Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 36

Ku Daraja Matasa a Ikilisiya

Ku Daraja Matasa a Ikilisiya

“Darajar matasa tana cikin ƙarfinsu.”​—K. MAG. 20:29.

WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane maƙasudi ne za mu iya kafa wa kanmu yayin da muke tsufa?

YAYIN da muke tsufa, za mu iya ɗauka cewa ba mu da amfani a ƙungiyar Jehobah kamar yadda muke da amfani a dā. Ko da yake ba mu da ƙarfi kamar dā, za mu iya yin amfani da hikimarmu da iyawarmu mu taimaka wa matasa don su zama da amfani a ƙungiyar Jehobah, kuma su kasance a shirye su yi ƙarin ayyuka. Wani dattijo da ya daɗe yana hidima ya ce: “A duk lokacin da na ga cewa ba zan iya yin ayyukan da na saba yi ba, ina godiya domin akwai matasa da suka cancanci yin waɗannan ayyukan kuma a shirye suke su yi aikin.”

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 A talifin da ya gabata, mun tattauna yadda matasa za su amfana idan suka kusaci tsofaffi. A wannan talifin, za mu tattauna yadda halaye kamar sauƙin kai, da sanin kasawarmu da nuna godiya da kuma bayarwa hannu sake, za su taimaka wa tsofaffi su ba wa matasa haɗin kai. Hakan zai amfani ikilisiya gabaki ɗaya.

KA ZAMA MAI SAUƘIN KAI

3. Mene ne Filibiyawa 2:3, 4 suka ce Kirista mai sauƙin kai zai yi, kuma ta yaya wannan halin zai taimaka masa?

3 Tsofaffi suna bukatar su zama masu sauƙin kai kafin su iya taimaka wa matasa. Mutum mai sauƙin kai yana ɗaukan wasu da muhimmanci fiye da kansa. (Karanta Filibiyawa 2:3, 4.) Tsofaffi da suke da sauƙin kai sun san cewa akwai hanyoyin yin abubuwa da yawa da ba su saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. Don haka, ba za su bukaci kowa ya yi abubuwa kamar yadda suke yi a dā ba. (M. Wa. 7:10) Za su iya taimaka wa matasa ta wajen gaya musu abubuwan da suka koya. Duk da haka, sun san cewa “yanayin duniyar nan yana canjawa.” Don haka suna bukatar su canja yadda suke yin abubuwa bisa ga sabon yanayin.​—1 Kor. 7:31, New World Translation.

Tsofaffi suna koya wa matasa abubuwan da suka koya (Ka duba sakin layi na 4-5) *

4. Ta yaya masu kula da da’ira suke nuna irin halin da Lawiyawa suka nuna?

4 Tsofaffi masu sauƙin kai sun san cewa yayin da suke tsufa, ba za su iya yin abubuwa kamar yadda suke yi a dā ba. Alal misali, ka yi tunanin masu kula da da’ira. Idan suka kai shekara 70, ana ba su damar soma wata hidima dabam. Hakan yana iya yi musu wuya. Sun daɗe suna jin daɗin yi wa ’yan’uwansu hidima kuma suna so su ci gaba da yin hakan. Amma sun fahimci cewa aikin zai fi dacewa da ’yan’uwan da ba su tsufa ba. Ta hakan suna nuna irin halin Lawiyawa a Isra’ila ta dā. A dokar da Jehobah ya ba Isra’ilawa, ya bukaci Lawiyawa su yi hidima a mazauni har sai sun kai shekara 50. Bayan sun daina hidimar, suna farin cikin taimakawa da kowane aiki da aka ba su a mazaunin. Suna yin hakan da ƙwazo kuma suna taimaka wa matasa. (L. Ƙid. 8:25, 26) A yau, idan masu kula da da’ira suka kai shekara 70, suna daina ziyartar ikilisiyoyi, amma suna taimaka da kuma ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiyar da suke.

