Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 43

Kada Ka Gaji!

Kada Ka Gaji!

“Kada mu gaji da yin abin da yake da kyau.”​—GAL. 6:9.

WAƘA TA 68 Mu Taimaki Mutane Su Bauta wa Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa muke farin ciki da kuma alfaharin zama Shaidun Jehobah?

ZAMA Shaidun Jehobah babban gata ne! Muna nuna cewa mu shaidunsa ne ta yi wa mutane wa’azi da koyar da su. Mukan yi farin ciki sa’ad da muka taimaka ma wanda yake “da zuciya ta samun rai na har abada” ya zama Mashaidi. (A. M. 13:​48, New World Translation) Yesu ma ya yi farin ciki “ta wurin ruhu mai tsarki” sa’ad da almajiransa suka gaya masa abin da suka cim ma a wa’azi.​—Luk. 10:​1, 17, 21.

2. Ta yaya za mu nuna cewa muna ɗaukan wa’azin da muke yi da daraja sosai?

2 Yin wa’azi yana da muhimmanci a gare mu. Manzo Bulus ya ce wa Timoti: “Ka lura sosai da kanka da kuma koyarwarka.” Ya kuma ƙara da cewa: “In ka yi haka, za ka ceci kanka da kuma masu jinka.” (1 Tim. 4:16) Don haka, wa’azinmu yana cetan rayuka. Muna lura da kanmu don mu talakawan Mulkin Allah ne. Ya kamata mu riƙa yin abubuwan da suke faranta ran Jehobah, kuma suka jitu da wa’azin da muke yi. (Filib. 1:27) Za mu nuna cewa ‘muna lura sosai da koyarwarmu’ idan muna yin shiri sosai kafin mu je wa’azi, kuma muna roƙon Allah ya taimake mu kafin mu yi wa’azi.

3. Shin kowa ne zai so saƙon Mulki da muke wa’azinsa? Ka ba da misali.

3 Ko da mun yi iya ƙoƙarinmu don mu yi wa’azi, wasu ba za su saurare mu ba. Ka yi la’akari da labarin wani ɗan’uwa mai suna Georg Lindal, wanda ya yi wa’azi a yankuna dabam-dabam na ƙasar Aisilan daga 1929 zuwa 1947. Ya rarraba dubban littattafai, amma ko mutum ɗaya bai zama Mashaidin Jehobah ba. Ya ce: “Wasu a wurin sun yi hamayya da ni, amma yawancinsu sun nuna halin ko-in-kula.” Har bayan da aka tura ’yan’uwa da suka kammala karatu a makarantar Gilead, an yi shekaru tara kafin wasu ’yan ƙasar sun yi baftisma. *

4. Yaya za mu ji idan mutane ba su yarda mu yi nazari da su ba?

4 Ba ma jin daɗi idan mutane sun ƙi mu yi nazari da su. Za mu iya ji kamar manzo Bulus, wanda ya yi ‘baƙin ciki ƙwarai, da kuma damuwa a kullum cikin zuciyarsa’ domin yawancin Yahudawa sun ƙi su amince cewa Yesu ne Almasihu. (Rom. 9:​1-3) A ce kana nazari da wani, kuma ka yi iya ƙoƙarinka don ka koyar da shi. Ƙari ga haka, ka yi addu’a sosai a madadinsa. Amma ba ya aikata abubuwan da yake koya, kuma hakan ya sa ka bukaci ka daina nazarin. Ko kuma a ce ba ka taɓa yin nazari da wani har ya yi baftisma ba. Shin hakan laifinka ne, ko kuma Jehobah bai amince da wa’azin da ka yi ba? A talifin nan, za mu amsa tambayoyi biyu: (1) Me zai nuna cewa muna yin nasara a wa’azinmu? (2) Me ya kamata mu sa rai a kai yayin da muke wa’azi?

ME ZAI NUNA CEWA MUNA YIN NASARA A WA’AZINMU?

5. Me ya sa a wasu lokuta ba ma samun sakamakon da muka zata a wa’azi?

5 Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mutumin da yake yin nufin Allah, ya ce: “A kome kuwa nasara yakan yi.” (Zab. 1:3) Amma hakan ba ya nufin cewa a duk abin da muke yi wa Jehobah, za mu sami sakamako yadda muke so. Rayuwar ’yan Adam cike take da wahala don mu ajizai ne. (Ayu. 14:1) Ƙari ga haka, waɗanda suke hamayya da mu za su iya yin nasarar hana mu yin wa’azi yadda muka saba. (1 Kor. 16:9; 1 Tas. 2:18) Me zai nuna wa Jehobah cewa muna nasara a wa’azinmu? Ga wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka amsa tambayar.

