarwa da suka yi don su iya yin hidimar majagaba ya sa su farin ciki? Christian ya ce: “Muna jin daɗin yin wa’azi yanzu, kuma muna farin cikin ganin yadda ɗalibanmu da kuma waɗanda muke komawa ziyara wurinsu suke koya game da Jehobah.”

17. Mene ne zai iya hana mu gwada sabuwar hanyar yin wa’azi?

17 Kada ka yi jinkirin gwada wasu hanyoyin yin wa’azi. (A. M. 17:16, 17; 20:20, 21) A lokacin annobar koronabairas, wata ’yar’uwa majagaba mai suna Shirley a Amirka, ta yi canje-canje a yadda take wa’azi. Da farko, ta yi jinkirin soma wa’azi ta waya. Amma bayan mai kula da da’ira ya koya musu yadda za su yi hakan, ta soma yin wa’azi ta waya sosai. Ta ce: “Da farko, na ji tsoron yin wa’azi ta waya, amma yanzu ina jin daɗin yin hakan. Muna samun mutane fiye da yadda muke yi a lokacin da muke zuwa gida-gida!”

18. Idan akwai wani abu da ke hana mu cim ma maƙasudinmu, mene ne zai taimaka mana?

18 Ka kafa maƙasudi kuma ka yi ƙoƙari ka cim ma maƙasudin. Idan muka shiga yanayi mai wuya, mukan roƙi Jehobah ya taimaka mana kuma mu yi tunanin yadda za mu magance matsalar. (K. Mag. 3:21) Wata mai suna Sonia da take hidimar majagaba a wani rukunin masu yaren Romany a Turai, ta ce: “Ina rubuta maƙasudaina a kan fallen takarda kuma in ajiye takardar a inda zan riƙa gani. A kan teburin da ke ɗakina, akwai zanen hanyoyi biyu da suka nufa wurare dabam-dabam. Idan ina so in yanke shawara, ina kallon zanen, kuma in yi tunanin wurin da shawarar za ta kai ni.” Sonia ta yi ƙoƙari ta kasance da ra’ayin da ya dace game da matsalolin da take fuskanta. Ta ce: “Nakan yanke shawara ko zan ɗauki yanayin da na shiga a matsayin katangar da za ta hana ni cim ma maƙasudina ko kuma in ɗauke shi a matsayin gada da za ta taimaka mini in cim ma maƙasudin.”

19. Ta yaya za mu nuna godiya don alherin da Jehobah ya yi mana?

19 Jehobah yana mana albarka a hanyoyi da yawa. Za mu iya nuna godiyarmu don albarkun nan ta wajen yin iya ƙoƙarinmu don mu sa a ɗaukaka sunansa. (Ibran. 13:15) Za mu iya yin abubuwa da yawa a hidimarmu ga Jehobah, kuma Jehobah zai yi mana albarka sosai. A kowace rana, mu nemi hanyoyi don mu ‘ɗanɗana mu ga’ cewa ‘Yahweh mai alheri ne.’ Ta haka, za mu zama kamar Yesu wanda ya ce: “Abincina shi ne in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.”​—Yoh. 4:34.

WAƘA TA 80 ‘Mu Ɗanɗana, Mu Gani, Jehobah Nagari Ne’

^ sakin layi na 5 Dukan abubuwa masu kyau sun fito daga wurin Jehobah ne. Yana yi wa kowa alheri, har da mugaye. Amma ya fi yin alheri ga bayinsa masu aminci. A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah yake yi wa bayinsa alheri. Ƙari ga haka, za mu koyi yadda Jehobah yake yi ma waɗanda suke yin ƙwazo a hidimarsa alheri.

^ sakin layi na 7 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 14 A dā, ana wallafa waɗannan jerin talifofin a Hasumiyar Tsaro, amma yanzu ana wallafa su a jw.org. Ka je GAME DA MU > LABARAI > CIM MA MAƘASUDAI NA IBADA.