5. Mene ne ka koya daga misalin Dan da Katie?

5 Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai suna Dan wanda ya yi shekara 23 yana yin hidima a matsayin mai kula da da’ira. A lokacin da Dan ya kai shekara 70, an tura shi da matarsa mai suna Katie yin hidimar majagaba na musamman. Shin suna jin daɗin sabon hidimarsu kuwa? Dan ya ce yanzu yana yin aiki fiye da dā! Yana yin ayyukan da aka ba shi a ikilisiya da ƙwazo, yana taimaka wa matasa su cancanci zama bayi masu hidima, kuma yana koya wa ’yan’uwa a ikilisiya yadda za su riƙa wa’azi a wuraren da akwai jama’a da kuma a kurkuku. Tsofaffi, ko da kuna hidima ta cikakken lokaci ko a’a, akwai abubuwa da yawa da za ku iya yi don ku taimaka wa ’yan’uwa. Me zai taimaka muku ku yi hakan? Ku ƙoƙarta ku saba da sabon aikin da aka ba ku, ku kafa sabbin maƙasudai wa kanku, kuma ku mai da hankali a kan abubuwan da za ku iya yi maimakon waɗanda ba za ku iya yi ba.

KA SAN KASAWARKA

6. Me ya sa ya dace mutum ya san kasawarsa? Ka ba da misali.

6 Mutumin da ya san kasawarsa ba zai so ya yi abin da ya fi ƙarfinsa ba. A sakamakon haka, zai riƙa farin ciki kuma ya ci gaba da yin aiki da ƙwazo. Za mu iya kwatanta mutumin da ya san kasawarsa da direba da yake hawan tudu. Direban zai bukaci ya canja zuwa giyar da za ta taimaka masa ya ci gaba da hawan tudun. Gaskiya ne cewa hakan zai sa motar ta yi tafiya a hankali, amma za ta ci gaba da tafiyar. Haka ma mutumin da ya san kasawarsa, ya san lokacin da ya kamata ya yi canje-canje domin ya iya ci gaba da bauta wa Jehobah kuma ya taimaka wa ’yan’uwansa.​—K. Mag. 11:2.

7. Ta yaya Barzillai ya nuna cewa ya san kasawarsa?

7 Ka yi tunanin misalin Barzillai wanda yake shekara 80 a lokacin da Sarki Dauda ya ce ya zo ya zama mashawarcinsa. Da yake Barzillai ya san kasawarsa, ya ƙi amincewa da hakan. Ya san cewa ba zai iya yin abubuwa da yawa ba domin tsufa. Saboda haka, Barzillai ya gaya wa Sarki Dauda ya ɗauki wani matashi mai suna Kimham a madadinsa. (2 Sam. 19:35-37) Kamar yadda Barzillai ya yi, haka ma tsofaffi a yau suna ba wa matasa damar yin ayyuka.

Sarki Dauda ya amince da shawarar da Allah ya yanke cewa Sulemanu ne zai gina haikali (Ka duba sakin layi na 8)

8. Ta yaya Sarki Dauda ya nuna cewa ya san kasawarsa a batun gina haikali?

8 Sarki Dauda ma ya nuna cewa ya san kasawarsa. Ya so ya gina wa Jehobah haikali da dukan zuciyarsa. Amma Jehobah ya gaya masa cewa Sulemanu, wanda matashi ne, zai gina masa haikalin. Sai Dauda ya amince da shawarar da Jehobah ya yanke kuma ya goyi bayan aikin da dukan zuciyarsa. (1 Tar. 17:4; 22:5) Dauda bai yi tunani cewa shi ne ya kamata ya yi wannan aikin ba, da yake Sulemanu ‘saurayi ne, kuma wayon rayuwa bai ishe shi ba.’ (1 Tar. 29:1) Dauda ya san cewa sai da taimakon Jehobah ne za a iya yin ginin, ba shekaru ko ƙwarewar masu shugabanci ne zai sa a yi hakan ba. Kamar yadda Dauda ya yi, tsofaffi a yau ma suna wa Jehobah hidima da ƙwazo ko da aikin da suke yi ya canja. Kuma sun san cewa Jehobah zai albarkaci matasan da suke yin aikin da suka yi a dā.

9. Ta yaya wani memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu ya nuna cewa ya san kasawarsa?

9 A zamaninmu, wani ɗan’uwa mai suna Shigeo ya nuna cewa ya san kasawarsa. A 1976, sa’ad da yake shekara 30, an naɗa shi memban kwamitin da ke kula da wani ofishinmu. A shekara ta 2004, ya zama mai tsara ayyukan kwamitin da ke kula da ofishin. Da ya tsufa sai ya ga cewa ba shi da ƙarfin yin ayyuka kamar dā. Ya yi addu’a a kan batun kuma ya yi tunanin dalilin da ya sa ya dace ɗan’uwan da bai tsufa ba ya ɗauki matsayinsa. Ko da yake ba shi ne mai tsara ayyukan kwamitin yanzu ba, yana ba da haɗin kai ga sauran ’yan’uwan da suke kwamitin. Kamar yadda muka gani a misalin Barzillai da Sarki Dauda da kuma Shigeo, mutum mai sauƙin kai da ya san kasawarsa, zai mai da hankali ga abubuwan da matasa suka sani maimakon waɗanda ba su sani ba. Zai ɗauke su a matsayin abokan aiki ba abokan gāba ba.​—K. Mag. 20:29.