Jehobah yana farin ciki don ƙoƙarin da muke yi mu yi wa’azi gida-gida, ta wasiƙa ko kuma ta waya (Ka duba sakin layi na 6)

6. Mene ne yake nuna wa Jehobah cewa muna nasara a wa’azinmu?

6 Jehobah yana mai da hankali ga ƙoƙarinmu da jimrewarmu. Jehobah yana farin ciki sa’ad da muka yi wa’azi da ƙwazo don muna ƙaunar shi ko da mutane ba su saurare mu ba. Manzo Bulus ya ce: ‘Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba, da ƙaunar da kuka nuna masa sa’ad da kuke taimakon tsarkaka ba, kamar yadda kuke yi har yanzu.’ (Ibran. 6:10) Jehobah yana tunawa da ƙoƙarinmu da ƙaunar da muke nuna masa ko da mutane ba su saurare mu ba. Manzo Bulus ya ce wa ’yan’uwa da ke Korinti: ‘Famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.’ Mu ma za mu iya samun ƙarfafa daga abin da Bulus ya gaya wa ’yan’uwan ko da ba mu sami sakamakon da muka yi zato ba.​—1 Kor. 15:58.

7. Me za mu iya koya daga abin da manzo Bulus ya faɗa game da hidimarsa?

7 Manzo Bulus ya ƙware a yin wa’azi, kuma ya kafa ikilisiyoyi a wurare da yawa. Amma a lokacin da wasu suka ce bai isa ya zama mai hidimar Kristi ba, Bulus bai ƙirga yawan mutanen da ya taimaka musu su soma bauta ma Jehobah ba. Amma da yake ƙaryata masu ƙoƙarin nuna cewa sun fi shi, manzo Bulus ya ce: ‘Na fi su ƙoƙari.’ (2 Kor. 11:23) Kamar manzo Bulus, mu tuna cewa ƙoƙari da jimrewa da muke yi ne ya fi muhimmanci ga Jehobah.

8. Me ya kamata mu tuna game da wa’azin da muke yi?

8 Wa’azinmu yana sa Jehobah farin ciki. Yesu ya aika mabiyansa guda 70 su je su yi wa’azi, kuma sa’ad da suka gama wa’azin, sun “dawo da murna.” Mene ne ya sa su murna? Sun ce: “Har aljanu ma suna jinmu idan mun umarce su cikin sunanka.” Amma Yesu ya yi musu gyara kuma ya ce: “Kada ku yi murna don aljanu sun ji ku, ku yi murna dai domin an rubuta sunayenku a sama.” (Luk. 10:​17-20) Yesu ya san cewa ba a kullum ne za su sami sakamako mai kyau a wa’azi ba. Hakika ba mu san mutane nawa ne suka zama Kiristoci bayan almajiran Yesu sun yi musu wa’azi ba. Ba sakamakon wa’azin da almajiran Yesu suka yi kaɗai ne zai sa su murna ba. Amma abin da ya kamata ya sa su farin ciki shi ne sanin cewa sun yi iya ƙoƙarinsu don su faranta ma Jehobah rai.

9. Wane sakamako ne za mu samu idan muka jimre a yin wa’azi? (Galatiyawa 6:​7-9)

9 Idan muka jimre a yin wa’azi, za mu sami rai na har abada. Idan muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi wa’azi, za mu nuna cewa muna barin ruhu mai tsarki ya yi mana ja-goranci. “Idan ba mu gaji” da yin abin da yake da kyau ba, Jehobah ya yi alkawari cewa zai ba mu rai na har abada ko da ba mu taɓa yin nazari da wani har ya yi baftisma ba.​—Karanta Galatiyawa 6:​7-9.

ME YA KAMATA MU SA RAI A KAI YAYIN DA MUKE WA’AZI?

10. Me ya sa wasu suke jin wa’azinmu, wasu kuma ba sa ji?

10 Abin da yake zuciyar mutane ne zai sa su ji mu ko su ƙi jin mu. Yesu ya bayyana hakan a kwatancinsa na manomin da ya yi shuki a ƙasa dabam-dabam, amma ƙasa guda ɗaya ne kawai ya ba da ’ya’ya. (Luk. 8:​5-8) Yesu ya ce ƙasa dabam-dabam ɗin suna nufin abin da mutane suka yi bayan sun ji “kalmar Allah.” (Luk. 8:​11-15) Kamar manomin, ba za mu iya sa irin da muka shuka ta ba da ’ya’ya a zuciyar mutane ba. Hakkinmu shi ne mu ci gaba da shuka iri na saƙon Mulkin Allah. Kamar yadda manzo Bulus ya faɗa, kowa ‘zai sami ladansa bisa ga aikinsa,’ ba bisa ga sakamakon aikin ba.​—1 Kor. 3:8.