KA NUNA GODIYA

10. Yaya tsofaffi suke ɗaukan matasa a ikilisiya?

10 Tsofaffi suna ɗaukan matasa a matsayin kyauta daga wurin Jehobah. Yayin da ƙarfinsu yake ƙarewa, tsofaffi suna godiya domin akwai matasa da suke da ƙarfi kuma suke a shirye su yi ayyuka a ikilisiya.

11. Ta yaya Rut 4:13-16 suka nuna yadda tsofaffi za su amfana idan suka amince da taimakon matasa?

11 Naomi, wadda aka rubuta labarinta a Littafi Mai Tsarki, ta kafa misali mai kyau ta wajen yarda wata matashiya ta taimaka mata. Da farko, Naomi ta gaya wa surukuwarta mai suna Rut ta koma wurin mutanenta. Amma da Rut ta nace cewa za ta bi Naomi zuwa Bai’talami, sai Naomi ta yarda Rut ta bi ta. (Rut 1:7, 8, 18) Dukansu biyun sun amfana daga hakan! (Karanta Rut 4:13-16.) Tsofaffi da suke da sauƙin kai za su bi misalin Naomi.

12. Ta yaya manzo Bulus ya nuna godiya?

12 Manzo Bulus ya yi farin ciki domin yadda ’yan’uwa suka taimaka masa. Alal misali, ya gode wa ’yan’uwan da suke Filibi domin kyaututtukan da suka tura masa. (Filib. 4:16) Ya yi godiya don yadda Timoti ya taimaka masa. (Filib. 2:19-22) Kuma ya gode wa Allah domin ’yan’uwan da suka zo su ƙarfafa shi a lokacin da za a kai shi Roma a matsayin ɗan fursuna. (A. M. 28:15) Bulus mutum mai ƙwazo ne da ya yi tafiya mai nisa zuwa wurare da yawa domin ya yi wa’azi kuma ya ƙarfafa ’yan’uwa. Amma ya nuna sauƙin kai kuma ya yarda ’yan’uwa su taimaka masa.

13. Ta yaya tsofaffi za su nuna godiya don matasa?

13 Tsofaffi, za ku iya nuna wa matasa godiya a hanyoyi da yawa. Idan matasa suna so su ɗauke ku zuwa wurin da kuke so ku je, ko su taimaka muku da cefane, ko wasu ayyuka dabam, ku bar su su yi hakan. Ku tuna cewa taimakon da suke ba ku wata hanya ce da Jehobah yake nuna cewa yana ƙaunar ku. Mai yiwuwa ku ga cewa za ku iya zama abokansu. A kowane lokaci, ku yi ƙoƙari ku taimaka wa ’yan’uwa matasa su kusaci Jehobah. Ku gaya musu yadda kuke farin ciki don yadda suke ba da kansu a ikilisiya. Ƙari ga haka, ku shaƙata tare da su kuma ku gaya musu labaranku. Idan kuka yi hakan, za ku nuna cewa kuna “godiya” ga Jehobah domin yadda ya jawo matasan nan zuwa ƙungiyarsa.​—Kol. 3:15; Yoh. 6:44; 1 Tas. 5:18.

KA RIƘA BAYARWA HANNU SAKE

14. Ta yaya Sarki Dauda ya nuna cewa shi mai bayarwa ne?

14 Misalin Sarki Dauda ya nuna mana wani hali mai muhimmanci kuma da tsofaffi suke bukata su kasance da shi, wato halin bayarwa hannu sake. Ya ba da kuɗi mai ɗimbin yawa da kuma wasu abubuwa masu daraja daga dukiyarsa domin a gina haikalin Jehobah. (1 Tar. 22:11-16; 29:3, 4) Ya yi hakan duk da cewa mutane za su kira haikalin da sunan Sulemanu. Idan yanzu ba mu da ƙarfin taimakawa da aikin gine-gine da ake yi a ƙungiyar Jehobah, za mu iya tallafa wa aikin nan ta wajen ba da gudummawa gwargwadon ƙarfinmu. Kuma za mu iya taimaka wa matasa su amfana ta wajen koya musu abubuwan da muka koya a rayuwarmu.