Ko da yake Nuhu ya yi shekaru da yawa yana wa’azi da aminci, babu wanda ya shiga jirgin tare da shi sai dai matarsa da yaransa da kuma matansu. Duk da haka, Nuhu ya yi wa Allah biyayya kuma ya yi aikin da aka ba shi! (Ka duba sakin layi na 11)

11. Me ya sa Jehobah ya yi farin ciki da wa’azin da Nuhu ya yi duk da cewa mutane ba su saurare shi ba? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

11 Bayin Jehobah sun daɗe suna yin wa’azi ga mutanen da ba sa so su saurara. Alal misali, Nuhu ya yi shekaru da yawa yana “wa’azin adalci.” (2 Bit. 2:5) Babu shakka ya ɗauka cewa mutane da yawa za su saurare shi, amma Jehobah bai gaya masa hakan ba. A maimakon hakan, sa’ad da Jehobah yake ba wa Nuhu umurni a kan yadda zai gina jirgi, ya ce masa: “Za ka shiga jirgin, da kai, da matarka, da ’ya’yanka, da matan ’ya’yanka.” (Far. 6:18) Da Jehobah ya gaya wa Nuhu girman jirgin, ƙila Nuhu ya gano cewa mutane da yawa ba za su saurare shi ba domin jirgin ƙarami ne. (Far. 6:15) Kamar yadda muka sani, ko mutum ɗaya bai saurare shi ba. (Far. 7:7) Shin Jehobah ya ce Nuhu bai yi iya ƙoƙarinsa ba ne? A’a. Jehobah ya yi farin ciki da Nuhu ya bi umurninsa.​—Far. 6:22.

12. Me ya taimaki Irmiya ya yi farin ciki a wa’azi duk da cewa mutane ba su kula shi ba, kuma sun yi hamayya da shi?

12 Annabi Irmiya ma ya yi shekaru fiye da 40 yana wa’azi duk da cewa mutane ba su saurare shi ba kuma sun yi hamayya da shi. Ya yi baƙin ciki sosai saboda “ƙasƙanci da ba’a” da aka yi masa. Don haka, ya so ya daina yin wa’azi. (Irm. 20:​8, 9) Amma Irmiya bai fid da rai ba! Me ya taimake shi ya ci gaba da yin farin ciki a hidimarsa? Ya mai da hankali ga abubuwa biyu masu muhimmanci. Na farko, saƙon Irmiya ya ƙunshi “bege mai kyau” na rayuwa a nan gaba. (Irm. 29:​11, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Na biyu, Jehobah ya zaɓi Irmiya ya yi magana a madadinsa. (Irm. 15:16) Mu ma muna yi wa mutane wa’azin saƙo mai daɗi a duniya da ke cike da wahala, kuma muna amsa sunan Jehobah a matsayin Shaidunsa. Idan muka mai da hankali ga abubuwa biyun nan masu muhimmanci, za mu yi farin ciki ko da mutane ba su saurare mu ba.

13. Me muka koya daga kwatancin Yesu da ke littafin Markus 4:​26-29?

13 Yakan ɗauki lokaci kafin mutum ya kasance da bangaskiya. Yesu ya nuna hakan a kwatancin da ya bayar game da wani manomi da ya yi barci. (Karanta Markus 4:​26-29.) Abin da manomin ya shuka ya tsira a hankali kuma manomin bai iya sa irin ya tsira da wuri ba. Mai yiwuwa kai ma za ka bukaci ka jira na dogon lokaci kafin ɗalibinka ya sami ci gaba. Kamar yadda manomin bai iya sa irin ya yi girma da wuri yadda yake so ba, mu ma ba za mu iya tilasta ma ɗalibinmu ya sami ci gaba da wuri kamar yadda muke so ba. Don haka, kada mu yi sanyin gwiwa idan ɗalibanmu ba sa samun ci gaba kamar yadda muka yi tsammani. Kamar manomin, muna bukatar mu yi haƙuri har sai ɗalibinmu ya yanke shawarar bauta ma Jehobah.​—Yak. 5:​7, 8.

14. Wane labari ne ya nuna cewa zai iya ɗaukan lokaci kafin mutane su soma saurarar mu?

14 A wasu wurare, yakan ɗauki lokaci kafin ɗalibi ya yanke shawarar yin baftisma. Ka yi la’akari da labarin Gladys da Ruby Allen waɗanda ’yan’uwan juna ne. A 1959, an tura su yin hidima a matsayin majagaba na kullum a wani gari da ke yankin Quebec na ƙasar Kanada. * Mutanen garin ba su saurari wa’azi ba, domin suna tsoron abin da maƙwabtansu da limamansu za su yi. ’Yar’uwa Gladys ta ce: “Mun yi awa takwas muna wa’azi kowace rana har na tsawon shekaru biyu, ba tare da ko mutum ɗaya ya saurare mu ba! Mutanen sukan buɗe ƙofa, idan sun gan mu, sai su rufe ƙofa su koma ciki. Amma ba mu yi sanyin gwiwa ba.” Daga baya, mutanen sun soma canjawa kuma wasunsu sun soma jin mu. A yanzu, akwai ikilisiyoyi uku a garin.​—Isha. 60:22.

15. Mene ne 1 Korintiyawa 3:​6, 7 suka koya mana game da yin wa’azi?

15 Ba mutum ɗaya ne yake taimaka ma wani ya zama mabiyin Yesu ba. Kowa a ikilisiya zai iya sa hannu wajen taimaka ma ɗalibi ya yi baftisma. (Karanta 1 Korintiyawa 3:​6, 7.) Alal misali, a ce wani ɗan’uwa ya ba ma wani mutum warƙa ko mujalla. Ɗan’uwan ya ga cewa bai da zarafin komawa ya tattauna da mutumin. Sai ya gaya ma wani ɗan’uwa ya ziyarci mutumin don ya tattauna da shi. Ɗan’uwan ya ziyarci mutumin kuma ya soma tattaunawa da shi. ’Yan’uwa dabam-dabam suna bin shi yin nazari da mutumin, kuma sun ƙarfafa mutumin a hanyoyi dabam-dabam. Kowane ɗan’uwa da mutumin ya haɗu da shi ya taimaka masa ya daɗa koya game da Jehobah. Don haka, dukan waɗanda suka taimaka ma ɗalibin za su yi murna sa’ad da ya yi baftisma.​—Yoh. 4:​35-38.

16. Me ya sa za ka iya yin farin ciki a yin wa’azi ko da kana fama da rashin lafiya ko tsufa?

16 Shin ba ka iya yin wa’azi kamar yadda kake yi a dā saboda rashin lafiya ko kuma tsufa? Za ka iya yin farin ciki domin yadda kake ƙoƙari ka yi wa’azi. Ka yi la’akari da misalin Sarki Dauda sa’ad da shi da mutanensa suka ceto iyalansu da kuma dukiyoyinsu daga Amalekawa. Sojojin Dauda ɗari biyu sun gaji kuma sun kasa yin yaƙi. Don haka, sun zauna don su yi gadin kayayyaki. Bayan da suka ci nasara a yaƙin, Dauda ya ce su raba ganimar daidai ga kowa, har da waɗanda ba su je yaƙin ba. (1 Sam. 30:​21-25) Labarin nan ya koya mana darasi mai kyau game da wa’azin da muke yi. Duk wanda ya saka hannu wajen taimaka ma ɗalibi, zai yi farin ciki sa’ad da ɗalibin ya yi baftisma.

17. Me ya sa ya kamata mu gode wa Jehobah?

17 Muna yi wa Jehobah godiya saboda yadda yake amincewa da hidimarmu. Ya san cewa ba za mu iya tilasta wa mutane su saurare mu ko su soma bauta masa ba. Amma yana lura da yadda muke yin iya ƙoƙarinmu da yadda muke ƙaunar sa, kuma yana yi mana albarka. Yana kuma koya mana yadda za mu yi murna don yadda muke wa’azi. (Yoh. 14:12) Muna iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai amince da wa’azinmu idan ba mu gaji ba!

WAƘA TA 67 Mu Yi “Wa’azin Kalmar Allah”

^ sakin layi na 5 Mukan yi farin ciki idan mutane sun yarda mu yi nazari da su, amma ba ma jin daɗi idan ba su yarda ba. Idan ɗalibinka ba ya samun ci gaba kuma fa? Ko idan ba ka taɓa yin nazari da wani har ya yi baftisma ba kuma fa? Hakan yana nufin cewa ba ka yin iya ƙoƙarinka a hidimarka ne? A wannan talifin, za mu ga abin da zai sa mu yi nasara a hidimarmu kuma mu yi farin ciki ko da mutane ba sa saurarar mu.

^ sakin layi na 14 Ka duba labarin Gladys Allen mai jigo, “I Would Not Change a Thing!,” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba 2002, a Turanci.