15. Wace kyauta mai daraja ce Bulus ya ba Timoti?

15 Ka yi tunanin yadda manzo Bulus ya nuna cewa shi ma mai bayarwa ne hannu sake. Ya gayyaci Timoti ya bi shi yin wa’azi a ƙasashen waje, kuma Bulus ya koya wa Timoti yadda yake wa’azi da kuma koyarwa. (A. M. 16:1-3) Abubuwan da Bulus ya koya wa Timoti sun taimaka wa Timoti ya ƙware a yin wa’azi da kuma koyarwa. (1 Kor. 4:17) Daga baya, Timoti ma ya koyar da wasu ’yan’uwa.

16. Me ya sa ɗan’uwa Shigeo yake koyar da wasu?

16 ’Yan’uwa tsofaffi a yau ba sa ɗauka cewa koya wa matasa abubuwan da suka sani zai hana su zama da amfani a ikilisiya. Alal misali, ɗan’uwa Shigeo wanda aka ambata ɗazu ya yi shekaru yana koyar da membobin Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu da ba su daɗe da samun matsayin ba. Ya yi hakan domin ya ba da goyon baya ga wa’azin Mulkin Allah a ƙasarsu. A sakamakon haka, a lokacin da ya kasa yin ayyukan da yake yi a dā, wani ɗan’uwa da ya ƙware ya ɗauki matsayinsa. Ɗan’uwa Shigeo ya yi fiye da shekaru 45 yana hidima a matsayin memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu, kuma ya ci gaba da koya wa ’yan’uwa matasa abubuwan da ya sani. ’Yan’uwa kamar Shigeo suna taimaka wa bayin Jehobah sosai!

17. Kamar yadda Luka 6:38 ta nuna, mene ne tsofaffi za su iya ba ’yan’uwa matasa?

17 Ganin ’yan’uwa tsofaffi maza da mata yana tabbatar mana cewa bauta wa Jehobah da aminci ita ce hanyar rayuwa mafi kyau. Ta misalinsu, suna nuna mana cewa yana da kyau mutum ya koyi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ya bi su. Sun san yadda ake yin abubuwa a dā. Duk da haka, sun kasance a shirye su canja yadda suka saba yin abubuwa. Tsofaffi da ba ku daɗe da yin baftisma ba, ku ma za ku iya taimaka wa matasa a hanyoyi da yawa. Alal misali, za ku iya gaya musu yadda sanin Jehobah ya sa ku farin ciki yanzu da kuka yi baftisma. Matasa za su yi farin cikin jin labarinku da kuma darussan da kuka koya. Idan kuka “bayar,” ta wajen koya wa ’yan’uwa matasa abubuwan da kuka sani a rayuwarku, Jehobah zai yi muku albarka sosai.​—Karanta Luka 6:38.

18. Ta yaya tsofaffi da matasa za su taimaka wa juna?

18 ’Yan’uwa tsofaffi, idan kuka kusaci matasa, za ku iya taimaka wa juna. (Rom. 1:12) Kowannenmu yana da wani abu mai amfani da wasu ba su da shi. Tsofaffi suna da hikima kuma sun koyi abubuwa da yawa a rayuwarsu. Matasa kuma suna da kuzari da ƙarfi. Idan matasa da tsofaffi suka zama abokai kuma suka yi aiki tare, za su sa a yabi Ubanmu na sama mai ƙauna, kuma ’yan’uwa a ikilisiya za su amfana.

WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna

^ sakin layi na 5 A ikilisiyoyinmu, akwai matasa maza da mata da yawa da suke yin iya ƙoƙarinsu domin su goyi bayan ƙungiyar Jehobah. Ko daga ina suka fito, tsofaffi a ikilisiya za su iya taimaka wa matasa su yi amfani da ƙarfinsu domin su yi wa Jehobah hidima.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTO: A lokacin da wani mai kula da da’ira ya kai shekara 70, an canja wa shi da matarsa hidimar da suke yi. Sun yi amfani da abubuwa da yawa da suka koya domin su koyar da ’yan’uwa a ikilisiyar da suke yanzu.